Afdaliyat Imam

Daga wikishia
(an turo daga Fifitar Imami)
Wannan rubutu ne dangane da fifikon Imam. Domin neman fifikon Imaman Shi'a (A.S), ku duba fifikon Ahlul Baiti (A.S).

Afdaliyat Imam (Larabci: أفضلية الإمام) daya daga cikin Sharuddan Imamanci wanda yake da ma'anar fifitar Imam cikin siffofi da kamala kan sauran mutane, a mahangar Malaman Kalam na Imamiya, dole Imami ya fifita kan sauran mutane cikin Ilimi, Addini, Tak'wa, Kyauta, Jarumta, haka cikin Lada nasa na Lahira, Malamai sun jingina da ka'idar Kubhu Tarjihu Bila-Murajjihu (Munin rinjayarwa ba tare da Mai rinjaye ba) da kuma Kai'idar Kubhu takdimul Mafdul alal Afdal (Munin Rinjjayar da wanda aka fifita kan wanda yake mafi fifita) da kuma Hadisin Annabi (S.A.W) da yake cewa (duk wanda yake shugabanci da jagorantar wasu jama'a alhali cikin wannan jama'a akwai wanda ya fi shi ilimi lallai zai jagorance su zuwa ga tabarbarewa har zuwa tashin kiyama.) Haka kuma cikin kafa dalili sun jingina da wasu ba'arin Ayoyin Alkur'ani. Galibin Ahlus-Sunna ba su yi Imani da wajabcin fifitar Imami ba sun tafi kan halascin Imamanci Mafdul (wanda jama'a suka zaba) idan akwai maslaha cikin hakan, a cewa Sa'adud-dini Taftazani babban Malamin Kalam a Mazhabar Ash'aranci a karni na takwas hijiri Kamari, a ra'ayin Ahlus-sunna da mafi yawan Firkokin Muslunci Imamanci gaskiya shi ne Imamancin wanda a kowanne zamani yake Afdal (Mafi fifita) kan sauran mutane, sai dai idan Imamancinsa zai haifar da fitina da hargisti da rashin zaman lafiya, daya daga cikin dalilan Ahlus-sunna kan haka shi ne Ijma'in Malamai kan tabbatuwar Imamanci Mafdul (wanda mutane suka zaba) daga ba'arin Kuraishawa bayan Kulafa'ur Rashidin ko da kuwa akwai Afdal (wanda ya fishi fifiko da falala) cikin mutane, haka kuma yana daga cikin dalilinsu akwai sallama zabar Halifanci zuwa ga kwamitin Shura mai dauke da mutane shida wanda halifa na biyu ya samar da shi tare da cewa a lokacin akwai wanda ya fi kowa cancanta da Halifanci. A mahangar Malaman `Yan Shi'a, Imaman Shi'a (A.S) bayan Annabin Muslunci (S.A.W) su ne mafifita cikin halittun Allah, Allama Majlisi ya tafi kan cewa babu wanda zai yi inkarin fifitar A'imma (A.S) sai mutumin da ya jahilci riwayoyi. Ana kiran hujjar da aka kafa dalili da ita kan afdaliya da fifitar Imam Ali (A.S) da sunan Burhan Afdaliya.

Fadaduwa da Kuma Sanin Mafhumi

Fifitar Imam Ali (a.s) a mahangar galibin Malaman Kalam na Imamiyya Ilimi, Tak'wa, Adalci, da Jarumtaka suna daga sharuddan Imamanci[1] a wasu ba'arin Masadir na Kalam an fassara Afdaliyat da ma'anar fifita cikin Ibada da kuma amfanuwa da ladan Allah[2] da wannan ne Malaman Kalam na Shi'a suke ganin larurar fifitar Imami kan sauran mutane cikin dukkanin Kamala daga falala ta ma'anawiya da ta gangar jiki misalin ilimi, addini, kyauta, Jarumtaka,[3] da kuma amfanuwa daga ladan lahira[4] kuma sun tafi kan cewa dole Imami ya zama mafi ilimi mafi sani mafi Jarumta mafi kyauta mafi hakuri mafi tsoran Allah a zamaninsa a cikin dukkanin mutane[5] domin mutane su samu damar biyayya gare shi[6] wasu sun ce ba larura bane Imami ya zama ya fifita kan sauran mutane cikin al'amuran duniya misalin dukiya da karfin iko saboda hadafi shi ne da'a ta hakika ga Imam da imani na hakika da shi bawai biyayya ta zahiri gare shi ba[7]

