Hindu Ƴar Utuba
Hindu Ƴar Utuba (Larabci: هند بنت عتبة) ita ce wadda aka fi sani da mai cin hanta, ta rasu, shekara ta 13 bayan hijira, ta kasance matar Abu Sufyan Sakar ɗan Harbu, kuma mahaifiya ce ga Mu'awiya, ta halarci yaƙin uhudu tare da mushrikai ta kasance tana tunzura su don yaƙar musulmi, bayan kammala yaƙin uhudu - wanda aka dauke shi a matsayin ɗaukar fansa a kan kisan da aka yi wa mushirikai a Badar - Hindu ta wulaƙanta gawar shahidan musulmi. Haka kuma ta je jikin gawar Hamza ɗan Abdul Muɗɗalib, Sai ta yanka ƙirjinshi, ta fito da hantarshi, da sauri ta tauna. kuma ta yi ɗankunne da awarwaro da kunnan shahidan Musulmi domin isgili. Ta musulunta bayan fatahu makka, kuma ta rayu har zuwa zamanin Halifa Umar ɗan Khaɗɗab.
Rayuwarta
Hindu bint Utba ɗan Rabi'atu ɗan Abdush-shamsi, mahaifinta ɗaya ne daga cikin manya kuraishawa,[1] mahaifiyarta kuwa ita ce Safiya bintu Umayya bin Harisa,[2] an ce tana daga cikin mafi kyawun matan Kuraishawa,[3] kuma tana cikin waɗanda suke da ra'ayi da daraja,[4] kuma wasu litattafai sun jingina wasu baitikan waƙa gareta.[5] Hindu ta auri Hafsu ɗan Mugira ɗan Abdullah Al-Makzumi baffan Khalid ɗan Walid,[6] ta haifi ɗanta mai suna Aban,[7] bayan wani lokaci sai ya sake ta,[8] Don haka ta zargi mahaifinta ya aurar da ita ga Hafsu ba tare da ya shawarce ta ba, kuma bare da nemi ra'ayinta ba,[9] sannan ta auri Abu Sufyan,[10] ta haifa masa Mu'awiya da Utba.[11] da Juwayriya da Ummu Hakam,[12] kuma a kan abin da Zahabi ya ambata, Abu Sufyan ya sake ta a ƙarshen rayuwarshi,[13] a zamanin halifa na biyu ta karbo aron Dirhami dubu hudu daga baitulmali, ta yi kasuwanci da su.[14] Ibn Jauzi ya ce ta rasu a shekara ta 14 bayan hijira, a zamanin halifa na biyu,[15] yayin da Ibn Hajar Al-asƙalani ya ambaci rasuwarta a zamanin halifancin Usman.[16]
Hindu Ta Je Yaƙin Uhudu
Hindu ta halarci yaƙin uhudu,[17] tare da mushrikai, tana zuga su don yakar musulmi,[18] kuma takasance tana karanta wadannan baitikan:
Mu `ya`yan ɗarik ne muna tafiya a kan shimfidu na alfarma ƙanshin tiraran Almuski a ko ina, amma makamunmu yana shirye. Idan kuka yarda, sai mu rungumi juna, kuma mu shinfiɗa muku shinfiɗar alfarma Amma idan baku yarda ba, to za mu rabu rabuwar har a bada.[19]
Wulaƙanta gawar shahidi Hamza da shahidan Uhudu
Hindu ta umurci bawanta marar imani da ya kashe ɗaya daga cikin mutum uku, Muhammad (S.A.W), Imam Ali (A.S) Hamza (A.S).[20] sai bawan nata ya kashe Hamza,[21] Hindu ta yanka ƙirjinshi da cikinshi,[22] ta fitar da hantarshi ta tauna da haƙoranta,[23] sannan ta ɗauki sassa na jikin Hamza da aka yanke ta tafi da su zuwa Makka.[24]
Ta Rera Wasu Baitika Kan WulakantaGawar Hamza
