Jump to content

Addu'a Ta Ashirin Da Bakwai Cikin Sahifa Sajjadiyya

Daga wikishia
Addu'a Ta Ashirin Da Uku Cikin Sahifa Sajjadiyya
Kwafin rubutun hannu na Sahifa Sajjadiyya, da rubutun Abdullahi Yazdi, an rubuta a watan Sha'aban 1102 hihira qamari
Kwafin rubutun hannu na Sahifa Sajjadiyya, da rubutun Abdullahi Yazdi, an rubuta a watan Sha'aban 1102 hihira qamari
Maudu'iAddu'a ga Masu gadin kan iyakokin Muslunci, sharuxxan masu gadin iyakoki, tarayyar dukkanin mutane cikin kare Muslunci
Ya fito dagaImam Sajjad (A.S)
MarawaiciMutawakkil Bin Haruna
Madogaran Shi'aSahifa Sajjadiyya
NazariSiyasatul Harbi Fi Du'a'i Ahlis Sugur, na Jafar Murtada Amili da Marzdaran Dar Du'aye Imam Sajjad (A.S) na Baitullahi Bayat Zanjani


Addu'ar ta ashirin da bakwai a cikin Sahifa Sajjadiyya ko Du'a'u Ahlil Sugur, (Larabci: دعاء أهل الثغور ) tana daga cikin addu'o'in da aka naƙalto daga Imam Sajjad (A.S) game da masu gadin kan iyakoki garuruwan Muslunci. Sayyidina Zainul Abidin (A.S) ya yi addu'a domin ƙarfafuwar iyakokin garuruwan Muslunci, ya roƙi Allah ya ba da lura ga masu gadin iyakoki, iklasi Imani, taƙawa da yawaitar adadinsu. Haka nan ya buƙaci baki ɗayan Musulmi su yi tarayya cikin ba da kariya ga Muslunci ta hanyar taimakawa mujahidai da masu gadin kan iyakoki, da kuma kulawa da iyalansu. Imam Sajjad (A.S) tare da Jaddada taimako na baɗini da Musulmi suke samu daga ubangiji cikin nasarorinsu kan Mushrikai, da gamawa da Kafirai matsayin wata shimfiɗa da take samar da yanayi da tabbatuwar al'ummar da za ta kasance kan tauhidi.

Jafar Murtada Amili a cikin littafin Siyasatul Harbi Fi Du'a'i Ahlis Sugur, ya yi sharhin dabarun yaƙi kariya ga kan iyakokin garuruwan Muslunci, tare da jingina da addu'a ta ashirin da bakwai cikin sahifa sajjadiyya. Wannan addu'a ta samu sharhi-sharhi masu tarin yawa cikin harsuna daban-daban, misalin littafin Diyaru Ashiƙin, na Husaini Ansariyan da Shuhud Wa Shenakt, na Hassan Mamduhi Kermanshahi cikin harshen Farsi, da kuma Riyadus Salikin, na Sayyid Ali Khan Madani, cikin harshen Larabci.

Darussa

Jigo na addu'a ta ashirin da bakwai cikin sahifa sajjadiyya, shi ne addu'a ga masu gadin kan iyakokin Muslunci a ko wane zamani, ana roƙa musu faɗaka da lura, haƙuri, tsayuwa ƙyam, iklasi, wadataccen tanadi, soyayyar juna da yawaitar adadi. A cewar Hassan Mamduhi Kermanshahi, wannan addu'a tana da ɗimbin ma'anoni, ta ƙunshi, kyawawan darussa na tauhidi, halaye na gari,Irfani, ma'anoni na ɓoye cikin fagen yaƙi da hukunce-hukunce da kuma ladubban yaƙi.[1]Jafar Subhani ɗaya daga cikin maraji'ain taƙlidi na Shi'a yana da ra'ayin cewa jumlar «اللَّهُمَّ وَ امْزُجْ مِیاهَهُمْ بِالْوَبَاءِ (Allah ka cuɗanya annoba cikin ruwan shan su) matsayin ɗaya daga cikin mu'ujizozi na ilimi na wannan addu'a, dalili kuwa shi ne kasantuwar a wancan zamani cututtuka suna yaɗuwa ta cikin ruwan sha.[2]

Darussan Wannan addu'a sune kamar haka:

