Rayuwar Barzahu

Daga wikishia

Rayuwar Barzahu (Larabci:الحياة البرزخية)tana nufin rayuwar rayuka a duniyar Barzahu,kuma tabbatar da wasu mastsaloli suna dogara a kanta, kamar ji daga matattu da yi tawasuli da su,duk irin wanna sun dogara ne da tabbatar da rayuwar Barzahu. Domin tabbatar da wanzuwar rayuwar Barzahu, mun dogara ne da wasu ayoyin Alkur’ani da suka yi nuni kan rayuwar wasu gungu na mutane, kamar shahidai, kazalika ruwayoyi ma sunyi nuni kan rayuwar Barzahu.

Abin da Rayuwar Barzahu Take Nufi

Rayuwar matattu a cikin duniyar Barzahu, ana kiranta da rayuwar Barzahu, kamar yadda wasu ayoyi da ruwayoyi suka nuna, cewa rayukan matattu suna rayuwa ne a cikin duniyar Barzahu, kuma suna iya sadarwa tsakaninsu da rayayyu, don haka suna jin muryoyinsu. Kuma suna amsa musu.

Gangan Jiki na Rayuwar Barzahu

An bayyana jikin ɗan adam a matsayin jiki na rayuwar Barzahu,sabo da alaƙarshi da rai bayan mutuwa,an kuma ce badole ba ne yazama irin wanna jiki na duniya, wato wanda yake ɗauke da jini da tsoka,amma dai yana ɗauke da wasu sifofi irin na jikin ɗan adam a duniya.[1] [tsokaci1].

Misalai daga Kur'ani

Sabo da tabbatar da rayuwar Barzahu ana kafa hujja da ayoyin alaƙur’ani mai girma kamar haka; Kamar ayoyin da suke nuna wanzuwar wasu gungu na mutane a matsayin rayayyu bayan mutuwa,kamar shahidai.

﴿وَلا تَحسَبَنَّ الَّذینَ قُتِلوا في سَبیلِ اللَّهِ أَمواتًا ۚ بَل أَحیاءٌ عِندَ رَبِّهِم یرزَقونَ﴾[2]

Kuma kada ku yi zaton wadanda aka kashe a kan hanyar Allah matattu ne, a'a, rayayyu ne a gurin Ubangijinsu.

﴿ قِيلَ ادْخُلِ الْجَنَّةَ ۖ قَالَ يَا لَيْتَ قَوْمِي يَعْلَمُونَ

An ce: Ku shiga Aljanna. Ya ce: Inama dai mutanena sun sunsan [abin da narabauta da shi]. Malamin tabsiri na Shi'a Allama ɗabatabai ya dauki wannan ayar, da kuma aya ta 154 a cikin suratul Baƙara (tsokaci na 2) a matsayin hujjar samuwar rayuwar Barzahu, sai ya ce abin da ake nufi da aljanna. a cikinta akwai aljannar Barzahu ba aljannar lahira ba[4].

﴿وَقُلِ اعْمَلُوا فَسَیرَی اللَّهُ عَمَلَکمْ وَرَسُولُهُ وَالْمُؤْمِنُونَ وَسَتُرَدُّونَ إِلَیٰ عَالِمِ الْغَیبِ وَالشَّهَادَةِ فَینَبِّئُکم بِمَا کنتُمْ تَعْمَلُونَ

Kuma ka ce ku yi aiki, sai Allah Ya ga aikinku, da ManzonSa da muminai, kuma da sannu za’a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibu da shaida, kuma Ya ba ku labari ga abin da kuka kasance kuna aikatawa.[5] A kan wannan ayar Annabi da wasu muminai suna sane da halin da mutane suke ciki[6]. Sanna akwai ayoyi da suke maga kan maganar Mala’iku da mamata,[7] da kuma cewa aljanna da wuta suna cikin rayuwar Barzahu ne,[8] kazalika da ayoyin da suke magana akan rayuwar annabawa a barzahu.[9]

Dalili Samuwar Barzahu daga Ruwayoyi

Wasu ruwayoyi sunyi nuni kan yadda rayuwar annabawa take a Barzahu,malamin hadisi mai bincike a ƙarni na huɗu ya tara wasu daga cikin wanna ruwayoyin a cikin littafin shi mai suna Rayuwar Annabawa bayan mutuwarsu, a wata ruwaya daga annabi tsira da aminci sutabbata a gare shi, cewa yaga annabi Musa tsira da aminci sutabbata a gare shi yana sallah a gurin ƙabarin shi a daran da yayi Mi’iraji.[10] Wasu malaman Sunna kuma sun ambaci rayuwar Barzahu ta annabawa, [11]. Alusi yana ganin rayuwar Annabawa ta Barzahu tafi rayuwar shahidai,kuma yace rayuwar wasu daga cikin annabawa zaiyiyu a tabbatar da ita da ingantattun hadisai.[12] ‘yan Shi’a sunyi imani da cewa,imamai sunsan halin da ɗan adam yake cikin,ammafa da izinin Allah,kuma sunyi imani da haka ne sakamakun dogaro kan wasu rawayoyi da suke cikin littafin Usulul Kafi a ƙarƙashin babi mai taken,imamai shaidun Allah ne akan ɗan adam,kuma suna kafa hujja da su kan samuwar rayuwar Barzahu.

Mahangar Wahabiyawa

Wasu Salafawa irin su ɗan Taimiyya[14] da Al-ƙayyim[15] sun yi imani da samuwar rayuwar Barzahu. Amma wasu Wahabiyawa suna tawili na musamman game da rayuwar Barzahu, saboda suna ganin cewa rayukan matattu ba za su iya sadarwa tskaninsu da rayayyu ba da kuma jin muryoyinsu ba[16].

Raddi

Magoya bayan rayuwar Barzahu sun yi imanin cewa karyata rayuwar Barzahu bai dace da ayoyin Kur’ani da ke magana kan rayuwa bayan mutuwa da kuma ci gaban rayuwar annabawa da waliyai bayan sun koma zuwa duniyar Barzahu. Kur’ani mai girma ya kuma bayyana rayuwar shahidai bayan rasuwarsu[17]. A mahangar Musulunci, mutuwa ba halaka ba ce da bacewa, a’a, sauyi ne daga wannan duniya zuwa wata duniya [18]. Sadarwa tsakanin masu rai da rayuka yana yiwuwa a cikin duniyar barzahu. Suna ganin cewa idan ba a karbi rayuwar annabawa ba bayan mutuwarsu, to, jawaban Kur’ani na annabawan da suka gabata, kamar su annabi Nuhu da Ibrahim tsira su tabbata a garesu [19]. Umarnin da Alkur’ani ya yi wa Annabi tsira da amincin Allah sutabbata a gareshi, ya dogara ne a kan maganar annabawan da suka gabatar[20] da kuma umarnin Alkur’ani ga muminai da su yi wa Annabi salati[21]. ba zai samu fa’ida ba, kuma suna ganin magaanr Salih da Shu’aibu [22] tsira da amincin Allah su tabbata a gare su tare da mutanensu waɗanda suka halaka [23] maganar Annabi tare da wadanda aka kashe a yakin Badar [24] da hadisin Amirul Muminin tare da wadanda aka kashe a yakin Jamal [25] a matsayin hujjar wannan ikirari na rayuwar mataattu a duniyar barzahu.