Shu'aibu Bin Salih
Shu'aibu Bin Salih mutum ne daga ƙabilar Banu Tamim wanda, bisa ga wasu ruwayoyi, zai yi miƙe kafin bayyanar Imam Mahadi (A.S). Wannan miƙe nasa ana ɗaukarsa ɗaya daga cikin alamomin bayyanar da ba su tabbata ba (Alamat gairi mahtuma).
A cewar ruwayoyin, Shu'aibu Bin Salih zai fito da runduna mai mutum dubu huɗu (4,000), masu baƙaƙen tutoci da fararen tufafi, sannan zai yaƙi Sufyani, ya kuma yi nasara a kansa. Wasu ruwayoyi sun bayyana cewa tsakanin fitowarsa da bayyanar Imam Mahadi (A.S) akwai tazarar watanni 72.
A ra'ayin Najmud-Din Ɗabasi, wani masani kan mazhabobin Musulunci, ruwayoyin da suka shafi Shu'aibu Bin Salih da fitowarsa suna da yawa har za a iya ɗaukarsu a matsayin mutawatir ma'anawi, ko aƙalla mustafiz. Sai dai ruwayoyin da suka yi bayani game da siffofinsa da yadda fitowarsa za ta kasance ba su da cikakkiyar inganci. A cewarsa, ruwaya guda ɗaya ce kawai daga Imam Rida (A.S) da ta inganta, wadda ta nuna cewa fitowar Shu'aibu Bin Salih tana daga cikin alamomin bayyanar da ba su tabbata ba.
A bayan Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, an yi ƙoƙarin danganta mutane da dama da Shu'aibu Bin Salih. Daga cikinsu akwai Hashimi Rafsanjani, wasu mayaƙan yaƙin Iran da Iraƙi, da kuma tsohon shugaban ƙasar Iran Mahmud Ahmadi Nejad, inda wasu suka yi zaton shi ne ko kuma yana kama da Shu'aibu Bin Salih.
Sai dai Ayatullahi Sayyid Ali Sistani ya yi gargaɗi cewa irin waɗannan daidaita mutane da alamomin bayyanar Imam Mahadi ba tare da hujja ba yana iya raunana imanin al'umma da kuma jefa mutane cikin ruɗani.
Siffofi Da Yadda Miƙewar Shu'aibu Bin Salih Zai Kasance
A cikin ruwayoyin da suka shafi bayyanar Imam Mahadi (A.S), an ambaci Shu'aibu Bin Salih, kuma wasu daga cikin waɗannan ruwayoyi sun bayyana fitowarsa a matsayin ɗaya daga cikin alamomin bayyanar Imam Mahadi.[1] Wasu ruwayoyin suna bayanin siffofinsa na mutum, yadda zai miƙe kafin bayyanar Imam Mahdi, da kuma matsayin da zai samu a lokacin bayyanar Imam. Ga bayanan kamar haka:
*Siffofinsa na kankin kai Ruwayoyi sun bayyana Shu'aibu Bin Salih da cewa: matashi ne;[2] mai launin fuska mai ɗan rawaya;[3] mai launin fata mai kama da alkama;[4]matsakaicin tsayi;[5] mai ƙaramin gemu;[6] daga ƙabilar Banu Tamim[7] ko kuma bawan wani daga Banu Tamim.[8]
- Yadda miƙewar tasa za ta kasance
Ruwayoyi sun bayyana cewa Shu'aibu Bin Salih shi ne kwamandan rundunar miƙewar wani Khurasani daga Banu Hashim, ko kuma bawan wani daga Banu Tamim.[9] kuma ƙarƙashin jagorancinsa ne za a fara wannan tawaye daga yankin Khurasan. ko kuma bawan wani daga Banu Tamim.[10] Game da wurin fitowarsa kuwa, wasu ruwayoyi sun ce zai fito daga Samarƙand,[11] wasu kuma daga Rayyu,[12] yayin da wasu suka ce daga Ɗaliƙan.[13]
A cikin ruwayoyi an ce rundunarsa za ta ƙunshi mayaƙa dubu huɗu (4,000),[14] masu ɗauke da baƙaƙen tutoci,[15] masu ɗaure baƙaƙen ɗamara,[16] kuma masu sanye da fararen tufafi.[17] Za su fafata da Sufyani a yankin Istakhr,[18] inda za su yi yaƙi da rundunarsa,[19] su kuma yi nasara a kanta. Bayan haka za su isa Baitul Maƙdis (Urushalima).[20] Haka kuma an ce duk wanda Shu'aibu Bin Salih ya yaƙa, yana samun nasara a kansa.[21]
Wasu ruwayoyi sun nuna cewa fitowarsa za ta kasance bayan fitowar Aufu Salami, amma kafin fitowar Sufyani.[22] Haka kuma an ce tsakanin fitowarsa da bayyanar Imam Mahadi akwai watanni 72.[23]
