Ibrahim Adhama
Ibrahim Adhama (arabic: إبراهيم بن أدهم) wanda ya rayu a tsakanin shekara ta 80-161, yana daga cikin Arifai wanda suka yi zamani daya da Imamai uku na Shi’a, Ma’ana Imam Sajjad (A.S) Imam Bakir (A.S) Imam Sadiƙ (A.S) ba a ambaci sunansa ba a dadaddun litattafan Ilimin Rijal na Shi’a ba, amma tare da haka wasu `Yan Shi’a suna Kidaya shi cikin Sufaye. Hakika Ibrahim Adhama ya fito daga babban gida da suka kasance Sarakunan garin Balakh, kwatsam sai aka ga ya karkata zuwa ga Zuhudu, bayan ya tuba sai ya tafi Makka ya je ya zauna da Manya-Manyan Sufaye na can, bayan wani lokacin sai ya koma garin Sham ya zauna a can har zuwa karshen rayuwarsa, ana ganin shi ne Tushen ba’arin wasu Darikun Sufaye daga Jumlarsu akwai Darikun Adhamiyya da Nakabashandiya. Bayani dangane da rayuwar Ibrahim Adhama Ayyukansa da Halayensa duk an nakalto su cikin litattafan Irfani, hakika Ibrahim Adhama yana ganin yin Aure da haihuwar `Ya`ya matsayin wani abu da basa haduwa da Zuhudu, Shakik Balakhi yana daga mafi shaharar Almajiran Ibrahim Adhama
Tarihin Rayuwa
Ibrahim Adhama Bn Sulaiman Bn Mansur, daya daga cikin Manya-manyan Jagororin Makarantar Zuhudu, [1] ya kasance daga cikin Arifan Karni na Goma h kamari [2] ana masa Alkunya da Abu Is’hak [3] ko kuma Al’ijili [4] an haifi Ibrahim Adhama a shekara ta 80, [5] ko 100 h kamari [6] cikin wasu Dangi Ajamawa [7] ko Larabawan Bani Tamim [8] a garin Balakh wani bangare daga Kurasan [9] Zahabi Marubucin littafin Tarikh Islam ya tafi kan cewa an haifi Ibrahim Adhama ne a cikin Garin Makka lokacin da Mahaifansa suka je aikin Hajji [10] hakika Ibrahim Adhama da Mahaifansa sun kasance daga Gidan Saurata [11] kuma Sarakuna [12] Manyan Mutane a garin Balakh [13] kan asasin rahotannin Tarihi hakika Ibrahim Adhama Karaga da kambun Sarauta da tarin kayan Alatu da more rayuwa basu rude shi ba, haka duka ya barsu ya yi hijira zuwa duniyar Zuhudu da talauci ya shagaltu da Sululki da tsarkake Nafsu. [14] An yi wallafe-wallafen litattafai masu yawan gaske game da halayensa da Nasihohinsa. [15] wasu ba’arin Masadir misalin Tazkiratul Auliya talifin Attar Naishaburi sun bada rohoto kan haduwar Ibrahim Adhama da Annabi Khidir, da kuma samun nasarar tsinkaye kan Ismul A’azam. [16]
Karkatuwa Zuwa Ga Zuhudu
Masadir daban-daban na Muslunci sun kawo bayanin dalilai daban-daban kan karkatuwar Ibrahim Adhama zuwa ga Zuhudu da watsi da duniya, daga jumlarsu akwai wani sauti na gaibi da ya ji lokacin da ya yi niyyar yin Farauta, [17] ko kuma jin muryar Barewa tana Magana, [18] ko kuma ganin wani Lebura da cikin kwanciyar hankali da Annashuwa tare da karancin abin more rayuwa, [19] kan asasin wani yanki daga rahotanni, hakika an bayyana cewa babban dalilin karkatuwarsa zuwa ga Zuhudu da watsi da duniya, shi ne tsoron Kwanciyar Kabari da kuma nisan tafiyar Alkiyama tare da rashin wadataccen guzuri da jabbariyar Ubangiji da rashin uzuri ga Bawa. [20] [yadasht 1] A Imaninsa, shiga Zuhudu da kaiwa ga Mukamin Salihai yana da Sharudda, daga jumlarsu: rufe kofar Ni’ima da bude