Sanya Baƙaƙen Kaya

Daga wikishia

Sanya baqaqin kaya, (Larabci: لبس السواد) ana nufin sanya baqaqin kaya da kuma lulluve gurare da tsinma kalar baqi, wannan alamace ta zaman makoki da baqinciki, wannan al’ada tayaxu a gun ‘yan shi’a tin farkon musulinci, kuma akwai misalai dayawa daga hadisai na imamai da suke qarfafa sa baqaqin kaya. Haqi malamai dayawa na fiqihu sunyi fatawa ta mustahabbi kan sa baqaqin kaya domin zaman makoki ga manyan mutane a cikin addini, kuma sukace hakan yana cikin abubuwan da ake girmama abin da Allah yakeso, kuma sukace ruwayoyin da sukace sa baqaqin kaya Makaruhi ne basu da alaqa da zaman makoki. Akwai litattafai na malaman fiqihu a shi’a, kamar na Sayyid Ja’afar Axxabaxaba’i Al’ha’iri da Sayyid Hasan Sadar da Al’mirza Attabri, duk litattafai ne masu zaman kansu kan bayanin mustahabbancin sa kaya baqaqe,saboda zaman makokin manyan mutane a addini. Sa baqaqin kaya ana ganin al’adace ta Abbasawa, amma wasu malaman tarihi suna ganin cewa su Abbasawa suna sanya baqaqin kaya ne saboda suna nuna alamar xaukan fansa daga waxanda suka kashe iyalan gidan manzo amincin Allah ya tabbata a garesu a lokacin Umayyawa, kazalika domin su tattaro da haxa kan ‘yan sh’a, wasu kuma suna ganin hana sa baqaqin kaya da imamai sukayi da yazo a wasu hadisai,ya faro ne sakamakon da kada suyi kama da Abbasawa.

Kalar kaya baqi alamace ta zaman makoki da shariftaka

Sanya baqaken kaya a al’adar mutane alama ce ta zaman makoki da baqinciki, saboda hakane ‘yan shi’a da masoya iyalan gidan manzo amicin Allah ya tabbata a garesu suke sawa,kuma suke sawa a qofofi da bango a ranakon saman makokin manya mutane a addini, musamman a wajan zaman makoki na imamu Husaini amicin Allah ya tabbata a gareshi.[1] yazo a cikin ruwaya daga imamu Sadiq cewa ya rinjayarwa da mata su sanya baqaqin kaya a lokacin da suke Idda ga macen da mujinta ya rasu, saboda baqin cikin mutuwar mujinta [2] kuma ance Idil Gadir shi ne ranar cire baqaqin kaya, [3] kuma zamu iya amfani da maganar imamai kan cewa xabi’ar baqar kala tana nuni kan baqin ciki ne. [4] Daga cikin kusosiyya ta fararan kaya, a kwai cika ido da sharfta da kuma xaukaka.Bisa ra’ayin Abil Hasani saboda wannan sifa ta baqaqin kaya Annabi da iyalan gidanshi tsira da amincin Allah ya tabbata a garesu suka sa baqin rawani a wani yanayi na masamman, kamar Algadir, kazalika rawanin Sharifai shima baqi ne koyi da manzo da iyalan gidanshi. [5]

Al’adar sa baqqin kaya domin zaman makoki

Bisa abin da ya zo a littafin Muhsin Hassam Muzahiri kan abin da ya shafi al’adar zaman makoki na ‘yan shi’a, su masu zaman makoki suna sa baqaqin kaya ne a ranakon zaman makoki, kuma kazalika suna sanya baqin gyalle wanda suke xauke da wasu kammomi na baqin ciki da kamomi na addini da sunayan imamai da shahidan Karbala a jikin qofofi da bango. [6]

Mustahabbancin sa baqaqin kaya zaman makoki da baqin cikin manyan mutane a addini

Sanya baqaqin kaya domin zaman makokin manya mutane a addini mustahabi ne a shari’a a mazahabin shi’a, malaman fiqihu dayawa sunyi fatawa kan hakan, kuma suna ganishi yana daga cikin girmama aiyukan Allah. [7] wasu daga cikin malaman taqlidi sunyi fatawa cewa mustahabi ne sanya baqaqin kaya a yayin zaman makoki na Ahlubati aminci ya tabbata a garesu, kamar Sayyid Ali Kamna’i da Sayyid Ali Assistani da Nasir Makarim Shirazi da Luxufullahi Assafi Al’gulfaigani da Husaini Wahid Al’kurasani. [8] amma ta fuskacin aiki malamai dayawa suna sanya baqaqin kaya a ranakon zaman makoki. [9] kamar yadda Al’mar’ashi Annajifi ya yi wasiya cewa idan ya mutu, a binneshi tare da baqaqin kayan da yake sawa a lokacin zaman makoki na wata Muharma da Safar. [10] Sai dai cewa akwai ruwayoyi da yawa da suke cewa sa kaya baqaqe makaruhi ne,[11] saboda waxanna ruwayoyin wasu daga cikin malaman fiqihu suka tafi kan cewa sanya baqaqen kaya a sallah ko kuma koda yaushe makaruhi ne, [12] sai dai cewa koda waxannan ruwayoyi na makaruhi sun inganta, to akwai wasu ruwayoyin da suke bayyana aiki da maganar iyalan gidan manzo amincin Allah ya tabbata a garesu gaba xaya, kuma hakan yana nuna halascin sa baqaqen kaya a lokacin zaman makoki,saboda haka sanya baqaqen kaya saboda girmama abin da Allah yakeso ya fita daga cikin wannan makaruhin. [13]

