Jump to content

Mikewar Assayid Hasani

Daga wikishia
(an turo daga Boren Sayyid Hasani)

Mikewar Assayid Hasani (Larabci: قيام السيد الحسني) na daga Alamomin bayyanar Imamul Mahadi (A.F) kan asasin riwayoyi, hakika Assayid Hasani zai kasance wani matashi daga garin Dailama da zai mike ya `daga sauti domin amsa kiran Imam Mahadi (A.S), za a samu mutane daga garin Talakan su taimaka masa, hakika motsin Assayid Hasani ya cudanya da bayyanar Imam Mahadi (A.F) a garin Kufa ko kuma kusa da garin, zai yiwa Imam Mahadi (A.F) mubaya'a Kan asasin wasu riwayoyi daban, na bayyana cewa zai mike ne a garin Makka kuma mutanen garin za su kashe shi, wasu ba'arin Malamai tare da jingina da wannan riwayoyi sun rinjayar da tsammanin cewa ba wani Assayid Hasani face Nafsuz Zakiyya da za a kashe a garin Makka, kuma ya kasance alamomin bayyanar Imam (A.F) na yankan shakku, wasu kuma sun yi shakku kan ingancin wadannan riwayoyi.

Alamomin bayyana

A cikin ba'arin wasu riwayoyi an hakaito mikewar wani mutum me suna Assayid Hasani da cewa yana daga Alamomin bayyana[1] daga cikin jumlarsu akwai abin da ya zo cikin hudubar Albayan ba'arinta ya yi bayani kan alamomin bayyanarsa, Assayid Hasani mu'amalarsa da Imam Mahadi (A.F) an hakaito maganarsa[2] ta bakin Najamud-dini Attabasi Masani Muhakkiki daga Shi'a akwai kusan hadisi bakwai zuwa takwas kan maudu'in Assayid Hasani,[3] za a fa'idantu daga gare su kan cewa mikewar Assayid Hasani tana daga alamomin bayyanar Imam Mahadi (A.F) cikin fadinsa wadannan riwayoyi sun kai haddin istifaza a ilimin hadisi, kuma za a iya samun nutsuwa kan cewa ba'arin wasu cikin hadisan lallai daga Imamai Ma'asumai (A.S)[4] suka zo, duk da cewa cikin abin da kowannen su ya kunsa akwai dan bambance-bambance.[5] Kan asasin riwayoyin da Malam Kadi Nurullahi Shushtari a littafinsa Ihkakul Hakki ya nakalto cewa Assayid Hasani yana daga cikin `ya`yan Imam Hassan Mujtaba (A.S)[6] a lokacin bayyanar Imamul Mahadi (A.F) zai motsa zai yi mubaya'a ga Imam Mahadi (A.F) tare da rundunar Sojoji[7]

Yaya motsin Ya Kasance

Kamar yanda Najamud-dini Attabasi yake fada: hakika riwayoyin da suka hakaito motsin Assayid Hasani mabanbanta juna ne[8] wasu cikinsu sun hakaita cewa motsin nasa zai fara ne daga garin Dailama Kufa ko kuma dai kusa da garin Kufa, zai yi ma Imam Mahadi (A.F) mubaya'a[9] amma kuwa wasu adadin riwayoyin daban sun hakaito cewa za a kashe shi a garin Makka.[10] Wani Hadisi da aka daganta shi ga Imam Sadik (A.S) hakika Assayid Hasani wani matashi ne mai kyawun fuska da zai fito daga garin Dailama ya yi yekuwa yaku iyalan Ahmad kuma amsa kiran wannan mutumin da kuka yi takaici da bakin cikin fakuwarsa, za a samu wasu mutane daga garin Talikan da suke da karfin imani makasa Azzalumai za su shiga garin Kufa, a wannan lokaci za su tsarkake yankunan Kufa daga marasa addini, za su maida kufa matsuguninsu masaukinsu, lokacin da labarin bayyanar Imam Mahadi (A.F) ya isu kunnen Assayid Hasani da Sahabbansa, zai nemi a nuna masa alamomin bayyana, bayan ganin karamomi daga Imamul Mahadi (A.S) sai shi da rundunarsa su yi wa Imam mubaya'a, illa mutum dubu arba'in daga Zaidiyya da suka ki yin mubaya'a.[11] Kan asasin wata riwaya a lokacin bayyanarsa (A.S) a Makka Assayid Hasani zai motsa sai mutanen garin su kashe shi su aika da kansa wurin Shami, sai dai kuma cikin wadannan riwayoyi sun kunshi cewa fitowar Assayid Hasani na daga alamomin farajin Imam, bawai alamomin bayyanarsa ba, haka kuma cikinsu an yi Magana kan sabani da zai kasance cikin `ya`yan Abbas da raunanar hukumarsu, akwai shakku kan ingancin isnadi da abin da hadisin yake kunshe da shi.[12]

