Wuri Mai Albarka

Daga wikishia

Wuri Mai Albarka (Larabci: البقعة المباركة) ko Wadi Muƙaddas ɗuwa ko kuma Wadi Aiman, wani wuri ne da Ubangiji ya yi Magana da Musa (A.S) ya zaɓe shi da Annabta, Al-Buƙ’atul Almubaraka (Wuri Mai Albarka) wani yankin ƙasa ne da cikin Alkur’ani aka yi ishara game da albarka da yake tare da ita, aksarin Malaman tafsiri suna ganin wannan wuri ya samu albarka ne sakamakon maganar da Allah ya yi wa Musa (A.S) a wurin, sakamakon tsarkakar wannan wuri Allah ya umarci Annabi Musa (A.S) da ya cire takalaminsa a wannan wuri.

Taƙaitacciyar Gabatarwa

Al-Buƙ’atul Almubaraka, yana nufin wani yankin ƙasa da yake tattare da albarka, kuma isɗilahi ne na Akur’ani da aka yi amfani da shi sau ɗaya cikin Alkur’ani, [1] lokacin da cikin dare Musa (A.S) ya nufi tafiya ƙasar Misa daga garin Madyana, sai wata wuta daga Dutsen Sina ta ɗauki hankalinsa sai ya nufi wurin wannan wuta, [2] bisa aya ta 30 suratul ƙasas “bayan ya isa wurin wannan wuta daga gefen daman kwazazzabo a wannan wurin mai albraka sai ya ji kira ya Musa ni ne Allah Ubangijin halittun duniya” a wannan lokaci ne Allah ya zaɓi Musa da Annabta ya kuma bashi Mu’ujizar Sanda da Farin Hannu. [3] A ba’arin wasu Matanan littafan riwaya na Shi’a, an siffanta Mahallan da aka binne Annabi (S.A.W) [4] da Imaman Shi’a (A.S) [5] a matsayin wuri mai albarka hakama an ambaci Karbala da wuri mai albarka. [6]

Wurin Da Yake

Labarin maganar da Allah ya yi da Hazra Musa (A.S) an yi ishara zuwa ga wannan Magana a wasu wuraren daban a cikn Alkur’ani , cikin suratul ɗaha da Annzi’at an kira wurin da Musa ya ji sautin Allah da sunan “Wadi Muƙaddas ɗuwa” [7] wuri ne sakamakon tsarkakarsa Allah ya umarci Musa (A.S) da ya cire takalminsa, [8] da wannan dalili ne Malaman tafsiri suke ganin Al-Buƙ’atul Almubaraka (Wadi Muƙaddas ɗuwa) ita ce dai “Wadul Aiman”, [9] wannan wuri yana nan a kudancin Saharar Sina, a lokacin tafiya Misra daga Madyana cikin ɓangaren dama anan Dutsen ɗuru yake [10] Amma cikin ba’ari daga riwayoyi an bayyana cewa abin da ake nufi da Al-Buƙ’atul Almubaraka shi ne garin Karbala, wannan riwayoyi waɗanda aka naƙalto su a cikin littafan Kamilul Az-Ziyarat [11] da Tahzibul Al-Ahkam [12] riwayoyin sun zo da Kalmar (Shaɗi Al-Wadil Al-Aiman) a cikin ayar an yi tawilin Furat da Buƙ’atul Al-Mubaraka da garin Karbala, Faizul Kashani ya yi ishara da wannan riwaya, [13] cikin littafin Al-Burhan fi Tafsir [14] da Biharul Al-Anwar [15]nan ma an kawo wannan riwaya, ba’arin marubuta suna ganin wannan ra’ayi ya saɓawa zahirin ayar, [16] cikin ba’arin littafan ziyarorin Imamai nan ma an ambaci makwancinsu da sunan Al-Buƙ’atul Al-Mubaraka. [17] [yadast 1]

