Jump to content

Daƙiƙa:Suratut Tahrim

Daga wikishia
Suratut Tahrim
Suratut Tahrim
Lambar Sura66
Juzu'i28
Jerantuwa Ta Sauka108
Adadin Ayoyi12
Adadin Kalmomi254
Adadin Haruffa1105


Suratut Tahrim ita ce sura 66 cikin juzi'i na 28 a Alƙur'ani, wannan sura ta sauka a Madina, sunanta ya samo asali daga aya ta farkonta, wannan sura tana magana kan labarin Annabi (S.A.W) tare da wasu daga matansa yayin da ya haramtawa kanshi wasu nau'o'in abinci, kuma wannan sura ta ƙunshi misali guda masu kyau daga wasy mata, sune Asiya matar Fir'auna da Maryam Ƴar Imran da misali guda biyu marar kyau, sune na matar Nuhu da Luɗ.

Daga cikin ayoyinta mashahurai akwai faɗar Allah maɗaukaki, (Ya ku waɗanda kuka yi Imani ku kiyaye kanku da iyalanku daga wuta wacce makamashinta sune mutane da duwatsu). Wannan aya tana magana da muminai kan haƙuri wajan bautar Allah da kuma haƙuri kan barin saɓo da kula da iyali wajan koyar da su abin da ya wajabta a kansu da ƙarfafarsu kan aikata alheri da hana su bin son zuciya da aikata abu marar kyau.

An rawaito ruwayoyi da yawa kan falalar karanta wannan sura daga ciki an rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta Suratut Tahrim, Allah ya bashi tuba na gaskiya.

Sanya Suna Da Ayoyi

An kirata da Suratut Tahrim saboda farkonta shi ne faɗar (Ya kai Annabi! Me ya sa kake haramta abin da Allah Ya halatta maka?)[1] inda surar ta fara da zargin Annabi (S.A.W) tare da nuna so da tausayi a kansa, yayin da Annabi (S.A.W) ya hana kanshi cin abinci mai kyau da haramtawa kanshi jin daɗi saboda neman yardar ɗaya daga cikin matanshi[2] kazalika wannan sura ana kiranta Suratul Mutaharrim da Suratul Lima Tuharrim da Suratun Nabiyyi.[3] Ayoyinta 12 kalmomi 254 da haruffa 1105, ta fuskacin yawa kuma tana cikin surori Mufassalat, abin nufi surar da take da ayoyi da yawa, amma kuma gajera[4] sannan tana cikin Mumtahinat[5]

Tsarin Da Aka Saukar Da Ita

Wannan sura ta sauka ne a Madina,[6] amma a jerin sauka ita ce aya sura 108, amma a jerin na yanzu cikin Alƙur'ani tana cikin juzi'i na 28 kuma ita ce ta 66 cikin surorin Alƙur'ani[7]

Asbabun Nuzul

Maganganu da dama aka ambata cikin litattafan tafsiri kan dalilin saukar ayoyin farko na wannan sura, amma mafi shahara da dacewa sune waɗannan: Manzon Allah (S.A.W) ya kasance a lokacin da yake tafiya gurin matarshi Zainab Ƴar Jahash, tana kawo mishi zuma wacce ta tanada dominshi, yayin da A'isha ta ji labarin hakan, sai abin ya yi mata zafi, sai ta haɗa baki da ɗaya daga cikin matan Annabi (S.A.W) wato Hafsa, domin su tambayi Manzon Allah( S.A.W) a yayin da ya kusanci ɗaya daga cikin matansa cewa, shin ka sha Sumgul Magafir wani nau'i ne na abu ne mai danƙo wanda ake samu daga bishiyoyi a ƙasar Hijaz, wanda yake ɗauke da wani ƙanshi marar daɗi.

