Ruhul Kudsi

Daga wikishia

Ruhul Kudsi, (Larabci: روح القدس) na nufin Tsarkakakken Ruhi, Halitta ce tsarkakka daga Aibobi da tawaya, wasu Halittu misalin Jibrilu, Halitta daga Alamul Amru, Karfi na Gaibu, Aklil Fa’alu, Ruhul Arwahu da Manya-Manyan Mala’iku Misdakai ne na Ruhul Kudsi, an danganta wasu ayyuka ga Ruhul Kudsi kamar misalin kaiwa Annabawa Wahayi, Taimakon Muminai, Mafarar Ilimin Annabawa, tushen jefo da hukunci da Ilimi ga Ahlil-Baiti (A.S) da ceto da Ranar Alkiyama. Ruhul Kudsi cikin Adabin Kiristoci Aknumi ne na uku ciki Aknumai guda uku (Uba, `Da, da Ruhul Kudsi) na’am wasu daga Malam Kalam din Kiristanci ba su yarda da Allantakar Ruhul Kudsi ba, an yi amfani da Kalmar Ruhul Kudsi cikin Alkur’ani, cikin Littafi Mai Tsarki, da kuma cikin Adabin Farisanci da Larabci, littafin (Tahlil Falsafi wa Irfani Ruhul Kudsi dar Mutuni Dini) talifin Fatima Ali Pur ya kunshi bayani kan matsayin da Ruhul Kudsi yake da shi a cikin Addinin Zartusht, Yahudanci, da Kiristanci da Muslunci.

Sanin Mafhumi da Matsayi

Ruhul Kudsi, yana nufin tsarkakakken Ruhi, wata Halitta ce da ta tsarkaka daga dukkanin aibobi da tawaya [1] cikin Kamus din Littafi Mai tsarki ya zo cewa Ruhul Kudsi ana kiransa Mukaddas sabaoda ya fito ne daga ayyuka tsarkaka da zuciyar Mumini ta hanyar alakar da yake da ita da Allah da Almasihu ana kiransa da Ruhullahi da Ruhul Almasihu [2] Wannan kalma ta zo cikin Alkur’ani da littafi Mai Tsarki, Hakika Alkur’ani ya yi Magana ka saukar da Alkur’ani ta hanyar Ruhul Kudsi [3] da kuma goyan Bayan Annabi Isa da ya yi [4] wannan kalma anyi amfani da ita cikin Adabin Farisanci

فیض روح‌القدس ار باز مدد فرماید دیگران هم بکنند آنچه مسیحا می‌کرد[]

Alherin Ruhu Mai Tsarki ya taimaki wasu sun yi abin da Almasihu ya yi [5]

Wane ne Ruhul Kudsi

An kawo fuskoki daban-daban kan wanene Ruhul Kudsi:

  • Jibrilu: wasu adadi daga Malaman Tafsiri suna ganin Mala’ika Jibrilu ne Ruhul Kudsi [6] kiran Mala’ika Jibrilu da sunan Ruhul Kudsi wata ishara kan Ruhaniyyarsa da tsarkakarsa da rawar da yake takawa cikin raya addini. [7]
  • wata Halitta ce a Alamul Amru: Allama Tabataba’I Yana ganin Ruhul Kudsi matsayin wata Halitta daga Alamul Amru kuma ba Mala’ika bane yana taimakawa cikin kai sakon Wahayi [8]
  • Manya-Manya Mala’iku: ya zo a riwaya daga Imam Sadik (A.S) cewa Ruhul Kudsi yana gaban Jibrilu da Mika’ilu a girmama, ya kuma kasance tare da Annabi (S.A.W) bayan wafatinsa ya koma wurin Imaman Shi’a [9] a wasu ba’arin riwayoyin Ruhul Kudsi shi ne Ruhul Kudsi da maganarsa ta zo cikin Alkur’ani [10] wanda yake saukowa tare da sauran Mala’iku a daren Lailatul Kadri [11]
  • Karfi na Gaibu: Ruhul Kudsi Ismul A’azam [12] ko kuma Karfi na Gaibu [13] wanda Isa Almasihu ya raya Matattu da taimakonsa, wannan karfi na Gaibu akwai shi cikin dukkanin Mumini amma cikin yanayi mai rauni, kuma yana taimakonsu daga nesantuwa daga aikata zunubi [14]
  • na farko: a cewar Sayyid Haidar Amoli, Masana Hikima sun ittifaki Ruhul Kudisi shi ne ya fara gangaro da hankali, na’an ya zo da sunaye mabanbanta daga ciki: Ruhul Kudsi da Aklul Fa’alu [15]
  • Ruhul Arwahi: a wasu ba’arin rubuce-rubucen Arifai, an yi Magana kan Ruhul Kudsi da taken Ruhul Arwahi cewa ba Halittar Allah bace [16]

Wazifofi

A cikin Alkur’ani da Hadisai an danganta wasu wazifofi zuwa ga Ruhul Kudsi.