- Rawar da zai taka lokacin bayyanar Imam Mahdi
Ruwayoyi sun bayyana cewa bayan rundunar Shu'aibu Bin Salih ta yi nasara a kan rundunar Sufyani, mutane 300 daga yankin Sham (Siriya) za su haɗu da shi. Daga nan zai sauka a Baitul Maƙdis, inda zai fara shirya al'amura domin bayyanar Imam Mahadi.[24] Bayan watanni 72 da fitowarsa, Imam Mahadi (A.S) zai bayyana. Shu'aibu Bin Salih zai yi wa Imam mubaya'a, kuma a wasu ruwayoyi an bayyana shi a matsayin mai ɗauke da tutar rundunar Imam na goma sha biyu.[25]
Binciken Ruwayoyin da suka shafi Shu'aibu Bin Salih
Najmud-Din Ɗabasi, wani masani kan mazhabobin Musulunci, bayan ya yi nazari a kan ruwayoyin da suka shafi Shu'aibu Bin Salih, ya bayyana cewa ruwayoyin da suka tabbatar da wanzuwar Shu'aibu Bin Salih da fitowarsa sun kai matsayin mutawatir ma'anawi, ko kuma aƙalla sun kai matsayin mustafiz. Amma ruwayoyin da suka yi bayani game da siffofinsa da yadda tawayensa zai kasance ba su kai wannan matsayi ba.[26]
A ra'ayinsa, daga cikin ruwayoyin da suka yi bayanin siffofin Shu'aibu Bin Salih, ruwayar Imam Rida (A.S) ce kaɗai take da ingantacciyar isnadi.[27]
Abin da wannan ruwaya ta Imam Rida (A.S) take tabbatarwa kawai shi ne cewa fitowar Shu'aibu Bin Salih tana daga cikin alamomin bayyanar Imam Mahadi waɗanda ba su da tabbacin faruwa (alamomin ghayr mahtum), kuma hakan zai faru kafin bayyanar Imam Mahdi.
Najmuddin Tabasi ya kuma yi nuni da cewa isnadin sauran ruwayoyin da suka yi bayani game da Shu'aibu Bin Salih yana da matsaloli.[28] Haka kuma ya ce, duk da cewa akwai kusan ruwayoyi 300 a cikin Kutub al-Arba'a da suka shafi Mahdaawiyya, babu wata ruwaya da ta ambaci Shu'aibu Bin Salih.[29]
Dangantakarsa Da Annabi Shu'aibu (A.S)
Shaik Saduƙ a cikin littafinsa An-Nubuwwa ya kawo wata ruwaya wadda ta nuna cewa wani mutum mai suna Shu'aibu Bin Salih yana ɗaya daga cikin manzannin da Annabi Shu'aibu (A.S) ya aika zuwa ga mutanensa, amma mutanen suka kashe shi.[30] Bisa wannan ruwaya, Ƙuɗbu Rawandi ya yi ra'ayin cewa Shu'aibu Bin Salih wanda zai miƙe a lokacin bayyanar Imam Mahadi (A.S) shi ne wannan mutum ɗaya da mutanensa suka kashe, sannan daga baya zai dawo duniya ta hanyar raj'a (komawa duniya).[31]
Sai dai Shaik Muhammad Sanad, ɗaya daga cikin malaman zamani, ya ƙi amincewa da wannan fahimta ta Rawandi. A cewarsa, Shu'aibu Bin Salih da aka ambata a ruwayar Sheik Saduƙ mai yiwuwa shi ne Annabi Shu'aibu (A.S) kansa, wanda zai dawo duniya tare da Khidir da Iliyas a lokacin raj'a, kuma ba shi ne Shu'aibu Bin Salih, kwamandan rundunar Khurasan, da aka ambata a ruwayoyin bayyanar Imam Mahadi ba.[32]
Mutanen Da Aka Taɓa Dangantawa Da Shu'aibu Bin Salih
A cikin wani faifan CD mai taken "Zuhur Besyar Nazdik Ast" (Bayyanar ta yi matuƙar kusa), wanda ya yaɗu sosai a Iran a shekarar 1389Sh/ 2010M, an yi iƙirarin cewa akwai kamanceceniya mai yawa tsakanin Mahmud Ahmadi Nejad, shugaban ƙasar Iran na lokacin, da Shu'aibu Bin Salih.[33] Ayatullah Sayyid Ali Sistani, ɗaya daga cikin manyan maraji'an taƙlidi na Shi'a, ya mayar da martani ga irin waɗannan daidaitawa, yana mai cewa suna raunana aƙidun al'umma.[34] Bisa wasu rahotanni, tun kafin wannan lokaci ma, an taɓa danganta Akbar Hashimi Rafsanjani da kuma wasu daga cikin manyan kwamandojin yaƙin Iran da Iraƙi da Shu'aibu Bin Salih.[35]
