Firka Najiya

Daga wikishia
Wannan Qasida ce game da Firqa Najiya . Domin sanin hadis Iftirak, duba hadis Iftirak.

Firka Najiya. (arabic: الفرقة الناجية) ko a ce tseratacciya Kungiya jimla ce a cikin Hadis Iftirak (rarrabuwa) wacce aka fassara da Shi'a Imamiyya. Ya Zo a cikin hadisin da aka jingina wa Annabi (S.A.W) cewa, bayansa al’ummar musulmi za su rabu kashi-kashi, kashi ɗaya ne kawai ya ke kan tsira. An ruwaito daga Annabi (S.A.W) da Imam Ali (A.S) cewa Firka Najiya Su ne ‘yan Shi’ar Ali (A.S) ce kawai.kuma An yi rubuce-rubuce daban-dabankan kan misali da yanayin ita Firka Najiya.

Muhimmancin Firka Najiya

Firƙa Najiya na nufin ƙungiya ko mazhabar da zata tsira a ranar Alkiyama, magana ce da aka jingina ta ga Annabi (SAWW) da ake kira Hadisin iftiraƙ. Kamar yadda ya zo a cikin wannan hadisi Annabi (S.A.W.W) ya yi hasashen cewa al’ummarsa za ta kasu kashi 73 bayan sa, alhalin bangare ɗaya ne kawai daga cikin su ya kasance ma’abocin tsira,[1] kowane bangare na musulmi ya yi ƙoƙarin bayyana wasu sharudda don su kasance misali na ɗariƙar Najiya da yazo a hadisin manzon Allah.[2]

Ingancin Hadis Iftirak

Akwai muhawara daban-daban game da ingancin Hadis iftiraƙ , Ibn Hazm Al-Andalusi (ya rasu a shekara ta 456 bayan hijira), ɗaya daga cikin malaman Ahlus Sunna, yana ganin hadisin bai kai a tsaya ayi bahasi kansh iba kuma be ingantaba ba,[3] amma kuma a wajen Ibn Wazir Malamin Fikhu kuma Mabiyin Mazhabar Zaidiyya (ya rasu a shekara ta 840 bayan hijira), yana ganin ɓangaran karshen hadisin ne ba daidai bane kuma an ƙirƙireshi ne (dukan su zasu shiga jahannama sai guda ɗaya ) [4] Sai dai wasu daga cikin littattafan hadisi na Shi'a[5] da Ahlus-Sunna[6] da wasu al'ummomi da marubuta na duniya[7] sun naƙalto kuma sun yarda da hadisin. Don haka an ce Hadisin Iftiraƙ shahararre ne kuma mustafizu [8] har yakai haddin Mutawatiri [9] ko kusa da Mutawatir a faɗar wasu malamai.[10] An ce kasancewar wannan hadisin Khabar Wahid ya sa ba za a iya dogaro da shi wajen tabbatar da iitiƙadi da tantance firƙa Najiya ba [11] Amma a cewar Ayatullah Sobhani, kasancewar wannan hadisi ya shahara a wajen Shi’a da kuma rawaitoshi daga malamai da ban daban na sunnah da shia shine yake tabbatarda firƙa Najiya. Littattafan Ahlus-Sunnah sune zasu ɗauke wan nan raunin da hadisin yakedashi ,dan haka kawoshi da akai a gurare mabanbanta ze iya sanyawa a yarda dashi kuma ayi amfani dashi.[12]