kofar tsanani, rufe kofar Izza, bude kofar Kaskanta, rufe kofar hutu da bude kofar zage dantse, rufe kofar bacci da bude kofar ido bude, rufe kofar wadata da bude kofar talauci, rufe kofar buri bude kofar mutuwa. [21] Muhsin Kara’ati, Marubuci na wannan zamani, ya ganin cewa zuhudu irin na Ibrahim Adhama ya saba da Mafhumin Zuhudu a Muslunci, [22] ya bayyana cewa irin wannan zuhudu na Ibrahim Adhama yana cikin Zuhudun da Annabin Muslunci (S.A.W) ya yi hani kanda tare da zargi kan masu yinsa, [23] Ibrahim Adhama yana ganin yin aure da haihuwa ya sabawa Zuhudu, [24] sannan yana ganin wajibi ne mai zuhudu ya kauracewa shiga cikin mutane ya ware kansa can gefe. [25]
Hijira Zuwa Makka Da Sham
Ibrahim Adhama bayan Tuba ya tafi garin Naishabur, tsawon shekaru tara yana zaune cikin wani Kogon wani Dutse da ake kira da suna Al-basra’u, [26] bayan nan kuma sai ya tafi Makka, [27] Zahabi Masanin tarihi da hadisi daga bangaren Ahlus-sunna, yana ganin dalilin da ya Ibrahim Adhama barin garin Balakh ba komai bane illa tsoron Abu Muslim Kurasani, [28] Ibrahim Adhama a zamansa a Makka ya samu damar sanin Manya-Manyan Sufaye misalin Sufyanul Sauri da Fudailu Bn Iyad [29] bayan nan kuma sai ya tafi Sham [30] ana ganin shi ne musabbabin habbakar zuhudu da Irfani a garin Sham. [31]
Wafati
Masadir daban-daban na tarihi sun nakalto cewa Ibrahim Adhama ya mutu a shekara ta 160 h kamari, [32] shekara ta 161 h kamari, [33] shekara ta 162 h kamari, [34] shekara ta 166 h kamari [35] an bada rahoton kan cewa ya mutu mutuwa ta dabi’a, [36] duk da cewa wasu sun yi Imani cewa an kashe shi ne a cikin daya daga Yakokin da aka yi da Rumawa [37] a wani yanki da ake kira Sukin [38] akwai sabanin kan batun inda aka binne shi, wasu suna ganin an binne shi a yankin Sur daya daga cikin garuruwan da suke a gabar Tekun Sham. [39]
Matsayi
Ana kirga Ibrahim Adhama cikin jerin Sahun Manyan Sufayen Muslunci misalin Hasanul Basari wanda ya mutu shekara ta 110 h kamari, Malik Dinar, Rabi’atu Adwiyya, Shakik Balakhi wanda aka fi sani Karaji [40]wanda ya mutu shekara ta 200 h kamari. [yadasht 2] wasu suna ganin a lokacinsa sunan Sufi ya samu yaduwa. [41] Hakika Sufayen garin Balakh daga jumlarsu akwai Ibrahim Adhama, sun tasirantu da Makarantar Sufanci ta Basara, da kuma hususiyoyin wannan makaranta misalin wuce gona da iri cikin Zuhudu, yawan Ibada, tsoro da lazimtar Talauci . [42] Ibrahim Adhama ya tasirantu da wasu fitattun Mutane a Sufanci misalin Hasanul Basari da Sufyanul Sauri, [43] daidai lokacin da Shi kuma Sufancin Sham ya tasirantu matuka da Ibrahim Adhama, [44] haka zalika sauyin zuhudu da ibada da kuma Tarbiyya ta Sufanci duka sun samu ne bisa la’akari da Tasirorinsa. [45] Ana kirga Ibrahim Adhama daga Jumlar Malaman Hadisi, [46] cikin littafin ilimin Rijal na Ahlus-sunna an yabe shi sosai a wurare da daman gaske kuma sun bayyana cewa yana daga cikin Sahabban Abu Hanifa da Sufyanul Sauri. [47] Abu Hanifa Shugaban Mazhabar Hanafiyya daga Ahlus-sunna [48] da Junaidu Bagdadi sun kasance suna ambatonsa da lakubba na