Daƙiƙa:Suratud Dukhan
Zukhruf Suratud Dukhan Jasiya | |
| Lambar Sura | 44 |
|---|---|
| Juzu'i | 25 |
| Jerantuwa Ta Sauka | 64 |
| Adadin Ayoyi | 59 |
| Adadin Kalmomi | 346 |
| Adadin Haruffa | 1475 |
| Makkiya/Madaniyya | Makkiyya |
Suratud Dukhan sura ce ta 44 cikin juzu'i na 25 a Alƙur'ani mai girma kuma sura ce da ta sauka a Makka, sunanta an same shi daga aya ta goma, wannan sura tana magana kan girman Alƙur'ani, bayanin saukarshi a daren Lailatul ƙadri, sannan tana magana kan Tauhidi da bayyana girman Allah maɗaukaki, kuma tana bayani kan makomar kafirai da ƙarshansu, kazalika wannan sura tana bayan ikan Annabi Musa (A.S) da tarihin Banu Isra'il tare da Fir'auna da mutanenshi, da bayani kan ranar Alƙiyama da bayani kan manufar da hadafin yin halitta.
Ruwayoyi da yawa sun zo kan falalar karanta ta, daga cikin akwai abin da aka rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta ta a daren Juma'a, Allah zai gafarta mishi zunubanshi, kuma an ambaci cewa ana karantata cikin ayyukan daren 23 ga watan Ramadan wanda shi ɗaya ne daga cikin dararan Lailatul ƙadri.
Sunanta Da Ayoyinta
Wannan sura ana kiranta da Dukhan saboda Allah ya sanya Dukhan wato hayaƙi ya zamo wata aya ta tsoratarwa ga Kafirai, kamar yadda ya zo cikin aya ta 10, ma'anarta (Ka jira ko ka yi dakon ranar da sama za ta zo da wani hayaƙi bayyananne)[1] ayoyinta 59 kalmominta 346 haruffa 1475,[2] ana la'akarinta a matsayin surorin Hawamim, abin nufin surorin da suka fara Hamin.[3]
Tsarin Da Aka Saukar Da Ita
Wannan sura ta sauka a Makka ne[4] amma a jerin sauka ita ce sura ta 64, amma yanzu a cikin surorin Alƙur'ani ita ace ta 44 cikin juzu'i na 25.[5]
Ma'anar Kalmominta
Mafi muhimmanci ma'anonin kalmomin wannan sura: (Rahwan):Wanda kwance ba tare da girgiza, ko kuma yalwace ba tare cunkoso ba. (Ƙaumu tubba'in): Mutanen tubba'u wanda Shi ne Abi Karb Al-Himyari.shugaba ne na ƙasar Yaman, wanda ya kasance mutumin kirki, amma mutanenshi sun kasance kafirai. (Al-Muhli): Abin da aka narkar daga tagulla da gubar; an kuma ce: dattin ko gurɓataccen man fetur. (I'itilluhu): Kama abu gaba ɗayanshi da kuma janshi da ƙarfi.[6]
Abun Ciki
Abin da wannan sura take ɗauke da shi ya kasu kama haka: Wannan sura tana farawa da huruful Muƙaɗɗa'a (Yanakkun haruffa), sannan bayani kan girman Alƙur'ani, da bayana kan saukarsa Lailatul ƙadri. Wannan sura tana magana kan Tauhidi, da bayai kan girman Allah a duniya. Wannan sura tana bayani kan Alƙiyama da makomar kafirai da nau'in azaba masu raɗaɗi da ake yi musu. Wannan sura tana ishara kan ƙissar Annabi Musa (A.S) da Banu Isra'il tare da mutanen Fir'auna. Wannan sura tana bayani kan hadafin yin halitta, da bayani kan cewa Allah bai halicci sama da ƙasa domin wasa ba.[7]
Falala Da Fa'idojinta
An rawaito falaloli da yawa kan karanta wannan sura; An rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta Suratud Dukhan da dare, Mala'iku dubu saba'in za su dinga nema mishi gafara.[9] An rawaito daga Imam Baƙir (A.S) duk wanda ya karata Suratud Dukhan a salloli na wajibi da na nafila, Allah a ranar Alƙiyama zai tashe shi yana mai Imani kuma zai sanya shi cikin inuwar al'arshi, kazalika zai mishi hisabi mai sauƙi kuma ya ba shi littafinshi a dama.[10] Wannan sura tana da abin da yakeɓanta da ita da yawa:
- An rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta wannan sura a daren Juma'a, to Allah zai gafarta mishi zunubinshi wanda ya gabata, kuma wanda ya rubuta ta ya rataye ta a jikinshi, to zai aminta daga sharrin Shaiɗan, duk wanda ya sanya ta ƙarƙashin fulanshi, zai yi mafaraki na alheri, zai aminta daga damuwa, idan kuma mutum mai ciwon kai na ɓari ɗaya, ya rubuta ta ya sha, to nan take zai warke, idan kuma aka rubutata aka sa a gurin sana'a da kasuwanci, to kuɗin mutum zai yi yawa kuma zai ci riba.[11]
Bayanin kula
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 14, shafi na 312.
