Barkat

Daga wikishia

Barkat (arabic: البركة) ko Albarka, na nufin Ni’momi da Tarin Alherin Allah kan halittunsa, wannan kalma ta zo sau uku cikin Alkur’ani, kuma duka ta zo a sigar Jam’i, ma’ana Albarkoki, sakamakon kasancewa ana jingina Albarka zuwa ga Allah a koda yaushe, sai ya zamana babu mai samar da Albarka sai Allah Ta’ala shi kadai. Imani, Tak’wa, Istigfari, Zikiri, Da’a ga Allah, da Adalci, da kuma Taushin Dabi’a suna daga Sabubban samun Albarkar Allah, Sabanin wasu Halayyar `Dan Adam misalin, Aikata zunubai, barin Umarni da Kyakkyawa da Hani da mummna, suna daga sabubban rashin samun Albarkar Allah. Ba’arin wasu halittun Allah suna daga cikin Mazhari da Alamomin Albarka; Annabawa kamar misalin Hazrat Nuhu (A.S) Salihan Muminai, Lokuta misalin Daren Lailatul Kadri, da wurare misalin Makka, da fuskokin Dabi’a kamar misalin Ruwan Sama duka suna cikin Samfurai da misalan Albarkokin Allah.


Sanin Mafhumi

Albarka na nufin Albarka tana nufin tarin Alheri. [1] Allama Tabataba’I yana ganin Albarka tana da ma’anar tabbatuwar Alheri Mai tarin yawa cikin wani Abu misalin samuwar Ruwa cikin Magudanarsa, [2]haka kuma yana ganin wannan kalma tana daga Kalmar ya danganta a ina aka yi amfani da ita, kuma kan wannan asasi ne Alheri cikin kowanne irin Abu yana dacewa da tanadin wannan Abun da kuma yanda aka yi amfani da Kalmar a cikinsa, Alal misali Albarka cikin Tsatso da Zuriya, na da ma’ana yawan `ya`ya, Albarka a cikin lokaci tana ishara kan yawan aikin da mutum ya yi a cikin wannan lokaci. [3] Isdilahin Albarka a cikin Alkur’ani Mai girma, yana bada ma’anar Ni’imomi da Alheran Allah masu tarin yawa, [4] kuma kan wannan asasi ne, aka fassara Albarka Sama da Ruwan Sama Mai yawan gaske, Albarkar Kasa, yawan Shuke-shuke da kayan marmari, [5] kalmar Tabaraka ta samo Asali ne daga Barkat, a cikin Alkur’ani ta zo dauke da ma’anar Mubalaga ai tarin Albarkoki kebance ga Allah, a wurare `yan kadan ne akayi amfani da ita kan wanin Allah a cikin Alkur’ani Mai girma [6] sannan sauran kalmomi da suke da irin ma’anarta a kebance an danganta su kan Mutane, wurare da sauran abubuwa cikin sura da yanayi na tarayya. [7] Kalmar Albarka cikin Alkur’ani Mai girma ta zo da sigar jam’i a cikin ayoyi guda uku [8] ba’ari daga cikinsu Ana ganinsu Alama ta yawan Albarkar Allah [9] kalmomi da suke da ma’ana iri daya da Barkat (Albarka) sune: Baraka [10] Barakna [11] Burikna [12] Mubarak [13] Muburakan [14]Suratul Al-Imran, aya ta 3; Suratu Maryam, aya ta 31; Suratul Muminun, aya ta 29; Suratul Q, aya ta 9. 15 Tabaraka [15] sau talatin da uku akayi amfani da su cikin Alkur’ani Mai girma, amfani da Kalmomin da aka ciro su daga Barkat kodayaushe suna zuwa tareda jingina su da Allah, wannan kansacewa dalili ne kan cewa Allah ne kadai yake iya samar da Albarka [16] kalmar Barkat a cikin Riwayoyi ma ta zo kuma daya daga cikin Rundunar Hankali ce [yadasht 1] Kishiyar gushewa daga Rundunar Jahilci, Malam Hassan Mustafawi [17] yana ganinsu Rundunar Jahilci da ma'anar Tawayar wani Abu kadan-kadan Sannu-sannu har zuwa rushewarsa ta baki daya da halaka [18] Mafhumin Barkat kari kan amfani da shi cikin Akur’ani da litattafan Muslunci, anyi amfani da shi kafin zuwan Muslunci, kyautar Albarkar ga Annabawa, da kuma daga bangaren Annabawa da Malamai zuwa ga Mutane, daya daga cikin misalsalai a wannan fage [19] tushen inda aka ciro (Barkat, Barkha) kalma ce daga Harshen Abranci (Barakha) wacce take da ma’anar Albarka kusan an yi amfani da ita sau 400 cikin Ahadul Atik sannan kuma anyi amfani da Kalmar a adadin wasu wurare a cikin Ahadul Jadidi na Yahudawa. [20]