girmama, [49] ta yanayin ta kai cewa wadannan lakubba sun cika Wakokin Arifai da Sufaye, [50] a cewar Zainul Abidin Shirawani wanda ya rayu tsakanin shekaru 1194-1253 h kamari, wanda ya kasance Marubuci kuma mawaki Sufi ya bayyana cewa ba a samu sunan Ibrahim Adhama cikin tsofaffin littafan ilimin Rijal na Shi’a, [51] Sayyid Muhsin A’araji Kazimi wanda ya rayu tsakanin shekaru 1130-1227 Malamin Fikihu na Shi’a yana ganin Ibrahim Adhama yana cikin Jerin Sahun Kumailu Bn Ziyad, Bishir Bn Haris Maruzi da AbaYazid Bastami kuma dukkaninsu Mazaje ne `Yan Shi’a Sufaye. [52] Yana ganinsa matsayin Tushen Darikun Sufaye, [53] da wannan ne Malamin yake ganin Darikun Sufaye [54] Adhamiyya Nakabashandiya sun samu ne daga Imam Sajjad (A.S) amma ta wasida da tsanin Ibrahim Adhama, [55][yadahst 3]
Alakarsa Da Ma’asumai (A.S)
Ibrahim Adhama ya yi zamani daya da Imam Sajjad (A.S) [56] Imam Bakir (A.S) da kuma Imam Sadiƙ (A.S), Masadir sun bada rahoto kan alakarsa dasu, akwai zaman da ya yi a wurin Imam Sajjad (S.A.W) sannan ganawarsa da Imami na hudu da wasiyyar da Imam ya yi masa shima ya zo cikin Masadir na Shi’a . [57] Zainul Abidin Sharawani, ya yi Magana kan Haduwar Ibrahim Adhama da Imam Bakir (A.S) [58] Muhammad Kazim Asrar Tabrizi wanda ya rayu tsakanin shekaru 1265-1315 h kamari, Mawaki Sufi a zamanin Sarakunan Kajariyawa, yana Ganin Ibrahim Adhama yana cikin Muridan Imam Bakir (A.S) [59] akwai riwaya da Ibrahim Adhama ya rawaito daga Imamai kuma an ambatonta ya zo cikin litattafan riwaya. [60] Cikin littafin Safinatul Al-Bihar da cikin wasu Masadir din daban ya zo cewa cikin waki’ar fitowar Imam Sadiƙ (A.S) daga Kufa zuwa Madina hakika Ibrahim Adhama yana cikin gayyar `yan rakiyarsa, [61] wasu riwayoyin sun nakalto cewa Ibrahim Adhama yana cikin Hadiman Imam Sadiƙ (A.S). [62]
Malamai Da Almajirai
Ibrahim Adhama ya nakalto riwaya daga Imam Bakir (A.S) da ta hannun Muhammad Bn Zayad Jahami, Abi Is’hak, Malil Bn Dinar, A’amash da kuma Mahaifinsa, [63] Mafi shaharar Almajirinsa shi ne Shakik Balakhi wanda ya kasance cikin Manyan Arifai daga Almajiran Imam Kazim (A.S) [64] kan asasin ra’ayin Mashhur [65] Shakik Muridi ne da ya samu tarbiyya a hannun Ibrahim Adhama, [66] kuma ya kasance Abokinsa. [67] Cikin Wakoki Da Adabi Hakika tsarin rayuwa da halaye da nasihohin Ibrahim Adhama ya yadu sosai cikin Baitukan Wakoki musammam wakokin Irfani da Sufanci, ta yanayin da hikayoyinsa sun bazu cikin Maudu’ai daban-daban misalin Tarihin rayuwa [68] Kissar Tubansa da hijira zuwa Zuhudu, [69] sababin Hijirarsa [70] haduwarsa da Annabi Khidir, [71] da dansa, [72] Munajati [73] Karamomi, [74] hikaya da Maudu’ai daban-daban [75] duka sun zo cikin ziri da zuben wakoki.
Bayanin kula
- ↑ Suhrvardi, Awarif al-Maarif, 1375, shafi na 4..
- ↑ Tabatabai, Shi'a dar Islam , 1378, shafi na 110.
- ↑ Salmi, Tabaqat al-Sufiyya, 1424H, shafi na 15; Hajowiri, Kashf al-Mahjub, 1375, shafi na 128.
- ↑ Ibn Kathir, Al-Bedaya da Al-Nehaya, 1407, juzu'i na 10, shafi na 135.
- ↑ Faqir Estehbanati, Kharabat, 1377, shafi na 129.