A Mahangar `Yan Shi'a Wajibi ne Imami ya Kasance ya Fifici Kowa

Malaman Kalam na Shi'a Imamiyya su na ganin fifita cikin Sharuddan Imamanci[8] a wannan mas'ala dukkanin su suna da ittifakin ra'ayi[9] sannan domin tabbatar da Afdaliyar Imami akwai dalilai na nakali da hankali.

Dalilai na Hankali

1.hakika Imami cikin Falaloli da Kamala, ko dai ya kasance daidai da Sauran Mutane ko kuma ya zama kasa da su, ko sama da su. Idan ya kasance daidai da sauran Mutane, ya zama kenan zabarsa a matsayin Imami rinjayarwa ne ba tare da Mai rinjaya ba, zabi daya daga cikin abubuwa da suke daidai da juna ba tareda dalili da zai sanya a rinjaya da dayansu hakika hankali baya karbar haka yana ma ganin sa abu ne da ba zai yiwuwa ba hakan ta faru daga Allah, idan kuma Imami ya zama kasa da sauran mutane a hankalce abu ne mai matukar muni rinjayar mutum da yake kasa da sauran mutane a kan mutanen, saboda haka dole ne Imami ya zama ya fifita ya daukaka a kan sauran mutane[10] 2.wajibi ne Imami ya kasance Ma'asumi, hakika Ma'asumi ya fifita kan wanda ba Ma'asumi ba, saboda haka dole ne Imami ya zama ya fifita kan sauran Mutane[11] 3.Annabi (s.a.w) yake ayyana Imami, kuma a koda yaushe Annabin Muslunci (s.a.w) ya zabar Mutum Mafi falala da daraja a matsayin Magajinsa[12]

Dalilai na Nakali

Hakika an kafa dalili da aya ta 35 cikin suratul Yunus[13] da kuma aya ta 19 ayar Sadikin cikin Suratul Tauba[14] da aya ta 9 cikin Suratul Zumar[15] kan fifitar Imami cikin wadannan ayoyi bayani ya zo karara kan fifita Mutum mai shiryarwa zuwa gaskiya kan mutumin da a kankin kansa yana da bukatar a shiryar da shi, fifita wadanda suke tare da masu gaskiya a kan wadanda suke tare da marasa gaskiya, fifita Malami kan wanda ba Malami ba, dukkanin wadannan ayoyi suna shiryarwa kan gabatar da fifitar mutum mafi falala da daraja kan wanda mutane suke baiwa falala da daraja[16] Domin tabbatar da sharadin fifitar Imami Malamai sun dogara da riwayoyi Bahrani, Manar Al-Huda, 1405 AH, shafi na 127-130. daga cikinsu akwai riwayar da aka nakalto daga Annabi (s.a.w):

مَنْ أَمَ قَوْماً وَ فِیهِمْ مَنْ هُوَ أَعْلَمُ مِنْهُ لَمْ یزَلْ أَمْرُهُمْ إِلَی السَّفَالِ إِلَی یوْمِ الْقِیامَةِ

Duk wanda ya jagoranci wata al'umma alhalin cikinsu akwai wanda ya fishi ilimi lamarin wannan al'umma ba zai gushe ba zuwa ga tabtarbarewa har zuwa tashin Kiyama[17] Wannan riwaya ta nuna munin Mafdul gabatar Mai falala kan Afdal wanda yake shi ne Mafi falala,[18] haka a cikin wata riwaya daga Ahlus-sunna an nakalto cewa Abu Darda ya kasance yana shiga gaban Abubakar lokacin da suke tattakawa sai Annabi (s.a.w) ya ce masa shin kana shiga gaban wanda ya fificeka a duniya da lahira ?[19] Malamai sun ce wannan riwaya ta bayani karara kan munin fifita Mafdul Mai Falala kan Afdal mafi Falala, saboda haka zai zama mafi dacewa shi ne wannan riwaya tana shiryarwa kan munin fifita Mai falala kan Mafi falala a cikin lamarin Imamanci[20]