  • Addu'a domin ƙafafa kan iyakokin garuruan Musulmi
  • Muhimmancin gadin kan iyakoki da kuma kare asalin Muslunci
  • Addu'a domin yawaitar adadin masu kare iyakoki da kaifafar makamansu
  • Addu'a domin tabbatuwar soyayya tsakanin Masu gadin iyakoki
  • Addu'a domin ƙarfafar Masu gadin iyakoki da nasarar Allah da kuma haƙuri
  • Addu'ar domin ƙaruwar lura da faɗakuwa da ilimi ga Masu gadin iyakoki
  • Raya tunawa da lahira cikin ƙwaƙwalen Masu gadin iyakoki domin gudun juya baya da abokan gaba
  • Addu'a domin Imani da taƙawa
  • Addu'ar domin mantawa da duniya yayin da mujahidai suke gwabza yaƙi da abokan gaba
  • Addu'a domin tunawa da aljanna da lura da ni'imominSa a fagen daga
  • Ni'imomin lahira sun wuce tunanin duk wani Mai tunani
  • Addu'a domin raunanar abokan gaba da gazawa a fagen yaƙi
  • Addu'a domin nasarar ƙoƙarin mujahidai da yaɗuwar tauhidia duk duniya
  • Addu'a domin cin nasara kan maƙiya a kan iyakokin Muslunci
  • Addu'a domin ganin bayan maƙiya Allah a faɗin duk duniya
  • Taka rawar da taimakon ɓoye yake yi cikin galaba kan maƙiya
  • Ganin bayan Kafirai, da gina al'umma masu tauhidi
  • Addu'a domin ƙarfafar hangen nesa da shiryarwa mai kyau ga Musulmi
  • Addu'a domin ƙarfafar dakarun Muslunci
  • Addu'a domin ƙarfafar dakarun Musulmi tare da Mala'iku
  • Ishara zuwa ga taimakon da Allah ke yi wa Musulmi a filin yaƙin Badar
  • Addu'a domin shagaltar da Mushrikai da Kafirai
  • Addu'a domin sanya kasala a jiki da tunanin Mushrikai yayin da suke Shirin yaƙi da Musulmi
  • Addu'a domin amfanuwar mujahidai da taimakon ɓoye kamar dai yadda ta faru a yaƙin Badar
  • Addu'ar domin gafalar maƙiya
  • Addu'ar fatan alheri ga mayaƙan Muslunci
  • Bayanin sharuɗɗan mayaƙan Muslunci (Nesantar son kai da riya)
  • Addu'a domin kyawuntar ƙarshen rayuwa
  • Addu'ar domin rabauta da shahada bayan nasara
  • Roƙon lada ga waɗanda suke kula da lamurran iyalan mayaƙan Muslunci da suka rasu a kan iyakoki
  • Samun Daraja cikin himmatu da damuwa da kishin Muslunci da kuma niyyar jihadi tare da abokan gaba
  • Roƙon ladan jihadi ga waɗanda ba su samu damar zuwa yaƙi saboda wani uzuri da kuma iyalan shahidai, Allah ya sanya su cikin sahun shahidai da salihai da abidai
  • Roƙon salati ga Muhammad (S.A.W) da iyalansa
  • Fa'idoji da darajojin taimakon da mutane da suke a bayan fagen daga ga jaruman Muslunci: kowa da kowa ya kamata ya sa hannu cikin ba da kariya ga Muslunci, ƙarfafa gwiwar dakarun Muslunci da samar da ƙarfin zuciya da fata ga gobensu, ƙarfafa zuciyar mutane domin ba da kariya, samar da haɗin kai da aiki kafaɗa da kafaɗa da juna cikin al'ummar Musulmi.[3]

Karanta Wannan Addu'a A Lokacin Yaƙi

Ba'arin ƴanshi'a suna karanta wannan addu'a sa'ilin da maƙiya Muslunci suka kawo hari kan ƙasashen Muslunci ko kan Musulmi. Alal misali lokacin yaƙin da Isra'ila ta dinga yi kan mutanen zirin Gaza, wasu jama'a daga mutanen Iran sun dinga shirya taro suna karanta wannan addu'a domin samun mafita ga al'ummar Falasɗinu.[4] Har ila yau daidai lokacin yaƙin Isra'ila kan mutanen Gaza da Labanun da ya faru a shekarar 2023-2024 binciko wannan addu'a a kafar Intanet ya yi matuƙar ƙaruwa.[Akwai buƙatar kawo madogara]

Sharhi-Sharhi

Cikin sharhin addu'a ta ashirin da bakwai cikin sahifa sajjadiyya, an rubuta wasu adadin litattafai, daga jumlarsu akwai:

  • Littafin Siyasatul Harbi Fi Du'a'i Ahlis Sugur, na Jafar Murtada Amili, littafi ne cikin fasalai guda huɗu tare da sharhi dabarun yaƙin ba da kariya ga iyakokin Muslunci.[5] Wannan littafi an buga shi ta hannun Al-markazul Islami Lil Dirasat, a shekarar 1428 hijira ƙamari. Har ila yau, akwai tarjamar Farsi da cibiyar Nashar Ma'arif ta buga a shekarar 2010 miladiyya.
  • Marzedaran Dar Du'aye Imam Sajjad (A.S), na Baitullahi Bayat Zanjani, littafi ne da yake ɗauke da fasalai guda 42, kamfanin Intisharate Mehri Amiril Muminin ne suka buga shi a shekarar 2010 miladiyya.[6]