- ↑ Dhahabi, "Siyar Al-Alam An-Nublah", 1406 AH, juzu'i na 7, shafi na 387-388.
- ↑ Pir Jamal Ardestani, Merat al-Afrad, 1371, shafi na 332.
- ↑ Dhahabi, Tarikh Islam, 1413 AH, juzu'i na 10, shafi na 44; Faqir Estehbanati, Kharabat, 1377, shafi na 129.
- ↑ Salmi, Tabaqat al-Sufiyyah, 1424H, shafi na 15.
- ↑ Dhahabi, Tarikh Islam, 1413 AH, juzu'i na 10, shafi na 45.
- ↑ Salmi, Tabaqat al-Sufiyya, 1424H, shafi na 15.
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asar, 1377, shafi na 48.
- ↑ Dhahabi, Tarikh Islam, 1413 AH, juzu'i na 10, shafi 45; Khwarazmi, Yanabi'ul al-Assarr, 2004, juzu'i na 1, shafi na 377.
- ↑ Sajjadi, Farhang Maref Islami, 1373, juzu'i na 1, shafi 126; Motahari, Majmu'eh Asar, 1377shafi na 237.
- ↑ Misali, duba: Attar Nishabouri, Tazkire Auliya, 1905, shafi na 94; Qashiri, Rasale Qashiriyeh, 1374, shafi 345, 430, 455; Hajowiri, Kashf al-Mahjub, 1375, shafi na 129; Mostamli Bukhari, bayanin tafsirin Sufanci, 1363, juzu’i na 1, shafi na 226; Nasfi, Raz Rabani Asrar Al-Wahi Sobhani, 1378, shafi 127, 163; Suhrvardi, Awarif al-Maarif, 1375, shafi na 3; Ghazali, fassarar Ahya Uloom al-Din, 1386, juzu'i na 3, shafi 185; Salmi, Al-Salami Tarin Ayyuka, 1369, juzu'i na 1, shafi.366; Ghazali, Kimiai Saadat, 2003, juzu'i na 1, shafi na 363; Meybodi, Kashf al-Asrar, 1371, juzu'i na 5, shafi.451; Samaani, Ruh al-Aroom fi Sharh Asma al-Mulk al-Fatah, 1384, shafi 169, 513; Ansari, Islamic Irfan, 1386, juzu'i na 2, shafi.462; Meshkini, nasiha da lafuzza na bayin Allah goma sha hudu (a.s) da kalmomi dubu da daya, 2013, shafi na 165; Faqir Estehbanati, Kharabat, 1377, shafi na 92; Faiz Kashani, Rah Roshan, 1372, juzu'i na 5, shafi na 220; Deilmi, fassarar Irshad al-Qulob Deilmi, 1349, juzu'i na 2, shafi na 277; Karajki, Nozha al-Nawazir, Tehran, shafi na 77; Jami, Nafahat al-Anas, 1858, shafi na 4
- ↑ Attar Nishabouri, Tazkire Auliya, 1905, shafi na 88; Shirvani, Riaz al-Sayaha, 1361, juzu'i na 1, shafi na 11; Ibn Khamis al-Mosli, Manaqib al-Abrar, 1427H, juzu'i na 1, shafi na 51.
- ↑ Ibn Kathir, al-Bedayah wa al-Nehayah, 1407 AH, juzu'i na 10, shafi na 135; Salmi, Tabaqat al-Sufiyya, 1424H, shafi na 15; Ibnul Mulqan, Tabaqat al-Awlia, 1427 AH, shafi na 37; Manawi, al-Kawakb al-Dariyyah Fi Sharh Al-Sada al-Sufiyyah, 1999, juzu'i na 1, shafi na 195; Zagzouq, Al-Susuf al-Islami encyclopedia, 1430 AH, shafi na 202; Ibn Khamis al-Mosli, Manaqib al-Abrar da al-Akhyar al-Akhyar a cikin Tabaqat al-Sufiya, 1427 AH, juzu'i na 1, shafi na 51.
- ↑ Hajowiri, Kashf al-Mahjub, 1375, shafi na 128.
- ↑ Mazaheri, Akhlaq wa Javan, 1387, juzu'i na 1, shafi 103
- ↑ Meshkini, nasa'ihu wa Sukhane Ceharda Ma'asum (a.s) wa Hezaro Yek Sukhan, 1382, shafi na 165.