Litattafan malaman fiqihu kan sa baqaqen kaya

Haqiqa malamai Mujtahidai na fiqihu a shi’a sun rubuta litattafai kan bayanin mustahabbancin sa baqaqen kaya domin nuna baqin ciki kan manya mutane a addini;

  • Akwai littafin Irshadul Ibad Ila Istihibabi Lubusis Sawad wanda Sayyid Ja’afar Axxabaxaba’i Al’ha’iri ya rubuta ya rasu a shekara ta 1321 hajira, xaya daga cikin mawallafin littafin Arriyad. [14]
  • Aga Buzurn Axxahirani ya ambaci littafi mai suna Tabyinur Rashad Fi Lubusis Sawad Alal A’immatil Amjad wanda Assayyid Hasan Sadar ya rubuta, ya rasu a shekara ta 1354 hajira, ya rubutashi ne da harshan Farisanci.[15]
  • Risala Muktasira Fi lubusis Sawad, littafi ne na karatun Al’mirza Jawad Attabrizi kan hukunce-hukuncan sanya baqaqen kaya, [16]a cikin wannan littafi ya yi bayani kan mustahabbancin sa baqaqin kaya a lokacin zaman makokin Ahlul Baiti amincin Allah ya tabbata a garesu, kuma ya amsa tambayoyi da yawa da akeyi kan sa baqaqen kaya. [17]

Tarihin sanya baqaqen kaya

Sanya baqaqen kaya, alamace ta baqin cikin a qasashe da yawa da al’adu da yawa, misali kamar agurin Farisawa da Rumawa da Rashawa da Jamanawa.[18] kuma akwai misalai ta yawa, kan cewa sanya baqaqen kaya yana alamar baqin ciki a gurin Larabawa. [19] kamar yadda aka ce a qasar Iraqi da wasu yankuna da yawa, sanya baqaqen kaya, alama ce ta baqin ciki tin qarni na farko na hijira. [20]

Tarihin Annabi da Imamai

Akwai ruwaoyi da yawa kan abin da yashafi sanya baqaqen kaya,ba tare da la’akarin inganci ko rashin shi ba ga kowace ruwaya ita kaxai, waxannan ruwayoyin suna nuni kan cewa annabi da iyalan gidanshi sun kasance suna sanya baqaqen kaya, idan makusantansu suka rasu domin nuna baqin cik, haka kuma abu ne da ya yaxu a tsakaninsu da mabiyansu.[21] Misali, tabbas Zainab ‘yar Umma Salma tasanya baqaqen kaya har zuwa kwana uku sanda Hamza xan Abdulmuxxali ya rasu, har sai da annabi ya tayata juyayi, [22] kamar yadda annabi da kanshi ya umarci Binta ‘yar Umas da ta sanya baqaqen kaya zuwa kwana uku saboda nuna baqin ciki kan mutuwar mijinta Ja’afar xan Abi Xalib, [23] kuma yazo a cikin sharhin Nahjul Balaga na Ibni abil Hadid, cewa imamu Hasan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi yaje kaban mutane yana sanye da baqaqen kaya bayan shahadar imamu Ali A S. [24] kamar yadda shiek Saduq ya faxa a cikin littafin Uyunu Akbarir Rida cewa, ‘yan shi’a da suakyi jana’izar imamu Kazim sun kasance suna sanyi da baqaqen kaya ne. [25] Bisa abin da Allama Al’majalisi ya naqalto a cikin littafin Biharil Anuwar cewa, bayan sauran iyalan gidan manzo waxanda sukayi saura a Karbala sun fara tafiya da umarni Yazidu, sai dukkan matan Hashimawa suka sanya baqaqen kaya na tsawan kwana bakwai domin nuna baqin cikin kan imamu Husaini A S. [26] Kuma Kulaini ya rawaito a cikin littafin Kafi cewa, imamu Sajjad A S ya kasance yana sa baqaqen kaya. [27] a cikin ruwayatul Gai a littafin Mahasin na Barqi, cewa bayan shahadar imamu Husaini A S, matan Bani Hashim sun sanya baqaqen kaya, idan imamu Ali xan imamu Husain ya kasance yana yimusu abinci. [28] kuma wannan ruwayar itace mafi qarfin dalili da ma’ana kan abin da ya shafi sanya baqaqen kaya. [29]

Al’ada ce da ta yaxu a tsakanin ‘yan shi’a a lokacin fakowar [Gaiba] imamul Mahadi A S

