Ajalul Musamma

Daga wikishia

Ajalul Musamma, (arabic: الأجل المسمى) wani Isdilahi ne na Alkur’ani da yake da ma’anar tabbataccen Ayyanannen lokacin karewar wani abu, Ajalin Musamma kishiya ne ga Ajalul Mu’allak wanda aka ce cikinsa za a iya samu raguwa ko karuwar lokacin karewar wani abu. Ajalul Musamma da ya zo a Alkur’ani yana Magana ne kan karshen rayuwar Mutum, dangane da Ajalul Musammam Malaman tafsiri suna da Mahanga daban-daban, daga cikin jumlar wadanan Mahanga wasu sun ce Ajalul Musamma shi ne tabbataccen lokacin mutuwar Mutum, haka kuma a ra’ayin wasu ba komai bane Ajalul Musamma sai duniyar Lahira.

Sanin Mafhumi

Asalin Makala: Ajali

Ajalul Musamma an ciro shi daga kalmomi biyu, Ajali da Musamma: Ajali yana wata Daura ta zamani ko kuma karshen wannan daurar wani abu [1] Musamma kuma yana nufi Ayyananne. [2] Wani lokaci Kalmar Ajali a cikin Alkur’ani tana zuwa tare da kaidi da Kalmar Musamma wacce Malaman Tafsiri suke kiran wannan Ajali da sunan Ajalul Musamma, wani lokacin kuma Kalmar tana zuwa ba tare da kaidin Musamma ba, daga ba’arin wuraren da ta zo babu Kaidin Musamma akwai aya ta 2 Suratul An’am wanda ake kiransa da sunaye kamar Ajalul Gairu Mahtum, ko kuma Khada’u gairu Mahtum ko Ajalul Mu’allak [3]

Tafsirai Mabambanta

Ajalul Musamma Isdilahi ne daga Alkur’ani ya zo a wurare har guda 21 cikin fagage daban-daban [4] alal misali aya ta 282 Suratul Bakara kan batun Bashi, Kalmar ta zo da ma’anar Ayyananne lokaci, haka zalika Kalmar Ajalul Musamma ta zo cikin Aya ta 2 Suratul An’am kan mutum :

‌«هُوَ الَّذِى خَلَقَكُم مِّن طِينٍ ثُمَّ قَضىَ أَجَلًا وَ أَجَلٌ مُّسَمًّى عِندَهُ»

[5]

Shi ne wanda ya halicce ku daga Yunbu sannan ya hukunta wani Ajali da kuma Ayyananne Ajali a wurinsa. Dangane da Ajalul Musamma cikin wadannan ayoyi akwai mabambanta ra’ayoyi da mahangar Malaman tafsiri [6]

  • wasu Jama’a suna cewa manufa daga Ajalul Musamma wata Daurar zamani ce ta rayuwar Mutum, daga lokacin mutuwa zuwa tashin Alkiyama, kishiyar daurar rayuwar Mutum a duniya wanda ya kasance Ajalul Gairu Musamma. [7]
  • wasu kuma suna ganin AJalul Musamma ba komai bane sai ِ Duniyar Lahira. [8]
  • Mahnagar wasu kuma shi ne, Karshen rayuwar Mutum da zuwa yanzu yake raye, kishiyar karshen rayuwar wadanda suka riga suka mutu. [9]
  • wasu ba’ari kuma sun yi Imani da cewa ma’anar Ajalul Musamma , shi ne Mutuwa. [10]
  • Allama Tabataba’i, yana ganin Ma’anar Ajalul Musamma da Ajalul Gairu Musamma (Mu’allak) duka biyu suna da ma’ana karshen Rayuwar Mutum; tare da bambanci dan kadan domin shi Ajalul Musamma wani lokaci ne da tabbas cikinsa Mutum yake mutuwa, kuma babu wanda ya san wannan lokaci sai Allah shi kadai,amma Ajalul Mu’allak lokacin mutuwar kowanne mutum ya dogara ne kan asasin sharuddan gangar jikinsa wanda zai iya yiwuwa bisa la’akari da dalilai na waje lokacin mutuwar tasa ya karu ko ya ragu [11]

Bambanci Ajalul Musamma Tsakanin Ajalul Mu’allaƙ

Ku duba:Ajalul Mu'allak

A Akidar Allama Tabataba’i, bambancin da yake tsakanin Ajalul Mu’allak da Ajalul Musamma, shi ne cewa a cikin Ajalul Musamma ba a samun Bada’u (canji da sauyi) lokacin nan dai da aka rubuta mutum zai mutu to cikinsa zai mutu babu ragi babu kari, amma a cikin Ajalul Mu’allak ana samun Bada’u, a cikin wani bayani shi ne cewa cikin Ajalul Musamma, Addu’a da Sadaka da dukkanin wani aiki da yake da tasiri cikin sauya lokacin mutuwa a cikin Ajalul Mu’allak to samsam baya tasiri cikin Ajalul Musamma [12] haka kuma kan asasin ayoyin Alkur’ani musammam ma aya ta 2 Suratul An’am da ta bayyana cewa Ajalul Musamma yana wurin Allah, an fitar da Natija cewa babu wanda ya san Ajalul Musamma sai Allah Ta’ala shi kadai. [13]

Bayanin kula

  1. قرشی، قاموس قرآن، ذیل واژه «اجل».
  2. قرشی، قاموس قرآن، ذیل واژه «اسم».
  3. Bayat, “Ajalul Mu'allak wa Ajalul Musamma Az Manzare ayat wa tajalli An dar Riwayat ” shafi na 8.
  4. ƙaraati, Tafsir Noor, 2013, juzu'i na 2, shafi.410
  5. Makarem, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 2, shafi.383.
  6. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi na 423 da na 424.
  7. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi.423
  8. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi.424.
  9. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi.424.
  10. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi.424.
  11. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 9 da na 10.
  12. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 9.
  13. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 7, shafi na 8.

Nassoshi

  • Bayat Muhammad Husaini «اجل معلق و اجل مسمی از منظر آیات و تجلی آن در روایات»،Siraj Munir, No. 22, 1395.
  • Tabatabaei, Sayyid Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Al-Qur'an, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na kungiyar Seminary Society, bugu na biyar, 1417H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majmall Bayan fi Tafsirin Qur'an, Tehran, Nasser Khosro, bugu na uku, 1372.
  • Qaraati, Mohsen, Tafsir Noor, Tehran, Cibiyar Al'adu ta Darussan Kur'ani, 2003.
  • Qureshi Banabi, Ali Akbar, Kamus Quran, Tehran, Laburaren Musulunci, bugu na 6, 1371.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1374.