Di'ibil Ɗan Ali Khuza'i

Daga wikishia

Di'ibil ɗan Ali khuza'i ya rayu tsakanin shekaru 148-245 kuma ya kasance daga cikin sahabban Imam Kazim (A.S). ya shahara ne sakamakon waƙa da ya rera da ake kira da ƙasidar ta'iyya, ya fara rera wannan waƙa gaban Imam Rida (A.S) a garin Marwe kuma Imam Rida (A.S) ya yaba masa kan wannan waƙa da ya rera a gabasa.

Di'ibil ya naƙalto hadisai daga Imamai daga jumlar abin da ya naƙalto za a iya ishara ga huɗuba shiƙshiƙiyya. Di'ibil khuza'i ya shahara da yin ba'a da izgili kan maƙiya Ahlul-baiti (A.S) cikin ƙasidunsa. a shekara ta 245 hijira ƙamari aka kashe shi dalili ba'a da izgiili da ya yi wa kan ɗaya daga cikin sarakunan Abbasiyawa, kuma an binne shi a garin Shush.

Gabatarwa Tare da Matsayi

Di'ibil ɗan Ali khuza'i ɗaya ne daga cikin mawaƙa kuma marawaitan hadisan Ahlul-baiti (A.S) a ƙarni na biyu zuwa na uku hijira ƙamari.[1] ƙasida ta'iyya ta kasance shahararriyar waƙa da aka rere game da tarihin Ahlul-baiti (A.S) da bayanin irin zalunci da aka yi a kansu, ya fara rerawa Imam Rida (A.S) wannan waƙa a garin Marwe, ƙasidar ta'iyya ta kasance ɗaya daga cikin ƙasidu da suka samu matuƙar karɗuwa wurin ƴan shi'a.[2]

Di'ibil khuza'i ya rera ƙasidu masu yawan gaske cikin yabo da juyayin Ahlul-baiti (A.S).[3] bayan samun labarin shahadar Imam Rida (A.S) ya rera masa ƙasidar raiyya cikin juyayin shahadarsa.[4] a cewar ba'arin masu dandaƙe bincike Di'ibil yana matsayi na musamman cikin adabin waƙoƙi.[5] “ɗabaƙatul As-shu'ara” da diwanin waƙoƙinsa ana lissafa su daga cikin rubuce-rubucen da ya yi.[6] a cewar Sayyid Muhsin Amini, marubucin littafin A'ayan Ash-shi'a, haƙiƙa diwanin waƙoƙin Di'ibil ya kasance yana nan har zuwa ƙarni na sha uku hijira ƙamari, amma bayan nan ba a ƙara ganinsa ba har yanzu.[7] ba'arin marubuta sun baƙin ƙoƙarinsu cikin tattaro waƙoƙinsa da aka naƙalto cikin litattafai daban-daban.[8]

Asalin sunansa Hassan, Abdur-rahaman ko kuma dai Muhammad, sai dai cewa ya fi shahara da laƙabin Di'ibil.[8] ana masa alkunya da Abu Ali[10] ko Abu Jafar.[11] an haife shi a shekara ta 148 hijira ƙamari.[12] ya kasance mutumin garin kufa amma ya yi tafiya zuwa garuruwa daban-daban.[13] nasabarsa tana danganewa zuwa ga ƙabilar khuza'atu ɗaya daga cikin ƙabilun ƙasar yaman.[14] Budailu ɗan Warƙa da ɗansa Abdulahi ɗan Budailu, sun kasance daga kakannin Di'ibil waɗanda dukkaninsu sahabban Annabi (S.A.W).[15] Abdullahi ɗan Budailu ya kasance daga cikin sahabban Imam Ali (A.S) wanda tare da ƙabilar khuza'atu ya sun kasance cikin rundunar Imam Ali (A.S) a yaƙin siffin suna yaƙar Mu'awiya ɗan Abu Sufyan kuma a wannan yaƙi ne ya rabauta da samun shahada.[16] amma wasu madogaran sun rubuta nasabarsa saɗanin abin da muka ambata.[17]

Naƙalin Hadisi

Di'ibil ya kasance daga sahabban Imam Kazim (A.S) da Imam Rida (A.S).[18] ya kuma riski Imam Jawad (A.S).[19] yana cikin jumlar marawaita da suka naƙalto huɗuba shiƙshiƙiyya.[20] mutum ne da yake da matsayi na musamman a cikin sahabban imaman shi'a.[21] Di'ibil ya naƙalto riwaya daga ɗaiɗaikun mutane misalin Sufyan Sauri, Malik ɗan Anas (Shuwagabannin mazhabar malikiyya), Sa'id ɗan Sufyan da Muhammad ɗan Isma'il.[22] haka nan Ali ɗan Ali ɗan Razin (ɗan uwan Di'ibil) Musan ɗan Hammad Yazidi, Aba Saltu Hirawi da Ali ɗan Hakim suna cikin daga jumlar sauran ɗaiɗaikun mutane da Di'ibil ya naƙalto hadisai daga wurinsu.[23]

Wafati

A cikin shekara 245 hijira ƙamari[24] aka kashe Di'ibil sakamakon ba'a da ya yi kan ɗaya daga cikin sarakunan Abbasiyawa.[25] an ce Di'ibil ya kasance mutum mai kaifin harshe da babu wani sarki ko wazir da ya kuɗuta daga ba'arsa da izgili, da yawa yawan mutane suna tsoran ba'arsa.[26] haka nan an bada rahoto cewa Di'ibil yana tsananin ta'assubanci cikin soyayyar Ahlul-baiti .[27] babu wanda yake yi wa ba'a da izigili sai maƙiyan Ahlul-baiti (A.S).[28] sakamakon ba'a da yake yi kan sarakuna, a ko da wane lokaci ya kasance cikin halin guje-guje da ɗuya don gudun kada su damƙe shi.[29] Ba'arin masu dandaƙe bincike sun ƙaddara cewa an kashe shi sakamakon ba'a da ya yi kan sarki Mutawakkil Abbasi baya da ya bada umarni a ruguje ƙabarin Imam Husaini (A.S), sai Di'ibi; ya rere ƙasidar juyayi da jimami rusa wannan ƙabari[30] cikin ba'arin madogarai an ambaci wasu wurare da lokuta daban da a anan aka ce ya mutu.[31] a rahotan Abul Fatuhu Razi marubucin littafin Tafsiru Ruhil Al-jinan, a ƙarshen rayuwar Di'ibil ya rera wasu baitukan waƙa da yake iƙrari da tauhidi, annabta da wilayar Imam Ali (A.S).[32] an rubuta wannan baitukan ƙasida a saman ƙabarinsa.[33] an Di'ibil da kansa ya yi wasiyya da a rubuta ƙasidar ta'iyya kan saman ƙabarinsa.[34] ƙabarin Di'ibil yana nan a garin Shush cikin ƙasar Iran.[35]