- ↑ Suhravardi, Awarif al-Maarif, 1375, shafi na 3.
- ↑ Qaraeti,Gunahsinasi, 2006, shafi na 197
- ↑ Qaraeti,Gunahsinasi, 2006, shafi na 197
- ↑ Attar Nishaburi, Tazkire Auliya, 1905, shafi na 93; Kashani, Majmu'eh Rasa'il Wa Musannafat Kashani, 1380, shafi na 54; Shahidi Thani, Munyatul al-Murid, 1409 AH, shafi na 228; Faqir Estehbanati, Kharabat, 1377, shafi na 92.
- ↑ Faqir Estehbanati, Kharabat, 1377, shafi na 92
- ↑ Zubeidi, Taj al-Arus, 1414 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 47.
- ↑ Attar Neishabouri, Tazkire Auliya, 1905, shafi na 87.
- ↑ Dhahabi, Tarihin Musulunci, 1413 AH, juzu'i na 10, shafi na 44.
- ↑ Salmi, Tabaqat al-Sufiyya, 1424H, shafi na 15; Faqir Estehbanati, Kharabat, 1377, shafi na 129.
- ↑ Ibnul Mulqan, Tabaqat al-Awlia, 1427H, shafi na 37.
- ↑ Kanun Nahsare wa farhn Islami Hasnat Isfahan, Sairi dar Sepehr Ekhlaq, 2009, juzu'i na 1, shafi na 107.
- ↑ Khwarazmi, Yanbua al-Asrar, 2004, juzu'i na 1, shafi na 377.
- ↑ Salmi, Tabaqat al-Sufiyya, 1424H, shafi na 15; Ibnul Mulqan, Tabaqat al-Awlia, 1427 AH, shafi na 39; Rozbahan Sani, Tohfa Ahl al-Irfan, 2013, shafi na 21.
- ↑ Ibn Imad Hanbali, Shazerat al-Dhahab, 1406 AH, juzu'i na 2, shafi na 282; Pir Jamal Ardestani, Merat al-Idrevan, 1371, shafi na 332.
- ↑ Khwarazmi, Yanbua al-Asrar, 2004, juzu'i na 1, shafi na 377.
- ↑ Khwarazmi, Yanboa al-Asrar, 2004, juzu'i na 1, shafi na 377, an nakalto daga Tazkireh Al-Awlia.
- ↑ Rozbahan Sani, Tohfa Ahl al-Irfan, 2013, shafi na 21.
- ↑ Zubeidi, Taj al-Arus Man Javaher al-Qamoos, 1414 AH, juzu'i na 13, shafi na 232; Khwarazmi, Yanbua al-Asrar, 2004, juzu'i na 1, shafi.377
- ↑ Ibnul Mulqan, Tabaqat al-Awlia, 1427 AH, shafi na 39; Ga wani lamarin kuma, duba: Zarkali, Al-Alam, 1989, juzu'i na 1, shafi na 31
- ↑ Ahmadpour,Kitabe Shenakt Akhlak Islami, 2005, shafi na 37.
- ↑ Ahmadpour,Kitabe Shenakt Akhlak Islami, 2005, shafi na 37.
- ↑ Salmi, Majmu'eh Asar Abu Abdul Rahman Salmi, 1369, juzu'i na 2, shafi.358.
- ↑ Kanun Nahsar wa Tarwij Farhang Islami Hasnat Isfahan, Sairi dar Sepehr Ekhlaq, 2009, juzu'i na 1, shafi na 107.
- ↑ Kanun Nahsar wa Tarwij Farhang Islami Hasnat Isfahan, Sairi dar Sepehr Ekhlaq, 2009, juzu'i na 1, shafi na 107
- ↑ Kanun Nahsar wa Tarwij Farhang Islami Hasnat Isfahan, Sairi dar Sepehr Ekhlaq, 2009, juzu'i na 1, shafi na 107
- ↑ Dayiratu Maref Buzurg Islami, Juzu'i na 1, karkashin kalmar Ibrahim Adham, shafi na 405
- ↑ Shirvani, Riaz al-Siyaha, 1361, juzu'i na 1, shafi na 12
- ↑ Attar Nishabouri, Tazkira Auliya, 1905, shafi na 86.
