Ajalul Mu'allak

Daga wikishia

Ajalul Mu’allak (arabic: الأجل المعلق) wani lokaci da ba Ayyananne ba ga mutuwar Mutum da kowanne lokaci da zai iya canjawa, wanda yake kishiyar Ajalul Musamma, (tabbataccen lokacin mutuwar Mutum) a Akidar Allama Tabataba’I hakika Ajalul Mu’allak lokacine na mutuwar Mutum wanda ya dogara da sharuddan Jikin Mutum zai iya yiwuwa sakamakon wasu dalili Mutum ya mutu da wuri ko kuma ya samu jinkirtar mutuwar.

Malaman Tafsiri sun yi bincike karkashin wasu ayoyin Alkur’ani daga jumlarsu akwai wannan gabar ta aya ta 2 Suratul An’am:

«ثُمَّ قَضىَ أَجَلًا وَ أَجَلٌ مُّسَمًّى عِندَهُ»

Sannan ya hukunta Ajali da kuma Ayyanannen Ajali a wurinsa. Kan asasin koyarwar Muslunci, abubuwa misalin Sadaka, Addu'a, Sadar da zumunci, kyawunta Mu’amala da Makota, kauracewa aikata zunubi, Ziyartar Imam Husaini (A.S) wadannan abubuwa da makamantansu suna jinkirta mutuwa, sabanin aikata ayyuka kamar misalin Zina, cutawa Mahaifa, Rantsuwar Karya, yanke alaka da Dangi, wadannan abubuwa suna gaggauta Ajali da mutuwa

Sanin Mafhumi

Asalin Makala: Ajali

A Adabin Harshen Larabci ana kiran zamanin kowanne abu ko kuma karshensa da sunan (Ajali) [1] idan aka yi amfani da Kalmar a kan Mutum to tana bada ma’anar karshen rayuwarsa ma’ana dai lokacin mutuwarsa [2] cikin Alkur’ani Magana ta zo dangane da Nau’uka biyu na Ajali, daya tare da Kaidin (Musamma) daya kuma ba tare da Kaidi ba, Malaman tafsiri suna kiran na biyun da sunayen Gairu Musamma, Khada’u Gairu Mahtum, [3] da kuma Ajalul Mu’allak [4] A Akidar Allama Tabataba’i, Ajalul Musamma, wani tabbataccen lokacin mutuwar Mutum ne wanda ba ya canjawa, kuma Allah kadai ya san wannan lokaci, sabanin Ajalul Mu’allak wanda yake da ma’anar lokacin mutuwar Mutum na Dabi’a wanda akwai yiwuwar ya canja [5] a imanin Malamin Ajalul Mu’allak, lokacin mutuwar Mutum ne amma kan asasin Sharuddan Jikinsa, misali kan asasin Sharuddan Gangar Jikin Mutum zai iya rayuwa shekara 100 ma’ana Ajalul Mu’allak nasa shekara 100 ne, amma zai kuma iya yiwuwa ya mutu kafin lokacin ko kuma ya jinkirta sakamakon wasu dalilai, wannan shi ne Ajalul Musamma nasa. [6]

Ku duba: Ajalul Musamma

Tushen Samuwar Mas’alar Ajalul Mu’allak

An tsunduma cikin bahasi cikin karshen aya ta 2 Suratul An’am dangane da Ajalul Mu’allak da Ajalul Musamma [7] cikin wannan aya Magana kan Ajalai guda biyu ta zo:

«هُوَ الَّذِى خَلَقَكُم مِّن طِينٍ ثُمَّ قَضىَ أَجَلًا وَ أَجَلٌ مُّسَمًّى عِندَهُ»