Shin Assayid Hasani Shi ne Dai Nafsuz Zakiyya?

Mulla Salihu Mazandarani Ma'abocin Sharhin Kitabul Al-kafi cikin Sharhin Hadisi daga alamomin bayyana ya kawo tsammani cewa akwai yiwuwar Assayid Hasani ya zamanto shi ne dai Nafsuz Zakiyya,[13] dalili kan hakan shi ne riwayar da ta hakaito kan cewa mutanen garin Makka za su kashe Assayid Hasani da kuma aikawa da kansa zuwa ga Shami Sufyani a lokacin bayyanar Imam (A.F),[14] Nafsuz Zakiya wani mutum ne daga tsatson Imam Husanini (A.S),[15] da a kashe shi a garin Makka kusa da Rukunu da Mukam Ibrahim da Masallacin Harami,[16] kuma kashe shi yana daga alamomi bayyanarsa na yankan shakku[17]


A Duba Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. Duba Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 16; Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 8, shafi na 225, H. 285; Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 270.
  2. Tabasi, “Sayyid Hosni dar hudubar Al-Bayan az Sanjad ta Matan” shafi na 52.
  3. Tabesi, "Nagareshi dar riwayat Hassani", shafi na 26
  4. Tabesi, "Nagareshi dar riwayat Hassani", shafi na
  5. Tabesi, "Nagareshi dar riwayat Hassani", shafi na 47
  6. Shushtri, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 29, shafi na 448.
  7. Shushtri, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 29, shafi na 448.
  8. Tabasi, “Halaye a cikin hadisai Hassani”, shafi na 47.
  9. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 15-16.
  10. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 8, shafi na 225, H. 285; Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 270.
  11. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 16; Yazdi Haeri, Elzam al-Nasib, 1422 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 218.
  12. Duba Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 7, shafi na 439-441.
  13. Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1380 AH, juzu'i na 12, shafi na 414.
  14. ,Dubi Salimian, FarhangNameh Mahdavit , 2008, shafi na 208.
  15. Duba Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 52, shafi na 223.
  16. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 1, shafi na 331.
  17. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi 650, h7.

Nassoshi

  • Salimian, Khodamorad, FarhangNameh Mahdawiyya, Qum, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation, bugu na biyu, 2008.
  • Shushtri, Qazi Noorullah, Ahqaq al-Haq da Izhaq al-Batil, Gabatarwa na Shahab al-Din Marashi, Qum, Hazrat Ayatullah Azami Marashi Marashi Najafi Public Library, 1409 AH.
  • Saduk Muhammad Bn Ali کمال‌الدین و تمام النعمة، علی‌اکبر غفاری
  • طبسی، نجم‌الدین، «نگرشی در روایات سید حسنی»، انتظار موعود، ش۳۱، زمستان ۱۳۸۸ش.
  • طبسی، نجم‌الدین، «سید حسنی در خطبه البیان»، انتظار موعود، ش ۳۲، بهار و تابستان ۱۳۸۹ش.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-kafi, Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugun 4, 1407H.
  • Mazandrani, Mulla Mohammad Saleh bin Ahmad, Sharh al-Kafi - Al-Asul da al-Rawzah, Abul Hasan Shearani ya inganta shi, Tehran, Al-Maktaba al-Islami, 1382H.
  • مجلسی، محمدباقر، بحار الانوا، بیروت، دار احیاء التراث العربی، ۱۴۰۳ق.
  • محمدی ری‌شهری، محمد، دانشنامه امام مهدی(عج)، قم، دا

ر الحدیث، ۱۳۹۳ش.