Rushe Maƙabartar Baƙi'a
- wannan wata ƙasida ce da aka rubuta ta game da waƙi'ar rushe baƙi'a, domin sanin shekarar da aka zartar da wannan rusau ku duba ranar rusau
Ruguje baƙi'a, (Larabci: هدم قبور أئمة البقي) ishara ce zuwa ga abin da ya faru bayana mamaye madina a shekara ta 1344 bayan hijira, tare da ruguje maƙabartar baƙi'a da wasu wurare bisa fatawar masu fatawa na madina ta hannun Shaik Abdullahi ɗan Bulaihid alƙalin alƙalan ƙasar saudiya a wancan lokaci; daga cikin wuraren muhimmai suka ruguje akwai makwancin Imaman shi'a guda huɗu: Imam Hassan (A.S), Imam Sajjad (A.S), Imam Baƙir (A.S) da Imam Sadiƙ (A.S). karo biyu wahabiyawa suna ruguje wannan wurare masu tsarki, karo na farko ya faru a shekarar 1220 na ƙarshe kuma ya faru a shekarar 1344 bayan hijira tare da dogara da fatawan mutane goma sha biyar daga malamansu na madina, bisa jingina da cewa baya halasta yin gini kan ƙaburbura da kuma wajabcin ruguje su, da wannan suka dogara suka rushe ƙaburburan maƙabartar baƙi'a, haƙiƙa ruguje baƙi'a ya jawo martani mutane da malamai masu tarin yawa daga Iran, Iraƙi, Fakistan da Tsohuwar Tarayyar Sobiyat da sauran ƙasashe, ƙasar daular Iran ta wancan lokaci cikin martani kan ruguje wurare masu tsarki a wurin musulmai ta shelanta zaman makokin kwana ɗaya a bakiɗayan cikin ƙasar, sakamakon hakan ne ta bayyana rashin amincewarta da sabuwar hukumar ƙasar saudiyya da aka kafa har tsawon shekaru uku.
Maƙabartar baƙi'a bayan rugujeta ana daidaita ta da ƙasa, amma mahallan ƙaburburan Imamai huɗu na shi'a an sanya musu alamar da duwatsu domin tantance su daga sauran ƙaburbura, ƙoƙarin malaman shi'a da daular game da neman hukumar da ta bada izinin yin rumfa a samanr ƙaburburan Imamai da kuma jan Katanga a geffansu, tare da cewa a farko-farko lamarin gwamnatin wancan lokaci har ta yarda sai dai cewa har zuwa yau ɗin nan ba a samu cimma wannan buƙata ba. Malaman shi'a ƙari kan nuna rashin amincewarsu da rushe maƙabartar baƙi'a, sun yi rubuce-rubuce na suka kan wahabiyawa da ruguje wurare masu tsarki da suka yi; daga jumlarsu akwai littafin Kashful Al-irtiyab, na Sayyid Muhsin Amin da Da'awatul Al-huda na Muhammad Jawad Balagi. An ce wahabiyawa sun kasance mutane na farko da suka ruguje wurare masu tsarki ƙarƙashin dogara da mahangar addini.
