Daƙiƙa:Tawalli
Wannan wani rubutu ne na siffantawa game da wata ma'ana ta fiƙihu, kuma ba za ta iya zama ma'auni ga ayyukan addini ba, domin ayyukan addini sai a koma zuwa ga wasu madogaran na daban. |
| Sanin Allah | |
|---|---|
| Tauhidi | Tabbatar Da Allah • Tauhidi Zati • Tauhidi Sifati • Tauhidi Af'ali • Tauhidi Ibadi • Siffofin Zati • Siffofin Fi'ili |
| Rassa | Tawassuli • Ceto • Tabarruki • Istigasa |
| Adalcin Allah | |
| Husnu Wa Ƙubhu • Bada'u • Amrun Bainal Amraini | |
| Annabta | |
| Ismar Annabawa • Khatamiyyat • Annabin Muslunci • Mu'ujiza• Asalantuwar Kur'ani | |
| Imamanci | |
| Aƙidu | Ismar Annabawa • Wilaya Takwiniyya • Ilmul Gaibi • Khalifatullahi • Gaibar Imam Mahadi • Mahadawiyya • Intizarul Faraj • Bayyana• Raja'a • Imamanci Na Nassi |
| Imaman | Imam Ali • Imam Hassan • Imam Husaini • Imam Sajjad • Imam Baƙir • Imam Sadiƙ • Imam Kazim • Imam Rida • Imam Jawad • Imam Hadi • Imam Askari • Imam Mahadi |
| Ma'ad | |
| Barzahu • Ma'ad Jismani • Hashar • Siraɗi • Taɗayurul Kutub • Mizan | |
| Fitattun Mas'aloli | |
| Ahlil-Baiti • Ma'asumai Goma Sha Huɗu • Karama • Taƙiyya • Marja'iyya • Wilayatul Faƙihi • Imanin Mai Aikata Manyan Zunubai | |
Attawalli (Larabci: التولي) wani Isɗilahi ne na ilimin Aƙida wanda yake yin hannu riga da Tabarri, shi Isɗilahin Tawalli a Shi'a yana nufin soyayyar iyalan gidan Manzo (S.A.W) da biyayya gare su da yarda da wilayarsu, Tawalli da Tabarri kalmomi ne masu kishiyantar juna, kuma suna cikin wajibai masu muhimmanci a addini, kai suna daga cikin mafi muhimmanci wajibai a shari'a[1] kamar yadda suke cikin rukunai da asasi masu muhimmanci na imani.[2])
Ƴanshi'a sun bawa wannan abubuwa guda biyu muhimmanci sosai, wato Attawalli da Attabari, har sai da abin ya kai ga cewa wannan abubuwa guda biyu sharaɗi ne wajan karɓar aikin nagari, ba za a karɓi aiki wani mutum ba matsawar bai yi imani da Tawalli da Attabari ba, riwayoyi masu yawa sun zo kan haka, kuma hakan yana bayyana ƙarara a ziyarar Ashura inda a cikinta aka bawa Tawalli ga waliyan Allah, da Tabarri daga Kafirai da Mushirikai da maƙiya saƙon da Annabi (S.A.W) ya zo da shi da waɗanda suka dasa ƙiyayya ga iyalan gidan Manzo (S.A.W).
Ma'anar Tawalli
Attawali bisa abin da ya zo a litattafan ƴanshi'a; shi ne so da ƙasgatawa da biyayya da yarda da wilayar Allah da manzonshi (S.A.W) da Iyalan gidanshi waɗanda basa aikata saɓo (A.S) wanda bisa al'ada Attabarri yana kishiyantar Tawalli ne a ma'ana.
Attawalli da Wilaya suna nufin biyayya ga waliyyan Allah da mabiyansu waɗanda su shugabanni ne a dukkan al'amura. Tawalli kalma ce da take kan sikelin kalmar taraƙƙa daga babin tafa'alla da aka ciro ta daga "Waliya" a ilimin sarfu, kuma ana amfani da kalmar (Al-Waliyyu)a kan bawa da aka ƴantar da mai gidansa da ya ƴantar shi, da ɗan ƙanin mahaifi da mai taimako da mai hardace tsatso da aboki namiji ko mace, wani lokacin ana ana sanya harafin ha'un a ƙarshen wannan kalma domin bambance mace da namiji, sai ace {Waliyyah), Tawalli yana nufin yarda da shugabanci da soyayya da yarda da shugabancin da gudanarwar wasu. Kalmar tawalli tana nufin so da sallamawa da bin umarnin Allah da Manzon (S.A.W) da iyalan gidanshi masu tsarki. Attawalli shi ne dai wannan soyayya domin Allah da ƙiyayya don Allah da suka zo a ruwayoyi da yawa. kodayaushe Attawalli yana tare da Tabarri daga maƙiya Allah da manzonshi da maƙiya iyalan gidan manzo (S.A.W) . Attawalli da Tabarri suna daga furu'ud-dini (Rassan addini) kuma wajibi ne ta fuskar fiƙihu.