Sabubba

Cikin Al’adun Muslunci, samun Albarkar Mutane ya dogara ne da ayyuka da halaye da maganganunsu, da wannan dalili ne cikin Alkur’ani Mai girma da Riwayoyin Ma’asumai, ake ganin wasu abubuwa misalin: Imani, Tak’wa, Istigfari, Da’a ga Allah da Amabatonsa, [21] Adalci, [22] Godiya, Tashin da Alfijir, [23] Taushin Dabi’a, [24] Musluntar da wanda Musulmi ba, [25] Bada Sadaka, [26] Kiyaye Tsafta, [27] Saukaka Aure, [28] Sadar da Zumunci, [29] Kasuwanci na gaskiya, [30] Kyawunta Makotaka, [31] Taimakawa `yan’uwa na Addini, [32] yin Azumi tareda cin abincin Sahur [33] suna cikin Jumlar sabubban saukar Albarka.

Imani da Tak’wa

Alkur’ani Mai girma a cikin aya ta 96 Suratul A’araf, hakika Imani da Tak’wa Aksarain Mutane sune Sharuddan samun Saukar Albarkar Sama da Kasa, sannan kan asasin abinda ya zo cikin Tafsirai dangane da wannan aya, ya bayyana cewa Imanin Tsirarun Mutane ba zai iya lamintar da saukar Albarka ga kowa da kowa ba. [34]

Istigfari

Cikin aya ta 52 Suratul Hudu da ayoyi 10-13 Suratul Nuhu saukar Albarkokin Allah daga Ruwan Sama ya dogare da kawar da shinge, kamar misalin zunubi ya kasance daya daga cikin Shinge da yake hana saukar Albarkoki, Istigfarin Bayin Allah ya kasance hanya ta samun Rahamar Allah. [35] Kan asasin Abin da ya zo cikin Alkur’ani Mai girma, Allah ya shardanta karo ni’imarsa da godiyar da Bayinsa suka yi masa kan ni’imar da ya basu, kishiyar Kafircewa Ni’ima wanda aka bayyana shi matsayin sababin karuwar Azaba [36] Imam Ali (A.S) yana ganin Istigfari matsayin hanyar samun saukar Arziki da Rahamar Allah. [37]

Shinge

Kan asasin litattafan Muslunci da Al’adunsa, hakika wasu Halaye da Maganganu suna zama sababin Haramtuwar Mutum daga samun Albarkokin Allah, aikata zunubi, sabawa umarnin Allah, barin Umarni da Kyakkyawa da Hani da Mummuna da galafa da ambaton Allah [38] suna daga jumlar sabubban da Alkur’ani da Riwaya suka bayyana su matsayin abubuwan da suke hana saukar Albarkoki.

