Istidraj
Istidraj (Larabci: الاستدراج ) bada lokaci ko ɗaga ƙafa, sunna ce daga cikin sunonin Allah, haka yana nufin Allah baya gaggauta azaba ga maƙaryata, a a yana ɗaga musu ƙafa tare da ba su dama, amma su ba sa anfani da damarsu domin su koma zuwa ga Allah, sai suke yaudarar kansu da kyautatawar Allah da nimar shi, sai suke manta niman gafarar Allah, kuma suka ci gaba da saɓawa Allah, to waɗannan daga ƙarshe azabar su za ta yi muni da yawa.
Ya zo a cikin wasu hadisai cewa duk wanda baya godewa Allah kan ni'imar da Allah ya yi masa, kuma ya ci gaba da saɓon Allah to irin wannan mutumin yana daga cikin mutanan da Allah yake ɗaga musu ƙafa domin su hankalta, amma su kuma ba sa faɗaka. malam Murtada Muɗahhari ya ce, Allah baya ɗagawa mutum ƙafa akan ni'imar shi sai dai idan ya yi anfani da ita a hanyar da ta saɓawa shari'a.
Ma'anar Ɗaga Ƙafa
العبد يذنب الذنب فيُملَى له وتُجدَّد له عندها النعم، فتُلهيه عن الاستغفار من الذنوب فهو مستدرَج مِن حيث لا يعلَم.
Imam Sadiƙ (A.S) ya ce, bawa yana aikata saɓo, sai Allah ya ɗaga mishi ƙafa kuma yana ƙara mishi ni'ima, amma sai wannan ni'imar ta shagaltar da shi daga barin istigfari, lallai yana daga cikin waɗanda Allah yake ɗagawa ƙafa ta yadda bai sani ba.
Shi istidraji ɗaga ƙafa ko bada dama kalma ce wace aka ciro ta daga cikin kur'ani, na farko aya ta 182 a cikin suratul A'araf, karo na biyu kuma aya ta 44 a cikin suratul ƙalam.[2] shi ɗaga ƙafa ko bada dama a cikin harshen Larabci yana nufin kusantar wani abu ko guri daki-daki sannu-sannu[3] Amma a gurin kwararru yana nufin ɗaya daga cikin sunnoni na Allah, kuma yana nufin Allah zai azabtar da azzalumai da masu saɓo masu keta haddin Allah da gangan, amma fa da sannu-sannu zai azabtar da su. kuma duk lokacin da suka so su yi zalinci da girman kai, Allah zai ƙara musu ni'ima, domin su ƙara girman kai da shagalta kan cewar Allah zai azabtar da su, kuma a ƙarshe Allah zai musu azaba mai tsanani.[4]
Ayoyin Istidraji
Akwai ayoyi da yawa da suka yi magana kan Istidraji kai tsaye ko saɓanin haka,[5] wato ɗaga ƙafa da bada dama wasu ayoyi ya zo da kalmar Imhal wato jinkirtawa ko bada dama, kamar aya ta 17 a cikin suratul ɗariƙ:"فَمَهِّلِ الْكافِرينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْداً ka bawa kafirai jinkiri, ka ba su lokaci kaɗan. a wasu daga cikin ayoyin kuma da kalmar Imla'a kamar dai aya ta 178 a cikin suratu Alu-Imran:
kada waɗanda suka kafurce su yi tinanin muna basu dama, wato mana ɗaga musu ƙafa, su yi tinanin hakan alheri ne gare su, a a ba haka bane, kawai mu muna ba su dama ne domin su ƙara laifi ne da kuma zunubi, kuma a gobe ƙiyama za su sha azaba mai ƙasƙantarwa.[6]
Sunnar Jinkirta Azaba Ta Ƙunshi Al'ummu Daban-daban
Wasu masu binciken kur'ani sun ce sunnar jinkirta azaba ba abu ba ne da ya keɓantu ga mutane ɗaiɗaiko ba, a a abu ne da ya shafi al'ummu daban-daban, sun faɗa hakan bisa dogaro kan aya ta 48 a cikin suratul Haj,
Kuma da yawa dafa ciki alƙaryu (Garuruwa) na ba su jinkiri, alhali kuwa suna zalunci, sa'an nan na kama su, kuma zuwa gare ni makoma take.[7]
Alamomin Jinkirta Azaba
Haƙiƙa ya zo cikin ruwayoyi da maganar wasu malamai wasu daga cikin alamomin jinkirta azaba ga su kamar haka:
- Gafala daga istigfari