Attawalli A Kur'ani
Daga cikin abin da ƙur'ani mai girma ya ƙarfafa akwai soyayyar Manzo (S.A.W) da iyalan gidanshi aminci ya tabbata a gare su da soyayya a tsakanin muminai, daga cikin ga wannan:
- Allah maɗaukake yana cewa: Ka faɗa musu cewa, bana buƙatar wani lada daga gareku, face soyayya ga makusantana.[3]
Wannan ayar tana nuni da cewa ladan Annabi (S.A.W) kan duk wahalar da ya sha wajan isar da sako, shi ne soyayya ga iyalan gidanshi
- Da faɗar Allah maɗaukake: Majiɓincin al'amarinku kaɗai shi ne Allah da manzonshi da waɗanda suka yi imani kuma suke tsaida sallah kuma suke ba da zakka a yayin da suke a halin ruku'i.[4]
Ita ma wannan ayar tana nuni kan wilayar Allah da Annabi (S.A.W) da ta masu jiɓintar lamarin musulmi(imamai).
- Allah yana cewa: Ya ku waɗanda kuka yi imani, ka da ku sake ku bi mutanen da Allah ya yi fishi kansu, su waɗannan mutanen sun ɗebe tsammani da faruwar ranar lahira kamar yadda kafurai suka ɗebe tsammani daga waɗanda suke cikin kabari.[5]
Wannan aya tana hani ga muminai da ka da su bi waɗanda ba muminai ba.
- Allah yana cewa: Daga cikin mutane akwai waɗanda suke ɗauka abin bauta kwatankwacin Allah kuma suna sonsu kamar yadda suke son Allah, amma waɗanda suka yi imani sun fi su tsananin son Allah.[6]
- Wata ayar ya ƙara cewa: Ya ku waɗanda kuka yi imani ka da ku ɗauki iyayanku da ƴan uwanku abin bi (waliyya ko shugabanni) matsawar sun fifita kafurci kan imani, duk wanda ya bi irin waɗannan mutanen daga cikinku, to lalle su azzalumaini.
Attawalli A Hadisi
Akwai hadisai da yawa da suka zo cikin litattafai na hadisi da na tafsiri kan ƙarfafar biyayya da son Allah da Annabi (S.A.W) da salihanbayi, a hannunmu akwai hadisai da yawa da suke nuni kan son iyalan gidan manzo (S.A.W) masamman ma Imam Ali (A.S) Sayyid Hashim Bahrani ya kawo hadisai 95 daga litattafan Ahlus-Sunna[7] da hadisi 52 daga litattafan Shi'a,[8] duk waɗannan hadisan suna nuni kan falalar imam Ali (A.S) da son shi da sauran imaman da suka fito daga tsatsonshi da mabiyansu.
Imam Rida (A.S) yana cewa, kamalar addini ita ce miƙa wuya da biyayya gare mu da kuma yin tawaye ga maƙiyammu.[9] wilaya tana da tasiri da yawa a duniya da lahira kamar yadda ya zo a ruwayoyi [10] yin zuhudu da yin kwaɗayi kan aiki da tsantseni kan duniya da sha'awar yin ibada da tuba kafin mutuwa da kuzari wajan yin ƙiyamul laili da barin kwaɗayin abin da yake hannun mutane da bin Allah kan abin da ya yi umarni da hani da ƙin son duniya da yin kyauta, amma abin da mutum zai samu a lahira shi ne, ba za a buɗa littafin aikinshi ba kuma ba za a yi mishi hisabi ba, za a ba shi littafinshi a hannun dama, za a rubuta mishi cewa ba zai shiga wuta ba, fuskaarshi za ta yi haske a sanya mishi tufafin aljanna, zai ceci mutum ɗari daga ƴangidansu kuma Allah zai kalle shi da rahama, za a sanya masa kambun aljanna kuma ya shiga aljanna ba tare da hisabi ba.[11]
Hikimar Tawalli
Duk wani mutum da yake da aƙida yana tsara rayuwa bisa wani tsari bayyananne, dole ne a yi mishi hukunci da wannan aƙida da wannan abin da ya sa a gaba kuma zai shatawa kansa layi bisa wannan aƙidar da yake da ita, ba zai taɓa yiyuwa ba ya nuna halin ko unkola ko yin ganda kan wannan abin da ya sa a gaba ba, sakamakon haka ne kuma zai kaishi ga rashin dai-daita mutane kan aƙidinsu ba da tinaninsu da aƙidarsu idan ya zamo abin da suke yi bai dace ba da abin da yake kai ba, saboda haka ne mukaga ƙur'ani yana gargaɗe mutane wajan nuna yarda da abin da waɗanda ba muminai ba suke kai na aƙidarsu da biyayya da soyayya gare su.