Bisa abin da yazo na tarihi,cewa ita al’adar sa kaya baqaqe ta kasance ta yaxu a tsakanin ‘yan shi’a bayan imamai a lokacin fakowa mai tsayi ta imamu Mahadi A S, a lokacin Bawaihiyin ne ake al’adar zaman makoki na Ahlul Baiti amincin Allah ya tabbata a garesu da baqaqen kaya, [30] ya zo a cikin littafin Kamil Fit tarik cewa, farkon zaman makoki na ‘yan shi’a kan imamu Husaini A S, ya kasance da umarnin masu yiwa Daular Dailami ta’azziyya a shekara ta 352 hijira, kuma aka umarci mata da su fita suna masu nuna alamar baqin ciki suna masu nuna baqin ciki a fuskokinsu. [31] wata waqa ta zo a cikin littafin Adabi Xaf ta wani mawaqi a qarni na biyar hijira, idan ya yi nuni kan sanya baqaqen kaya, domin nuna baqin ciki kan imamu Husaini A S . [32] Ana cewa Kawaji Ali Siya Fush [wanda yake sanye da baqaqen kaya] wanda ya rasu a shekara ta 830 hijira kuma xaya daga cikin jikokin Safiyud Din Al’ardabili kuma xaya daga cikin kakannin Safawiyin, ya shahara da wannan laqabi na Siya fush ne saboda ya kasance yana sanya baqaqen kaya koda yaushe a wajan zaman makoki na imamu Husani A S, kamar yadda mutumannan xan qasar Italiya Bituro Dila Faliya ya faxa a lokacin ziyararshi a qasar Iran a shekara ta 1207 hijira cewa, mutane suna fituwa zuwa zaman makoki a ranakun Muharram da Safar suna sanye da baqaqen kaya. [34]

Marubucin nan xan qasar Faransa Al’faransi dukwant gubinu yana siffata baqaqen kaya da sarakuna da wazirai da ma’aikata suka kasance suna sawa a lokacin mulkin Qajari a lakacin zaman makoki [35] kumar yadda tisharliz Jims wanda yake shi likita ne xan qasar Ingla, yake cewa, kayan zaman makoki na al’ada a watan Muharram da Safar a lokacin mulkin Qajari a qasar Iran sune baqaqe, saboda mafi yawaanacin mutane suna sanya baqaqen kaya ne tin daga farkon Muharram. [36]

Baqqen kaya na Abbasawa ne

Muhsin Hassam Muzahiri mai bincike kan zaman takewa xan Shi’a yana jingina cewa, wanda yafi kowa shahara kan qarfafa sanya baqaken kaya a tarihin Musulinci shi ne Abu Muslim Alkurasani da shi da abokanshi, kuma ance suna ne waxanda suka fara xaga baqar tuta a musulinci, hakan yasa ake yimusu laqabi da Musaauwada [wato masu baqaqen kaya] jinginasu da baqar kala. [37] haqi Banul Abbas sunyi bure kuma suka sanar da sanya baqaqen kaya, saboda xaukar fansa daga waxanda suka kashe iyalan gidan manzo Amincin Allah ya tabbata a garesu. [38] wasu masu bincike na tarihi suna ganin sanya baqaqen kaya alamace ta Banil Abbas, kuma hakan ba komai ba ne sai nuna koyi da nadama kan abin da ya faro da ahlul baiti saboda ‘yan shi’arsu. [39] bisa ra’ayin Jurji Zaidan wanda ya rasu a shekara ta 1332 hijira cewa, sanya baqaqen kaya ya zaman al’adar gamnatin Abbasiyawa, kai har abin ya kai ga duk wanda zai shiga gun Kalifa sai ya sanya abaya baqa wacce zata rufe duk kayan da ya sa.. [40] kuma wasu suna ganin hanin imamai kan sanya baqaqen kaya a wasu hadi sai, [41] ya faru ne domin su hana kamance-ceniya da Abbasiyawa waxanda saka kwace haqin mulki na iyalan gidan manzo amincin Allah ya tabbata a garesu baki xaya. [42] Ali Abu Husaini ya ambaci banbanci wajan sanya baqaqen kaya tsakanin Banil Abbas da ‘yan shi’a;

  • ‘yan shi’a suna sa baqaqen kaya ne domin baqin ciki a wasu rnaku sanannu,amma Abbasiyawa sun zavi baqaqen kaya ne a ranakun da ba na baqin ciki ba da kuma kaya na yau da kullin. [43]
  • ‘yan shi’a suna sanya baqaqen kaya ne domin raxin kansu da nuna soyayyarsu da baqin ciki a cikin zuciyarsu ga iyalan gidan manzo,savanin Abbasiyawa sun kasance suna sa sharaxi kan sanya baqaqen kaya kuma suna azabtar da duk wanda yaqi yin aiki da hakan. [44]
  • Sanya baqin tufafin Abbasiyawa yana faruwa ne bisa dokoki da lura da su, savanin ‘yan shi’a, ba bu wata doka da take tilastawa mutum ya sanya baqin tufafi a tsakaninsu. [45]