Daƙiƙa:Suratut Tagabun
Suratul Suratut Tagabun Suratul | |
| Lambar Sura | 64 |
|---|---|
| Juzu'i | 28 |
| Jerantuwa Ta Sauka | 110 |
| Adadin Ayoyi | 18 |
| Adadin Kalmomi | 242 |
| Adadin Haruffa | 1091 |
| Makkiya/Madaniyya | Madina |
Suratut Tagabun sura ce ta 64 cikin juzi'i na 29 a Alƙur'ani, wannan sura an sauke ta a Madina, an sami sunanta daga aya ta 9, «يوم التغابن» tana nufin ranar alƙiyama, ranar da wata ƙungiya za ta yi asara, yayin da wata ƙungiya kuma za ta samu nasara, wannan sura tana magana kan kaɗaita Allah da siffofinshi da yin biyayya ga Annabi (S.A.W), kazalika tana magana kan ranar tashin alƙiyama, tana kwaɗaitar da mutane da su lura da ayyukansu na zahiri dana baɗini.
Daga cikin ayoyinta da suka shahara akwai faɗar Allah maɗaukaki (Dukiyoyinku da ƴaƴanku ba komai bane face fitina, amma fa a gun Allah akwai lada mai girma). Inda malaman tafsiri suka ce: Lallai, duk abin da zuciya ta kamu da tsananin sonsa, to, fitina ne, ko dukiya ce, ko ƴaƴa, ko mata ko wani matsayi, da faɗar Allah: (Idan kuka bai wa Allah rance mai kyau, zai ninka muku ladansa), wannan aya tana ƙarfafa muhimmmanci infaƙi (taimako) domin Allah, kuma tana tana koɗaitarwa kan aikata shi.
Akwai ruwayoyi da yawa da suka zo kan falalar karanta Suratut Tagabun, daga cikinsu an rawaito daga Annabi (S.A.W) duk wanda ya karanta Suratut Tagabun, Allah zai hana shi yin mutuwar Fuju'a ko mutuwar faɗ ɗaya.
Sanya Suna Da Ayoyinta
Ana kirann wannan sura da Tagabun saboda faɗar Allah maɗaukake cikin aya ta 6 a wannan sura, (Ranar da zai tara ku domin ranar taruwa; wannan ita ce ranar asara da nadama), wannan rana ita ce ake kiranta da Tagabun wato ranar alƙiyama,[1] ƙila koma ance Tagabun shi ne riƙo da sharri da mantawa da alheri ko kuma akasi, shi mumini ya bar rabanshi na duniya, amma ya karɓi rabonshi na lahira, sai ya bar abin da yake sharri ne gare shi, sai ya ɗauki abin da yake alheri ne gare shi,saboda haka ne mumini ya zamo mutuman mai samun riba, amma shi kafiri ya bar rabonshi na lahira, sai ya karɓi rabonshi na duniya, sai ya bar alheri, ya ɗauki sharri, saboda haka ya zamo wanda aka yi wa asara,A wannan rana ne za a bayyana wanda ya ci riba da wanda aka yi wa asara[2] Ance ƴan aljanna sun daki hancin ƴan wuta.[3]
Ayoyin wannan sura 18 tana da kalmomi 242 haruffa 1091. Itama wannan sura tana cikin surori Mufassalat, sune sororin da suke ɗauke da ayoyi da yawa amma basu da tsayi[4] kuma cikin surori Mumtahinat[5]
Tsarin Da Aka Saukar Da Ita
Wannan sura ta Tagabun ta sauka a Madina[6] wasu kuma sun ce wataƙila ta sauka ne a Makka[7] amma a jerin sauka ita ce 110 da ta sauka ga Annabi (S.A.W) amma yanzu a cikin Alƙur'ani ita ce 64 cikin juzi'i na 28 a surorin Alƙur'ani[8]
Ma'anonin Wasu Daga Cikin Kalmominta
Ma'anoni masu muhimmanci na wasu kalmominta: (At-Tagabun): Sayan abu daga ma'abocinsa ƙasa da farashinsa. (Fitnatun): Jarrabawa da ibtila'i (Yuƙa): Al-Wiƙaya, kiyaye abu daga dukkan abin da zai cutar dashi. (Shuhha): Matsananciyar rowa, abin nufi daga «يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ» shi ne wanda yake iya danne rowarshi da kwaɗayi.[9]
Abun Ciki
A taƙaice wannan sura tana ɗauke da abubuwa guda shida;
- Tana Magana kan Tauhidi da siffofin da ayyukan Allah.
- Kwaɗaitar da mutane kan kula da aikinsu a zahiri da baɗini, da kada su gafala da lura da aiyukan mutanen da suka gabace su.
- Wannan sura tana magana kan tashin alƙiyama, cewa ita wata rana ce da za a daki hanci wasu mutane, wasu kuma za su rabauta.
