Maganar Allah Tare da Musa
Maganar Allah tare da Musa (Larabci:تَكلِيم الله لموسى (ع)) Yana nufin zance da Allah ya yi da Annabi Musa, wadda aka ce ya gudana kai tsaye ba tare da shiga tsakani na mala’ika ba. An ɗauki maganar da Allah ya yi da Annabi Musa (a.s) a matsayin wani abu daya keɓanta da shi da kuma wata falala a gare shi. A wasu ayoyi na ƙurr’ani kamar aya ta 164 a cikin suratun Nisa’i, an bayyana cewa Allah ya yi magana da Musa, Sifa ta Kalimullah (wanda Allah ya yi magana da shi) ta keɓanta ga Annabi Musa (AS), kuma saboda haka ake kiran Yahudawa da sunan “Kalimi”.
Wasu malaman Shi’a irin su Sheikh ɗusi sun yi imanin cewa maganar da Allah ya yi wa Musa (A.S) gaskiya ce. A cikin hadisai an yi la’akari da maganar Allah ba tare da amfani da baki ko harshe ba. Akwai ra'ayoyi daban-daban game da yadda Allah yayi magana da annabi musa kamar haka: Wasu malaman tafsirin Shi'a sun yi imani da cewa Allah ya halicci muryoyi masu amo da suke fidda sauti , ta hakan yayi magana da Annabi musa, wasu kuma sukace : Allah bai ambata mana yadda maganar ta faru ba, haka nan ma ba mu samu hanyar fahimtar yanda ya yi magana ba daga tafsirin Alkur’ani. Wasu malaman musulmi sun yi imanin cewa ban da Musa (A.S), Allah ya yi magana da Annabin Musulunci (S.A.W) kai tsaye.
Kasancewar Musa (A.S) Abokin Maganar Allah
Kamar yadda aya ta 164 a cikin suratun Nisa’i ta ce, Allah ya yi magana da Musa (A.S)” «کَلَّمَ الله مُوسی تَکْلیماً؛ kuma Allah ya yi magana da Musa magana.[1] A cikin aya ta 144 a cikin suratul A’araf, an ambaci cewa Allah ya yi magana da annabi Musa,[2] kuma wannan magana ana ganin ita ce dalilin fifikonsa a kan dukkan mutane. wasu malaman musulmi[3] da yahudawa,،[4] suna ganin tabbas wannan kebanta da Sayyidina Musa (a.s) yayi da wannan siffa itace dalilin fifiko da falalar da yake da ita.[5]
An ambaci siffar Kalimullah musamman ga Annabi Musa (a.s)[6] kuma ance wannan sifa ta Annabi Musa ita ce ta sa ake kiran Yahudawa da sunan “Kalimi”[7] Wasu malaman musulmi sun yi imani da cewa Allah ma ya yi magana da Manzon Allah (S.A.W.W) a mi’iraji, hakama hadisai sun tabbatar da wannan magana[8] kuma Sun yi imani cewa sadarwa ta kai tsaye da Allah ta kebanta da Annabin Musulunci (SAWW) da Musa (a.s) ne.[9]
An ɗauki maganar Allah a matsayin magana ba tare da jiki ba , Domin yin magana da harshe da igiyar murya alama ce ta samun jiki, alhali kuwa Allah ba shi da jiki[10] Imam Ali (a.s) a ƙarƙashin wannan maganar yana cewa: maganar Allah da Sayyidina Musa (a.s) magana ce da ba ta da buƙatar kowane sassa na jiki da sauran abubuwan buƙatar yin magana na nan duniya,[11] Hakanan Imam Rida (a.s.) ya yi bayyana cewa maganar Allah tare buƙatar amfani da baki ko harshe ko wani abu mai kama da hakan, tabbas maganar Allah tasha bamban da maganar da halittu ke yi da juna.[12]