Matsayi Da Muhimmancin Maƙabartar Baƙi'a
Baƙi'u, jannatu baƙi'i ko kuma baƙi'u al-garƙad (sunayae ne na baƙi'a tun kafin zuwan Annabin muslunci[1]) ta kasance mafi muhimmancin maƙabartar musulmi a garin madina,[2] bisa raiwayoyin muslunci wannan maƙabartar ta kasancewa maƙabartar da take da muhimmancin a wurin Annabi Muhammad (S.A.W).[3] baƙi'a wuri ne da aka binne imaman shi'a guda huɗu da kuma adadi mai yawan gaske daga sahabbai da tabi'ai.[4] kafin ruguje ta a cikin shekara ta 1220 da rusheta na ƙarshe ta hannun wahabiyawa akwai gine-gine da suka kasance saman ƙaburburan Imaman da aka binne a wurin da sauran mutane.[5]
Bisa rahotanni, makwancin Imaman shi'a baitul ahzan da wasu wurare daban, a shekarar 1297 sun kasance a maƙabartar baƙi'a,[6] waɗannan gine-gine bayan ruguje su karo na farko. A lokacin da aka kwato garin madina daga hannun wahabiyawa, ƙarƙashin umarnin Mahmud na biyu wanda ya kasance sarki a masarautar usmaniyya an sake gina su a shekarar 1234.[7]
Kamar da yadda Murad Mirza, ɗan Abbas Mirza wanda ya shahara da sunan Husamul Salɗana cikin littafinsa ya rubuta cewa alal aƙalla har kusan zuwa shekara ta 1297 bayan hijira cikin hubbaren Imam Hassan (A.S), Imam Sajjad (A.S), Imam Baƙir (A.S) da Imam Sadiƙ (A.S) da suke a maƙabartar baƙi'a ƙarin kan mihrab akwai zarihi da aka yi da itace da kuma baitul ahzan (ɗakin juyayi) da ake dangata shi da Sayyida Faɗima (S) da ya kasance a bayan hubbaren Imaman shi'a,[8] bisa rahotan da ya zo daga littafin safarname Izikhan ƙashƙayi, wanda ya rubuta shi shekara biyu kafin ruguje baƙi'a, ya rubuta cewa ƙaburburan imaman shi'a guda huɗu sun kasance a wuri guda sai dai cewa an tantance ƙabarin kowanne guda daga cikinsu.[9] Izikhan ƙashƙayi ya yi magana game da mahallan ƙaburburan mutanen misalin Ibrahim ɗan Annabi da Abdullahi ɗan Jafarul ɗayyar, cikin wani lungu kusa da baƙi'a, ya ce ya ga mahallan ƙaburbura da aka dangata su ga Safiyya gwaggon Annabi, Atika ƴar Abdul-muɗɗalib, Ummu banin mahaifiyar Abbas da wasu adadin mutanen daga bani hashim.[10]
Bayan Rushe Bakiɗayan Maƙabartar Baƙi'a
Kamar yadda Muzaffar A'alam wakilin daular Iran a Jidda, cikin wata wasiƙa zuwa ga dawwamammen kwamitin hajji a ranar 21 ga watan azar shekara ta 1330 ya rubuta cewa bayan wahabiyawa sun ruguje maƙabaratr baƙi'a a shekarar 1344.[11] maƙabartar cikin bakiɗayan gine-ginen ƙaburburan Imaman shi'a sun lalace da manyan mutane a addini bama zaka iya tantance su ba.[12] cikin wannan wasiƙa ya ƙarfafa laruran neman haɗin kai da izinin mahukuntan daular saudiya domin sake gina bango tare da tagogi na ƙarfe a gefen ƙaburburan imaman shi'a guda huɗu.[13] tare da, Rasul Jafariyan ya yi Imani kan cewa ganawar Abdur-Rahim Sahibul Fusul ha'iri wanda ya rayu tsakanin shekaru 1294-1367 bayan hijira, ɗaya daga cikin malaman garin Tehran, wace ta kasance tsakaninsa da sarkin Abdul-aziz sa'adi, wannan ganawa ce ta hana baje wani ɓangare daga ƙaburbura Imaman shi'a da ƙasa da daidaita su da ƙasa, wanda haka ya taimata wajen tantance ƙaburburansu.[14]
