Tushen aƙida da mazhabar shia
Asalan Mazhabar Shi'a, (Larabci: أصول المذهب الشيعي) tushen Mazhabr Shi'a sun hada da Tauhidi, Annabta, Ma'ad, Adalci da Imamanci. A wajen `yan Shi'a, inkarin kowace ka'idoji guda uku na farko (tauhidi da Annabci da tashin kiyama) waɗanda su ne Asalan addini yana haifar da Kafirci, amma rashin imani da kowace ka'idoji guda biyu na adalci da imamanci yana kaiwa ga barin Shi'a, ba barin Addinin Musulunci ba. Sanya Imamanci a ƙarƙashin tsarin addini yana daga cikin Akidar da ta bambanta Shi'a da sauran mazhabobin Musulunci, don haka ne ake kiransu Imamiyya Haka nan kuma imani da ƙa'idar adalci ya banbanta Mu'utazila da Ash'ariya kuma ya sanya an sawa Shi'a da Mu'utazila sunan Adaliyya.
Matsayi
Mazhabar Shi'a ana kiransu da tushen shi'a kuma guda biyar ne akwai (Tauhidi, Annabci, Ma'ad, Imamanci da Adalci) [1]wadanda su ne tushen Mazhabar Shi'a.[2] Rashin Imani da kowannensu zai iya sa mutum yabar Shi'a. Tabbas rukunan guda uku na tauhidi da annabci da tashin ƙiyama suna daga cikin Asalan Addini, kuma rashin imani da ɗaya daga cikinsu yana haifar da Kafirci da barin Addinin Musulunci.[3]
Asalai Da Shi'a Suka Kebantu Da Su Koma Bayan Ahlus-sunna
imamanci[4] da Adalci[5] Asalai guda biyu na Mazhabar Shi'a
Imamanci
- Tushen Kasida: Imamanci
Imani da cewa imamanci (sanya shugaba ga al'ummar musulmi bayan wafatin Hazrat Muhammad (S.A.W) abu ne na Ubangiji[6] kuma Allah ne ze naɗa wanda yaso[7] a aƙidar shia Allah ya naɗa mutum goma sha biyu daga cikin 'ya'yan Manzon Allah (S.A.W) Sunayen imamai bisa tsarin imamanci kamar haka: Imam Ali (A.S), Imam Hassan (A.S), Imam Husaini (A.S), Imam Sajjad (A.S), Imam Bakir (A.S), Imam Sadiƙ (A.S). a.s., Imam Kazim (A.S), Imam Rida (A.S), Imam Jawad (A.S), Imam Hadi (A.S), Imam Hassan Askari (A.S), Imam Mahadi (A.F).[8]
Mene ne Ya Sa Imamanci Yake Da Ka'idoji Daga Tushen Shi'a
A cewar Mohammad Husaini Kashif Al-Ghita a cikin littafin Aslush Shi'a wa Usuliha, imamanci shi ne babban abin da ya bambanta shi'a da sauran mazhabobin Musulunci[9] Saboda haka ake kiran wanda suka yadda da Imamancin imamai goma sha biyu wanda aka fi sani da Shi'a Imamiyya.[10] kuma imamanci yana daga cikin ka'idojin mazhabar shi'a[11] Kuma duk wanda bai yarda da shi ba zai fita daga da'irar shi'anci.[12]
Adalcin Allah
- Tushen Kasida: Adalcin Allah
Imani da cewa Allah yana yin adalci kuma ba ya zalunci a tsarin halitta da na shari'a[13] Adaliyya (Shi'a da Mu'utazila) suna ganin hankali a lokuta da yawa yakan fahimci Kyawunta da Munana ayyuka. cewa . ma'ana Allah Yana aiki ne a kan kyawawan abubuwa, kuma ba ya yin zalunci domin zalinci abune mai muni,[14] Kuma Ash'ariyya sunyi imani da cewa ma'auni na adalcin hali aikin Allah ne. Kuma duk abin da Allah yake aikatawa mai kyau ne kuma adalci, ko da mutane sun gan shi a matsayin zalunci.[15]
Mene ne Yasa Adalci Yake Daga Ƙa'idoji Da Tushen Shi'a
A cewar masanin falsafar nan na Shi'a Misbahu Yazdi (1313-1399H), ana ɗaukar adalci ɗaya daga cikin ƙa'idojin Mazhabar Shi'a da Mu'utazila saboda muhimmancinsa a Ilimin Kalam.[16] Malamin shi'an nan Murtada Mutahhari ma yana cewa : abin da yasa adalci ya kasance ɗaya daga cikin ka'idojin shi'a, shi ne ɓullowar wasu aƙidu kamar inkarin iktiyari (zabi) da 'yancin dan Adam da zabi a tsakanin a ayyukansa acikin wasu mutane daga Musulmai. wanda a kan haka bai dace ba a hukunta wanda aka tilastawa. tare da cewa kuma Allah yana adalcin[17] Shi'a da Mu'utazila suna ganin tilasta mutum ga aiki ya saba wa adalcin Ubangiji, don haka ne aka sansu da sunan Adaliyya.[18]
Ƙa'idoji da Tushen Muslunci
- Tushen Kasida: Asalan Addini
- Tauhidi: imani da samuwar Allah, Kaɗaita shi da rashin abokin tarayya.[19]
- Annabci: Imani da cewa Allah ya aiko mutane a matsayin annabawa don shiryar da mutane[20] Annabi na farko shi ne Hazrat Adam (A.S)[21] kuma na ƙarshe shi ne Hazarat Muhammad (S.A.W).[22]
- Ma'ad: Imani da cewa za a tayar da mutum bayan Mutuwa kuma za ayi hisabi na ayyukansa na alheri da na sharri.[23]
Bayanin kula
- ↑ Duba: Mohammadi Rishahri, Encyclopaedia of Islamic Beliefs, 2005, juzu'i na 8, shafi na 99.