Zuciyata ta huce daga abin da Hamza ya yi min a yaƙin uhudu ta hanyar fasa cikinshi da futo da hantarshi. Yanzu na warke daga wannan baƙin cikin mai tsanani da nake fama da shi.[25] Manzon Allah (S.A.W) ya siffantata a matsayin mai cin hanta, a lokacin da ta ciji hantar Hamza a yakin Uhudu.[26] kuma ana kiran `ya`yanta da `ya`yan mai cin hanta.[27] Bayan Hindu da mata mushrikai da suke tare da ita sun wulaƙanta gawawwakin shahidan yakin uhudu, ban da gawar Hanzala ɗan Abi Amir, saboda mahaifinshi yana cikin rundunar mushrikai.[28] sai Hindu ta yi ɗan kunne da awarwaro da kunnuwa da hancin shahidai dan cin mutunci da isgili gare su.[29]
Musuluntarta
Hindu ta musulunta a ranar da aka fatahu Makka, kuma ta musulinta ne bayan da mijinta Abu Sufyan ya musulunta.[30] Don haka aka ambaci sunanta a cikin Sahabbai,[31] kuma wasu litattafai sun yi shakka kan musuluntarta ko kuma suna ganin ba gaskiya ba ne.[32]
Manzon Allah (S.A.W) ya yi hukunci da cewa jinin Hindu ya halatta,[33] a lokacin da ta zo wurinshi don musulinta da yin kalmar shahada, sai ta rufe fuskarta, bayan ta yi kalmar shahada sai ta buɗe fuskarta.[34] Kamar yadda Ibn Asakir ya rubuta, Manzon Allah ya ce mata: Kada ki yi shirka da Allah, kuma kada ki yi zina kuma kada ki yi sata Sai Hindu ta ce: ya ubangiji `ya`yan mu ƙanana ne kuma ka kashesu sanda suka zama manya, Sai Annabi ya ce Allah ya kashe su(Allah ka la'ancesu) Hindu,[35] ya zo a cikin wasu litattafai cewa Hindu ta shahara da yin zina a garin Makka.[36] amma akwai wasu dalilai da suke kore hakan.[37]
Annabi ya tambayi Hindu bayan ta musulunta cewa, Ya kike ganin Musulunci? Sai ta kada baki ta ce mishi, babu abin da ya fishi kyau, ba dan abin uku ba, ruku'u, hijabi, da ihun baƙin bawa a saman Ka'aba (wato muryar Bilal Habashi a lokacin kiran sallah)sai Manzon Allah ya ce, Amma ruku'u babu wata sallah idan babu shi, kuma shi hijabi wani abu ne ya fishi sitirta jiki,shi kuma Bilal, bawan Allah ne abin alfahari.[38] Hinduu ta shaida yaƙin Yarmuk tare da mijinta Abu Sufyan, kuma ta kasance tana ingiza musulmi da su yaƙi Rumawa.[39]
Bayanin kula
- ↑ Ibn Abdul al-Barr, Al-Isti'ab, juzu'i na 2, shafi na 715.
- ↑ Ibn Habib, Al-Muhabar, shafi na 19.
- ↑ Al-Dhahabi, Tarikhul Islam, juzu'i na 3, shafi na 298.
- ↑ Al-Dhahabi, Tarikhul Islam, juzu'i na 3, shafi na 298.
- ↑ Bashir Yamout, Sha'iratul Arab Fij jahiliyya wal islami, juzu'i na 1, shafi na 128.
- ↑ Ibn al-Atheer, Usudul Ghaba, juzu'i na 6, shafi na 293;
- ↑ Ibn Saad, Al-Thabaqat Al-Kubra, juzu'i na 8, shafi na 187.
- ↑ Al-Tabarani, Al-Mu’jam Al-Kabir, juzu’i na 25, shafi na 69.
- ↑ Sabt bin Al-Jawzi, Miryah al-Zaman fi Tavarikh al-Ayan, juzu'i na 5, shafi na 204.
- ↑ Ibn Sa’d, Tabaqat al-Kubra, juzu’i na 8, shafi na 187.
- ↑ Ibn Asakir, Tarikhu Madina Damashki, juzu'i na 27, shafi na 180.
- ↑ Al-Baladhuri, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 5, shafi na 5.
- ↑ Al-Dhahabi, Tarikhul Islam, juzu'i na 3, shafi na 299.
- ↑ Al-Dhahabi, Tarikhul Islam, juzu'i na 3, shafi na 299.
- ↑ Sabbat Ibn Al-Jawzi, Mir'atul Zaman Fit Tawarikhi Al-Ayan, juzu'i na 5, shafi na 206.
- ↑ Ibn Hajar Asqlani, Al-isaba, 1415, Juzu’i na 8, shafi na 347.