Haka nan kuma an yi sharhi kan addu'ar dakarun kan iyakoki daga littafin sahifa sajjadiyya, misalin Diyare Ashiƙin na Husaini Ansariyan,[7] da Shuhud Wa Shenakt na Muhammad Hassan Mamduhi Kermanshahi[8] da Sharhe Wa Tarjume Sahife Sajjadiyye na Sayyid Ahmad Fihiri.[9]

Addu'a ta ashirin da bakwai sahifa sajjadiyya an yi sharhi a kanta da harshen larabci, cikin litattafai misalin Riyadus Salikin na Sayyid Ali Khan Madani,[10] Fi Zilalis Sahifatis Sajjadiyya na Muhammad Jawad Mugniyya,[11] Riyadul Arifin, talifin Muhammad Bin Muhammad Darabi[12] da Afaƙur Ruhi, na Sayyid Muhammad Husaini Fadlullahi[13] Har ila yau, an samu waɗanda suka rubuta sharhi kan ɗaiɗaikun kalmomin da suke cikin wannan addu'a, kamar misalin littafin Ta'aliƙat Alas Sahifatis Sajjadiyya na Faizul Kashani[14] da Sharhu Assahifatis Sajjadiyya na Izzud-dini Al-jaza'iri.[15]

Bayanin kula

  1. Mamdohi Kermanshahi, Shuhud Wa Shenakt , 2009, Vol. 2, ku. 449.
  2. Sobhani, Farhange Aqayid Wa Mazahibil Islamiyya, 2016, Juz. 6, shafi. 407.
  3. Ansari, Diyar Asheqan, 1994, Juz. 7, shafi na 25-76; Mamdohi, Kitabe Shuhud Wa Shenakt
  4. «قرائت دعای «اهل ثغور» به نیت رهایی مردم غزه با صدای میثم مطیعی»، Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
  5. سیاسه الحرب فی دعاء اهل الثغور Shafin Kitabpediya
  6. شرحی بر دعای بیست و هفتم Shafin Gisoom
  7. Ansari, Diyar Asheqan, 1994, Juz. 7, shafi na 25-76.
  8. Mamdohi, KItabe Shuhud Wa Shenakt, 2009, Juz. 2, shafi na 469-509.
  9. Fahri, Sharhe Wa Tafsir Sahifa Sajjadiyah, 2009, juzu'i. 2, shafi na 453-473.
  10. Madani Shirazi, Riad al-Salkin, 1435 AH, Juz. 4, shafi na 177-280.
  11. Mughniyyah, Fi Zilal al-Sahifa, 1428 AH, shafi na 347-368.
  12. Darabi, Riyadh al-Arifin, 1379, shafi na 343-372.
  13. Fadlallah, Afaqur Ruhi, 1420 AH, Juz. 2, shafi na 39-78.
  14. Faiz Kashani, Ta'aliqat Ala Sahifa al-Sajjadiyyah, 1407 AH, shafi na 61-65.
  15. Jazayeri, Sharhu Al-Sahifa Al-Sajjadiyah, 1402, shafi na 147-155.

Nassoshi

  • Ansarian, Hossein, Diyare Ashiqin: Cikakken Sharhi Akan Sahifa na Sajjadieh, Tehran, Payam Azadi, 1993.
  • Jazayeri, Ezzul-Din, Sharhu Sahifa al-Sajjadiyyah, Beirut, Dar al-Ta'arif Publications, 1402H.
  • Darabi, Muhammad bin Muhammad, Riyadh al-Arifin fi Sharh al-Sahifa al-Sajjadiyyah, bincike na Hossein Dargahi, Tehran, Asvah Publishing, 1379.
  • Sobhani, Jafar, Farhange Aqayid Wa mazahib Islami, Qum, Tohid, 2016.
  • Fadlallah, Sayyid Muhammad Hussein, Afaqur Ruhi, Beirut, Dar al-Malik, 1420H.
  • Fahri, Sayyid Ahmad, Sharhe Wa tarjame Sahifeh Sajjadieh, Tehran, Asvah, 2009.
  • Faiz Kashani, Mohammad Bin Mortaza, Ta;'aliqat Ala Al-Sahaifa Al-Sajadiyeh, Tehran, Cibiyar Al-Pakheeh da Al-Thaqafiyyah, 1407H.
  • «قرائت دعای «اهل ثغور» به نیت رهایی مردم غزه با صدای میثم مطیعی»،Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, labarin da aka buga: Agusta 8, 2014, ziyarci: Oktoba 1, 2014.
  • Madani Shirazi, Sayyid Ali Khan, Riyad al-Salkin fi Sharh Sahifa Seyyed al-Sajdin, Qom, Al-Nashar al-Islami Institute, 1435H.
  • Mughniyeh, Muhammad Jawad, A Inuwar Al-Sahifa Al-Sajjadiyyah, Qum, Dar Al-Kitab Al-Islami, 1428H.
  • Mamdohi Kermanshahi, Hassan, Shuhud Wa Shenakt, gabatarwar Ayatullahi Jawadi Amoli, Qom, Bostan Ketab, 2009.