- ↑ Attar Nishabouri, Tazkira Auliya, 1905, shafi na 85
- ↑ Asiri Lahiji, Asrar al-Shoud fi Ma'rifah al-Haq al-Mu'boud, Bita, shafi na 182.
- ↑ Shirvani, Riaz al-Sayaha, 1361, juzu'i na 1, shafi na 11.
- ↑ Arji Kazemi,Uddatul al-Rijal, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi na 60.
- ↑ Shirvani, Riaz al-Sayaha, 1361, juzu'i na 1, shafi.7; Mirza Shirazi, Manahaj Anwar al-Merfafa fi Sharh Misbah al-Sharia, 1363, juzu'i na 1, shafi na 645.
- ↑ Golpinarli, Maulana Jalaluddin, 1363, shafi na 246; Mashkoor, Farhang Farq Islami, 1372, shafi na 309.
- ↑ Mirza Shirazi, Manahaj Anwar al-Merfafa fi Shrah Misbah al-Sharia, 1363, juzu'i na 1, shafi na 645.
- ↑ Shirvani, Riaz al-Sayaha, 1361, juzu'i na 1, shafi na 190.
- ↑ Namazi Shahroudi, Mustadrakat Alam Rijal al-Hadith, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 118; Qomi, Safina al-Bahar, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 289.
- ↑ Shirvani, Riaz al-Sayaha, 1361, juzu'i na 1, shafi na 190.
- ↑ Tabrizi, Manzar Olya, 2008, shafi na 140
- ↑ Ibn Tavus, Mahj al-Dawat, 1411H, shafi na 75.
- ↑ Qomi, Safina al-Bahar, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 289; Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib (AS), 1379 Hijira, Mujalladi na 4, shafi na 241.
- ↑ Jazayeri, Riyadh Abrar, 1427 AH, juzu'i na 2, shafi 136; Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib (AS), 1379 AH, Mujalladi na 4, shafi na 248; Majlesi,Hayatul Imam Jafar Sadiƙ (AS), 1398H, shafi na 22.
- ↑ Dhahabi, Tarikh Islam, 1413 AH, juzu'i na 10, shafi na 44.
- ↑ Sajadi, Farhang Maarif Islamic, 1373, juzu'i na 2, shafi na 1068
- ↑ Faqir Estehbanati, Kharabat, 1377, shafi na 124.
- ↑ Safi Alisha, Irfan al-Haq, 1371, shafi na 121; Motahari, Majmu'eh Asar, 1377, shafi na 48.
- ↑ Salmi, Tabaqat Sufiya Ansari, 1424H, shafi na 18.
- ↑ Shah Nematullah Vali, Diwan na Shah Nematullah Vali, 1380, shafi na 996; Attar Nishaburi, Elahinamah Attar, 1355 AH, shafi na 219; Asiri Lahiji, Asrar al-Shoud fi Ma'rifah al-Haq al-Mu'boud, Bita, shafi na 182.
- ↑ Khalkhali, Adham Khalkhali Rasa'il Farsi, 2013, shafi na 141.
- ↑ Maulavi, Masnavi Manavi, 1373, shafi na 520.
- ↑ Attar Nishaburi, Elahinamah Attar, 1355 AH, shafi na 277.
- ↑ Attar Nishabouri, Mantikul Al-Tayr, 1373, shafi na 232.
- ↑ Attar Nishaburi, Elahinamah Attar, 1355 AH, shafi na 402
- ↑ Maulavi, Masnavi Manavi, 1373, shafi na 279.
- ↑ Attar Neishabouri, "Musibat Nameh", 1354 AH, shafi na 225; Molavi, Diwan Kabir Shams, 2004, shafi na 717; Attar Nishaburi, Elahinamah Attar, 1355 AH, shafi na 69, 350; Faiz Kashani, Divan Faiz Kashani, 2013, juzu'i.4, shafi.79; Attar Nishaburi, Mazhar al-Agaib, 1323, shafi na 98; Faiz Kashani, Irfan Masnavi, 1379, shafi na 178.
Nassoshi
- Ibn al-Mulqan, Umar bin Ali al-Masri, Tabaqat al-Awlia, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, bugu na biyu, 1427H.
- Ibn Khamis al-Mosli, Hossein bin Nasr bin Muhammad, Manaqib al-Abrar da al-Akhyar al-Akhyar a cikin Tabaqat al-Sufi, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 1427H.