- ↑ Al-Qummi, Tafsiri Al-Qummi, juzu'i na 1, shafi na 111.
- ↑ Al-Qummi, Tafsiri Al-Qummi, juzu'i na 1, shafi na 111.
- ↑ Ibn Abd al-Barr, Al-Isti'ab, juzu'i na 4, shafi na 1922.
- ↑ Al-Mufid, Al-Irshad, juzu'i na 1, shafi na 83.
- ↑ Ibn al-Jawzi, al-Muntazem, juzu'i na 3, shafi na 179.
- ↑ Ibn al-Athir, Usudul al-Ghaba, juzu'i na 1, shafi na 530.
- ↑ Ibn al-Athir, al-Kamel, juzu'i na 2, shafi na 159.
- ↑ Al-Balazari, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 4, shafi na 287.
- ↑ Ibn Hisham, Seerah al-Nabawiyyah, juzu'i na 2, shafi na 92.
- ↑ Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 30, shafi na 296.
- ↑ Al-Manqari, Waqqa Safin, shafi na 179.
- ↑ Ibn al-Athir,Usud al-Ghaba, juzu'i na 1, shafi na 530.
- ↑ Al-Salehi, Sublul al-Huda, juzu'i na 4, shafi na 220.
- ↑ Ibn al-Athir, Usdul al-Ghaba, juzu'i na 6, shafi na 292.
- ↑ Ibn al-Athir,Usdul al-Ghaba, juzu'i na 6, shafi na 293; Al-Isfahani, Marifatul Sahaba, juzu'i na 6, shafi na 3460.
- ↑ Al-Sushtari, Qamoos al-Rijal, juzu'i na 12, shafi na 350.
- ↑ Al-Diyar Bakri, Tarikh al-Khamis, juzu'i na 2, shafi na 94.
- ↑ Al-Maqrizi, Imtaa al-Isma, juzu'i na 13, shafi na 389.
- ↑ Ibn Asakir, Tarikhi Madinati Damashk, juzu'i na 70, shafi na 178
- ↑ Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj Al-Balagha, juzu'i na 1, shafi na 336.
- ↑ Mahdi bin Rizkullah, Maza'imu wa Akta'u, juzu'i na 1, shafi na 54.
- ↑ Ibn Asaker, Tarikhu Madinati Damashk, juzu'i na 70, shafi na 182.
- ↑ Ibn al-Athir, Usdul al-Ghaba, juzu'i na 6, shafi na 293.
Nassoshi
- Ibn Abi al-Hadid, Abd al-Hamid, "Sharh Nahj al-Balagha", Al-Haqqi: Muhammad Abul-Fazl Ibrahim, Qum - Iran, Publisher: Ayatullah Al-Marashi Library, 1404 AH.
- Ibn al-Athir al-Jazari, Ali ibn Muhammad, "Usdul Al-ghaba Fi Marifati Sahaba", Beirut - Lebanon, mawallafi: Darul Fakr, 1409H.
- Ibn al-Athir al-Jazari, Ali ibn Muhammad, ""Kamil Fit Tarikh", Beirut-Lebanon, Al-Nasher: Dar al-Asaq, 1385H.
- Ibn Al-Jawzi, Abd al-Rahman bin Ali, "Al-Mantazm", Al-Muhaqqan: Muhammad Abd al-Qader Atta da Mustafa Abd al-Qader Atta, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar al-Kutub al-Elamiya , 1412 AH.
- Ibn Habib, Muhammad, "Al-Mohbar", Al-Haqq: Ilza Lichten-Shitter, Beirut-Lebanon, Publisher: Dar Al-Afaq Al-Jadila, D.T.
- Ibn Hajar al-Asqlani, Ahmed bin Ali, "Al-isabah fi Tamyiz al-Sahaba", Al-Muhaqqan: Abd Al-Mawati Adel Ahmed da Ali Muhammad Ma'awad, Beirut - Lebanon, Publisher: Dar Al-Kutub Al -Ilamiya, juzu'i na 1, 1415H.
- Ibn Saad Al-Waqadi, Muhammad, "Al-Taqabat al-Kubra", Beirut - Lebanon, Publisher: Dar Al-Kutub Al-Elamiya, juzu'i 2, 1418 AH.
