Ranar Rusau

Daga wikishia

Ranar rusau (Larabci یَومُ‌الهَدْم) ita ce ranar da aka ruguje maƙabartar Baƙi'i, wanda ya kama ranar takwas ga watan Shawwal 1344 H ƙamari. Wahabiyawa sun kai hari Madina tare da rusa wasu wurare na Musulunci ciki har da ƙaburburan maƙabartar Baƙi'i.[1] Wahabiyawa sun kai hari Madina a watan Safar shekara ta 1344 h ƙamari.[2] A wannan harin an lalata hubbaren Annabi da wuraren ibada[3] Bayan wata bakwai a watan Ramadan 1344h ƙamari, Shaikh Abdullah bin Bolaihed wanda ya rayu tsakanin shekaru (1284-1359 h ƙamari) ya kasance Alƙalin Makka,[4] ya shiga garin Madina, ya karɓi umarnin rusa ƙaburbura.[5] wanda ya samu umarnin ne daga Muftin Madina, bayan faruwar hakan wato ruguje maƙabartar sarki Abdul Aziz Sarkin Saudi Arabiya, ya yaba da wannan abin da ya aikata a cikin wata wasika da ya aike wa Abdullahi bin Balihid a ranar 12 ga watan Shawwal 1344H.[6]

A gun ‘yan Shi’a, ana kiran ranar[7] ga watan Shawwal (Yaumul Hadam) (wato ranar rusau).[8] ‘Yan Shi’a na gudanar da tarukan tunawa da wannan waƙi’a da tadabburi da nuna bacin rai na abin da akai a maƙabartar Baƙi'i, Ayatullah Safi Golfaigani[9] ɗaya daga malaman shi'a da ake taƙlidi dasu ya kira wannan rana da ranar ruguje maƙabartar Baƙi'i ta Duniya. ya kuma buƙaci dukkan musulmi da su yi Allah wadai da rusa M aƙabartar da wahabiyyawa sukai da sauran wurare masu tsarki da kuma neman a maido da shi.[10] Wahabiyawa sun fara aikin rugurguza maƙabartar a shekara ta 1806 miladiyya daidai da 1220 hijriyya. Har ila yau, bisa umarnin Sa’ud Bn Abdulaziz, sun rusa Maƙabartar kuma sunyi mummunar ɓarna a ƙabura Imamai huɗu da kuma ƙubbar Sayyida Fatima (S) da aka fi sani da Bayt Al-Ahzan[11] A cewar Abdul Rahman Jabarti. Sojojin Wahabiyyawa sun yi nasarar rusa ko ina banda Haramin Manzon Allah (S.A.W).[12]

Bayanin kula

  1. Najmi, Tarikh Harami A'immeh Baqi, wa Asare Digar dar madineh Munawwara, 2006, shafi na 51.
  2. Hajri, al-Baqi, kissatu al-Tadmir, 1411 AH, shafi na 113-139; Amini, Baqi al-Gharqad, 2006, shafi na 49.
  3. Hajri, al-Baqi, kissatu al-Tadmir, 1411 AH, shafi na 113-139; Amini, Baqi al-Gharqad, 2006, shafi na 49
  4. Zarkali, Al-Alam, 2002, juzu'i na 4, shafi na 91.
  5. Al-Balaghi, Al-Arada Ali al-Wahhabiyyah, 1419 AH, shafi na 41-39; Hajri, al-Baqi, kissatu al-Tadmir, 1411 AH, shafi na 113-139; Amini, Baqi al-Gharqad, 2006, shafi na 49.
  6. العساف، «عبدالله بن سلیمان البلیهد.. القاضی والمستشار فی زمن التأسیس».
  7. [[پرونده:یوم الهدم.jpg|بندانگشتی|نصب بنر عزا در حرم امام حسین(ع) به‌مناسبت یوم‌الهدم (اردیبهشت ۱۴۰۰ش)
  8. «تصاویر مراسم عزاداری سالروز تخریب قبور ائمه بقیع در حرم امام حسین(ع)»، خبرگزاری حوزه.
  9. «آیین بزرگداشت یوم‌الهدم در مسجد زیارت قدمگاه برگزار می‌شود»، خبرگزاری شبستان
  10. «تخریب قبور ائمه بقیع(ع) خیانت بزرگ به اسلام است»، پایگاه اطلاع‌رسانی حوزه
  11. Jabrati, Aja'ib Asar, Dar al-Jeel, juzu'i na 3, shafi na 91
  12. Jafarian, Panjo Safarnameh, 2009, juzu'i na 3, shafi 196

Nassoshi

Amini, Mohammad Amin, Baqi al-Gharqad fi dirasati Shameela, Tehran, Mash'ar, 2006.