Bayan ruguje baƙi'a da sauran wurare masu tsarki na musulmi, an samu wani yunƙuri daga daular Iran,[15] Afganistan,[16] da malaman shi'a daga Najaf,[17] ƙum, Indiya.[18] da Fakistan[19] domin sake gini kan saman ƙaburburan baƙi'a, sai dai cewa babu wata natija da nasara da aka cimma, kai hatta neman bada izinin gina bango a gefan ƙaburburan Imaman shi'a shima yaci tura daular saudiya bata lamicewa yin hakan ba duk da cewa da farko ta nuna yardarta kan haka sai dai kuma har zuwa yanzu ba a samu nasara kan hakan ba.[20] tare da haka bangon maƙabartar baƙi'a a zamanin mulkin sarki Fahad ɗan Abdul-aziz an sake gina si. Sai dai kuma a shekarun 1428-1419 bayan hijira, hanyoyin da maziyarta suke shiga cikin baƙi'a da fitowa an shimfiɗe su da duwatsu.[21]
Kan asasin mabambantan rahotanni, a wannan zamani da muke ciki ta hannun wata hukuma mai taken (uamrni da kyakkyawa da hani da munkari) a ƙasar saudiya, an zuba jama'an wannan hukuma kusa ƙofar shiga baƙi'a suna hana maziyarta neman tabarukki.[22] har zuwa yau, makwancin imaman shi'a a baƙi'a da ƙaburburan manyan mutane a muslunci babu abin da zaka samu daga gare su in banda sai guntayen duwatsu.[23] a wannan zamani halin baƙi'a ina aka kwatanta shi da wancan lokaci na rugujeta ya ɗan fi kyawunta daga wancan.[24]
Abubuwa Da Suka Jawo Ruguje Baƙi'a
A shekarar 1220 bayan hijira, wahabiyawa bayan shekara ɗaya da rabi da mamaya daga ƙashe dai bayan yaɗuwa fari a garin madina sun samu nasarar kwace garin.[25] bisa abin da ya zo daga madogarai, Sa'ud ɗan Abdul-aziz bayan kwace ikon garin madina, ya tsayar da baki ɗayan kuɗaɗen da suke cikin ma'ajiyar haramin Annabi, sannan ya bada izinin ruguje gine-gine tarihi da ƙubbobi a garin madina daga jumlarsu maƙabartar baƙi'a.[26] kan wannan asasi ne hubarren Imaman shi'a guda huɗu da ƙubboba da ake dangantawa ga Sayyida Faɗima (S) da ake kiransa da baitul ahzan (ɗakin juyayi) cikin farkon hari da wahabiyawa suka kai a shekarar 1220 sun rushe ko kuma dai sun taɓu sosai.[27] Bayan wannan waƙi'a. daular Usmaniyya ta aiko da dakaru domin kwato garin madina daga hannun wahabiyawa, a watan zil hijja shekarar 1227 dakarun daular usmaniyya sun kwato garin madina daga hannun wahabiyaw, bayan wannan nasara ne Mahmud na biyu sarki na talatin a jerin sarakunan masarautar usmaniyya a shekarar 1234 ya fitar da umarnin sake gina hubarren Imaman shi'a.[28]
Wahabiyawa a watan safar shekarar 1344 bayan hijira, sun sake kawo hari kan garin madina a karo na biyu,[29] cikin wannan hari sun haifar da asara cikin haramin Annabi da wurare na addini.[30] bayan wata bakwai, a watan Ramadan shekarar 1344, Shaik Abdullahi Bulaihid wand aya rayu tsakanin shekaru 1284-1359 alƙalin alƙalai,[31] ya shigo madina ƙarƙashin fatawowin malaman wahabiyawa ya fitar da hukunci ruguje maƙabartar baƙi'a.[32] a ranar takwas ga watan shawwal shekara ta 1344 bisa fatawar Abdullahi Bulaihid Alƙalin alƙalan ƙasar saudiya da ta ɗoru kan fatawar malaman madina, an ruguje bakiɗayan kufaifayin tarihi na maƙabartar baƙi'a daga jumlarsu harda mahallan ƙaburburan imaman shi'a.[33] malamai 15 daga madina ne suka bada fatawa kan aikata haka,[34] cikin wannan fatawa an hana gini kan ƙabari bisa ijma'in malamansu, tare da hukuncin rusa ƙaburburan.