- Wannan sura tana bayani kan biyayyar Annabi (S.A.W) da tabbatar da ƙa'idojin annabta
- Wannan sura tana bayani kan yin taimako domin Allah, da jan hankali cewa kada mutum ya yaudari kanshi da kuɗi ko ƴaƴa ko mata, da duk wani abu da zai hana mutum zuwa ga Allah maɗaukaki.[10]
Shahararrun Ayoyi
- Faɗar Allah maɗaukaki: (Dukiyoyinku da ƴaƴanku ba komai bane face fitina, amma fa a gun Allah akwai lada mai girma).[12] malaman tafsiri sune duk wani abu da mutum zai so da yawa, kuma zai hana mutum aikata abun da ya wajabta ya aikata, na duniya da lahira to fitina ne, shin wannan abu kuɗi ne ko ɗa ko mace ko matsayi, babu bambanci, amma abin da ya sa Allah ya ambaci kuɗi da ƴaƴa; Saboda sune babbar fitina, duk yadda mutum ya girmama jin daɗin duniya, to fa abin da yake gun Allah shi ne alheri kuma mafi wanzuwa.[13]
- Faɗar Allah maɗaukaki: (Idan kuka bai wa Allah rance mai kyau, zai ninka muku ladansa).[14] ya zo cikin litattafan tafsiri, abin da ake nufi da bawa Allah rance shi ne, yin taimako domin Allah, sai Allah ya kirashi da ba shi rance, saboda haka ake kiran kuɗin da aka bayar da rance mai kyau, saboda a kwaɗaitar da mutane, sakamakon wannan rance shi ne sakamako mai kyau a duniya da lahira.[15]
Falaloli Da Fa'idoji
Akwai falaloli da yawa kan karanta wannan sura, ga wasu daga ciki; An rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta :Suratut Tagabun, Allah zai hana shi yin mutuwar Fuju'a.[16] An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) duk wanda ya karanta Suratut Tagabun a cikin sallah ta farilla, za ta kasance mai cetonsa a ranar alƙiyama, kuma ta kasance mai bayar da shaidar gaskiya a wurin wanda ya amince da shaidarta. Sannan ba za ta rabu da shi ba har sai ya shiga Aljanna[17] An rawaito daga cikin abin da ya keɓanta da wannan sura, akwai; An rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karantata ya shiga gurin sarki ko shugaba azzalumi, to Allah zai kiyayeshi daga sharrinshi.[18]
Bayanin kula
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 16, shafi na 142-152.
- ↑ Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, juzu'i na 10, shafi na 24.
- ↑ Alusi, Ruhul Ma'ani, juzu'i na 28, shafi na 441.
- ↑ Khurramshahi, Mausu'atul Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, juzu'i na 2, shafi na 1256.
- ↑ Ma'arifat, At-Tamhid, juzu'i na 1, shafi na 313.
- ↑ Ɗusi, At-Tibyan, juzu'i na 11, shafi na 235.
- ↑ Fakhrur Razi, At-Tafsirul Kabir, juzu'i na 30, shafi na 19.
- ↑ Ma'arifat, Ulum Qur'an, juzu'i na 2, shafi na 168.
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 16, shafi na 148- 155.
- ↑ Makarim Shirazi,Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 18, shafi na 239.
- ↑ Khamagar, Sakhtare Surahaye Qur'an Karim.
- ↑ Suratut Tagabun aya ta 15.
- ↑ Mugniyya, Tafsirul Kashshaf, juzu'i na 7, shafi na 344.
- ↑ Suratut Tagabun aya ta 17.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 19, shafi na 322.
- ↑ Zamakhshari,Tafsirul Kashshaf, juzu'i na 4, shafi na 1649.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami, juzu'i na 3, shafi na 571.
- ↑ Bahrani, Tafsirul Burhan, juzu'i na 9, shafi na 307.
Nassoshi
- Qur'an Karim
- Alusi, Shahab, Ruhul Ma'ani fi Tafsiril Kur'anil Azim was Sab'ul Masani, Beirut, Lebanon, Dar Ihya'ut Turas al-Arabi, bugu na 1, 1421H.
- Bahrani, Hashim bin Sulaiman, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Beirut, Lebanon, Dar Ihya'ut Turas al-Arabi, bugu na 1, 1429H.
- Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husain, Almizan fi Tafsiril Qur'an, Qum, Iran, Darul Al-Mujtaba, bugu na 1, 1430H.
- Ɗabrisi, Fadl Bin Hassan, Tafsir Jawami'ul Jami', Qum, Iran, Cibiyar Nashril Islami ta Jamia'atul Mudarrisin, bugu na 2, 1430H.
- Ɗabrisi, Fadl Bin Hassan, Majma'ul Bayan, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Amira, bugu na 1, 1430H.
- Ɗusi, Muhammad bin Hasan, At-Tibyan fi Tafsiril Qur'an, Qum, Iran, Cibiyar Nashril Islami, bugu na 1, 1431H.
- Fakhrur Razi, Muhammad bin Umar, At-Tafsirul Kabir, Beirut, Lebanon, Darul Kutubil Ilmiyya, bugu na 4, 1434H.
- Khurramshahi, Bahaud-Din, Mausu'atul Qur'an Wad Dirasatil Qur'aniyya, Iran, Tehran, Al-Asdiƙa, 1377Sh.
- Musawi, Abbas bin Ali, Al-Wadihu Fit Tafsir, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Ghadir, bugu na 1, 1433H.
- Ma'arifat, Muhammad Hadi, Tadris Al-Ulum al-Qur'aniyya, fassarar Abu Muhammad Faƙili, Dar Nashr Ad-Da'awatul Islamiyya, 1371Sh.
- Ma'arifat, Muhammad Hadi, At-Tamhid fi Ulumil Qur'an, Qum, Iran, Dhawil Qurba, bugu na 1, 1428H.
- Mugniyya, Muhammad Jawad, Tafsirul Kashif, Beirut, Lebanon, Darul Anwar, bugu na 4, ba a ambaci shekarar bugawa ba.
- Makarim Shirazi, Nasir, Al-Amsal fi Tafsiri Kitabillah al-Munzal, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Amira, bugu na 2,1430H.
- Zamakhshari, Mahmud Bin Umar, Al-Kashshaf, Beirut, Lebanon, Dar Sadir, bugu na 1, 1431H.