Kulaini ya rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa haƙiƙa idan Allah ya so bawan shi da alheri bawan zai aikata wani zunubi, sai kuma Allah ya biyo bayan wannan zunubi da wata masifa da zata tunatar da shi da yin istigfari, idan kuma Allah ya so bawa da sharri, to bawan zai aikata wani zunubi, sai Allah ya yi mishi wata ni'ima domin ya mantar da shi neman gafara, kuma zai cigaba da saɓo alhalin yana cikin ni'imar Allah. wannan shi ne faɗin Allah ta'ala: da sannu za mu jinkirta musu azaba ta fuskacin da basu sani ba.[8]
- Rashin godiyar Allah:
Ya zo a wani hadisin daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa; ni'ima idan ba a yi godiya kanta ba, lalle wannan ni'ima Istidraji ce, sai wanda ya rawaito riwayar ya ce, na faɗawa Aba Abdillah na roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba ni dukiya, kuma ya ba ni, kuma na roƙi Allah ya ba ni ɗa, ya ba ni, na ce ya bani gida. ya ba ni gida ya azurta ni, sai na ji tsoron kada wannan ya zama istidrai ne, sai ya ce: "Na rantse da Allah, matukar kana godiya, to ba zai zama istidraji ba.”[9]
- Samun Damar Yin Wani Abu Da Saɓawa Abin Da Aka Saba da Shi:
Fakhrur Razi ɗaya daga cikin malaman tafsiri na Ahlus-Sunna kuma malamin tauhidi a ƙarni na shida ya yi imani da cewa samun damar da mutane masu aikata saɓo suke yi na yin wani abu ya saɓawa wa al'ada istidraji ne.[10]
- Anfani Da Ni'ma Cikin Hanya Ta Haramun:
Murtada Muɗahhari ya ce: Istidraji baya haɗuwa tare da ni'ima sai idan ma'abcoin ni'ima ya yi amfani da ita a hanyar haramun, ko kuma ya yi almubazzaranci ko ruɗuwa da ita.[11]
Talifai Na Musamman
Wasu ba'arin marubuta daga Iraniyawa sun wallafa littafi na musamman kan cikin taken "Istidraj Suƙuɗun Kambe Kam" sun yi jawabi filla-filla dalla-dalla cikin wannan littafi game da istidraji, da faifaice ma'anarsa , da bayanin irin yadda tsananin azaba take kasancewa a cikinsa, sabubba da alamominsa, cibiyar saƙafa da al'adu ma'arif na kur'ani suka buga wannan littafi a shekarar 2007 miladiyya.
Bayanin kula
- ↑ Kulaini,AL-kafi,j 2 shafiu na 4252
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Amsal, juzu'i na 5, shafi na 311..
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 8, shafi na 346.
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Amsal, juzu'i na 5, shafi na 313..
- ↑ Mamouri, "Barasi Sunnat Istidraj dar Kur'an wa mirasi tafsiri", shafi na 105.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 4, shafi na 79.
- ↑ Mamouri, “Barasi sunnat Istidarj dar Kur'an wa miras tafsiri” shafi na 115.
- ↑ Kulaini Kafi, juzu'i na 2, shafi na 452.
- ↑ Kulaini Kafi, juzu'i na 2, shafi na 97.
- ↑ Al-Razi, Mafiatihul al-Ghaib, juzu'i na 21, shafi na 431.
- ↑ Motahari,Majmu Asare, juzu'i na 27, shafi na 626.
Nassoshi
- Al-Tabatabai, Mohammad Hossein, "Al-Mizan in Tafsir al-Qur'an", Beirut - Lebanon, mawallafi: Est
- Al-Razi, Muhammad bin Omar, "Mufatih al-Gheeb", Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Ihya al-Tarat al-Arabi, juzu'i na 3, 1420H.
- Al-Kulaini, Muhammad bin Yaqoob, "Al-Kafi", al-Haqq: Ali Akbar al-Ghafari, Tehran - Iran, mawallafi: Dar al-Kutub al-Islamiyya, juzu'i na 4, 1407H.
- Motahari, Morteza, ""Majmu Asare", Tehran - Iran, Mawallafi: Sadra, Mujalladi na 14, 1390.
- Ma'amouri, Ali, "Barasi Sunnat Istidaraje dar Kur'an wa mirase tafsiri", "Alkur'ani da Hadisi", No. 1, 1386.
- Marafa, Mohammad Hadi, "Al-Tamhid fi Ulum Al-Qur'an", Qom - Iran, Al-Nasher: Est.
- Makaram Al-Shirazi, Nasser, "Al-Amsal fi Tafsir Kitab Allah al-Manzil", fassarar Muhammad Ali Azarshab, Qum - Iran, mawallafi: Madrasah Al-Imam Ali bin Abi Talib , juzu'i na 1. 1421 AH.