[35] tare da haka, saɓanin aƙidun wahabiyawa bisa imanin mashhur daga ahlus-sunna da ƴan shi'a wannan fatawa da suka bayar da cika karo aƙidun muslunci, kuma ziyartar ƙaburburan mutanen masu daraja da ƙima a addini da ƙaburburan muminai suna ganinsa mastayin mustahabbi.[36] kan asasin isnadi da yakem a hannu, haƙiƙa bayan ruguje baƙi'a, sarki Abdul-aziz na saudiya cikin wata wasiƙa a rnar 12 ga watan shawwal shekarar 1344 cikin saƙonsa zuwa ga Abdullahi ɗan Bulahid ya yaba masa kan ruguje maƙabartar baƙi'a.[37]
Saƙonni Da Martani
Raddodin malamai da wallafe-wallafe Ruguje wurare masu tsarki a wurin musulmai musammam ma baƙiu'a ya motsar da raddin manyan malaman shi'a misalin Sayyid Abul Hassan Isfahani da Abdul-Karim Ha'iri Yazdi, daga manyan malaman hauzar najaf da ƙum ta kai ga sun dagatar da karatu tare da rufe kasuwanni don nuna damuwarsu kan wannan ta'addanci.[38] Muhammad Khalisizade da Sayyid Hassan Mudarris suma sun yi martani kan ruguje baƙi'a tare da neman ɗaukar mataki na gaske kan waɗanda suka aikata rushe wurare masu daraja.[39]Sayyid Husaini ɗabaɗaba'I ƙummi, wanda aka fi sani da Ayatullahi ƙummi shima yana cikin jumlar maraji'an shi'a da ya tashi tsaye yana fafutika tsawon shekaru kan neman sake gina ƙaburburan baƙi'a da aka ruguje, ma'aikatar harokin wajen Iran domin tabbatar da buƙatarsa ta shirya tattaunawa tare da daular saudiya.[40] Imam Khomaini shima ya kasance yana ganin babban dalilin da yua sanya wahabiyawa rushe ƙaburburan waliyyan Allah, ya samo asalin da rashin ingantacciyar fahimtar addini da karakcewa.[41] Muhammad Husaini Kashiful Giɗa, cikin watan wasiƙa da ya yi kan Abdullahi ɗan Bulaihid, Alƙalin alƙalan wahabiyawa, cikin bayani martabobin aƙidun shi'a ga tauhidi, ya gayyace ɗan bulaihid d aya zo su tattauna, sannan idan har bai amsa wannan gayyata to lallai alama ce ta raunin hujjoji da yake dogara da su.[42]
Sayyid Mushin Amin bisa ruguje wurare masu tsarki ya yi tafiya zuwa yankin hijaz ya kuma wallafa littafin Kashful Al-irtiyab, domin kawo tarihin wahabiyawa da ayyukansu.[43] wannan littafi ya tattaro bayani kan aƙidun wahabiyawa da wasu abubuwa kan raddin aƙidun wahabiyawa ƙarƙashin taken taƙaitaccen tarihin naƙadi da bincike kan wahabiyawa, an tarjama wannan littafi zuwa harshen farisanci.[44] Muhammad Jawad balagi najafi cikin risala mai suna Raddul Al-fatawa bi hadmi ƙuburil Al-A'immati fil Al-baƙi'I, ya yi suka kan maginan tunanin wahabiya game da rusa wurare masu tsarki.[45] cikin wani littafin daban mai suna Da'awatul Al-huda ilal Al-wara'i fi Al-af'ali wal Al-fatawa, ya yi raddi kan fatawar rusa wurare masu albarka.[46] haka nan mawaƙa masu yawa sun bayyana takaicinsu game da rusa ƙaburburan baƙi'a cikin zirin baitukan waƙoƙi.[47]