Kazalika ƙur'ani yana kira ga ɗan'adam ya zama mai hadafi bayyanne a rayuwarsa ta yau da kullin, shi ne mutum kodai ya zama cikin masu imani ko cikin kafirai da munafunci, wannan wani abu ne da duk wani mai hakanli yake iya fahimta, saboda haka muke cewa dole ya zamo mutum yana da wani ma'auni na babbance gaskiya da ƙarya, da imani da nifaƙi, a nan muke cewa Tawalli da Tabbari suna Sanya mutum ya zama mai karkata ga gaskiya da rashin ɗaukan mataki tsakiya kana bin da ya shafi addini, dole ne ya zamo mutum a irin wannan yanayin ya ɗauki mataki kan abin da ya shafi addin kuma mataki bayyanan ne, hadda ma abin da ya shafi duniya da ɗaukan mataki mai inganci bisa dogaro kan Tawalli da Tabbari.
Tawalli Da Tabarri
Idan mutum ya yi tinani kan aikin Tawalli zai gano cewa yana lazimtar Tabarri baya rabuwa da shi, wannan yana nufin cewa wajibi ne ga mutum mumini ya yi biyayya ga iyalan gidan Manzo (S.A.W) kuma tilas ya yi bara'a daga maƙiyansu, amma fa hakan baya nufin kafurta sauran musulmi mabiya mazhabobin Muslunci, waɗanda ba su yi imani da Tawalli da Tabarri, saboda mafi yawancinsu imamanci ba ginshiƙi bace ba a gurinsu, ita imama kawai ginshiƙi ce a mazahabin Shi'anci.
Shahid Muɗahhari ya yi nuni kan cewa, biyayya da so bas a nufin mutum ya sauka daga kan abin da yake tabbatace da bari aƙidar da mutum yake kai, domin ya zauna da dukkan mutane lafiya tare da cewa aƙidarsu ta saɓawa tashi, yana cewa su mutane ba sa yin tinani dukkansu ta hanya guda ɗaya kuma basa haɗewa wajan jin abin da suke ji, kazalika ba sa haɗuwa su so abu guda ɗaya, cikin mutane akwai adili da azzalimi da mutuman kirki kazalika cikin al'umma akwai azzalumi a adili da fasiƙi, wani abu ne wanda ba zai yiyuwa ba irin waɗannan mutanen su haɗu kan son wani mutum wanda yake ƙoƙari domin cimma wani hadafi wanda ba kowa ba ne yake son shi, to dole ne a sami karo da wasu mutane da ba sa son hakan.
Mutum ɗaya ne cikin al'umma yake iya samun soyayyar dukkan mutane duk da bambance-bambancensu wanda shi ne maƙaryaci mai yaudara wanda yake nunawa kowana mutum abin da yake so ya gani ko ya ji, amma idan mutum ya kasance mai fuska ɗaya tabbas wasu mutane za su so shi kuma za su zama abokanshi, a dai-dai lokacin da wasu za su yi adawa da shi, saboda haka waɗanda yake yin abin da suke so, za su kasance tare da shi, amma waɗanda suka yi saɓani da shi za su yaƙe shi. Kamar wasu kiristoci ne da suke faɗar soyayya a kansu da kira zuwa ga addininsu bisa soyayya, kuma suna cewa shi mutum cikakke bashi da komai sai soyayya, babu komai a duniya sai soyayya, kai wai soyayya ce za ta iya jan hankalin mutum, da wasu daga cikin Mabiya addini Hindu suma suna da wannan ra'ayi. Abin da yake jan hankalin mutum a cikin addini kiristanci da addinin Hindu shi ne soyayya. suna cewa mutum ya kamata ya karkata zuwa kowane abu kuma ya nuna mishi soyayya, misali idan muka so kowa, to babu abin da zai hana kowa ya so mu, daga cikin waɗan da za su so mu harda mutanen banza, sakamakon ba su ga wani abu a gurinmu ba sai soyayya. Ya kamata waɗannan mutanen su sani cewa soyayya kawai ba ta wadatarwa, domin ya kamata ace yana tafiya kan wani abu bayyanan ne, ita wannan soyayyar ya kamata a ce an gwamata da gaskiya da haƙiƙa, hakan zai sa a tafiyar da komai bisa wani tsari sannan ne, to idan mutum ya zamo haka, to abin zai haifar mashi da maƙiya shin ya sani ko bai sani ba, kuma a ƙarshe hakan ne zai kai ga wasu mutanen su yi hamayya da abin da mutum ya zo da shi.
