Jump to content

Wasa Da Sallah

Daga wikishia

Wasa da sallah (Larabci: الاستخفافُ بالصلاة) shi ne yin sakaci da wasa da yin sallah a kan lokaci, hakan yana bayyana ne ya yin da mutum yake rama ta bayan fitar lokacinta ko tauye wani rukuni ko wajibi.

An yi saɓani kan cewa wana abu ne yake nuna cewa mutum yana wasa da sallah, wasu suka tafi kan cewa jinkirta sallah ba tare da uziri ba, shi ne wasa da sallah, da rashin nutsuwa a lokacin sallah da ƙarancin tsoran Allah duk suna cikin wasa da sallah, daidai lokacin da wasu kuma suke ganin cewa waɗannan abubuwa ba sa abubuwa da suka zo a ruwayoyi da aka yi alƙawarin azaba ga duk wani mai wasa da sallah.

Malaman fiƙihu na Shi'a sun yi imani da haramcin yin wasa da Sallah kuma tasiri da sakamako na yin wasa da sallah ya zo cikin riwayoyi, daga ciki akwai rashin samun ceton Ahlul-baiti, da cewa ba za a karɓi sallar mutum ba, da kuma rashin tsawon kwana, da cewa mutum zai mutu ƙasƙantacce, da azabar kabari.

Haɗarin Wasa Da Sallah

Shaik Ɗarihi ya ambata a cikin littafin Majma'ul Bahraini cewa rashin yin sallah a kan lokaci yana nufin wulaƙanta ta kuma sakamakon hakan shi ne ƙaryata da kuma kuma ƙin yarda da ita.[1] Wasu masu bincike sun tafi kan cewa wannan bayanin yana nuna ƙin yarda da matsayin sallah da muhimmancinta, amma ba kore samuwar asalin halascin sallar ba.[2]

Riwayoyi da yawa sun zo suna hana Muminai yin sakaci da wasa da sallah.[3] An kuma tara waɗannan riwayoyi a babi ɗaya mai zaman kan shi a cikin littafin Wasa'ilush Shi'a.[4] Ita sallah ana la'akari da ita a matsayin wata alama ta addinin Muslunci. Saboda haka ne idan mutum ya yi wasa da ita zai zama kamar ya yi wasa da addinin ne gaba ɗaya kuma wata ƙila wannan ne ya sa aka yi gargaɗi da yawa da kuma alƙawarin azaba mai tsanani iga Mai wasa da sallah.[5]

Malaman fiƙihu na Shi'a sun yi ijma'i cewa yin wasa da sallah haramun ne a Shari'a,[6] Shaik Murtada Muɗahhari yana cewa duk wanda yake wasa da sallah zai shiga ƙarƙashin wannan ayar faɗin Allah maɗaukaki a cikin suratul Mudassir"قالوا لَمْ نَكُ مِنَ الْمُصَلِّين"(Mu ba mu kasance cikin masu yin sallah ba),[7] wasa da sallah zai fitar da mutum daga cikin masu sallah a ranar ƙiyama.[8]

Wasu Daga Abubuwa Da Ake La'akari A Matsayin Wasa Da Sallah

An ambaci wasu abubuwa da yawa waɗanda idan nutun yana yinsu to yana cikin masu wasa da sallah ga masu muhimmmanci daga cikinsu;

  • Mutum ya rama sallah saboda sakaci da lalaci.[9]
  • Barin sallah ba tare da uziri na Shari'a ba.
  • Rashin kulawa da wajibai ya yin sallah, kamar barin nutsuwa ko barin zikiri na ruku'u da sujjada.[10]
  • Rashin halartar sallar jam'i sakamakon nuna rashin muhimmancinta[11]
  • Jinkirta sallah daga farkon lokacin ta ba tare da wani dalili karɓaɓɓe ba.[12]
  • Rashin koyan hukunce-hukuncen sallah, da yin zikiri da sauri ta yadda kamar ba a yi su ba a ingatacciayr hanya, musamman a ruku'Iu da sujjada.[13])

Wasu masu bincike suna ganin cewa alƙawarin azaba a lahira da haramcin yin wasa da sallah kamar yadda ya zo a riwaya, bisa dogaro da hakan waɗannan abubuwa da aka ambata waɗanda su ne ake nufi da wasa da sallah sun taƙaita ne kan abubuwan da suke wajibi, ba su ƙunshi abubuwan da suke mustahabbi ba[14] a ɗaya hannun kuma wasu suna ganin cewa wasa da sallah mataki mataki ne, kamar yadda barin mustahabbi ga waliyan Allah yana iya zama rashin kula da sallah da kuma wasa da ita.[15]

Sakamakon Wasa Da Sallah

Sakamako mai muni ga duk mutumin da yake wasa da sallah ya zo a cikin riwayoyi, ga abin da ya fi bayyana daga cikinsu;

  1. Rayuwarshi ba zata yi albarka ba.
  2. Dukiyarshi ba za ta yi albarka ba.
  3. Fuskar Mai wasa da Sallah za ta yi baƙi babu annuri.
  4. Ba za a karɓi aikinshi ba.
  5. Ba za a karɓi addu'arshi ba
  6. Kuma idan wasu suka yi mishi addu'a ba za a karɓa ba.
  7. Mai wasa da sallah zai mutu ƙasaƙantacce
  8. Kuma zai mutu yana mai jin yinwa
  9. Zai mutu yana mai jin ƙishirwa ko da ya sha ruwa da yawa
  10. Duhun kabari da kewa
  11. Za a azabtar da shi a kabari
  12. Za a ja shi a kan fuskarshi a ranar alƙiyama a gaban mutane.
  13. Kuma za a yi mishi hisabi mai tsanani
  14. Za a yi mishi azaba mai raɗaɗi a ranar lahira.
  15. Kuma ba zai sami rahamar Allah ba.[21]