Shi ne wanda ya halicceku daga Yunbu sannan ya hukunta Ajali da kuma Ayyanannen Ajali a wurinsa. Kan asasin wannan aya, Malaman Tafsiri sun ce: akwai Ajalai guda biyu ga Mutum, Tabbatacce da wanda ba tabbatacce ba [8] na farko shi ne Ajalul Musamma wanda ya zo da wannan suna a cikin ayar, na biyun kuma shi ake kira da Ajalul Mu’allak. [9] Na’am akwai wasu Tafsiran daban dangane da wadannan nau’uka biyu na Ajali [10] misali wasu sun ce: abin nufi daga Ajalul Musamma cikin ayar, shi ne daurar rayuwar Mutum, daga mutuwa zuwa farkon Ranar Alkiyama, sannan kuma abin da ake nufi daga Ajalul Gairu Musamma, Rayuwar Mutum ta cikin Duniya, [11] haka kuma wasu sun c: abin nufi daga Ajalul Musamma karshen rayuwar Mutanen da zuwa yanzu suna raye, sabanin daya Ajalin wanda yake nufin karshen rayuwar wanda suka riga suka mutu [12]

Dalilai Masu Tasiri kan Ajali

Kan asasin ayoyin Alkur’ani da Hadisai, aikata wasu ayyuka yana zama sababin jinkirta Ajalul Mu’allak ko gaggauta shi [13] Sayyid Muhammad Husaini Tabataba’i tare da dogara da aya ta uku da hudu cikin Suratul Nuhu ya rubuta cewa: Bautar Allah, Tak’wa da Da’a ga Annabi, suna jinkirta Mutuwa [14] Shaik Tusi ya nakalto daga Imam Sadiƙ (A.S): (wadanda suke mutuwa sakamakon zunubai da suka aikata sun fi yawa daga masu Mutuwa ta Dabi’a, sannan wadanda suke samun tsawon rayuwa sakamakon kyawawan ayyuka, sun fi yawa daga masu samun tsawon a dabi’ance) [15] Ya zo cikin riwaya cewa abubuwa misalin Sadaka, Sadar da Zumunci, Kyawunta Mu’amala da Makwabta, Nesanta daga Zunubi, Ziyartar Imam Husaini (A.S), Yawaita Godiya ga Allah da Karanta Suratul Tauhid bayan Sallah, suna jinkirta Ajalul Mu’allak, [16] haka zalika aikata wasu ba’arin zunubai misalin Zina, cutawa Mahaifa, Rantsuwar Karya da Yanke dangantaka da Alaka da Dangi suna gaggauta Ajalul Mu’allak. [17]

Bayanin kula

  1. قرشی، قاموس قرآن، ذیل واژه «اجل».
  2. Abu Talebi, “Ajalu”, shafi na 161
  3. Bayat, “Ajalu Musamma wa Ajalu Muallak az Manzare Ayat wa tajalli An dar Riwayat” shafi na 8.
  4. Duba Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 9 da juzu'i na 12, shafi na 30.
  5. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 10.
  6. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 10.
  7. Misali, duba Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu’i na 4, shafi na 423 da 424; Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, Mujalladi na 7, shafi na 8-10.
  8. Duba Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 9;
  9. Duba Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 12, shafi na 30.
  10. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi na 423 da na 424.
  11. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi.423.
  12. Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi 424.
  13. Abu Talebi, “Ajalu”, shafi na 163
  14. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 20, shafi na 28.
  15. Sheikh Tusi, Amali, 1414 AH, shafi na 305.
  16. Abu Talebi, “Ajalu”, shafi na 163.
  17. Abu Talebi, “Ajalu”, shafi na 163 da 164.

Nassoshi

  • Abu Talebi, "Ajalu", Deir al-Maarif of the Holy Qur'an, Qom, Bostan Kitab, 2013.
  • Bayat, Mohammad Hussain, اجل معلق و اجل مسمی از منظر آیات و تجلی آن در روایات»،Siraj Munir, No. 22, 1395.
  • Tabatabaei, Sayyid Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Al-Qur'an, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na al'ummar Seminary Qum, bugu na 5, 1417H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majmall Bayan fi Tafsirul Qur'an, Tehran, Nasser Khosro, bugu na uku, 1372.
  • Tousi, Muhammad bin Hassan, Tashihu: Cibiyar Al-Baath, Al-Mali, Qum, Darul Thaqafa, 1414H.
  • Qureshi, Ali Akbar, Kamus Qoran, Tehran, Dar Al-Kitab Islamia, bugu na 6, 1371.