A mahangar Ahlus-Sunna Imamancin wanda mutane suka fifita ya halasta

Galibin Ahlus-sunna ba sa ganin Afdaliyat fifitar Imami a matsayin sharadi na wajibi kuma sun tafi kan halascin Imamanci wanda mutane suka fifita. Asha'ira: Malaman Kalam na Asha'ira basu yarda da wajabcin fifitar Imami ba, da wannan ne ma suke ganin halascin Imamanci wanda mutane suke so kan wanda yake mafi fifita[21] amma tare da haka Khadi Abubakar Bakillani Malamin Kalam na Asha'ira a karni na biyar shi yana ganin fifita daya daga cikin siffofi ne na wajibi kan Imami sai dai idan akwai wani abu da ya zama shinge da zai hana gabatar shi a wannan hali, imamanci zabin mutane tana halasta[22] hakika Malamin a yunkurinsa na tabbatar da wajabcin fifita ya jingina da dalilai masu tarin yawa daga cikinsu akwai Hadisin Annabi (S.A.W)

«یَؤُمُّ القَومَ اَفْضَلُهُم؛

Mafi falalar cikin Mutane shi ne yake jagorantar su.[23] Bakillani ya tafi kan cewa idan akwai tsoran yiwuwar afkuwar rikice-rikice da fitinntinu da kuma jinkirta Hukunce-hukuncen addini, da fatan Makiyan Muslunci kan rusa Muslunci, wannan uzuri karbabbe a zai sanya a ajiye mafi fifita a gabatar da zabin mutane a kansa[24]haka kuma a cewar Sa'adud-dini Taftazani daya daga cikin Malaman Kalam a karni na takwas galibin Ahlus-sunna sun yi Imani kan Imamancin mutumin da yake da fifita kan sauran Mutane a kowanne zamani da lokaci sai dai idan imamancinsa zai haifar da hargitsi da fitintinu[25]

Mu'utazilawa: hakika Mu'utazilawa basu tafi kan wajabcin fifitar Imami kan sauran mutane ba suna ganin halascin gabatar da mai falala ko da akwai wanda ya fifice shi falala[26] Khadi Abdul-Jabbar Mu'utazili daga cikin fitattun Malaman Kalam na Mu'utazilawa a karni na 4-5 ya tafi kan cewa akwai wurare da ake gabatar da Mai falala kan Mafi falala da cancanta sune kamar haka:

  • idan ya zama shi mafi fifitar bashi da wasu siffofin da suke sharadi cikin Imami misalin Ilimi da sanin siyasa.
  • idan shi Mafi falala din ya kasance Bawa ko kuma yana da wasu cututtuka da rashin tsayuwa cikin ra'ayi da ko rashin tsayar da haddodi shari'a da Jihadi.
  • idan ya zama shi Mafi falala da fifitar bai kasance daga Kuraishawa ba ,shi kuma wanda mutane suke so bakuraishe ne[27]

Dalilai

Hakika Ahlus-sunna sun bayyana dalilansu kan Imamanci Mai falala daga cikinsu akwai: 1.Ijma'in Malamai kan tabbatuwar Imamanci mai falala daga cikin Kuraishawa bayan Khulafa'ur Rashidin ko da kuwa akwai wanda ya fishi falala a lokacin 2.Umar Bn Khaddab ya mika Imamanci zuwa ga kwamitin Shura mai dauke da mutane shida tare da cewa a cikin wannan kwamiti akwai Ali (A.S) da Usman Bn Affan wanda sun fifita kan sauran mutane. 3.fifita wani al'amari ne a boye wanda gano shi yana da matsala kuma akwai sabani[28]

Fifitar Imami a lahira

Domin tabbatar da Imami cikin amfanuwa da ladan Lahira an kafa hujja da wasu adadin dalilai[29] daga cikinsu akwai:

