A'ayad Sha'abaniyya

Daga wikishia
‌Taron Bikin Murnar Nisfu Sha'aban a Cikin Masallacin Jamkaran Qum Iran

A'ayad Sha'abaniyya (Larabci:الأعياد الشعبانية ) ko Ranaku ne na maulidin Imaman Shi'a waɗanda da dama a cikin watan Sha'aban aka haife su, Kamar yadda majiyarmu ta ruwaito Imam Husaini (A.S) a ranar 3 ga watan Sha'aban[1] wasu kuma sun ce 5 Sha'aban na shekara ta 3 bayan hijira,[2] Imam Sajjad (A.S) a ranar 5[3] ko 9 sha'aban[4] da Imam Mahadi (A.S) a ranar 15 ga watan Sha'aban[5] Har ila yau, wasu majiyoyi na ganin an haifi Sayyiduna Abbas (A.S) a ranar 4 ga watan Sha'aban.[6] da kuma Haihuwar Sayyidina Ali Akbar ɗan Imam Husaini a ranar 11 ga wannan wata.[7] amma a wasu wurare an rubuta wasu ranaku na haihuwar Imam Sajjad[8] da Imam Mahdi (A.S).[9] Haka nan ba a kawo ranar haihuwar Sayyidina Abbas.[10] da Ali Akbar ba.[11]

Kafe Banner Bikin Sha'aban a Haramin Imam Ali (A.S) Sha'aban shekara ta 1445 h,q

A waɗannan ranaku ne wasu `yan Shi'a suke gudanar da bukukuwa ta hanyar ƙawata tituna da masallatai da wuraren ibada dan taya Ahlul-baiti (AS) farin ciki ta hanyar a waƙe-waƙe da yabon Imamai (A.S) da kuma gabatar da kyaututtuka. A ƙasar Iran, ana gudanar da wannan gagarumin biki ne a tsakiyar watan Sha'aban a cikin masallacin Jamkaran,.[12] A ƙasar Iraki, yayin da suke gudanar da bukukuwan tsakiyar Sha'aban, `yan Shi'a su na tafiya da ƙafa don ziyartar Imam Husaini (A.S). Haka nan kuma mabiya Shi'a a wasu ƙasashe su na gudanar da bukukuwan nisfu-Sha'aban a ƙasashensu kamar Bahrain da Misra da Indiya.[13]

A cikin kalandar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ranar 3 ga watan Sha'aban ita ce ranar haihuwar Imam Hussaini kuma matsayin ranar Soja, 4 ga watan Sha'aban ita ce ranar haifuwar Sayyidina Abbas a matsayin ranar majikkatan yaƙi, 5 ga watan Sha'aban Maulidin Imam Sajjad, ranar Sahifa Sajjadiyya, ranar 11 ga watan Sha'aban ita ce ranar haihuwar Ali Akbar kuma ranar samari, ranar 15 ga watan Sha'aban ita ce ranar haihuwar Imam Mahdi (A.S) ita ce ranar waɗanda aka zalunta ta duniya.[14]

Bayanin kula

  1. Ibn Mashhadi, Al-Mazar, 1419 AH, shafi na 397; Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahjad, 1411 AH, shafi na 826, 828; Seyyid bin Taus, Iqbal al-Amal, 1367, shafi na 689-690.
  2. Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 27.
  3. Erbali, Kashf al-Ghumma, 1381 AH, juzu'i na 2, shafi.73.
  4. TabarsiIlamul Alwara, 1390 AH, shafi 256; Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib, 1379 Hijira, Juzu'i na 4, shafi na 175.
  5. Misali, duba Kiulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu’i na 1, shafi na 514; Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 339; Sadouq, Kamaluddin, 1395 Hijira, juzu'i na 2, shafi.424.
  6. Urdubadi, hayatu Abi al-Fazl al-Abbas, 1436 AH, shafi na 64.
  7. Muqram, Maqtale al-Hussein (AS), 1426H, shafi na 267.
  8. Tabarsi, Ilamul Alwara, 1390 AH, shafi 256; Ibn Shahr Ashub, Manaqib al Abi Talib, 1379, juzu'i na 4, shafi na 175.
  9. Duba Erbali, Kashf al-Ghumma, 2013, juzu'i na 2, shafi na 437.
  10. Urdubadi, hayatu Abi al-Fazl al-Abbas, 1436 AH, shafi na 64.
  11. Mir, "Ali bin Hossein".
  12. نگاه کنید به «مروری بر جشن‌های مردمی اعیاد شعبانیه در سراسر کشور»، خبرگزاری ایسنا.
  13. «سنت جشن نیمه شعبان در کشورهای جهان اسلام»، قم‌نیوز.
  14. "Tqwimi Rasmi 1402 Shamsi", shafi na 14-15

Nassoshi

  • Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghamma fi Marafah al-Aima (AS), na Seyyed Hashim Rasouli Mahalati, Tabriz, Bani Hashemi, bugun farko, 1381H.
  • Ibn Mashhadi, Muhammad bin Jafar, al-Mazar, bincike: Javad al-Qayoumi al-Isfahani, Qum, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1419 AH.
  • Ibnshahrashob, Muhammad bin Ali, Manaqib al Abi Talib, wanda: Muhammad Hossein Ashtiani da Seyyed Hashim Rasouli, Kum, mawallafin Allamah, bugu na farko, 1379 H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bugun Ali Akbar Ghafari, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
  • Muqram, Abd al-Razzaq, Maktal al-Hussein (a.s.), Beirut, Al-Khursan Press Institute, 1426H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tammam al-Naimah, bincike na Ali Akbar Ghafari, Tehran, Islamia, bugu na biyu, 1395H.
  • Sayyed bin Taus, Ali bin Musa, Iqbal al-Amal, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1367.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad fi Mafarah Hajjullah Ali al-Abad, Qum, Congress of Sheikh Mofid, na farko, 1413 AH.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Misbah al-Mutahajjid, Beirut, Cibiyar Fiqh al-Shia, 1411H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Ilamul Al-Wara Alam Al-Huda, Tehran, Islamia, bugu na 3, 1390H.
  • Urdubadi, Muhammad Ali, Hayat Abi al-Fazl al-Abbas, Karbala, Darul Kafil, 1436H.
  • «تقویم رسمی ۱۴۰۲ شمسی»، پایگاه اطلاع‌رسانی مرکز تقویم مؤسسه ژئوفیزیک دانشگاه تهران، تاریخ بازدید: ۲۴ بهمن ۱۴۰۲ش.
  • «سنت جشن نیمه شعبان در کشورهای جهان اسلام»، قم‌نیوز، تاریخ درج مطلب، ۱۱ خرداد ۱۳۹۴ش، تاریخ بازدید: ۲۴ بهمن ۱۴۰۲ش.
  • میر، محمدعلی، «علی بن حسین»، دانشنامه جهان اسلام، بنیاد دایرة المعارف بزرگ اسلامی.
  • «مروری بر جشن‌های مردمی اعیاد شعبانیه در سراسر کشور»، خبرگزاری ایسنا، تاریخ درج مطلب: ۱۶ اسفند ۱۴۰۱ش، تاریخ ابازید: ۳ اسفند ۱۴۰۲ش.