Aikata Zunubi da Sabawa Umarnin Ubangiji

Zunubai da Sabawa Umarni sabubba ne na cire Albarka daga Dukiya da rayuwar Mutum, Malaman Tafsirin Alkur’ani Mai girma cikin tafsirin aya ta 96 Suratul A’araf Hakika wadanda suka kasance suna aikata Zunubai da karyata Annabawa, kari kan Azabar Allah da take kansu to karshensu zai kasance an haramta musu samun Albarkokin Sama da Kasa. [39] Ayyuka da suke jawo Haramtuwar Mutane daga samun albarkar Allah sune kamar: Barin Sallah, [40] Tauye Awo, [41] kin bada Zakka, [42] Barna [43] Ha’inci, [44] Sata, Shan Barasa, Alfasha, [45] Rantsuwar Karya cikin Mu’amala [46]

Barin Umarni da Kyakkyawa da Hani da Mummuna

Barin Umarni da Kyakkyawa da hani da Mummuna, yana daga shingaye hana saukar Albarka, kan asasin riwayoyi daga Annabin Muslunci (S.A.W), Samun Albarkar Allah kadai yana faruwa ne a lokacin da Mutane suke yin Umarni Kyakkyawa da Hani da Mummuna, da kuma tarayya da Taimakekeniya cikin Ayyukan Alheri tsakanin junansu, idan kuma ya zamana basa Umarni da Kyakkyawa da Hani da Mummuna to ni’ima da Albarka za su yanke a kansu [47]

Misdakai

kan asasin ayoyin Alkur’ani Mai girma, Allah ya ajiye ba’arin wasu Halittunsa matsayin Mazhari Mabayyana da Alamomin Albarkarsa, daga jumlarsu akwai Annabawa da Salihan Muminai, Alkur’ani Mai girma, Ba’arin wasu Wurare, ba’arin wasu lokuta, da kuma wasu fuskokin Dabi’a . sannan babban dalili kan kasancewar Albarkar Alkur’ani [48] shi ne shiryar da Mutane da yake yi [49] Annabawa da sauran Mutane da a cikin Alkur’ani aka kiraye su da Ma’abota Albarka sune kamar haka: Nuhu (A.S) da Mutanensa da suka Hau Jirgi [50] Ibrahim da `Ya`yansa Isma’il da Is’hak, [51] Musa (A.S) [52] Isa (A.S), [53] Annabin Muslunci (A.S) [54] da Salihan Muminai [55] Haka kuma akwai ba’arin wasu Wurare a Doran Kasa da suka kassance tare da Albarka kamar misalin Makka, [56] Sham, [57] Baitul Mukaddas [58] Wadi Turi [59] Daren Lailatul Kadri yana cikin Jumlar Lokuta da ake amsa Addu’a , Gafarta Zunubai da saukar Alkur’ani [60] an kiraye shi da Dare Mubarak (Dare Mai Albarka) [61] haka kuma akwai fuskoki da tajallin Dabi’a misalin saukar Ruwan Sama wanda cikin Alkur’ani aka kiraye shi da Mubarak. [62]