- Ibn Abd al-Barr, Yusuf bin Abd Allah, "Al-Isti'ab Fi Marifati Sahaba", Al-Haggiq: Ali Muhammad Al-Bajawi, Beirut - Lebanon, Mawallafi: Dar Al-Jil, 1412 Hijira.
- Ibn Asaker, Ali bin Hossein, "Tarikhu Madinati Damashke", al-Haqq: Ali al-Sheiri, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar al-Fakr, 1402H.
- Ibn Hisham, Abd al-Malik, "Al-Sira al-Nabawiya", al-Muhaqqun: Mustafa al-Saqqa, Ibrahim al-Ibiari, and Abdul Hafiz al-Shalbi, Beirut - Lebanon, publisher: Dar al-Marfa' a, d.t.
- Al-Isfahani, Ahmed bin Abdullah, "'Marifah Sahabah'", mai bincike: Muhammad Hassan Ismail Al-Shafa'i, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Kutub Al-Elamiya - Manuscripts na Muhammad Ali Beizun, 1419 AH.
- Bashir Yumut, ""Sha'iratul Arab Fij Jahiliyyah wal Islam", Beirut - Lebanon, mawallafi: Al-Muqabah Al-Ahliyya, 1352H.
- Al-Balazari, Ahmed bin Yahya, "Ansab al-Ashraf", al-Muhaqqan: Sohail al-Zakar, Wariyad al-Zarkali, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar al-Fakr, 1417 AH.
- Al-Diyar Bakri, "Tarikh Al-Khamis fi Ahaval Anfas Al-Nafis", Beirut - Lebanon, Al-Nasher: Dar Al-Esq, D.T.
- Al-Zahabi, Muhammad bin Ahmed, "'Tarikh al-Islam'", Al-Haggiq: Omar Abd al-Salam Tadmari, Beirut - Lebanon, Publisher: Dar al-Kitab al-Arabi, 1409 AH.
- Sabat Ibn Al-Jawzi, "Mir'atuz Zamani fit tawarikh Al-ayan", Damascus - Sham, Mawallafi: Dar Rishala Al-Amani, 1434H.
- Shahata, Mohammad Saqr, Mu'awiya bin Abi Sufyanw wa shubuhat Ward Muftariat", Alexandria - Egypt, mawallafi: Dar al-Kulfifa al-Rashdin, D.T.
- Al-Shushtri, Mohammad Taqi, ""Kamus Rijal", Qom - Iran, mawallafi: Estado al-Nashar al-Islami, 1410 AH.
- Al-Salehi, Muhammad bin Youssef, "Sublul Al-Huda wa Al-rahad fi siratil Khair al-ibad" - Beirut - Lebanon, Al-Nasher: Dar Al-Kutub Al-Elamiya, 1414H.
- Al-Tabarani, Suleiman bin Ahmad, "Al-Majam al-Kabir", mai bincike: Hamdi bn Abdulmajeed al-Salfi, Alkahira - Masar, mawallafin: Laburaren Ibn Taimiyyah, 1415 Hijira.
- Al-Qummi, Ali bin Ibrahim, "'Tafsir Al-Qummi'", al-Muhaqq: Tayyab al-Musawi, Qom - Iran, mawallafi: Dar al-Kitab, 1404H.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, "Bihar al-Anwar al-Jamaa Lederer Akhbar Imamat al-Athar", Beirut-Lebanon, mawallafi: Dar Ihiya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
- Al-Mufid, Muhammad, "Al-Irshad fi Marifah Hajjullah Ala Al-ibad", Qom - Iran, Sheikh Al-Mufid, juzu'i 1, 1413H.
- Al-Maqrizi, Taqi al-Din, "Imta'a al-Ismaa," mai bincike: Muhammad Abdul Hamid Al-Namisi, Beirut-Lebanon. , Mawallafi: Dar Al-Kutub Al-Elamiya, 1420H.
- Al-Manqari, Nasr bin Muzahim, 'Waqqa Siffin, edita: Abd al-Salam Muhammad Harun, Qum - Iran, mawallafin: Laburaren Ayatullah al-Mar'ashi, 1404H.
- Mahdi bin Rizq Allah, Maza'imu wa Akta'u, kurakurai, sabani, da shubuhohinsa a cikin littafinsa: Rayuwar Manzo Muhammad, Nazari mai Muhimmanci, Madina - Masarautar Arabiya, Mawallafi: King Fahd Complex, D.T.