- Ibn Shahr Ashub Mazandarani, Muhammad Bin Ali, Menaqib Al Abi Talib (AS), Qom, Allameh, 1379H.
- Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, Mahj al-Dawaat da Manhaj al-Ibadat, Kum, Dar al-Zakhair, 1411H.
- Ibn Imad Hanbali na Damascus, Shahab al-Din Abu al-Falah, Shazarat Al-Zahaab fi Akhbar Man Al-Zahaab, binciken Al-Arnaut, Beirut, Dar Ibn Kathir, 1406H.
- Ibn Kathir Damaschi, Ismail Ibn Omar, al-Badaya wa al-Nehaya, Beirut, Darul Fikr, 1407H.
- Ahmadpour, Mahdi, Kitabe Shenakt Akhlak Islami, 11 na Musulunci, Qum, Cibiyar Bincike ta Kimiyya da Al'adun Musulunci, 2005.
- Asiri Lahiji, Muhammad, Asrar al-Shoud fi Ma'rifah al-Haq al-Maboud, Bija, Bita.
- Arji Kazemi, Mohsen bin Hassan, Kum, Ismailiyyah, 1415H.
- Ansarian, Hossein, Irafane Islami: bayanin Misbah al-Sharia, Qum, Dar al-Irfan, 1386.
- Pir Jamal Ardestani, Merat Al-Afrad, Tehran, Zovar Publications, bugun farko, 1371.
- Tabrizi, Mohammad Kazem bin Mohammad, Manzar Auliya, Tehran, Islamic Majlis Shuvari Library and Document Center, 2008.
- Jami, Abdul Rahman, Nafhat Al-Anas, Calcutta, Lisi Press, 1858.
- Jazayeri, Nimatullah bin Abdullah, Riaz Al-Abrar fi Manaqib al-Imath al-Athar, Beirut, Al-Tarikh Al-Arabi Foundation, 1427 AH.
- Khwarazmi, Kamal al-Din Hossein, Yanbu' al-Asrar fi Nisathai al-Abrar, Tehran, Association of Cultural Artifacts, 2004.
- Dayiratul Almareef Buzurg Islami, Juzu'i na 1, Tehran, Cibiyar Encyclopaedia ta Musulunci, 1374.
- Deilmi, Hasan bin Mohammad, Irshad al-Qulob Deilmi, Mostarhami, Tehran, kantin sayar da littattafai na Bouzarjamhari ya fassara, bugu na uku, 1349.
- Dhahabi, Muhammad bin Ahmed, Tarikh al-Islam da rasuwar mashahurai da malamai, wanda Omar Abd al-Salam Tadmari ya yi bincike a Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1413H.
- Rozbahan Thani, Ebrahim bin Sadr al-Din, Tohfa Ahl al-Irfan, Tehran, Yalda Qalam, bugu na biyu, 1382.
- Zubeidi, Mohammad Murtaza, Taj al-Arus Man Javaher al-Qamus, Beirut, Dar al-Fikr, 1414 AH.
- Zarkali, Khair al-Din, Al-Alam, Beirut, Dar Al-Alam Lamlayin, bugu na 8, 1989.
- Zagzouk, Mahmoud Hamdi,Mausu'atu Tasawwuf Islami, Alkahira, Ministry of Endowments, Majlis-ul-Aali for Islamic Affairs, 1430 AH.
- Sajjadi, Sayyid Jafar,Farhang Maref Islami, Tehran, Jami'ar Tehran, bugun ta uku, 1373.
- Salmi, Muhammad bin Al-Husayn, Tabaqat al-Sufi, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, bugu na biyu, 1424H.
- Salmi, Mohammad bin Hossein, Majmu'eh Asar, Abu Abdul Rahman Salmi, Tehran, Cibiyar Buga Ilimi, 1369.
- Samaani, Ahmad, Ruh al-Rawm fi Sharh Asma al-Mulk al-Fatah, Tehran, Scientific and Cultural Publications, 2nd edition, 2004.
- Suhravardi, Shahabuddin Abu Hafs, Awarif al-Maarif, wanda Abu Mansour Esfahani ya fassara, Tehran, wallafe-wallafen kimiya da al’adu, bugu na biyu, 1375.
- Shahidi Thani, Zainul-Din bin Ali, Munyatul al-Murid, Qum, Makarantar Islamic Media, 1409H.