Soyayyar da alƙur'ani ya zo da ita bata nufin mu yi mu'amala da kowane mutum bisa son zuciyarshi da abin da yake so ba, ba komai muke yi ba sai abin da zai jawo hankalinshi zuwa gare mu. Soyayya ba ta nufin mubar mutum ya yi abin da ya so, kuma mu ƙarfafe shi kan hakan, a a wannan ba soyayya bace ba, a a wannan rashin gaskiya ce, ita soyayya tana tare da gaskiya kuma tana haifar da alkairi.[12]
Matsayin Tawalli A Aƙidar Shi'a
A aƙidar Shi'a anan ganin Tawalli a matsayin wani sakamako wanda ya samu sakamakon soyayyar iyalan gidan manzo (S.A.W), kai shi fa Tawalli yana cikin ginshiƙi da asasi a gun ƴanshi'a wanda aka yi magana kanshi wajan bincike kan ɓangarori da yawa kamar a fiƙihu da aƙida da aklaƙ da sauransu, kai abun ya kai cewa tawalli da tabarri sharaɗi ne guda biyu domin karɓar aikin mutum mai kyau, wannan kuma shi ne abin da ruwayoyi da yawa suka yi nuni kanshi, inda wasu ruwayoyin suka yi la'akarin tabarri da tawalli a matsayin wani reshe daga cikin rassan addini kuma wajibi ne a shari'a.[13] inda ake faɗawa wanda ya kusa mutuwa da kuma mamaci[14] tawalli da tabarri suna cikin mabuɗai na sanin aƙidar shi'a, abin nufi soyayyar iyalan gidan Manzo (S.A.W) da kuma tawaiye daga maƙiyansu, wannan sharuɗɗa ne guda biyu na karɓar aiki mai kyau ba tare dasu ba babu wani aiki da za'a karɓa.
Tawalli da tabarri suna cikin rassan (Furud-dini) kuma a fiƙihu wajibi ne,[15] to wannan ya nuna cewa waɗannan abubuwan suna da muhimmanci a gun ƴanshi'a.[16]
Abin da Ake Kira Tawalli
Ta yiwu wasu suga cewa abin da ake nufi da miƙa wuya ga iyalan gida manzo (S.A.W) shi ne mutum ya so su, sai dai cewa wannan fahimtar kuskure ce, abin da ake nufi da tawalli shi ne yin imani da imamancinsu da fifita su kan kowa da yin imani cewa su ne halifofin Manzo (S.A.W)[17] kuma a taƙaice mu ce tawalli ya ƙunshi abubuwa kamar haka:
- Yarda da wilayar Allah da Annabi (S.A.W) da imamanci iyalan (A.S) gidan Manzo (S.A.W)
- Son Allah da dukkan annabawa (A.S) da imamai da Sayyida Zahra (A.S)
- Son muminai da waɗanda suke kan hanyar Allah.
Tawalli Da Tabarri A Cikin Ziyarar Ashura
Akwai jumlar da ta zo cikin ziyarar Ashura wacca take nuni kan tawalli da tabarri, ga wasu yankuna daga ciki:
یا اَباعَبْدِاللهِ اِنّی سِلْمٌ لِمَنْ سالَمَکمْ وَ حَرْبٌ لِمَنْ حارَبَکمْ اِلی یوْمِ الْقِیامَةِ؛
Ya Aba Abdullah ni mai son aminci ne ga wanda ya so aminci tare da kai, kuma ni mai son yaƙi ne ga wanda ya so yaƙi tare da kai.
یا اَبا عَبْدِاللهِ اِنّی اَتَقَرَّبُ اِلی اللهِ وَ اِلیٰ رَسُولِهِ، وَ اِلیٰ امیرِالْمُؤْمِنینَ وَ اِلیٰ فاطِمَةَ، وَاِلَی الْحَسَنِ وَ اِلَیک بِمُوالاتِک، وَ بِالْبَرائَةِ مِمَّنْ قاتَلَک وَ نَصَبَ لَک الْحَرْبَ.
• Ya aba Abdullah haƙiƙa ni ina neman kusanci ga Allah da Manzonshi da Amirul Mu'uminin da Faɗima da Hassan da kanka da biyayyarka, kuma ina tawaye da bara'a daga waɗanda suka yaƙe ka kuma daga waɗanda suka assasa ƙiyayarka.