  • Isma: Wajibi ne Imami ya kasance Ma'asumi. Duk wanda yake da isma to a lahira yana da fifiko kan sauran mutane[30] saboda Imami sakamakon Ismarsa zahirinsa da badininsa abu guda ne

Ta wannan fuska ne da kuma kari kan fifitarsa ta zahiri to yana da fifita a badini kuma yafi kowa amfanuwa da ladan a lahira[31]

  • Nauyayyan Taklifi da kuma lada mai yawa: hakika Imami fuskanin daukar nauyin Imamanci, taklifinsa ya fi nauyi daga na sauran mutane kuma da wannan dalili ne ladansa ya fi yawa daga na sauran mutane.[32]
  • kasancewarsa Hujja: Imami Hujja ne kamar yanda Annabi (S.A.W) yake hujjar Allah, kuma kamar lada da sakamakon Annabi (S.A.W) yafi yawa daga na mutane haka lada da sakamakon Imami yake[33]

Fifitar Imaman Shi'a

Asalin Makala: fifitar Ahlul-Baiti

Malaman Shi'a sun tafi kan cewa bayan Annabi (S.A.W) Imaman Shi'a sun kasance[34] mafi fifita da falaladaga sauran mutane tun daga sauran Annabawa da Mala'iku da sauran mutane[35] riwayoyin da suke shiryarwa kan fifikon A'imma (A.S) kan dukkanin halittu riwaya Mustafiza bari ma dai Mutawatira ce Allama Majlisi[36] ya tafi kan cewa duk wanda ya yi zurfafa bincike cikin riwayoyi babu shakka zai kai ga gano fifitar Annabi (S.A.W) da A'imma (A.S) Jahili ne kadai zai yi inkarin fifitarsu, a ra'ayinsa ba za a iya kirga hadisai da suke tabbatar da hakan ba[37] A wata riwaya daga Imam Rida (A.S) ta hanyar Mahaifinsa har zuwa Imam Ali (A.S) Annabi (S.A.W) ya ce: ya Ali kamar yanda Allah ya fifita Annabawa a kan Mala'iku Makusanta haka ya fifitani kan baki dayan Annabawa, ya Ali ! hakika fifiko a bayana ya gareka da A'imma (A.S) bayanka, Hakika Mala'iku Hadimanmu ne da Masoyanmu[38] Dangane da fifitar Imam Ali (A.S) kan sauran Sahabbai da Sauran Mutane akwai dalilai masu yawa daga Kur'ani da Riwayoyi[39] Allama Hilli cikin Kashaful Murad[40] ya kawo dalilai 25 sannan Ibn Maisam Bahrani cikin littafin Annajatu Fil Alkiyama[41] ya kawo dalili 22 kan fifitar Imam Ali (A.S) daga cikin akwai: Ayar Mubahala, Ayar Muwadda, Hadis Dairu, Hadis Manzilat, Hadis Rayat[42] An ce dukkanin Mu'utazilawan Bagdad daga cikinsu akwai Ibn Abi Alhadid wanda ya yi Sharhi kan Nahjul Al-Balaga da wasu ba'arin Mu'utazilawan Basara suma sun tafi kan cewa Imam Ali (A.S) yana da fifita kan Halifofi uku da ma sauran Sahabbai[43]

Burhan Afdaliya

Wani Burhani ne da ake amfani da shi kan tabbatar da fifitar Imam Ali (A.S) ana iya sanin wannan burhani da sharhin da zai zo a kasa:

  • mukaddima ta farko: kan Asasin dalilan Kur'ani da Riwaya Imam Ali ya kasance mafi fifita kan Sahabbai da sauran Musulmai.
  • mukaddima ta biyu: daga cikin sharuddan Imami dole ya kasance mafi fifita kan sauran mutane cikin siffofin Kamala na mutum.
  • Natija: saboda Imam Ali Ali (A.S) ya kasance Imami kuma Magajin Annabi (S.A.W)[44]

Shubuhohi

Afdaliyat az Nazare Akli

Wasu gungun Jama'a daga Ahlus-sunna sun kawo suka kan fifitar Imam, ba'arin sukansu ya kasance kamar haka:[45]