Wacce Ƙungiya ce Zata Tsira Ranar Lahira

Akwai sabanin ra'ayi tsakanin malaman mazhabobin musulinci daban-daban game da tantance ainihin ita Firkah Najiya. Sau da yawa kowannen su ya ɗauki mazhabar sa ko firƙar sa a matsayin ita ce najiya wato wadda zata tsira. sauran kuma 72 halakakku: [13] Jamaluddin Razi ɗaya daga cikin malaman Imamiyya a cikin littafin sa tabsirat Al-Awam Fi Ma'arifati makalatil Al-Anam, [14] Jafar bin Mansur Al-Yaman, ɗaya daga cikin malaman Isma’iliyya, a cikin littafin “Sara'ir wa Asrar al-Nuɗaƙaa”[15] da Shahristani ɗaya daga cikin malaman Sunna a littafin “Milal wa Nehl[16] suna ganin mazahabar su a matsayin misali na ɗariƙar Najiya. A ƙoƙarin bayyana waxe firƙa ce najiyya wani lokacin kowa yana duba wan nan Hadisin firƙa 73 ne sai ya ɗauki iya ɓangaran da Ya yi masa a ciki ya yi amfani da shi a kansa dan ya ce shi ne ake nufi da firƙa najiya [17] kuma kowace mazhaba tana ganin itace. [18] Kamar yadda binciken Ali Aghanouri ya nuna, ruwayoyin wannan Hadisin, akwai tafsiri guda goma sha biyar mabanbanta akanta,[19] wacce tafsirinta guda takwas su ke nuni da yadda da wilayar Imam Ali (AS) ko bin Ahlul Baiti (AS) ko kuma ‘yan Shi’a na Imam Ali (AS) [20] Ko da yake a cewar sa, a wasu nassosin da su ka zo babu kalmar najiya ko ceto ko firƙa najiya ko makamancin hakan.[21]

Ra'ayin Malaman Shi'a

Shaik Saduk Malamin Shi'a A ƙarni na hudu, a cikin littafin Kamalud-Addini wa Tamamin an-Ni'ima, yana mai nuni da hadis Saklaini, kan cewa duk wanda ya yi riƙo da Alkur'ani da Manzon Allah (SAWW) da iyalan gidansa tsarkaka tabbas zai kasance cikin Firkah Najiya [22] Haka kuma Allama Majlisi a cikin Bihar-Anwar ya naƙalto daga Imam Ali (A.S) cewa ‘yan Shi’a ma’abota tsira ne.[23] Hakanan Allamah hilli ya naƙalto hadisai da yawa kuma ta hanyar su yake tabbatar da mabiyan Manzo da iyalin sa a matsayin misalin firkah Najiya[24] kuma ya kawo hadisai na tabbatar da mazhabar shi'a ita ce gaskiya [25] Haka kuma hadis Safina yana ɗaya daga cikin dalilan da suke ganin cewa mabiya Ahlul Baiti (A.S) sun tsira, domin ya zo a cikin wannan hadisi cewa duk wanda yabi hanyar Ahlulbait to tabbas zai tsira.[26]

Amma Ahlus-Sunna, sun yi nuni da wasu hadisai, suna ganin Firka Najiya ita ce jama'a [27] ko kuma mafi rinjaye [28] na mabiyan Kulafa'ur Rashidin.[29] Haka nan kuma akwai wata ruwaya daga Hadisin iftiraƙ wanda yake nuni da dukkan mazhabobin Musulunci ban da zindiƙai zasu tsira ran Alƙiyama.[30] Wasu su na ganin wannan hadisi kadai yana nuni da Mabiya Mazhabar Ahlil-baiti (A.S) duk da cewa babu wani lafazi karara da ya bayyana haka[31]

Fihirisar Littafi

Littafin Firƙa Najiya na Ibrahim bin Suleiman ƙatifi
  • An yi rubuce-rubuce a fagen Firka Najiya. Agha Bozur Tehrani ya kawo wasu daga cikin rubuce-rubuce malaman Shi'a dangane da haka a cikin littafinsa Al-Dhariyyah.[32]
  • Al-Sawaram al-Madhiyyah fi firkaNajiya, na Seyyed Mohammad Mahdi Hosseini Qazvini Hilli.[33] A cikin wannan littafi an tabbatar da cewa firka Najiya su ne Imami Shi'a goma sha biyu.[34] Kuma tana kunshe da baitukan wakoki kimanin dubu ashirin da biyar[35] Malaman Shi'a sun yaba da wannan littafi.[36]Kuma Allama Majlisi yana ganinsa matsayin daya daga cikin mafi kyawun litattafai da aka rubuta akan wannan batu.[37] Wannan littafi kuma ana kiransa da "Al-Sawaram Al-Madizia".[38]