- Shirvani, Zain El-Abdin, Riaz Al-Sayaha, Tehran, Saadi Publishing House, 1361.
- Safi Alisha, Mohammad Hassan bin Mohammad Baqer, Irfan al-Haq, Tehran, Safi Alisha, bugu na biyu, 1371.
- Tabatabai, Mohammad Hossein, Shia dar Islam, Qum, Islamic printing, bugun 13, 1378.
- Attar Neishaburi, Fariduddin, Tazkira al-Awlia, Leiden, Leiden Press, bugun farko, 1905.
- Ghazali, Abu Hamid Mohammad,Ihya Ulum al-Din, wanda Moayed al-Din Khwarazmi ya fassara, Tehran, Cibiyar Buga Ilimi da Al'adu, bugu na 6, 1386.
- Ghazali, Abu Hamed Mohammad, Kimiyai Saadat, Tehran, Kamfanin Buga Ilimin Kimiyya da Al'adu, bugu na 11, 2013.
- Faqir Astehbanati, Ali, Kharabat dar bayan hikmat, jajircewa, tsafta da adalci, Tehran, Aineh Ersat, 1377.
- Faiz Kashani, Mohammad Bin Shah Morteza, Rah Roshan, Mashhad, Astan Quds Razavi, 1372.
- Qaraati, Mohsen, Ghuna Shinasi, Tehran, Darussa daga Cibiyar Al'adun Kur'ani, bugu na 8, 2006.
- Qashiri, Abolqasem Abdul Karim, Risale Qashiriyeh (fassara), Tehran, wallafe-wallafen Kimiyya da Al'adu, bugu na 4, 1374.
- Qomi, Abbas, Safina Al-Bahar, Qom, Aswa, 1414H.
- Kashani, Abdul Razzaq, Kashani na haruffa da ayyuka, Tehran, rubuce-rubucen gado, bugu na biyu, 1380.
- Kanun Bahar wa tarwij Farhang Islami, Hasnat Isfahan, Sairi Dar Sepehr Ekhlaq, Qom, Sahife Khard, 2009.
- Karajki, Mohammad bin Ali, Nazha al-Nawazir a cikin fassarar Mine Al-Jawahir, Tehran, Islamia, Beta.
- Golpinarley, Abdul Baqi, Mirlana Jalal al-Din: Zanjadan, Flasfah, Aqar and Affiliates of the Annas, Tarjam and Tawdiqi, Thaiqi, and Thaiqi.
- Majlesi, Mohammad Baqer, hayat Imam Jafar Sadiq (AS), Musa Khosravi, Tehran, Islamia, bugun na biyu, 1398H.
- Mostamoli Bukhari, Ismail, Sharh AT-Ta'arruf Limazhab Tasawwuf, Tehran, Asatir Publications, 1363.
- Mashkoor, Mohammad Javad, Farhnag Feraku Islam, Mashhad, Astan Quds Razavi, bugu na biyu, 1372.
- Meshkini Ardabili, Ali, Nasa'ihe wa Sukahane Ceharda Ma'asum (a.s) wa Hezaro Yek Sukhan, Qum, bugun Al-Hadi, bugu na ashirin da hudu, 1382.
- Motahari, Morteza, Majmu'eh Asar Shahid Motahari, Tehran, Sadra, bugu na 8, 1377.
- Mazaheri, Hossein, Akhlaq wa Javan, Qom, Shafaq, bugu na 4, 2007.
- Manawi, Mohammad Abdul Raouf, Al-Kawakib al-Dariyyah fi tarajimati Al-Sada al-Sufiyyah, Beirut, Dar al-Esq, 1999.
- Meybodi, Abulfazl Rashiduddin, Kashf al-Asrar wa Uddatul al-Abrar, Tehran, Amir Kabir Publications, bugu na biyar, 1371.
- Mirza Shirazi, Abul Qasim, Manahaj Anwar al-Merfafa fi Sharh Misbah al-Sharia, Tehran, Khanqah Ahmadi, bugu na 2, 1363.
- Nasfi, Azizuddin, Raz Rabbani , Tehran, Amir Kabir Publications, 1378.
- Namazi Shahroudi, Ali, Mustadarkat Alam Rizal al-Hadith, Tehran, dan marubuci, 1414 Hijira.
- Hajwiri, Abolhasan Ali, Kashf al-Mahjoub, Tehran, Tahuri, bugu na 4, 1375.