  • fifita baya lazimta gabatuwa da rinjaya: saboda zai iya yiwuwa Mafdul mutumin da aka baiwa falala a wasu wurare ya rinjaya kan Afdal mafi falala. Alal misali idan mutumin da aka baiwa falala cikin jagorantar mutane da gudanar da al'amuran addini da siyasa ya zama yafi iko daga mutumin da yake mafi falala a kansa, imamancinsa da jagorancinsa zai kasance ya rinjaya[46] cikin amsa an ce kafin mu kaddara wannan suka naku ya kamata ku sani kuna Magana ne kan fifita cikin imamanci da cewa fifita ce da ta takaitu cikin hukunce-hukunce da ayyukan ibada saboda haka wannan suka naku bai samu wuri ba, saboda mikdarin da aka sallama cikin Imami shi ne fifiko cikin Siffofin da samuwarsu cikinsa suka zama larura kuma gudanarwar siyasa tana daga cikin wadannan siffofi, haka cikin wannan suka kuna Magana ne kan fifito ta wata fuska alhali abin da aka nufa daga fifitar Imam shi ne fifita ce Mudlaka saki babu kaidi fifita a cikin dukkanin siffofi da kamala da suka zama larura[47]

Fifiko a Mahangar Hankali da nakali

  • Samfuri wanda kwata-kwata baya dacewa da Afdaliya: an ce Nazariyar fifita bata dacewa da Samfurin zamanin Annabi (S.A.W) da halifofi don ayyana Imami ko Kwamandan Yaki[48] daga cikin kwamandancin Zaidu a yakin Mutata tare da cewa ga jafar Ibn Abu Talib, haka Kwamandancin Usamatu Bn Zaidu samuwar Imam Ali (A.S)[49] a ranaku na karshen rayuwar Annabi (S.A.W) da kuma mika zabar Halifa da Umar ya yi zuwa ga Kwamitin Shura mai dauke da mutane shida tare da samuwar Ali (A.S) da kuma Usman Bn Affan[50] a cikin bada amsa kan wannan Magana da farko dai cikin zabar kwamandancin Yaki babu batun Mudlakin fifiko kadai ana la'akari da fifiko cikin abubuwan da suke da alaka da yaki kuma Usamatu da Zaidu suna da wannan fifikon

sannan dangane da Kwamandancin Usama wasu sun ce a wannan rana da aka nada shi kwamanda hakika Imam Ali (A.S) yana can wurin jinyar Annabi (S.A.W) kusa da gadon jinyarsa, kuma Annabi (S.A.W) bai yi Magana game da Shigar Imam Ali (A.S) rundunar da Usamatu yake yiwa kwamandanci ba, da wannan dalili ne babu taklifi kan Imam Ali (A.S) kan shiga Rundunar[51] sannan hujjar aikin Umar ya ginu ne kan asasin hujjar aikin Sahabbai wanda kuma `Yan Shi'a basu yarda da shi ba[52]

