Azuhur Ta Shari'a
Azuhur ta shari’a (arabic: الزوال) ko zawali, lokacin da mikakken ita ce ko wani abu da yake tsaye inuwarsa take kwanciya da shimfixuwa a qasa domin ayyana lokacin sallar Azuhur, wannan inuwa tana isa mafi gajertarsa a yini, Azuhur ta shari’a shi ne lokacin fara sallar Azuhur.
Kan asasin fatawar Malaman Fiqihu yayin da inuwa ta shimfixu a qasa da surar Amudi, shi ne lokacin da inuwar Amudin za ta isa zuwa da mafi gajertar miqdari, ana kiransa zawalin rana ko Azuhur ta shari’a. [1]
An yi bahasi kan Azuhur ta shari’a cikin babukan lokutan sallah, [2] da Azumin Matafiyi cikin litattafan Fiqihu, wasu ba’arin hukunce-hukuncen da suke da alaqa da Azhur ta shari’a sun kasance kamar haka:
- Azuhur ta Shari’a tana caccanjawa kan asasin yanayin yankuna da kwanakin shekara. [3]
- Fatawar Malaman fiqihu shi ne da zarar shiga Azuhur to lokacin sallar Azuhur ya fara. [4]
- kan ra’ayin Malaman fiqihu idan Mai Azumi ya yi tafiya kafin shigar Azuhur ta shari’a Azuminsa ya qarye. [5]
- idan Matafiyi ya isa qasarsa kafin Azuhur ko wani gari da yake da niyyar zama a garin zuwa kwanaki goma, idan ya zama bai yi wani abu da yake karya Azumi ba kafin ya isa wurin dole wannan rana ya xauki Azumi, idan kuma ya yi wani abu da yake qarya Azuminsa a wannan, to Azumin wannan rana ba wajibi bane a kansa. [6]
Bayanin kula
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 252; Imam Khumaini,Tauzihul Al-Masa'il, 1391, fitowa ta 729, shafi na 116; Makarem Shirazi, Tauzihul Al-Masa'il, 1429 Hijira, Sashen Sallah, Mas'ala ta 672.
- ↑ Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 673.
- ↑ Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Arwa Al-Wughta, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 252; "Me ya sa ake samun bambanci hatta a cikin makusantan Ufukai ?", tushen bayanin Hozha.
- ↑ Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi na 250; Imam Khumaini,Tauzihul Al-Masa'il, 1391, fitowa ta 731, shafi na 117; Makarem Shirazi, Tauzihul Al-Masa'il, 1429 Hijira, Sashen Sallah, Mas'ala ta 673.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il Maraji'a, 1381, juzu'i na 1, shafi na 953.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 994.
Nassoshi
- Bani Hashemi Khomeini, Sayyid Mohammad Hasan,Tauzihul Al-Masa'il Maraji'a Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na Kum Theological Seminary Society, 1381.
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah,Tauzihul masa'il Qum, Cibiyar Edita da Buga Imam Khumaini, 1391.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tauzihul Al-Masa'i;l Qum, Wallafar Mazhabar Imam Ali Bin Abi Talib, 1429H.
- Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Urwa Al-Wuthagha, Qom, Islamic Publication Institute alaka da Madrasin Society, 1421 AH.
- «چرا اوقات شرعی در دو افق نزدیک به هم اختلاف مشهود دارد؟»، پایگاه اطلاع رسانی حوزه، تاریخ درج: ۱۸ شهریور ۱۳۹۳ش، تاریخ بازدید: ۲۱ مرداد ۱۴۰۲ش.