Bayanin kula

  1. Ibn Hanbal, Musnad, 1419 AH, juzu'i na 3, shafi na 145; Ibn Majah, Sunan Ibn Majah, Dar al-Fikr, juzu'i na 2, shafi na 364; Alameh Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 28, shafi na 4; Hakim Neishaburi, al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 1, shafi na 281; Tirmizi, Sunan al-Tirmidhi, 1403 AH, juzu'i na 5, shafi na 26; Haytami, Majmaal al-Zawaed, 1406 AH, juzu'i na 1, shafi na 260; Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir, 1404 AH, juzu'i na 17, shafi na 13; Dani, Al-Sunan al-Afran, 1416 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 624.
  2. Agha Nuri, "Hadisi Iftiraku Ummat Rabon...", shafi na 133.
  3. Ibn Hazm, Al-Fasl, 1405 S, Kashi na 3, shafi na 292.
  4. Ibn Waziri, Al-Awasim wa Al-Qawasim, 1415 S, Part 3, shafi na 170-172.
  5. Misali, duba Sheikh Sadouq, Al-Khasal, 1362, juzu'i na 1, shafi na 584-585; Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 28, shafi na 13
  6. Misali, duba Ibn Hanbal, Musnad, 1414H, juzu’i na 3, shafi:569; Ibn Abi Asim, Sunna, 1419 AH, Mujalladi na 1, shafi na 75-80; Tabarani, Al-Mu'jam al-Kabir, Matabata Alama, juzu'i na 18, shafi na 51.
  7. Misali, duba al-Baghdadi, al-Farq bein Al-Farq, 1408 AH, shafi na 8-5; Sobhani, Buhus fi Milal wa-al-Nahl, Al-Nashar al-Islami Publishing House, juzu'i na 1, shafi na 25-26.
  8. Subhani, Buhus fi Milal wan-Nihal, Kamfanin Buga na Musulunci, juzu'i na 1, shafi na 23; Muzaffar, Hujjar Gaskiya, 1422 q., juzu’i na 5, shafi na 289.
  9. Ibn Tavus, al-Taraif, 1420 AH, juzu'i na 1, shafi na 287 da juzu'i na 2, shafi na 74 da shafi na 259; Manavi, Faiz al-Qadir, 1391 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 20.
  10. Al-Amdi, Al-Ihkam fi Asool al-Ihkam, Dar al-Kitb al-Ilmiyah, juzu'i na 1, shafi.
  11. Agha Nuri, "Hadis Iftiraku Ummat...", shafi na 136.
  12. Sobhani, Buhus Fi Milali WAN-Nihal, Kamfanin Buga na Musulunci, Kashi na 1, shafi na 25.
  13. Baghdadi, al-Farq bein Al-Farq, 1408 AH, shafi na 11-21; Esfraini, al-Tabasir Fi al-Din, 1408 AH, shafi na 23-25; Multi Shafi'i, Al-Tanbiyyah wa Arrad, 1413 AH, shafi na 12.
  14. Razi, Tabsrat al-Awam, 1985, shafi na 194–1
  15. Ja’afar bin Mansoor al-Aliman, Sirair wa Asrar al-Natqa, 1404H, shafi na 243.
  16. Shahrashtani, Millam da Al-Nahl, 1364, juzu'i na 1, shafi na 19-20.
  17. Agha Nuri, "Hadis IFtiraku Ummat ...", shafi na 133.
  18. Agha Nuri, "Hadis IFtiraku Ummat ...", shafi na 133
  19. Agha Nuri, "Hadis IFtiraku Ummat ...", shafi na 134
  20. Agha Nuri, "Hadis IFtiraku Ummat ...", shafi na 134
  21. Agha Nuri, "Hadis IFtiraku Ummat ...", shafi na 131
  22. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1395 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 662.
  23. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 28, shafi na 11.
  24. Misali, duba Allameh Hali, Minhaj al-Karamah, 1379, shafi na 50.
  25. Allama Hilli, Minhaj al-Karamah, 1379, shafi na 111-35.
  26. Misali, duba Muzaffar, Dalai al-Saddeq na Nahj al-Haq, 1422 AH, Mujalladi na 2, shafi na 28; Hosseini Milani, Tasheed al-muraje'at wa-Tafnid al-Makabarat, 1385, shafi na 439.
  27. Ibn Majah, Sunan Ibn Majah, 1430 AH, juzu'i na 5, shafi na 128-130.
  28. Al-Amadi, Al-Ahkam Fi Asul Al-Ahkam, Dar Al-Kitab Al-Alamiya, Mujalladi na 1, shafi na 219.
  29. Ibn Majah, Sunan Ibn Majah, 1430 AH, Mujalladi na 1, shafi na 28-29.
  30. Daylami, al-Firdus bima'athur al-Khattab, 1406 AH, juzu'i na 2, shafi na 63.
  31. Qurbani, Kasurat Girayi Najat Wa Mushkilat Hadisi Firka Najiyeh, Ilahiyat lamba Na 1,
  32. Aghabozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, juzu'i na 1, shafi na 98-99
  33. Hakim, Al-Mufalsal fi Tarikh Al-Najaf, 1427 AH, juzu'i na 5, shafi na 191.
  34. Muhaddith Nouri, Khatama Mustadrak al-Wasail, Stara, juzu'i na 2, shafi.131; Aghabozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, juzu'i na 1, shafi na 98-99.
  35. Sadr, Takmala Amal al-Amal, 1429 AH, juzu'i na 6, shafi na 108.
  36. Misali, duba Muhadith Nouri, Khatama Mustadrak al-Wasail, Stara, Mujalladi na 2, shafi na 131; Aghabozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, juzu'i na 1, shafi na 98-99.
  37. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 292.
  38. Amin, Ayan al-Shia, 1403H, juzu'i na 10, shafi na 146.