Bayanin kula

  1. Rabbani Golpayegani, Imamat dar Bineshi Islami, 1396, shafi na 188 da 191.
  2. Mohaghegh Hali, Al-Maslak fi Usul Al-Dini, 1414 AH, shafi na 205; Homsi Razi Al-Manqiz Min Al-Taqlid, 1412 AH, Juzu’i na 2, shafi na 286; Bahrani, Manar al-Hadi, 1405H, shafi na 121.
  3. Duba: Allameh Hilli, Kashf al-Morad, 1382, shafi na 187; Bahrani, Al-Najat fi Al-Qiyamah, 1417 AH, shafi na 66; Muzaffar, Dalai al-Saddeq, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 237 da 238.
  4. Mohaghegh Hali, Al-Maslak fi Usul Al-Din, 1414 AH, shafi na 205; Homsi Razi, Al-Munqiz Min Al-Taqlid, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 286; Bahrani, Manar al-Hadi, 1405 AH, shafi na 121 da 122.
  5. Fazel Moqdad, Ershad Al-Talebin, 1405 AH, shafi na 336; Bahrani, Al-Najat fi Al-Qiyamah, 1417 AH, shafi na 66.
  6. Muzaffar, Dala'il Al-Sidki, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 237.
  7. Muzaffar, Dala'il Al-Sidki, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 240.
  8. Duba: Mohaghegh Hilli, Al-Maslak fi Usul Al-Din, 1414 AH, shafi na 198; Allameh Hilli, Kashf Al-Morad, 1382, shafi na 187; Fazel Moqdad, Al-Lawa'am Al-Ilahiyyah, 1422 AH, shafi na 333; Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi na 121.
  9. Duba: Fazel Moqdad, Irshad Al-Talebin, 1405 AH, shafi 336; Bahrani, Manar Al-Huda, 1405 AH, shafi na 122; Muzaffar, Dala'il Al-Sidki, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 233..
  10. Duba: Mohaghegh Hilli, Al-Maslak Fi Asul Al-Din, 1414 AH, shafi na 206; Allameh Hilli, Kashf Al-Morad, 1382, shafi na 187; Fazel Moqdad, Al-Lawa'am Al-Ilahiya, 1422 AH, shafi na 333; Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi na 125
  11. Bahrani, Al-Najat fi Al-Qiyamah, 1417 AH, shafi na 65.
  12. Bahrani, Al-Najat fi Al-Qiyamah, 1417 AH, shafi na 66.
  13. Allameh Hilli, Kashf al-Morad, 1382, shafi na 187; Fazel Miqdad, Irshad Al-Talebin, 1405 AH, shafi na 336; Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi na 126.
  14. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi na 126.
  15. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi na 127.
  16. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405 AH, shafi na 126 da 127.
  17. Sadouq, Thawab Al-Amal, 1406 AH, shafi na 206; Tusi, Tahdhib al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 56.
  18. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi na 130.
  19. Ibn Hanbal, Fadael As-Sahabah, 1403 AH, juzu'i na 1, shafi na 152, 154 da 423; Abu Na'im Esfahani, Fada'il Al-Khulafa Al-Rashdin, 1417H, shafi na 39.
  20. Bahrani, Manar Al-Huda, 1405H, shafi na 129.
  21. Eji-Jorjani, Sharh al-Mawakif, 1325 A.H., juzu'i na 8, shafi na 373; Taftazani, Sharh Al-Makasid, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 246 da 247.
  22. Baghalani, Tamhid Al-Awael, 1407H, shafi na 471.
  23. Baghalani, Tamhid Al-Awael, 1407H, shafi na 474-475.
  24. Baghalani, Tamhid Al-Awael, 1407H, shafi na 475.
  25. Taftazani, Sharh Al-Maqasid, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 291.
  26. Qazi Abdul Jabbar, Al-Mughni, 1965-1962, mujalladi na 20, kashi na farko, shafi na 215; Ibn Abi Al-Hadid, Sharhin Nahj Al-Balaghah, 1404 AH, Juzu'i na 1, shafi na 3, Mujalladi na 2, shafi na 296 da Mujalladi na 3, shafi na 328.
  27. Duba: Qazi Abdul Jabbar, Al-Mughni, 1965-1962, juzu'i na 20, kashi na farko, shafi na 227-230.
  28. Taftazani, Sharh Al-Maqasid, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 247.