Bayanin kula

  1. Al-Tarihi, Majma'ul Bahrain, 1375, juzu'i na 4, shafi na 48.
  2. Tayyeb Hosseini da Julai, "Mafhume Shinashi Istighfaf Wa Ida'atus Salat Wa Tahawun Nesbat Beh An", shafi. 62.
  3. Tayyeb Hosseini da Julai, "Mafhume Shinashi Istighfaf Wa Ida'atus Salat Wa Tahawun Nesbat Beh An", shafi. 58.
  4. Al-Hurrul al-Amili, Wasa'il al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 23.
  5. «هشدارهاي اجتماعي؛ سبك‌ شمردن دين و نمادهاي ديني»،Shafin yanar giza gizo na Hauza Ilmiyya..
  6. Al-Shahrudi, Kitab Hajji, 1402 AH, juzu'i na 1, shafi na 17; Madani al-Kashani, Barahinul Hajji Lil Fuqaha Wal Hujjaj, 1411H, juzu’i. 1, shafi. 15.
  7. Suratul Madassir, aya ta 43.
  8. Motahari, Ashnayi Ba qur'ani (10), 2010, shafi na 170 da 171.
  9. Tabrizi, Sarat al-Najat, 1427 AH, juzu'i. 10, ku. 429.
  10. «كتاب الصلاة/ بررسي معني استخفاف در نماز/ تعداد نمازهاي واجب»،Shafin yanar gizo na Mohammad Taqi Shahidi's .
  11. Al-Khoei, Sarat al-Najat, 1416 AH, juzu'i. 3, shafi. 332.
  12. Yousefian da Ilhami, Akhlaq Islami, 1376, juzu'i na 1, shafi na 53.
  13. Yousefian da Ilhami, Akhlaq Islami, 1376, juzu'i na 1, shafi na 53.
  14. Tayyeb Hosseini da Joulai, "Mafhumshinasi Istifaf Wa Iza'a Namaz Wa Tahawune Nesbat Ba An", shafi na 66-63 da 74.
  15. Tayyeb Hosseini da Joulai, "Mafhumshinasi Istikhfaf Wa Iza'a Namaz Wa Tahawune Nesbat Ba An", shafi na 74.
  16. Alkulaini, Kafi, 1407 AH, Juz. 3, shafi. 269.
  17. Sheikh al-Saduq Man Lay Hazra Al-Faqih, 1367, juzu'i. 1, shafi. 206.
  18. Sheikh Al-Sadooq, Amali, 1376, shafi. 484.
  19. Al-Barqi, Al-Mahasen, 1371 AH, Juz. 1, shafi. 79.
  20. Ibn Tavus, Falahul Al-Sa'el, 1406 Hijiriyya, shafi na. 22.
  21. Ibn Tavus, Falah Al-Sa'eel, 1406 Hijiriyya, shafi na. 22.

Nassoshi

  • Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, Fallah Al-Sa'eel Wa Najah Al-Masa'il, Qum, ofishin yada farfagandar Musulunci, bugu na farko, 1406H.
  • «اهميت نماز»،Shafin Makiran, bugawa: 25 Mehr 1388 Hijira, kwanan duba: 26 Mehr 1403 AH.
  • Tabrizi, Javad, Sarat al-Najat, Qum, Dar al-Siddiqah al-Shahida, bugun farko, 1427H.
  • Al-Har al-Amily, Muhammad bin Hasan, Wasa'ilul Al-Shi'a, Qum, Al-Bait Foundation, 1409H.
  • Al-Khoei, Sayyid Abu al-Qasim, Sarat Al-Najat (Al-Mahashi), Kum, Publishing Office, bugu na farko, 1416H.
  • Al-Shahrudi, Sayyid Mahmoud bin Ali, Kitabul Hajji, Qum, Mu’assasa Ansari, bugu na farko, 1402H.
  • Sheikh Al-Sadooq, Muhammad Bin Ali, Amali, Tehran, Kitabji, bugu na 6, 1376.
  • Sheikh Al-Sadooq, Muhammad Bin Ali, Man La Yahdara Al-Faqih, Nash Al-Sadooq, 1367.
  • Tareehi, Fakhr al-Din, Majma'aul Al-Bahrain, bincike: Sayyid Ahmad Al-Hussaini, Tehran, Library Mortazavi, bugu na uku, 1375.
  • Tayeb Al-Hosseini, Al-Sayed Mahmoud da Maryam Julai, "Mafhumshinase Istighfaf Wa Iza'at Namaz Wa Tahawun Nesbat Beh An", a cikin mujallar nazarin fikihu na zamani, lamba 4, kaka da bazara 2016.
  • «كتاب الصلاة/ بررسي معنى استخفاف در نماز/ تعداد نمازهاي واجب»، Shafin yanar gizo na Mohammad Taqi al-Shahidi, bugawa: 13 Shahrivar 1395, duban rana: 19 Mehr 1403.
  • «هشدارهاي اجتماعي؛ سبك‌شمردن دين و نمادهاي ديني»،Shafin yanar gizo nawatsa labarai na Al-Hawza, ranar bugawa: 8 ga Nuwamba, 1390, kwanan duba: Mehr 16, 1430.
  • Yousefian, Nematullah da Ali Asghar Elhami, Akhlaq Islami, Amuzeshaye Akidati Siyasi Mumassiliya Wali al-Faqih fi Sepah, Qum, bugun farko, 1376.