Kasancewarsa Wuri Mai Al-Barka

Galibin Malaman tafsiri na Shi’a da Ahlus-sunna suna ganin dalilin albarkar wannan wuri ta samu ne sakamakon maganar da Allah ya yi tare da Musa (A.S) wuri ne da a cikinsa ne aka zaɓi Musa (A.S) da Annabta. [18] Allama ɗabaɗaba’i ya tafi kan cewa wannan wuri ya zama mai albarka ne sakamakon maganar da Allah ya yi da Musa a wajen, [19] amma wasu ba’ari suna ganin samuwar Bishiyoyi da ƴaƴan itaciya sune sababin Albarkar wurin, [20] ɗabarasi yana cewa wannan wuri shi ne dai wurin da Allah ya yi Magana da Musa ya umarce shi da cire takalminsa, [21] Allama ɗabaɗaba’i shima yana ganin dalilin albarkar wannan wurin ya samo asali daga umarnin da Allah ya bawa Musa na cire takalminsa, [22] marubucin littafin Al-Tibyan fi tafsirul Al-Kur’an kan asasin wata riwaya daga Imam Ali (A.S) yana ganin cewa umarnin Allah ga Musa (A.S) shi ne dalilin samun albarkar wannan wuri. [23] A gefe guda kuma, cire takalmi da Musa (A.S) ya yi ana ɗaukarsa ƙololuwar tawali'u na ƙarshe don karɓar saƙon Allah. <ref><Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 13, shafi na 168./ref>

Bayanin kula

  1. Heydari, “Buk'atu Mubarakeh”, juzu’i na 5, shafi na 612.
  2. Duba: Mustafavi, Tahaƙiƙ fi Kalamat al-ƙur'an al-Karim, 1360, juzu'i na 1, shafi na 315.
  3. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1374, juzu'i na 16, shafi na 75-77.
  4. Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419H, shafi na 55.
  5. Shahid I, al-Mazar, 1410 AH, shafi na 34, 65; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419H, shafi na 555.
  6. Ibn ƙolwieh ƙommi, Kamel Al-Ziyarat, 1356, shafi na 49; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419H, shafi na 115.
  7. Suratul Taha, aya ta 11-12, Suratul Nazaat, aya ta 16.
  8. Suratul Taha, aya ta 12.
  9. Faiz Kashani, Al-Asfi, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi na 902.
  10. Heydari, “Buk’atu Mubarakeh”, juzu’i na 5, shafi na 613.
  11. Ibn ƙolwieh, Kamel Al-Ziyarat, 1356, shafi na 48-49.
  12. Sheikh Tusi, Tahzeeb Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 38.
  13. Faiz Kashani, Al-Asfi, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi na 927.
  14. Bahrani, Al-Burhan, 1416 AH, juzu'i na 4, shafi na 265.
  15. Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 13, shafi na 25.
  16. Heydari, “Baka’a Mubarakeh”, juzu’i na 5, shafi na 614.
  17. Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 97, 160-161, juzu'i na 107, shafi na 152
  18. Sheikh Tusi, Al-Tibyan, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 7, shafi.392; Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 7, shafi.392; Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 16, shafi na 32; Ibn Juzi, Zadal al-Masir,1422 AH, juzu'i na 3, shafi na 383
  19. Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 16, shafi na 32.
  20. Sheikh Tusi, Al-Tibyan, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 7, shafi na 392.
  21. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 7, shafi na 392.
  22. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 16, shafi na 32
  23. Sheikh Tusi, Al-Tibyan, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 7, shafi na 164

Nassoshi

  • Ibn Juzi, Abd al-Rahman bin Ali, Zadal Al-Masir, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1422H.
  • Ibn ƙolwieh, Jafar bin Muhammad, wanda: Abdul Hossein Amini, Kamel Al-Ziyarat, Najaf, Dar al-Mortazawieh, 1356 ya inganta.
  • Ibn Mashhadhi, Muhammad Ibn Jafar, Al-Mazar Al-Kabir, Edited by: Javad ƙayyumi Isfahani, ƙum, Islamic Publication Office mai alaka da kungiyar malamai ta Kum Seminary Society, 1419 AH.
  • Bahrani, Sayyid Hashim, Al-Burhan fi Tafsir ƙur'an, Tehran, Ba'ath Foundation, 1416H.
  • Heydari, Hassan, “Baka’a Mubarakah” in the encyclopedia of the Holy ƙuran, 1382.
  • Shahidi Awwal, Muhammad Bn Makki, Al-mazar, editan: Muhammad Baƙer Mohd Abtahi Esfahani, ƙum, Makarantar Imam Mahdi, 1410H.
  • Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin ƙur'an, ƙum, ƙum seminary community, 1417H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma Al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosrow Publications, 1372.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tibyan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, Bita.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Tahzeeb Al-Ahkam, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Faiz Kashani, Mhilmasan, Al-Asfi Fi Tafsirul Al-ƙur'an, Kum, Cibiyar Buga Ofishin Da'awar Musulunci, 1418H.
  • Majlesi, Muhammad Baƙir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
  • Mostafavi, Hassan, Tahkik fi Kalmat Kur'anil Alkareem, Tehran, Kamfanin Fassara da Bugawa, 1360.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1374.