To sai Hafsa ta tambaye shi wannan tambayar, sai Annabi (S.A.W) ya ba ta amsa cewa shi bai sha Sumgul Magafir ba, amma dai ya sha zuma, saboda haka sai Manzon Allah ya yi rantsuwa cewa ba zai sake shan wannan zumar ba,tsoran ka da ƙudan zuma ya je ya sha ko ya ci wannan sumgu, sai Annabi (S.A.W) ya ja mata kunne cewa kada ta faɗawa kowa domin kada abin ya yaɗu cewa Annabi (S.A.W) ya haramtawa kanshi abincin da yake halal ne, domin kada mutane su yi koyi da shi, su haramtawa kansu abin da yake halal ne, ko kuma tsoran kada Zainab ta ji domin abin zai mata ciwo sosai, amma abin ban takaici sai da ta yaɗa wannan sirri, saboda haka Annabi (S.A.W) ya ji zafin wannan abu sosai, kawai sai wannan ayoyi suka sauka, domin bayanin abun da ya faru, kuma domin hana sake faruwar abun a gaba a gidan Annabi (S.A.W).[8]

Ma'anar Wasu Daga Kalmominta

Ma'anar kalmomin da suka fi muhimmmanci a wannan sura: (Tuharrimu): Haramtawa kai ko hana kai (Tahilla): Halasta abu ta hanyar aikata kaffara (Tazahara): Taimakawa juna domin cutar da Annabi (S.A.W). (Ƙanitatun): Mata masu bin Allah (Sa'ihatun): Masu yin azumi ko masu yin hijira[9]

Abun Ciki

A taƙaice wannan sura ta ƙunshi abubuwa guda huɗu; Wannan sura tana bada labarin Annabi (S.A.W) tsakaninshi da wasu daga cikin matanshi, yayin da ya haramta wasu nau'uka na abinci ga kanshi, sai aya 1-5 ta sauka tana zargi ga matan Annabi (S.A.W). Wannan sura tana magana da muminai kan tarbiyya da kulawa da iyali da tilascin yin tuba daga barin zunubi, daga 6-8. Aya ta 9 tana magana da Annabi (S.A.W) kan yaƙar kafirai da munafukai. Daga aya 10-12 suna bayani kan gungu biyu na mata na gari, waɗannan mata sune Sayyida Maryam da Asiya matar Fir'auna, da kuma mata gungu na biyu sune matar Nuhu (A.S) da matar Luɗ (A.S) kuma Allah yana gargaɗe ga wannan gungu na biyu da kiransu da su yi koyi da gungu na farko.[10]

Shahararrun Ayoyi

Daga cikin ayoyinta mashahurai akwai faɗar Allah maɗaukaki,(Ya ku waɗanda kuka yi Imani ku kiyaye kanku da iyalanku daga wuta wacce makamashinta sune mutane da duwatsu).[12] ya zo cikin litattafan tafsiri cewa ayar tana magana ne da muminai kan haƙuri wajan bautar Allah da kuma haƙuri kan barin saɓo da kula da iyali wajan koyar da su abin da ya wajabta a kansu da ƙarfafarsu kan aikata alheri da hana su bin son zuciya da aikata abu marar kyau, da kwaɗaitar das u kan aikata alheri.[13]

Faloli Da Fa'idoji

Akwai falalo da yawa kan karanta wannan sura, ga kaɗan daga ciki;

  • An rawaito daga Ananbi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta Suratut Tahrim, Allah zai azurta shi da tuba na gaskiya[14]
  • An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) ya ce duk wanda ya karanta Suratuɗ Ɗalaƙ da Tahrim cikin sallar farilla, Allah zai kare shi daga tsoro da baƙin ciki a ranar alƙiyama, kuma ko ya shiga wuta Allah zai mishi afuwa, sannan zai shigar da shi aljanna saboda karantasu da dawwama da karantasu, saboda surori ne na annabi(S.A.W).[15]

Akwai abin da ya keɓanta da wannan sura da ya zo a ruwayoyi da yawa, ga wasu daga ciki:

  • An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) duk wanda ya karanta wannan sura ga marar lafiya, to zai sami sauƙi, duk wanda ya karanta ta ga wanda jikinshi yake rawa, to zai daina, kuma duk wanda ya karanta ta ga wanda ya suma, to zai farfaɗo, idan aka karantata ga wanda ya kasa bacci da dare, to za ta sa shi bacci, idan mutuman da yake da bashi da yawa ya dawwama yana karanta ta, to zai biya bashi duk abin da ake binshi da yardar Allah[16]

Bayanin kula

  1. ↑ Suratut Tahrim; aya 1.
  2. ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, shafi na 191.
  3. ↑ Alusi, Ruhul Ma'ani, juzu'i na 28, shafi na 472.
  4. ↑ Khurramshahi, Mausu'atul Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, shafi na 1257.
  5. ↑ Ma'arifat, At-Tamhid, juzu'i na 1, shafi na 313.
  6. ↑ Ɗusi, Tafsir At-Tibyan, juzu'i na 11, shafi na 266; Fakhrir Razi, At-Tafisrul Kabir, juzu'u na 30, shafi na 37.
  7. ↑ Ma'arifat, At-Tamhid, juzu'i na 2, shafi na 168.
  8. ↑ Ɗusi, Tafsir At-Tibyan, juzu'i na 11, shafi na 266, Fakhrur Razi, At-Tafsirul Kabir, juzu'i na 30, shafi na 37; Zamakhshari, Tafsir Al-Kashshaf, juzu'i na 4, shafi na 1657, Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 19, shafi na 352; Alusi, Ruhul Ma'ani, juzu'i na 29, shafi na 472.
  9. ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 16, shafi na 193-210.
  10. ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 18, shafi na 278.
  11. ↑ Khamagar, Sakhtare Surahaye Qur'an Karim.
  12. ↑ Suratul Tahrim, aya ta 6.
  13. ↑ Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, juzu'i na 10, shafi na 46.
  14. ↑ Zamakhshari, Tafsir Al-Kashshaf, juzu'i na 4, shafi na 1664.
  15. ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 18, shafi na 278.
  16. ↑ Bahrani, Al-Burhan, juzu'i na 9, shafi na 325.

Nassoshi

  • Qur'an Karim.
  • Alusi, Shihab, Ruhul Ma'ani fi Tafsiril Qur'anil Azim was Sab'ul Masani, Bairut, Lebanon, Daru Ihya'it Turasil Arabi, bugun farko, 1421H.
  • Bahrani, Hashim Bin Sulaiman, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Bairut, Lebanon, Daru Ihya'it Turasil Arabi, bugun farko, 1429H.
  • Fakhrur Razi, Muhammad Bin Umar, At-Tafsirul Kabir, Beirut, Lebanon, Darul Kutubil Ilmiyya, bugun na huɗu, 1434H.
  • Khurramshahi, Bahauddin, Mausu'atul Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, Iran, Tehran, Cibiyar Al-Asdiƙa, 1377Sh.
  • Ma'arifat, Muhammad Hadi, At-Tamhid fi Ulumil Qur'an, Qom, Iran, Zawil Qurba, bugun farko, 1428H.
  • Ma'arifat, Muhammad Hadi, Tadrisu al-Ulumil Qur'aniyya, fassarar Abu Muhammad Faƙili, Daru Nashrid Da'watil Islamiyya, 1371Sh
  • Makarim Shirazi, Nasir, Al-Amsal Fi Tafsiri Kitabil-Lahil Munzal, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Amira, bugun na biyu, 1430H.
  • Musawi, Abbas Bin Ali, Al-Wadihu Fit Tafsir, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Ghadir, bugun farko, 1433H.
  • Zamakhshari, Mahmud Bin Umar, Al-Kashshaf, Beirut, Lebanon, Dar Sadir, bugun farko, 1431H.
  • Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husain, Almizan fi Tafsiril Qur'an, Qom, Iran, Darul Al-Mujtaba, bugun farko, 1430H.
  • Ɗabrisi, Fadlu Bin Hassan, Majma'ul Bayan, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Amira, bugun farko, 1430H.
  • Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, At-Tibyan fi Tafsiril Qur'an, Qom, Iran, Cibiayar Annashril Islami, bugun farko, 1431H.