Muhammad Jawad Balagi Najafi cikin littafin Ar-raddi Ala Al-wahabiyya, tare da dogara da hadisai daga Annabi (S.A.W), Imam Ali (A.S), Imam Sadiƙ (A.S) da sauransu, da kuma dogara da sannniyar al'ada da ta yaɗu tsakanin musulmi tun farkon muslunci ya yi martani da raddi kan aƙidun wahabiyawa, sannan da suka dogara da su kan ayyukansu hadisai da basu da alaƙa da manufofi da hadafinsu, saboda a cewar Balagi cikin hadisan da suka jingina da su an hana yin gine-gine misalign Katanga a kan ƙaburbura ne bawai gine-ginen da ake yinsu a geffan ƙaburburan ba da suke kewaye da su.[48] An ce wahabiyawa sune mutane na farko da suke fara rusa ƙaburburan jagororin mazhabobi bisa dogara da ra'ayi da fahimta ta addini. Tare da haka a wasu wurare an samu wasu mutane da ba wahabiyawa da suka yi yunƙurin ruguje baƙi'a bisa zargin cewa cikin ma'ajiyar haramin Imaman shi'a da yake maƙabartar baƙi'a akwai wasu litattafai da suke ɗauke da suka kan halifofi, sai dai kuma ba su yi nasarar ruguje su ba.[49] Wasu adadi daga malaman fiƙihun shi'a, sun yi fatawa kan larurar sake gina hubbaren imaman shi'a da suke maƙabartar baƙi'a.[50] daga jumlar waɗannan malamai akwai Muhammad Fadlullahi Lankarani, Nasir Makarim Shirazi da Luɗfullahi Safi Gulfaigani, suna ganin yunƙurin sake gina ƙaburburan baƙi'a matsayin wajibi ko kuma wajibi kifa'i. Sayyid Ali Husaini Sistani daga maraji'an shi'a shi yana ganin hakan matsayin halas a shari'a ba wajibi ba.[51]
Yunƙuri Na Mutane Da Daula
Bayan ruguje maƙabartar baƙi'a, musulmai mazauna tsohuwar tarayyar sobiyat da kuma musulmai daga ƙasashen Turkiyya, Afganistan, Sin da Mangoliya cikin wasiƙu da suka aiko sun buƙaci kiyaye wurare masu tsarki a makka da madina.[52] A shekarar 1304 hijira shamsi, ƙasar Iran tare da fitar takardar sanarwa a ranar 16 ga watan safar shekarar 1344 bayan hijira ta sanar da zaman makoki a bakiɗayan ƙasar.[53] mutanen sun shirya zaman makoki a babban birnin Tehran.[54] wasu madogarai sun bada rahoton shirya tarurruka na dubban mutane a gefan ƙofar shiga birnin Tehran don nuna rashin amincewa kan keta alfarma da wahabiyawa suka yi kan wurare masu tsarki a madina.[55]
Daular Iran cikin ɗaukar mataki a ranar 11 ga watan Isfandi shekara ta 1304 hijira shamsi, bisa damuwa da lafiya da tsaron mahajjatan Iran ta hana zuwa aikin hajji ta dagatar da tafiya saudiya a wannan shekara.[56] cikin sanarwa da gwamnatin Iran ta fitar hukumance a ɗaya ga watan tir shekarar 1305 ta bayyana cewa tsageranci wahabiyawa kan wurare masu tsarki na maƙabartar baƙi'a abu ne da ya ƙoanwa muminai ya sanya su zaman makoki, cikin nuna damuwarta da kuma tunatar da ƙasar saudiya rashin kiyaye aƙidun sauran musulmi da kuma alfarma wurare masu tsarki, ƙasar Iran ta yi watsi da goran gayyata da saudiya ta aiko mata na babban taron hijaz.[57] da wannan dalili ne a wancan zamani ƙasar Iran ta jinkirta yarda da halascin daular sa'udawa.[58] tare da haka, a shekarar 1307 hijira shamsi, bayan daular saudiyya ta aike da wasiƙu zuwa ga ƙasashen musulmi ciki kuwa harda ƙasar Iran, ta shelanta ɗaukar nauyin kula da ɓangaren tsaron lafiya da rayukan mahajjata,[59] a watan khordad shekara ta 1308 an fara samun kyawuntar dangantaka tsakanin Iran da Saudiya,[60] daga ƙarshe a hukumance saudiyya ta cire haramcin aikin hajji na shekaru huɗu daga kan ƙasar Iran.[61]
Bayanin kula
- ↑ Jafarian, Asare Islami Makka wa Madina, 2013, shafi na 322.