  • Isar da Wahayi zuwa ga Annabawa: kan asasin Imani da cewa Jibrilu ne Ruhul Kudsi, kai wahayi da Sakon Allah ga Annabawa yana cikin ayyukansa.
  • taimako da Tallafawa Annabawa da Waliyyan Allah: cikin wata ayar Alkur’ani da Magana ta zo dangane da goyan bayan Isa Almasihu ta hanyar Ruhul Kudsi, kan asasin Ra’ayin Malaman tafsiri goyan baya ya zo ne da ma’anar taimako, [17] wasu ba’ari suna ganin Linjila matsayi Misdakin Ruhul Kudsi [18]
  • Mafarar Ilimin Annabawa: ya zo a ba’arin wasu riwayoyi cewa akwai Ruhu guda biyar cikin Annabawa da Wasiyyai, Ruhul Kudsi ya kasance daya daga cikinsu, ta hanyarsa ne Annabawa suke sanin abubuwa, [19]
  • jefa Hukuncin Allah zuwa ga Ahlil-Baiti (A.S), kan asasin wasu riwayoyi, Ahlil-Baiti kan asasi hukuncin Allah, Annabi Dauda da abinda Ruhul Kudsi ya jefa cikin zuciyarsa da shi suke hukunci. [20]
  • Ceto a ranar Alkiyama:kan asasin wani Hadisi daga Annabin Muslunci (S.A.W) ya ce: Ruhul Kudsi shi ne Farkon wanda zai fara yin ceto a ranar Alkiyama. [21]
  • Taimako ga Muminai: kan asasin Riwayoyi Ruhul Kudsi, ba zai gushe ba yana taimakon Muminai matukar sun dawwama cikin bada kariya ga Annabi (S.A.W) da Ahllil-Baiti (A.S) [22] an samu Rahoto daga Ibn Asir Masanin tarihin Muslunci cewa: Annabi (S.A.W) ya roki Allah ya sanya Ruhul Kudsi cikin Taimakon Hassanu Bn Sabit Shahararren Mawaki a lokacin Jahiliya, kuma bayan musluntarsa ya kasance yana yabon Annabi da sukan Makiyansa, Matukar dai bai gushe kan kariya ga Muslunci da sukan Makiyan Muslunci To Allah ya sanya Masa Ruhul Kudsi [23]

Uluhiyyya

Cikin Adabin Kiristanci, Ruhul Kudsi ya kasance Aknumi na uku daga Aknumai guda uku (Uba `Da, Ruhul Kudsi) [24] cikin littafi Mai Tsarki an jingina rayuwa gare shi [25] kan asasin littafi Mai Tsarki, Hakika Muminai a lokacin Tuba suna samun Ruhul Kudsi, shine kuma yake tsarkake su daga Datti da kazantar zunubi, [26] na’am Malaman Kalam din Kiristanci sun samu sabanin ra’ayi kan yarda da Allantakar Ruhul Kudsi, wasu daga cikinsu sun yi inkarin Allantakarsa suna ganin cewa Mala’ika ne [27] Wasu ba’ari kuma sun yi Imani cewa Ruhul Kudsi ba wata halitta ce mai cin gashin Kanta, bari dai shi Tajalline na Allah, kuma sun yi Imani da Allantakarsa. [28]