Batutuwa Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ An-Nu’mani, Al-Ghayba, bab na 14, shafi na 262, hadisi na 12.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 53.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 54.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 54.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 54.
- ↑ Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 189; Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 54.
- ↑ Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 189.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 53.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 53.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 52.
- ↑ Shaik Ɗusi, Al-Ghayba, shafi na 444; Rawandi, Al-Khara’ij wal-Jara’ih, juzu’i na 3, shafi na 1155, hadisi na 61; Mu’jam Ahadith al-Imam al-Mahdi, juzu’i na 4, shafi na 495.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 53.
- ↑ Shaik Ɗusi, Al-Ghayba, shafi na 444; Rawandi, Al-Khara’ij wal-Jara’ih, juzu’i na 3, shafi na 1155, hadisi na 61; Mu’jam Ahadith al-Imam al-Mahdi, juzu’i na 4, shafi na 495.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 53.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 52; Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 188.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 52; Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 188.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 52.
- ↑ Mu’jam Ahadith al-Imam al-Mahdi, juzu’i na 4, shafi na 105.
- ↑ Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 192.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 52; Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 188; Al-Maqdisi ash-Shafi’i, Iqd ad-Durar, shafi na 195, hadisi na 199.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 54.
- ↑ Shaik Ɗusi, Al-Ghayba, shafi na 444.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 52; Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 188.
- ↑ Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 52; Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 213.
- ↑ Shaik Ɗusi, Al-Ghayba, shafi na 463–464; Mu’jam Ahadith al-Imam al-Mahdi, juzu’i na 2, shafi na 105; Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 53 da 127; Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 192; Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan, Manshurat ar-Radhi, shafi na 44. Haka kuma a duba: Al-Muttaqi al-Hindi, Kanz al-Ummal, juzu’i na 14, shafi na 588, hadisi na 39667 da 39666; Ibn Hammad Marwazi, Al-Fitan, Dar al-Fikr, shafi na 188.
- ↑ «درس خارج مهدویت- بحث شعیب بن صالح – سال ۹۰».
- ↑ أَخْبَرَنَا مُحَمَّدُ بْنُ هَمَّامٍ قَالَ حَدَّثَنِي جَعْفَرُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ مَالِكٍ قَالَ حَدَّثَنِي عَلِيُّ بْنُ عَاصِمٍ عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ أَبِي نَصْرٍ عَنْ أَبِي الْحَسَنِ الرِّضَا(ع) أَنَّهُ قَالَ قَبْلَ هَذَا الْأَمْرِ السُّفْيَانِيُّ وَ الْيَمَانِيُّ وَ الْمَرْوَانِيُّ وَ شُعَيْبُ بْنُ صَالِحٍ فَكَيْفَ يَقُولُ هَذَا هَذَا (An-Nu’mani, Al-Ghayba, bab na 14, shafi na 262, hadisi na 12.).
- ↑ «درس خارج مهدویت- بحث شعیب بن صالح – سال ۹۰».