- ↑ Jafarian, Asare Islami Makka wa Madina, 2013, shafi na 322.
- ↑ Jafarian, Asare Islami Makka wa Madina, 2013, shafi na 328.
- ↑ Jafarian, Asare Islami Makka wa Madina, 2013, shafi na 322.
- ↑ Jafarian, Asare Islami Makka wa Madina, 2013, shafi na 330.
- ↑ Hossam al-Sultaneh, Dalil al-Anam, 1374, shafi na 152.
- ↑ Jafarian, Panjah Safarnama Hajj Qajari, 1389 AH, juzu'i na 3, shafi na 196.
- ↑ Hossam al-Sultaneh, Dalil al-Anam, 1374, shafi na 152.
- ↑ Ayazkhan Qashqai, Safarnama Haj Ayazkhan Qashqai, 1389 AH, shafi 455.
- ↑ Ayazkhan Qashqai, Safarnama Haj Ayazkhan Qashqai, 1389 AH, shafi 455.
- ↑ Qadi Askar, Takhrib wa Baz-Sazi Baqi’, 1386H, shafi na 41.
- ↑ Qadi Askar, Takhrib wa Baz-Sazi Baqi’, 1386H, shafi na 95-96.
- ↑ Qadi Askar, Takhrib wa Baz-Sazi Baqi’, 1386H, shafi na 95-96.
- ↑ جعفریان، «چه شد که پس از تسلط وهابیان، صورت قبور ائمه بقیع سالم ماند؟»، سایت خبرآنلاین.
- ↑ Duba: Qazi Askar, Takhrib wa bas sazi Baqi, 2006, shafi na 158-95.
- ↑ Duba: Qazi Askar, takhrib wa baz sazi Baqi, 2006, shafi na 153-154.
- ↑ 2006, shafi na 63.
- ↑ 2006, shafi na 167-168.
- ↑ 2006, shafi na 156-158.
- ↑ Qazi Askar, takhrib wa baz sazi Baqi, 2006, shafi na 159; Duba kuma: Qazi Askar, takhrib wa baz sazi Baqi, 2006, shafi na 158-95
- ↑ Jafarian, Asare islami Makka wa Madina, 2013, shafi na 332.
- ↑ Jafarian, Ba Karwan Safa, 1383 AH, shafi 135-137.
- ↑ Jafar, Asare Islami Makkah wa Madina, 1382H, shafi na 333.
- ↑ Jafar, Asare Islami Makkah wa Madina, 1382 Hijira, shafi na 332.
- ↑ Jabrati, Al-aja'ibu Asare, Dar Al Jail, juzu'i na 3, shafi na 91.
- ↑ Ghalib, Man Akhbar Al-Hijaz, 1395 Hijira, shafi na 104; Jabrati, Al-aja'ibu Asare, Dar Al Jail, juzu'i na 3, shafi na 91.
- ↑ Jabrati, Al-aja'ibu Asare, Dar Al Jail, juzu'i na 3, shafi na 91.
- ↑ Jafarian, Panjah Safarnama Hajj Qajari, 1389 AH, juzu'i na 3, shafi na 196..
- ↑ Majarayi, Al-Baqi Qissata al-Tadmir, 1411 AH, shafi na 113-139; Amini, Baqi al-Gharqad, 2006, shafi na 49
- ↑ Majarayi, Al-Baqi Qissata al-Tadmir, 1411 AH, shafi na 113-139; Amini, Baqi al-Gharqad, 2006, shafi na 49
- ↑ Zarkali, Al-Alam, 2002, juzu'i na 4, shafi na 91.
- ↑ Balaghi, Ar-raddi ala Wahabiya, 1419 AH, shafi na 39-41; Majarayri, Al-Baqi Qissata al-Tadmir, 1411 BC, shafi na 113-139; Amini, Baqi al-Gharqad, 1386 AH, shafi na 49.
- ↑ Majarayi, Al-Baqi Qissata al-Tadmir, 1411 BC, shafi na 113-139; Amini, Baqi al-Gharqad, 1386 AH, shafi na 49; Najmi, Tarikh Haram Imamah, 1386H, shafi na 51.
- ↑ Balaghi, Arrad Ala Al-Wahhabiyyah, 1419 AH, shafi na 45.
- ↑ Balaghi, Arrad Ala Al-Wahhabiyyah, 1419 AH, shafi na 40.
- ↑ Madani, Al-Tarikh al-Amin, 1418 AH, shafi na 431-450; Amini, Baqi al-Gharqad, 2006, shafi na 12.
- ↑ العساف، «عبدالله بن سلیمان البلیهد.. القاضی والمستشار فی زمن التأسیس».
- ↑ Amini, Baqi al-Gharqad, 2006, shafi na 53; Qazi Askar,Takhrib wa baz sazi Baqi, 2006, shafi na 49.
- ↑ Qazi Askar, Takhrib wa baz sazi Baqi, 2006, shafi na 54.
- ↑ Qazi Askar,Takhrib wa baz sazia Baqi, 2006, shafi na 148 da 151.
- ↑ Imam Khumaini, Sahifa Imam, 1378, juzu'i na 18, shafi na 175.
- ↑ Mokhtari, “Sah Sanad Az Aalama Sheikh Muhammad Hussein Kashif Al-Ghita,” shafi na 217.
- ↑ Muhammad Ali, Mujam Al-Mu'allafat Al-Islamiyya Al-Radd Ala Al-firqati al-Wahhabiyyah, 1430 AH, shafi na 375-376.
- ↑ Muhammad Ali, Mujam Al-Mu'allafat Al-Islamiyya Al-Radd Ala Al-firqati al-Wahhabiyyah, 1430 AH, shafi na 375-376.
- ↑ Al-Rifa'i, Ma'ajm Kitab Fi Hajj, 1427 AH, shafi 171.
- ↑ Muhammad Ali, Mujam Al-Mu'allafat Al-Islamiyya Al-Radd Ala Al-firqati al-Wahhabiyyah, 1430 AH, shafi na 480
- ↑ Madani, Al-Tarikh Al-Amin, 1418H, shafi na 366-368; Amini, Baqi al-Gharqad, 2006, shafi na 341-335.
- ↑ Balaghi, Arrad Ala Al Wahhabiyyah, 1419 AH, shafi na 69-72.
- ↑ Jafarian, Safawiyya dar Arsat al-Din..., 1379 AH, juzu'i na 2, shafi na 783 da 842.
- ↑ Amini, Baqi al-Gharqad, 1386H, shafi na 55.
- ↑ Qadi Askar, Takhrib wa Baz-Sazi Baqi’, 1386H, shafi na 160.
- ↑ Qadi Askar, Takhrib wa Baz sazi Baqi’, 1386 AH, shafi 55-56; Amini, Baqi al-Gharqad, 1386 AH, shafi na 52-53.
- ↑ Makki, Mudarres Qahraman Azadi, 1359 AH, juzu'i na 2, shafi na 682; Qadi Askar, Takhrib wa Baz-Sazi Baqi’, 1386 AH, shafi na 49-50.
- ↑ Qadi Askar, Takhrib wa Baz-sazi Baqi’, 1386H, shafi na 50.
- ↑ Qadi Askar, Takhrib wa Baz-sazi Baqi’, 1386 AH, shafi na 50-51.
- ↑ Alkalin Soja, Takhrib wa Baz-sazi Baqi’, 1386H, shafi na 72.
- ↑ Alkalin Soja, Takhrib wa Baz-sazi Baqi, 1386 Hijira, shafi na 73-75.
- ↑ Mohaqqiq, Isnadin rawabit Iran wa Arabistan sa'udi, 1379 AH, shafi na 61.
- ↑ "Barasi tarikhi rawabit Iran wa Arabistan dar maudu'i Hajji", shafi na 18.
- ↑ Qazi Askar, Takhrib wa baz sazi Baqi, 2006, shafi na 77.
- ↑ "Barasi tarikhi rawabit Iran wa Arabistan dar maudu'i Hajji", shafi na 17.
Nassoshi
- "Barsi rawabit Iran wa Arabistan dar maudu'i Hajji", a cikin Mujallar Miqat Hajj, No. 92, Summer 2014.
- Al-Rifai, Abduljabbar, mujam ma kataba aka rubuta a Hajj, Tehran, Mash’ar, 1427 BC.
- Amini, Mohammad Amin, Baqi al-Gharqad, Tehran, Mashaar, 2006.
- Ayazkhan Qashqaei, Safarnameh Hajj Ayazkhan Qashqaei beh Makka, Madina wa Atabat Aliyet dar Ruzgare Ahmad Shah Qajar, na Rasul Jafarian, Tehran, littafin Alam, 2009.
- Balaghi, Mohammad Javad, Arradd Ala al-Wahhabiyyah, bincike na Sayyid Mohammad Ali Al-Hakim, Beirut, Mu’assasa ta Ahlul-Baiti don Farfaɗo da Al’ada, 1419 AH/1998 Miladiyya.
- Hossam Al-Saltanah, Dalil Al-Anam: fi sabili ziyarati baitillahi haram, wanda Rasoul Jafarian Tehran ya inganta, Mash’ar ya buga, 1374 Hijira.
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Sahifa Imam, Tehran, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini, 1378.
- Jaafarian, panjo safarnameh Hajji, Tehran, Nash Alam, 2009.
- Jabarti, Abdurrahman, Aja'ibul Asare, Bairut, Dar Al Jail.
- Jafar, Rasul, Asare Islami Makka wa Madina, Qum, Mash'ar, 1382.
- Jafarian, Rasul, Safawiyyah dar Arsat al-Din, Farhang wal-Siyast, juzu'i na 2, Qom, Howzah-e-Hawza va Danishgah, 1379 AD.
- Jafarian, Rasul, tba karwan Safa , Tehran, Mash'ar, 2003.
- Mokhtari, Reda, “Sah Sanad Az Alamah Sheikh Muhammad Hussein Kashif al-Ghita”, a cikin mujallar Kitab Shi’a, No. 3, Bahar wa Tabistan 1390 AH.
- Qadi Askar, Ali, Tahreeb wa Bas sazi Baqi’, ruwayar isnadin Tehran, Mash’ar, 1386H.
- Zarkali, Khair Al-Din, Al-A’lam, Beirut, Dar Al-Ilm Lil Al-Millain, 2002 Miladiyya.
- العساف، منصور، «[http://www.alriyadh.
- جعفریان، رسول، «چه شد که پس از تسلط وهابیان، صورت قبور ائمه بقیع سالم ماند؟»، در سایت خبرآنلاین، تاریخ درج مطلب: ۲۹ آبان ۱۳۸۹ش، تاریخ بازدید: ۵ مرداد ۱۳۹۷.
- Madani, Abdul Aziz, Al-Tarikh Al-Amin Lamdina Seyyed Al-Murslin, Qum, Al-Amin
- Muhakkikul, Ali, asnad rawabit Iran wa Arabistan sda'udi (1304-1357 AH), Tehran, Cibiyar Hulda da Jama'a da Yada Labarai ta Ma'aikatar Harkokin Waje, Tehran, 1379H.
- Muhammad Ali, Abdallah, mujam Al-mu'allafat Al-islamiyya fi Ar-raddi ala Al-firkati al-wahabiyya, Bija, [Cibiyar Al-Zahra Al-Islami], 1430H/2009 Miladiyya.com/965193 عبدالله بن سلیمان البلیهد.. القاضی والمستشار فی زمن التأسیس]»، در سایت الریاض، تاریخ درج مطلب: ۳ ذی القعده ۱۴۳۵ق، تاریخ بازدید: ۶ مرداد ۱۳۹۷ش.