- ku duba: Kalimullahi (Laƙabi)
Magana Kai Tsaye Ba Tare da Hijabi ba
A cewar malaman musulmi, zancen da Allah ya yi da Annabi Musa (a.s) kai tsaye ne[13] ba tare da shiga tsakani na mala'ika ba.[14] Ɗabarsi, marubucin Tafsirin Majmaul-Bayan, ya ce bambancin maganar da Allah ya yi da sauran annabawa shi ne , Allah ya yi magana da Musa (A.S) ba tare da wani a tsakani ba.[15] a wannan kalar maganar ana jin muryar amma ba'a ganin mai maganar, Domin akwai wani mayafi da cikas da ke hana ganin mai maganar.[16]
Sheikh Ɗusi ya ganin maganar da Allah ya yi da Annabi Musa (a.s) tabbas kai tsaye ce a gasken gaske.[17] Wasu malaman tafsiri sun ɗauki lafazin “taklima" a cikin ayar «وَ کَلَّمَ الله مُوسی تَکْلیماً»[18] a matsayin shaida na haƙiƙanin maganar kuma kai tsaye .Maganar Allah haƙiƙace ba majazi ba wato ba ta hanyar aron wani abu kamar murya ko wani abu mai kama da haka ba.”[19] A cewar Allama ɗabaɗaba'i, mawallafin Tafsirin al-Mizan, maganar da Allah ya yi wa Musa haƙiƙa ce kuma tana da tasirin magana ta kai tsaye, kamar yanda kowa ke magana a fahimci ma'anar abin da yace , to Allah yayi magana kai tsaye da annabi musa ba ta harshe da makogwaro ba.[20]
Hanyar da Allah Ya yi Magana tare da Musa (A.S)
Makarim Shirazi, malamin Shi’a kuma mai tafsiri , ya yi imanin cewa, Allah ya yi magana da Annabi Musa (AS) ta hanyar samar da sautin igiyar sauti,[21] hakanan Sheikh Ɗusi ma yace: Allah yana samar da muryoyi a jikin wasu abubuwan halitta danya isar da magana ga kunnuwa[22] wasu masu tafsiri kuma sun ruwaito cewa Allah ya halicci sauti da magana sai Musa (a.s) ya ji.[23]
A ɗaya ɓangaren kuma, Allama ɗabaɗaba'i ya yi imani da cewa Allah bai ambata mana yadda yake magana ba, haka nan muma bamu fahimci hakan daga tafsirin Alkur’ani ba, Muhammad Javad Mugniyh, ɗaya daga cikin malaman Shi’a. yana cewa Allah yayi shiru akan yadda yake magana da annabawansa kuma bai bayyana mana ba.[24] don haka Mu ma mun yi shiru a kan haka kuma ba buƙatar dogon sharhi.[25]
Bayanin kula
- ↑ Suratul Nisa’i, aya ta 164.
- ↑ Sheikh Tusi, al-Tabayan, Beirut, juzu'i na 3, shafi na 394; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 11, shafi na 267.
- ↑ Sheikh Tusi, al-Tabayan, Beirut, juzu'i na 3, shafi na 394; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 11, shafi na 267.
- ↑ «لقب حضرت موسی به فارسی چه میباشد و نبوت ایشان چگونه بود؟»، انجمن کلیمیان تهران.
- ↑ ƙureshi, Tafsiri Ahsan al-Hadith, 1377, juzu'i na 1, shafi na 470; Rashid Reza, Al-Manar, 1990, juzu'i na 3, shafi na 4
- ↑ Fazlullah, Tafsirin Man Wahayi Al-ƙur'an, 1419 AH, Juzu'i na 20, shafi na 202
- ↑ «لقب حضرت موسی به فارسی چه میباشد و نبوت ایشان چگونه بود؟»، انجمن کلیمیان تهران.
- ↑ Banu Amin, Makhzan Al-Irfan dar Tafsiri ƙur'an, 1361, juzu'i na 2, shafi na 379.
- ↑ Boroujerdi, Tafsir Jame, 1366, juzu'i na 2, shafi.462.