- ↑ Khurramshahi, Mausu'atul Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, juzu'i na 2, shafi na 1250.
- ↑ Ma'arifat, At-Tamhid Fi Ulumil Qur'an, juzu'i na 1, shafi na 313.
- ↑ Ɗusi, Tafsir At-Tibyan, juzu;i na 10, shafi na 450, Fakrur Razi, At-Tafsirul Kabir, juzu'i na 27, shafi na 202.
- ↑ Ma'arifat, At-Tamhid Fi Ulumil Qur'an, juzu'i na 1, shafi na 169.
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 14, shafi na 325-341.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 16, shafi na 115-116; Ɗabaɗaba'i, Tafsir Almizan, juzu'i na 18, shafi na 131-132.
- ↑ Khamagar, Sakhtare Surahaye Qur'an Karim.
- ↑ Zamakshari, Al-Kashshaf, juzu'i na 4, shafi na 1477.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami, juzu'i na 3, shafi na 319.
- ↑ Bahrani, Al-Burhan, juzu'i na 9, shafi na 5.
Nassoshi
- Bahrani, Hashim Bin Sulaiman, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Beirut – Lebanon, Dar Ihya'il Turasil Arabi, bugu na 1, 1429H.
- Fakhrur Razi, Muhammad bn Umar, At-Tafsirul Kabir, Beirut – Lebanon, Dar al-Kutub al-Ilmiyyah, bugu na 4, 1434H.
- Khamagar, Muhammad, Sakhtare Surahaye Qur'an Karim, Cibiyar Farhangiyye Qur'an wa Itrate Nurus Saƙalain, Qom, Mawallafar Nashra, bugu na 1, 1392Sh.
- Khurramshahi, Baha'ud-Din, Mausu'atul Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, Iran – Tehran, Cibiyar Al-Asdiƙa, 13377Sh.
- Ma'rifat, Muhammad Hadi, At-Tamhid Fi Ulumil Qur'an, Qom – Iran, Zawil Qurba, bugu na 1, 1428H.
- Makarim al-Shirazi, Nasir, Al-Amsal Fi Tafsir Kitabillahi Al-Munzal, Beirut – Lebanon, Cibiyar Al-Amira, bugu na 2, 1430H.
- Musawi, Abbas Bin Ali, Al-Wadihu Fit Tafsir, Beirut – Lebanon, Cibiyar Al-Ghadir, bugu na 1, 1433H.
- Qur'an Karim.
- Zamakhshari, Mahmud Bin Umar, Al-Kashshaf, Beirut – Lebanon, Dar Sadir, bugu na 1, 1431H.
- Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husain, Almizan fi Tafsiril Qur'an, Qom – Iran, Dar Al-Mujtaba, bugu na 1, 1430H.
- Ɗabrisi, Fadl Bin Hassan, Tafsir Jawami'il Jami', Qom – Iran, Cibiyar Annashrul Islami na Jama'atul Mudarrisin, bugu na 2, 1430H.
- Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, At-Tibyan fi Tafsiril Qur'an, Qom – Iran, Cibiyar Annashrul Islami, bugu na 1, 1431H.