Nassoshi

  • Aghabuzur Tehrani, Mohammad Mohsen, al-Dhari'a al-Tsanif al-Shia, Beirut, Dar al-Azwa, 1403H.
  • Aghanouri, Ali, “Hadis Iftirak Ummat; Quotations and Implications", a cikin mujallar Haft Asman, lamba 18, bazara 2013.
  • Al-Amadi, Ali bin Muhammad, Al-Ahkam Fi Asul Al-Ahkam, Beirut, Dar Al-Katb Al-Alamiya, [Bita].
  • Amin, Mohsen, Aayan al-Shi'a, Beirut, Dar-e-Taqqin for the Press, 1403 AH.
  • Baghdadi, Abd al-Qahir, Al-Farq bein Al-Farq da Biyaan al-Farq al-Najiya Menhm, Beirut, Dar al-Jeel-Dar al-Afaq, 1408H.
  • Esfraini, Shahfur bin Taher, Al-Tabasir fi al-Din wa tamyiz firkah najiya an firakul Halikin suka , wanda Mohammad Zahid Kothari ya yi bincike a Beirut, 1408 AH/1988 miladiyya.
  • Ibn Abi Asim, Ahmad bin Amr, Sunnah, Riyadh, bugun Bassem bin Faisal Jubareh, 1419H/1998 Miladiyya.
  • Ibn Hanbal, Ahmad, Musnad, Bincike na Abul Ma'ati Noori, Alam al-Kitab, Beirut, 1419H.
  • Ibn Hazm, Abu Muhammad, Al-Faisal Fi-Millam da Al-Ahwa da Al-Nahl, Beirut, bugun Muhammad Ibrahim Nasr da Abd al-Rahman Umira, 1405H/1985 miladiyya.
  • Ibn Majah, Muhammad Ibn Yazid, Sunan Ibn Majah, Muhammad Fouad Abdul Baqi's research, Beirut, Dar al-Fikr, [Beta].
  • Ibn Tawoos, Sayyid Ali, Al-Taraif Fi Ma'rafah Madhahab Al-Tawaif, Beirut, Ali Ashour, 1420 AH/1999 Miladiyya.
  • Ibn Wazir, Muhammad Ibn Ibrahim, Al-Awasim da Al-Qawasim fi al-Dhabbab on Sunna Abi al-Qasim, Beirut, bugun Shoaib Arnout, 1415 AH/1994 AD.
  • Jafar bin Mansour Aliman, Sirrin Natqa, Mustafa Ghalib, Beirut, ya yi bincike a kansa, 1404H.
  • Tirmizi, Muhammad bin Isa, Sunan al-Tirmidhi, Beirut, Darul Fikr, 1403 AH.