- ↑ Makarem Shirazi, Yek Sado hashtad pursheh wa pasukh, 2006, shafi na 75.
- ↑ Sheikh Sadouƙ, Al-Tauhidi, 1398H, shafi na 79.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 4, shafi na 152.
- ↑ Mughniyeh, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 2, shafi.495
- ↑ Tayeb, Ateeb Al Bayan, 1378, juzu'i na 5, shafi na 452.
- ↑ Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 3, shafi na 218.
- ↑ Fazlullah, Tafsirin Man Wahayi Al-Qur’an, 1419 AH, Juzu’i na 20, shafi na 202.
- ↑ Sheikh Tusi, al-Tabayan, Beirut, juzu'i na 3, shafi na 240.
- ↑ Suratul Nisa’i, aya ta 164.
- ↑ Qortubi, Al-Jamae Laahkam al-Qur'an, 1364, juzu'i na 6, shafi na 18.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, Juzu'i na 2, shafi na 315 da 316.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh 1374, juzu'i na 6, shafi.363.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Rasa'il al-Ashhar, 1414H, shafi na 95.
- ↑ Hosseini Shirazi, Tabayin al-Qur'an, 1423 AH, shafi 115.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 316.
- ↑ Mughniyeh, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 2, shafi na 495.>
Nassoshi
- Ibn Qayyim Jozi, Hadi al-Arwahi ila al-Bilad al-Afarah, Beirut, Alam al-Katb, Bita.
- Ibn Kathir, Ismail bin Amr, Tafsir al-Qur'an al-Azeem, Research: Muhammad Hossein Shamsuddin, Dar al-Kitab al-Alamiya, Beirut, Muhammad Ali Bizoon's pamplets, bugu na farko, 1419 AH.
- Bano Amin, Makhzan Al-Irfan dar Tafsir Kur'an, Tehran, Muslim Women's Movement, 1361.
- Boroujerdi, Seyyed Mohammad Ibrahim, Tafsir Jame, Tehran, Sadr Publications, bugu na 6, 1366.
- Hosseini Shah Abdul Azimi, Hossein bin Ahmad, Tafsir Esna Ashhari, Tehran, Miqat Publications, bugun farko, 1363.
- Hosseini Shirazi, Sayyed Mohammad, Tabayin al-Qur'an, Beirut, Darul Uloom, bugu na biyu, 1423H.
- Rashid Reza, Tafsir al-Manar, Misr, Al-Masriyah al-Katab, 1990.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, al-Tawhid, mai bincike kuma mai karantawa: Hashim Hosseini, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na farko, 1398H.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Rasa'il al-Ashhar, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na biyu, 1414H.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsir al-Qur'an, gabatarwa: Sheikh Agha Bazar Tehrani, bincike: Ahmad Qasir Ameli, Beirut, Darahiya al-Trath al-Arabi, Bita.
- Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Al-Qur'an, Qum, Islamic Publications Office, bugu na biyar, 1417H.
- Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
- Tayeb, Seyyed Abdul Hossein, Atyeb al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Islam Publications, bugu na biyu, 1378.
- Fakhr Razi, Muhammad Ibn Umar, Al-Tafsir al-Kabir (Mufatih al-Ghayb), Beirut, Darahiya al-Trath al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
- Fazlullah, Seyyed Mohammad Hossein, Tafsir Man Wahayi Al-Qur'an, Beirut, Dar al-Mulak Lalprinta da Al-Nashar, bugu na biyu, 1419H.
- Qurtubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jamae Ahkam al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow Publications, bugu na farko, 1364.
- «لقب حضرت موسی به فارسی چه میباشد و نبوت ایشان چگونه بود؟»، انجمن کلیمیان تهران تاریخ بازدید: ۱۷ آبان ۱۴۰۰ش.
- Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
- Mughniyeh, Mohammad Javad, Tafsir al-Kashif, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, bugun farko, 1424H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, bugun farko, 1374.
- Makarem Shirazi, Nasser,Yek sado hashtad pursehe wa pasukhi, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, 2006.