  29. Duba: Mohaghegh Hilli, Al-Maslak fi Usul Al-Din, 1414 AH, shafi na 205 da 206; Homsi Razi, Al-Munqiz Min al-Taqlid, 1412 AH, Juzu'i na 2, shafi na 286 da 287; Bahrani, Manar Al-Huda, 1405 AH, shafi na 122; Rabbani Golpayegani, Imamat dar Bineshi Islami, 1396, shafi na 203-208.
  30. Mohaghegh Hilli, Al-Maslak fi Usul Al-Din, 1414 AH, shafi na 205; Homsi Razi, Al-Munqiz Min Al-Taqlid, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 286.
  31. Rabbani Golpayegani, Imamat dar Bineshi Islami, 1396, shafi na 204
  32. Mohaghegh Hilli, Al-Maslak fi Usul Al-Din, 1414 AH, shafi na 205; Homsi Razi, Al-Munqiz Min Al-Taqlid, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 286; Bahrani, Manar al-Hadi, 1405H, shafi na 122.
  33. Mohaghegh Hilli, Al-Maslak fi Usulul-Din, 1414 AH, shafi na 206; Homsi Razi, Al-Munqidh Man al-Taqlid, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 287.
  34. Mohaghegh Hilli, Al-Maslak fi Usulul-Din, 1414 AH, shafi na 206; Homsi Razi, Al-Munqiz Min al-Taqlid, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 287.
  35. Duba: Sadouq, Al-Iqtiqadat, 1414 AH, shafi na 93; Mofid, Awal Al-Makalat, 1413 AH, shafi na 70 da 71; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 26, shafi na 297; Shabar,Haq Alyaqin, 1424 AH, shafi na 149
  36. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 26, shafi na 297; Sharh, Haq Al-yaqin, 1424H, shafi na 149.
  37. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 26, shafi na 297 da 298.
  38. Sadouq, Uyoun Akhbar Al-Reza (AS), 1378 H., Juzu'i na 1, shafi na 262, h. 22; Don neman bayani kan hadisai na fifikon Imamai (A.S) duba: Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 26, shafi na 267-319.
  39. Duba: Allameh Hilli, Kashf Al-Morad, 1382, shafi na 211-238; Bahrani, Al-Najat fi Al-Qiyamah, 1417 AH, shafi na 148-165; Rabbani Golpayegani, Barahin wa Nususi Imamat, 1396, shafi na 26-48.
  40. Allameh Hilli, Kashf Al-Morad, 1382, shafi na 211-238.
  41. Ibn Maitham Bahrani, Al-Najat fi Al-Qiyamah, 1417 AH, shafi na 148-165.
  42. Duba: Allameh Hali, Kashf al-Morad, 1382, shafi na 211-238; Bahrani, Al-Najat fi Al-Qiyamah, 1417 AH, shafi na 148-165; Rabbani Golpayegani,Barahin wa Nasusi Imamat, 1396, shafi na 26-48.
  43. Ibn Abi Al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 7-9.
  44. Duba: Bahrani, Al-Najat fi Al-Qiyamah, 1417 AH, shafi na 148; Rabbani Golpayegani, Barahin wa Nususi Imamat, 1396, shafi na 21.
  45. Duba: Rabbani Golpayegani, Imamat dar Bineshi Islami, 1396, shafi na 194-200.
  46. Duba: Qazi Abdul Jabbar, Al-Mughni, 1965-1962, juzu'i na 20, kashi na farko, shafi na 227-230; Eji-Jorjani, Sharh al-Mawakifi, 1325 A.H., juzu'i na 8, shafi na 373; Taftazani, Sharh Al-Maqasid, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 246 da 247.
  47. Rabbani Golpayegani, Imamat dar Bineshi Islami, 1396, shafi na 197 da 198.
  48. Rabbani Golpayegani, Imamat dar Bineshi Islami, 1396, shafi na 198.
  49. Mohaghegh Hilli, Al-Maslak fi Usul al-Din, 1414 AH, shafi na 207
  50. Taftazani, Sharh Al-Maqasid, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 247.
  51. Rabbani Golpayegani, Imamat dar Bineshi Islami, 1396, shafi na 199.
  52. Rabbani Golpayegani, Imamat dar Bineshi islami 1396, shafi na 199 da na 200.

Nassoshi

  • Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid bin Hibatullah, sharh Nahj Al-Balaghah, bincike da gyara na Muhammad Abulfazl Ibrahim, Qum, Mazhabar Ayatullah Marashi, bugu na farko, 1404H.
  • Ibn Hanbal, Ahmad Ibn Hanbal, Fadael Sahaba, bincike na Wasillah Muhammad Abbas, Beirut, Cibiyar Risala, bugun farko, 1403H.
  • Ibn Maytham Bahrani, Maytham Ibn Ali, Al-Najat fi Al-Qiyaama fi tahkiki Amril Imamati, Qum, Majmael al-Fikr al-Islami, bugu na farko, 1417H.
  • