Jump to content

Ni'ima

Daga wikishia

Ni'ima (Larabci: النعمة) wata baiwa ce ta zahiri (kamar kuɗi) da ruhaniya da Allah yake azurta mutum da ita, addini ya yi magana kan ni'imomi da yawa kai ataƙaice mutum ba zai iya ƙididdige ni'ima ba, kazalika mutum ba zai iya godewa Allah kan ni'imomi da ya yi mashi ba.

﴿وَإِنْ تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللَّهِ لا تُحْصُوها إِنَّ اللَّهَ لَغَفُورٌ رَحِيمٌ﴾ Suratul Nahli aya ta 18. Rubutun hannu na Hamid Amadi cikin salon rubutu na sulus

Ƙur'ani ya kira ga muminai da su tina da ni'imomin da Allah ya yi musu, kuma su kiyayi kafurcewa ni'ima, saboda kafurcewa ni'ima ko rashin godiya na iya bayyana ta wani ɓangare na zuciyar ko ta harshe ko ta hanyar aiki wanda hakan yana iya jawo abu marar kyau kamar gushewar ni'ima, da azaba a lahira, da rashin karɓar addu'a.

Ni'ima ta rabu gida biyu, ta duniya da ta lahira, daga cikin misali na ni'imomi; Hali na gari da shiriya da kyan fuska da aminci kamar yadda ake la'akari da wilayar Ahlul-Baiti (A.S) a matsayin mafi girman ni'ima. Amma ni'ima ta duniya tana iya zama jarrabawar Allah ga mutum. Idan ba a gwama ni'ima da godiya ba, da amfani da ita ta hanyar da ta dace ba, to ni'imar na iya zama wata alama ce ta fushin Allah da sababi na gafalar mutum.

Ma'anar Ni'ima

Ni'ima tana nufin arziƙi da dukiya da sauran abubuwan da Allah yake azurta mutum da shi.[1] Bisa abin da Ibn Manzur ya faɗa a cikin Lisanul Arab, ita ni'ima ta Allah wata baiwa ce wacea babu wanda yake iya ba da ita sai Allah, kamar ido da kunne, saboda babu wani mutum da zai iya bawa wani kyautar irin waɗannan abubuwan sai Allah.[2]

Riwayoyi sun yi nuni cewa ni'imomi ba zai yiwu ba mutum ya iyakancesu.[3] Kazalika mutum ba zai iya godewa ni'imar da Allah ya yi mishi ba.[4]

Misalai Na Ni'imomi Da Nau'ukanta

Allama Ɗabaɗaba'i bisa dogaro da aya ta 18 suratul Nahli yana cewa, duka duniya tarin ni'imomi ne daga Allah wanda ba zai yiwu mutum ya iya ƙididdigesu da iyakancesu gabaki ɗaya ba.[5] A wata riwaya da ta zo cikin littafin Al-Amali na Shaik Ɗusi, Imam Ali (A.S) yana nuni kan ni'imomi Allah kamar rayuwa da kyan fuska da yawaitar iyali da hankali da shiriya da horewa ɗan'adam sammai da ƙassai.[6]

Ni'imomi Na Zahiri Da Na Ruhaniya

Imam Sadiƙ (A.S):
Wallahi mu ne ni'aimar Allah da ya yi a kan bayinSa kuma albarkacinmu mai nasara ya ya samu nasara

Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i. 24, shafi. 51.

Ni'imomi Na Duniya Da Na Lahira

  • Ni'imar duniya; kamar halittar mutum, da tsirrai da ƙasa da sama.
  • Ni'imar lahira; kamar Aljanna da idon ruwa da kayan marmari da mata masu kyau kuma masu tsarki a aljanna.[9]

Godewa Ni'ima Da kafurce Mata

Ƙur'ani yana kira ga muminai da jumloli kamar فَاذْكُرُوا آلَاءَ اللَّهِ Ya ku muminai ku tina ni'imomin Allah da﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ﴾ ya ku waɗanda kuka yi imani ku tina ni'imar Allah a kanku,[10] kuma a hannu guda ƙur'ani ya zargi masu kafurcewa ni'ima a ayoyi da dama, kuma ya ƙarfafa godiya ga ni'imar Allah.[11]

Nasir Makarim Shirazi malamin tafsiri na Shi'a yana cewa kafurcewa ni'ima yana tabbata ta hanya uku; mutum ya raina ni'ima cikin zuciyzrshi, da mantawa da ita ko rashin ambatonta a magana, da amfani da ni'ima a hanyar da ba ta dace ba.[12] Sakamako mai muni ya zo a cikin addini ga mutumin da yake kafurcewa ni'ima, daga cikinsu akwai rashin sanin Allah, da gushewar ni'ima, da halaka da azabtar da shi a ranar lahira, Istidraji wato zai ta yin saɓo Allah ya yi kamar ba ya ganin shi, to amma ba haka ba ne yana tara shi ne, mai rashin godiya za a same shi da hassada.[13] Kuma za a rufe ƙofar alhairi gare shi,[14] za a gaggauta yi mishi azaba a Duniya,[15] mai rashin godiya ba a karɓar addu'arshi,[16] abu na ƙarshe irin wannan mutuman zai sha matsa a kabari.[17]

Jarabawa Ce Ta Allah Ga Wanda Aka yawaita Mishi Ni'ima

Bisa abin da ya zo a aya ta 15 cikin suratul Fajri, yawan ni'ima ga mutum ba dole ba ne ya zama dalili na cewa wannan mutumin yana da kusanci ga Allah, kai yawan ni'imar na iya zama jarrabawa gare shi.[18] Allama Majlisi yana ƙarfafawa bisa dogaro da wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa ruƙo da addini da imani sune alamar cewa Allah yana son mutum, amma dukiya da matsayi a kan-kansu ba sa nuni da cewa Allah ya yarda da mutum.[19] ya zo a cikin wasu ayoyi cewa yawan ni'ima ga mai saɓo, wani nau'i ne na azaba ga mutum kaɗan-kaɗan,[20] Bisa wata riwaya daga imami na shida (A.S) yana cewa yawaita ni'ima ga mutum yana sashi ya gafala da yin istigifari.[21] Murtada Muɗahhari yana cewa yawan ni'ima idan ya haɗu da godiya da amfani ta yadda ya dace, to zai yiwu ta zamo alama ce ta rahamar Allah ga mutum, saɓanin abin da ya gabata abin nufi ba azaba ba ce da kaɗan-kaɗan.[22]

Bayanin kula

  1. Ibn Faris, Mu'ujam Maqayes al-Lugha, juzu'i. 5, shafi. 446.
  2. Ibn Manzoor, Lasan al-Arab, juzu'i. 12, shafi. 580.
  3. Al-Tusi, Amali, shafi. 492.
  4. Misbah, Sajjada Suluk, juzu'i. 1, shafi na 412-435.
  5. Tabatabai, Mohammad Hossein, Tafsir al-Mizan, juzu'i. 12, shafi. 60.
  6. Al-Tusi, Amali, shafi. 492.
  7. Mostafavizadeh, Barsi Wajeh Ni'imat Az Manzare Tawail Dar Qur'an Wa Riwayat Ma’asumin, shafi na. 25.
  8. Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i. 24, ku. 48; Makarem Al-Shirazi, Payame Qur'an, juzu'i. 6, shafi. 387.
  9. Makarem Al-Shirazi, Tafsir al-Amsal, juzu'i. 17, shafi. 349.
  10. Suratul Araf, aya ta 74; Suratul Ahzab, aya ta:9.
  11. Duba: Suratul Baqarah, aya ta 152; Suratul Ibrahim, aya ta 7; Suratul Naml, aya ta 40; Suratul Lukman, aya ta 12; Suratul Saba, aya ta 15-17; Suratul Nahl, aya ta:112.
  12. Makarem Al-Shirazi, Akhlaƙ Dar Kur'ani, shafi. 60.
  13. Misbah al-Sharia, shafi. 104.
  14. Al-Kulaini, Kafi, juzu'i. 4, shafi. 33.
  15. Al-Mofid, Amali, shafi. 237; Al-Tusi, Amali, shafi. 450.
  16. Al-Laithi Al-Wasiti, Uyunul Al-Hikam Wa Mowa'iz, shafi na. 524.
  17. Al-Sadooq, Ilalush Al-Shara'i, juzu'i. 1, shafi. 309.
  18. Makarem Al-Shirazi, Tafsir al-Amsal, juzu'i. 20, shafi. 187.
  19. Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i. 65, shafi. 202.
  20. Al-Ma'amuri,Barsi Sunnate Istidraj Dar Qur'an Wa Miras Tafsiri," shafi. 105.
  21. Al-Kulaini, Kafi, juzu'i. 2, shafi. 452.
  22. Motahari, Majmu'eh Asar, juzu'i. 27, shafi. 626.

Nassoshi

  • Ibn Faris, Ahmed Ibn Faris, Mu'ujam Maqayes al-Lughga, Research: Abd al-Salam Muhammad Haroun, Qum, Islamic Information School, 1404 AH.
  • Ibn Manzoor, Muhammad Bin Makram, Lasan al-Arab, Qum, Cibiyar Buga Adabin Al-Hawza, 1405H.
  • Al-Sadooq, Muhammad Bin Ali, Ilalush Al-Shara'i, Qum, Kantin sayar da littattafai na Dauri, 2006/1385.
  • Tabatabai, Sayyed Muhammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir Qur'an, Qom, Al-Nashar Islamic Library, Juzu'i na 5, 1417 Hijira/ 1996 Miladiyya.
  • Al-Tusi, Muhammad bin Al-Hassan, Al-Amali, Qum, Darul Taqfa, 1414H/1993 Miladiyya.
  • Al-Laithi Al-Wasiti, Ali bin Muhammad, Uyunul Al-Hikam Wal Mawa'iz, Bincike: Hossein Hosni Birjandi, Kum, Darul-Hadith, 1997/1376 Miladiyya.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jami'a Ledurer Akhbar al-Imath al-Athar (amincin Allah ya tabbata a gare shi), Beirut, Al-Wafa Foundation, juzu'i na 2, 1404 AH/1984 AD.
  • Al-Masbah Al-Yazdi, Mohammad Taqi, Sajjada Suluk, Qum, Imam Al-Khomeini (R.A.) cibiyar ilimi da tattaunawa, 2011/1390.
  • Al-Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Amali, bincike: Hossein Astad Wali da Ali Akbar Ghafari, Qum, taron Sheikh Al-Mofid, 1413 AH/1992 AD.
  • Misbah al-Sharia (wanda aka jingina ga Imam Sadik, Amincin Allah ya tabbata a gare shi), Beirut, Al-Alami Publishing House, 1400H/1980 Miladiyya.
  • Mostafavizadeh, Sayyed Mohsen, Barsi Wajeh Ni'imat Az Manzare Tawil Dar Qur'an Wa Riwayat Ma'asumin (A.S) , "Thesis na Master", Tehran, Islamic Azad University, 2013/1392.
  • Motahri, Morteza, Majmu'eh Asar, Tehran, Dar Sadra, Juzu'i na 14, 2011/1390.
  • Mamouri, Ali, Barsi Sunnate Istidraj Dar Qur'an Wa Mirasi tafsir, Journal of Qur'an and Hadith Studies, Fabrairu 2016, fitowa ta 1.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, Akhlaƙ Dar Qur'an, Qum, Imam Ali Ibn Abi Talib (a.s) Wallafe-wallafe, 1999/1378.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, Tafsir al-Amsal, wanda: Rukunin Man al-Bahakin, Kum, Imam Ali Bin Abi Talib (a.s) Madbaba'in Madrasah, juzu'i na 1, 1379 suka shirya kuma suka shirya shi.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, Payam Qur'an, Tehran, Dar al-Kutub Islami, 2002/1381.