- ↑ Duba: Mohammadi Rishahri, Encyclopaedia of Islamic Beliefs, 2005, juzu'i na 8, shafi na 97.
- ↑ Kashif Al-ghita, Asl al-Shia da Usuls, Imam Ali (AS), shafi na 210; duba
- ↑ Lahiji, Gohar Murad, 2003, shafi na 467; Duba Sobhani, Al-Ilahyat, 1417 AH, juzu'i na 4, shafi na 10.
- ↑ Mesbah Yazdi, Amuzeshi Akayid, 2004, shafi na 161.
- ↑ Kashf al-Ghitāf, Asalul Shia wa Usuliha, Cibiyar Imam Ali (A.S), shafi na 211.
- ↑ Duba Lahiji, Gohar Murad, 2003, shafi na 585.
- ↑ Khazaz Razi, Kefaiya al-Athar, 1401 AH, shafi na 53-55; Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 1, shafi na 254-253.
- ↑ Kashf al-Ghitāf, Aslul Shi'a wa usuliha, muassaseh Imam Ali (A.S), shafi na 221.
- ↑ Aslul Shi'a wa usuliha, muassaseh Imam Ali (A.S), shafi na 222
- ↑ https://makarem.ir/maaref/fa/article/index/407905
- ↑ Kashf al-Ghitāf, Aslul Shi'a wa usuliha, muassaseh Imam Ali (A.S), shafi na 212
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asar, Sadra, juzu'i na 2, shafi na 149.
- ↑ Sobhani, Rasa'il wa Makalat, 1425 AH, juzu’i na 3, shafi na 32.
- ↑ Sobhani, Rasa'il wa Makalat, 1425 AH, juzu’i na 5, shafi na 127
- ↑ Mesbah Yazdi, Amuzeshi Akayid, 2004, shafi na 161.
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asar, Sadra, 1390, juzu'i na 2, shafi na 149.
- ↑ Majmu'eh Asar, Sadra, 1390, juzu'i na 2, shafi na 149.
- ↑ Kashf al-Ghitāf, Aslul Shia wa Usulija, muassaseh Imam Ali (A.S), shafi na 219.
- ↑ Kashf al-Ghitāf, Aslul Shia wa Usulija, muassaseh Imam Ali (A.S), shafi na 220.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 11, shafi na 32.
- ↑ Suratul Ahzab, aya ta 40.
- ↑ Lahiji, Gohar Murad, 1383, shafi na 595; Kashif al-Ghata, Asl al-Shia da ka'idoji, Imam Ali (AS), shafi na 222.
Nassoshi
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Kitab al-Tahara, Tehran, Imam Khumaini (a.s) Cibiyar Edita da Wallafa, 1427H/1358H.
- Khazaz Razi, Ali bin Muhammad, Kufaiya al-Athar a cikin nassin Ali Imamai na karni na goma sha biyu, wanda: Abdul Latif Hosseini Koh
- Kamri, Qom, Bidar, 1401 Hijira ya inganta.
- Sobhani, Jafar, Rasael wa Makalat, Qum, Imam Sadiƙ (a.s.), 1425H.
- Sobhani, Jafar, Al-Tauhidin Ali Hoda Al-Kitab da Sunnah da Al-Aql, wanda Sheikh Hassan Ameli ya rubuta, Qum: Mu’assasa Al-Imam Al-Sadiq, bugu na 4, 1417 Hijira.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tamma Al-Naimah, Edited by: Ali Akbar Ghafari, Tehran, Islamia, 1395 AH.
- https://makarem.ir/maaref/fa/article/index/407905" Ain Rahmat, 9 ga Yuni 1401.
- Kashif al-Ghata, Mohammad Hossein, Asl al-Shi'a and Usuls, Alaa Al-Jafar's research, Imam Ali (A.S.) Foundation, Beta.
- Lahij Abdul Razzaq, Gohar Murad, Gabatarwa zuwa Zainul Abdin Ghorbani, Tehran, Sayeh Publishing House, bugun farko, 2003.
- Majlesi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
- Mohammadi Rishahri, Muhammad, Ilimin Aqidun Musulunci, Qum, Dar al-Hadith, 2005.
- Misbah Yazdi, Mohammad Taqi, Amuzeshi Akayid. Tehran, Kungiyar Buga Farfagandar Musulunci, bugu na 17, 1384.
- Motahari, Morteza, Majmu'eh Asar, Tehran, Sadra Publishing House, 1390.