Bayanin kula
- ↑ Al-Tabrasi, Mishkat al-Anwar fi Gurar al-Akhbar, shafi 125.
- ↑ "Al‑Bahrani, Al‑Hadā’iq al‑Nāḍira, Juzu’i na 18, shafi na 423."
- ↑ Aya ta 23 daga suratul Shūrā
- ↑ Aya ta 55 daga suratul Mā’ida
- ↑ Aya ta 13 daga suratul Mumtaḥina
- ↑ Aya ta 165 daga suratul Baqarah
- ↑ “Al‑Bahrani, Ghayat al‑Marām, Juzu’i na 6, shafi na 46 zuwa 71.”
- ↑ “Al‑Bahrani, Ghayat al‑Marām, Juzu’i na 6, shafi na 46 zuwa 72-91”
- ↑ “Al‑Majlisī, Biḥār al‑Anwār, Juzu’i na 27, shafi na 58.”
- ↑ “Al‑Majlisī, Biḥār al‑Anwār, Juzu’i na 27, shafi na 74-78.”
- ↑ “Al‑Majlisī, Biḥār al‑Anwār, Juzu’i na 27, shafuka 78 zuwa 79, da kuma Juzu’i na 26, shafi na 158.”
- ↑ “Ash‑Shahīd Muṭahharī, Jādhbatu wa Dāfi‘atu ‘Alī ( عليه السلام ), shafi na 145. Kuma duba: Ash‑Shahīd Muṭahharī, Imām ‘Alī ( عليه السلام ) Fi ƙuwwaihil Jaziba Wa Dafi'a, Tarjameh Ja‘far Ṣādiq al‑Khalīlī, a gabatarwar littafin.”
- ↑ “Al‑Ḥurr al‑‘Āmilī, Wasā’il ash‑Shī‘a, Juzu’i na 16, shafi na 176.”
- ↑ “Kāshif al‑Ghithā’, Kashf al‑Ghithā’, Juzu’i na 2, shafi na 251.”
- ↑ “Al‑Ḥurr al‑‘Āmilī, Wasā’il ash‑Shī‘a, Juzu’i na 16, shafi na 176.”
- ↑ “Kāshif al‑Ghithā’, Kitāb Kashf al‑Ghithā’, Juzu’i na 2, shafi na 251.”
- ↑ “Al‑Bahrānī, Kitāb ash‑Shihāb ath‑Thāqib fī Bayān Ma‘nā an‑Nāṣib, shafi na 144.”
Sadarwa Ta Waje
Nassoshi
- Al‑Bahrānī, Hāshim, Gāyat al‑Marām wa Ḥujjat al‑Khiṣām fī Ta‘yīn al‑Imām, bita: ‘Alī ‘Āshūr, Bayrut, Ma’aikatar Tarihin Larabawa, bugu na 1, 1422 H/2001 M.
- Al‑Bahrānī, Yūsuf, Al‑Ḥadā’iq an‑Nāḍira, Qum, Ma’aikatar Buga Littattafan Musulunci, 1408 H.
- Al‑Bahrānī, Yūsuf, Ash‑Shihāb ath‑Thāqib fī Bayān Ma‘nā an‑Nāṣib, bita: Mahdī Rajā’ī, Qum, bugu na 1, 1419 H.
- Al‑Kur’ani Mai Tsarki.
- Al‑Majlisī, Muḥammad Bāqir, Biḥār al‑Anwār, Bayrut, Mu’assasat al‑Wafā’, 1403 H/1983 M.
- Al‑Muṭahharī, Murtaḍā, Imām ‘Alī (A.S) a cikin ƙarfinsa na ja da turawa, fassara: Ja‘far Ṣādiq al‑Khalīlī, Bayrut, Mu’assasat al‑Ba‘tha, bugu na 2, 1412 H/1992 M.
- Al‑Ḥurr al‑‘Āmilī, Muḥammad bn al‑Ḥasan, Wasā’il ash‑Shī‘a, Qum, Ma’aikatar Āl al‑Bayt (A.S) don farfaɗo da turāth, 1410 H.
- Aṭ‑Ṭabrisī, ‘Alī bn al‑Ḥasan, Mishkāt al‑Anwār fī Ghurar al‑Akhbār, bita: Mahdī Hūshmand, Qum, Dār al‑Ḥadīth, bugu na 1, 1418 H.
- Kāshif al‑Ghithā’, Ja‘far, Kashf al‑Ghithā’, Mashhad, Ofishin Yaɗa Labaran