Bayanin kula

  1. Dehkhoda, Amsal wal-Hikam , 1383, juzu’i na 1, shafi na 104, 114, 359.
  2. Tabatabaei, Al-Mizan, juzu'i na 15, shafi na 173.
  3. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 7, shafi na 281-280.
  4. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi na 697.
  5. Sheikh Tusi, al-Tabayan, 1383H, juzu'i na 4, shafi na 477..
  6. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 15, 173.
  7. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi na 516, 596.
  8. Suratul A'araf, aya ta 96; Suratul Hud, aya ta 48 da ta 73.
  9. Gadami, “Albarka: Pedayes Payidari wa Afzuni Khairi dar Padidahaye Az Suye Khoda,”, juzu’i na 5, shafi.486.
  10. Suratul Faslat, aya ta 10.
  11. Suratul A'araf, aya ta 137; Suratul Isra, aya ta 1; Suratul Anbiya, aya ta 71 da ta 81; Suratul Saba, aya ta 18; Suratul Safat, aya ta:113
  12. Suratul Namal, aya ta 8.
  13. Suratul An'am, aya ta 92 da ta 155; Suratul Anbiya, aya ta 50; Suratul S, aya ta 29.
  14. Mubarakatu
  15. Suratul Noor, aya ta 61 da ta 35; Suratul Dukhan, aya ta 3.
  16. Gadami, “Albarka: Pedayes Payidari wa Afzuni Khairi dar Padidahaye Az Suye Khoda,”, juzu’i na 5, shafi.486
  17. Mustafawi, At-Tahkik fi Al-kalemat Al-Kur’an Al-Kareem , 1368, juzu’i na 11, shafi na 39.
  18. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 22
  19. Gadami, “Albarka: Pedayes Payidari wa Afzuni Khairi dar Padidahaye Az Suye Khoda,”, juzu’i na 5, shafi.484
  20. Karimi, Barkat, juzu'i na 11, shafi na 744.
  21. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 70, shafi na 341.
  22. Laithi Wasti, Ayoun Al-Hekam da Al-Mo'az, 1376, shafi na 188
  23. Nahj al-Balagheh, be Tashihu Sobhi Saleh, harafi 12.
  24. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 119.
  25. Sadouq, Ilalul Al-Shara'i, 1385 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 583.
  26. Suratul Baqarah, aya ta 276; Laithi Vasti, Ayoun Al-Hekam wa Al-Mowa'iz, 1376, shafi na 195; Kulaini, Al-Kafi, 1403H, juzu'i na 4, shafi na 2.
  27. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 73, shafi na 110.
  28. Ibn Hanbal, Musnad, 1416 AH, Juzu'i na 6, shafi na 82, 145.
  29. Nahj al-Balagheh, Tashihu Sobhi Saleh, 1414 AH, shafi na 164, hadisi na 110; Kofi Ahwazi, Al-Zuhd, 1402H, shafi na 39.
  30. Ibn Hanbal, Musnad, 1416 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 402.
  31. Alameh Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 71, shafi na 97.
  32. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 71, shafi na 395.
  33. Ibn Hanbal, Musnad, 1416 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 12.
  34. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 8, shafi na 201; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 14, shafi na 321; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 6, shafi na 266.
  35. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 10, shafi.444; Juzu'i na 20, shafi na 45.
  36. Suratul Ibrahim, aya ta 7.
  37. Qomi Mashhadi, Tafsiri Kanz al-Daqa'iq, 1368, juzu'i na 13, shafi na 454.
  38. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 73, shafi na 314.
  39. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi.698; Fakhr Razi, al-Tafseer al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 14, shafi na 322.
  40. Ibn Tavus, Falahul Al-Sa'el, 1406H, shafi na 22.
  41. Sadouq, Ilalaul Al-Shara'i, 1385 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 584.
  42. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 505.
  43. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 505.
  44. Laithi Vasti, Ayoun Al-Hekam wa Al-Mowa'iz, 1376, shafi na 134.
  45. Alameh Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 76, shafi na 19, 23.
  46. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 5, shafi na 162.
  47. Sheikh Mofid, Al-Muqni'a, 1413 AH, shafi na 808.
  48. Suratul An'am, aya ta 92 da ta 155; Suratul Anbiya, aya ta 50; Suratul S, aya ta 29
  49. Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 7, shafi na 387.
  50. koma zuwa: Tabarsi, Majma al Bayan, 1372, juzu'i na 5, 255; Beidawi, Anwar al-Tanzil, 1418 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 137.
  51. Tabarsi, Majmam Al-Bayan, 1372, juzu'i na 8, shafi.709; Qortubi, Al-Jamae na Ahkam al-Qur’an, 1364, juzu’i na 15, shafi na 113; Beidawi, Anwar al-Tanzil, 1418 AH, juzu'i na 5, shafi na 16; Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 10, shafi na 325
  52. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 7, 330; Tabari, Jame Al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 19, shafi na 82.
  53. Suratu Maryam, aya ta 31; Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 16, shafi na 66; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 21, shafi na 535; Qortubi, Al-Jamae Lahkam al-Qur'an, 1364, juzu'i na 10, shafi na 70.
  54. Suratul Kauthar, aya ta 1; Sheikh Tusi, al-Tabayan, 1385 AH, juzu'i na 10, 417; Ibn Arabi, Tafsirin Kur’an Karim, 1978, juzu’i na 2, shafi na 460.
  55. Suratul Baqarah, aya ta 269; Suratul Hud, aya ta 48.
  56. Suratul Al-Imran, aya ta 96; Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 387; Makarem Shirazi, Tafsir al-Nashon, 1371, juzu'i na 3, shafi na 14.
  57. Suratul A'araf, aya ta 137; Suratul Anbiya, aya ta 71 da ta 81; Suratul Saba, aya ta 18; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 14, shafi na 348; Allameh Tabatabaei, Al-Mizan, 1390 AH,Juzu'i na 8, shafi na 228; Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 2, 149; Qortubi, Al-Jamae na Ahkam al-Qur’an, 1364, juzu’i na 7, shafi na 272; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 22, shafi na 190-201; Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 4, shafi na 725.
  58. Suratul Isra'i, aya ta 1.
  59. Fakhr Razi, Al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 24, shafi na 593.
  60. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 9, shafi na 93.
  61. Suratul Dukhan, aya ta 3.
  62. Suratul Qaf, aya ta 9.

Nassoshi

  • Allameh Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar al-Ahiya al-Trath al-Arabi, 1403H.
  • Allameh Tabatabai, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1390 AH.
  • Baidawi, Abdullah bin Umar, Anwar al-Tanzil da Asrar al-Tawil, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1418H.
  • Dehkhoda, Ali Akbar, Amsar wal-Alhekam, Tehran, Amir Kabir, 2003.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, al-Tafsir al-Kabir, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H.
  • Gadami, Gholamreza, "Albarka: Paidayesh Payidare wa Fazuni Barkat dar Padidaha aza suye Khoda", Encyclopedia of the Holy ƙur'an, ƙom, Bostan Kitab, 2013.
  • Ibn Arabi, Muhammad Ibn Ali, Tafsir ƙur'an Al-Karim, bugun Mustafa Ghalib, Beirut, Dar Al-Andalus, 1978.
  • Ibn Hanbal, Ahmad, Musnad, Beirut, Al-Risala Institute, 1416 AH.
  • Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, Falahul Al-Sa'il da Najah Al-Masail, Kum, Bostan Kitab, 1406H.
  • Karimi Mahmud, «برکت»، دائرة المعارف بزرگ اسلامی،Tehran, cibiyar babban littafin tarihin Musulunci, 2013.
  • Kofi Ahwazi, Hossein bin Saeed, Al-Zuhdu, Gholamreza Irfanian Yazdi ya gyara, ƙom, Al-Matabah Al-Alamiya, 1409H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, al-Kafi, wanda Ali Akbar Ghafari ya shirya da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyya, 1407H.
  • Laithi Wasti, Ali bin Muhammad, Ayoun al-Hekam da al-Mo'az, ƙom, Dar al-Hadith, 1376.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Darul Katb al-Islamiyya, 1371.
  • ƙomi Mashhadi, Mohammad bin Mohammad Reza, Tafsir Kanz al-Daƙaeƙ da Bahr al-Gharaib, editan Hossein Dargahi, Tehran, Kungiyar Buga da Buga na Ma'aikatar Shiriya, 1368.
  • ƙortubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jamee Ahkam al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosrow, 1364.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Muƙni'a, ƙum, Sheikh Mofid Hazara World Congress, 1413 AH.
  • Sheikh Sadouƙ, Ali bin Muhammad, Ilalul Al-Shara'i, ƙum, Kantin sayar da littattafai na Davari, 1385H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsir al-ƙur'an, Ahmad Habib Ameli, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, 1383 H.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Jame al-Bayan fi Tafsir ƙur'an, Beirut, Darul Marafa, 1412H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosro, 1372.
  • Mustafawi, Hassan, Tahƙiƙ fi Kalemat al-ƙur'an, Tehran, Ministry of Culture and Islamic Guidance, bugun farko, 1368.