Bayanin kula

  1. Zamakhshari, Al-Kashshaf, 1407 AH, juzu'i na,shafi na 162.
  2. Hawks, Kamus Kitab Mukaddas, 1394, shafi na 424.
  3. Suratul Nahal, aya ta:102.
  4. Suratul Baqarah, aya ta 87, 253; Suratul Ma’edah, aya ta:110.
  5. Diwan Hafez, Hafez's Ghazaliyats, Ghazal 143.
  6. Duba: Tusi, Al-Tabayan, Beirut, juzu'i na 1, shafi na 340; Makarem Shirazi, Tafsir Namunaeh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 339.
  7. Duba: Abuhian Andalusi, Al-Bahr Al-Muhit, 1420 AH, Juzu'i na 1, shafi na 481; Makarem Shirazi, Tafsir Namunaeh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 339
  8. Tabatabaei, Al-Mizan, juzu'i na 13, shafi na 196-198.
  9. Qummi, Tafsirul Qummi, 1404H, juzu'i na 2, shafi na 279.
  10. Suratul Kadri, aya ta 4.
  11. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 94, shafi na 14
  12. Abuhian Andalusi, Al-Bahr Al-Muhait, 1420H, Mujalladi na 1, shafi na 481.
  13. Duba: Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 339.
  14. Duba: Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 339.
  15. Amoli, Jame al-Asrar, 1347, juzu'i na 1, shafi na 688.
  16. Jili, Al-Insan al-Kamal fi Marafah al-Awakhir wa al-Awael, 1418 AH, shafi na 150.
  17. Fakhr Razi, Mufatih al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 3, shafi na 596; Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 1, shafi na 207.
  18. Duba: Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 339; Tusi, Al-Tabayan, Beirut, juzu'i na 1, shafi na 340.
  19. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi na 1, shafi na 272.
  20. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 398.
  21. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahihin, Beirut, juzu'i na 4, shafi na 496-498.
  22. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 102.
  23. Ibn Athir, Asdal Ghabah, 1409H, juzu'i na 1, shafi na 482.
  24. Hawks, Kamus Kitab Mukaddas, 1394, shafi na 424.
  25. Hawks, Kamus Kitab Mukaddas, 1394, shafi na 424
  26. Hawks, Kamus Kitab Mukaddas, 1394, shafi na 424
  27. McGrath,Dar-Amadi bar Ilahiyat Masihi, 2005, shafi na 309-310.
  28. Soleimani Ardestani, Dar-Amadi bar Ilahiyat Tadbiki Islam wa Masihiyat, 2013, shafi na 126-127.

Nassoshi

  • Alqur'ani.
  • Amoli, Seyyed Haider bin Ali, Jame al-Asrar da al-Morzam al-Nur, wanda Henry Corbin da Osman Ismail Yahya suka yi bincike a Tehran, 1347.
  • Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Asad al-Ghabha fi Marafah Sahabah, Beirut, Darul Fikr, 1409/1409/1989.
  • Abuhian Andalsi, Muhammad bin Yusuf, Al-Bahr al-Muhait fi al-Tafsir, bincike na Sedqi Muhammad Jamil, Beirut, Darul Fikr, 1420H.
  • Jili, Abdul Karim bin Ibrahim, Al-Hussan al-Kamal fi Marafah al-Akher va-Awal, Research by Salah Muhammad Awaidah, Beirut, Dar al-Kutb Al-Alamiya/Manshurat Muhammad Ali Bizoun, 1418 AH/1977 AD.
  • Hakim Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, Al-Mustadrak Ali Al-Sahiheen, Beirut, Daral-e-Marefa, Bita.
  • Divan na Hafez's Ghazals.
  • Zamakhshari, Mahmoud, al-Kashf kan haqiqanin Gawamaz al-Tanzir, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1407H.
  • Soleimani Ardestani, Abdur Rahim,Dar-Amadi bar Ilahiyat Tadbiki Islam wa Masihiyat, Qum, Kitab Taha, 1382.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Dar Ahaya al-Trath al-Arabi, Bita.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosro, 1372.
  • Allameh Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1390 AH.
  • Allameh Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatih al-Ghaib, Beirut, Dar Ahaya al-Trath al-Arabi, 1420H.
  • Qomi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsirin Qami, Sahih Tayyib na Musawi Al-Jaziari, Qum, Darul Kitab, 1404H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, Tehran, Islamic Darul Kitab, 1407H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1374.
  • McGrath, Alistair, Dar-Amade bar Ilahiyat Masiyat, wanda Isa Dibaj ya fassara, Tehran, Kitab Roshan, 2005.
  • Hawkes, James,Kamus Kitab Mukaddas, Asatir Publishing House, 2014.
  • "Tahlil Falsafe Irfani Ruhul Kudsi dar Mutuni Dini, An Buga"].