- ↑ «درس خارج مهدویت- بحث شعیب بن صالح – سال ۹۰».
- ↑ Sheikh Saduƙ, An-Nubuwwa, shafi na 139.
- ↑ Rawandi, Al-Khara’ij wal-Jara’ih, juzu’i na 2, shafi na 552; juzu’i na 3, shafi na 1167.
- ↑ Rawandi, Al-Khara’ij wal-Jara’ih, juzu’i na 2, shafi na 552; juzu’i na 3, shafi na 1167.
- ↑ «ادعای تشابه شعیب بن صالح و جناب رئیس جمهوری!».
- ↑ «انتقاد آیت الله سیستانی از "ظهور نزدیک است"».
- ↑ «حامیان مستند انحرافی ظهور، به دنبال مقاصد سیاسی هستند».
Nassoshi
- Maƙdisi ash-Shafi’i, Yusuf bin Yahya, Iƙd ad-Durar fi Akhbar al-Muntazar, Maktabat al-Manar, Zarqa, 1410.
- Muttaƙi Hindi, Alauddin Ali, Kanz al-Ummal fi Sunan al-Aƙwal wal-Af’al", gyara: Safwat as-Saƙƙa, Beirut, Cibiyar ar-Risala, 1401H..
- Nu’mani, Muhammad bin Ibrahim, Al-Ghayba, bincike: Faris Hasan Karim, Qum, Madin, 1426H.
- Ibn Hammad Marwazi, Nu’aim, Al-Fitan, bincike: Suhail Zakkar, Beirut, Dar al-Fikr, babu shekara.
- Ibn Tawuus, Al-Malahim wal-Fitan fi Zuhur al-Gha’ib al-Muntazar, Qum, Mawallafar t ar-Radhi, babu shekara.
- Mu’jam Ahadith al-Imam al-Mahdi (AJ), ƙarƙashin kulawar Ali Kaurani, Qum, Cibiyar Ma’arif Islamiyya, 1411H.
- Rawandi, Ibn Hibbatullah, Al-Khara’ij wal-Jara’ih, Qum, Cibiyar Imam Mahdi, 1409H.
- Sanad, Muhammad, Fiƙh Ala'imuz Zuhur, Najaf, Cibiyar Nazari ta Musamman kan Imam Mahdi, 1425H.
- Shaik Saduk, Muhammad bin Ali, An-Nubuwwa, Tehran, Hukumar Buga Littattafai da Yaɗa Ayyuka ta Ma’aikatar Al’adu da Shirye-shiryen Musulunci, 1381Sh.
- Shaik Ɗusi, Al-Ghayba, bincike: Abdullah Tehrani da Ahmad Nasih, Qum, Cibiyar Ma’arif Ilahiyya, 1990M.
- ادعاي تشابه شعيب ابن صالح و جناب رئيس جمهوري!، (Iƙirarin kamanceceniya tsakanin Shu’aib bin Salih da shugaban ƙasa.),Shafin Aftab News, ranar wallafa labarin: 16 ga Agusta 2010M, ranar duba shafin: 19 ga Agusta 2018M.
- حامیان مستند انحرافی ظهور، به دنبال مقاصد سیاسی هستند،(Masu goyon bayan shirin fim ɗin da ake zargi da karkata game da bayyanar Imam Mahdi, suna neman manufofin siyasa.),Shafin Khaneh-ye Mellat, ranar wallafa labarin: 11 ga Afrilu 2011M, ranar duba shafin: 19 ga Agusta 2018M.
- انتقاد آیت الله سیستانی از "ظهور نزدیک است"،(Suka da Ayatullah Sistani ga Bayyanar ta yi kusa.), Shafin Tabnak, ranar wallafa labarin: 4 ga Afrilu 2011M, ranar duba shafin: 19 ga Agusta 2018M.
- «درس خارج مهدویت- بحث شعیب بن صالح – سال ۹۰».(Darasin Wajen Koyarwar Mahdawiyya Tattaunawa kan Shu’aib bin Salih Shekara ta 90), shafin Ayatullah Najmud-Din Ɗabasi, ranar wallafa: 3 ga Fabrairu 2013M, ranar duba shafin: 19 ga Agusta 2018M.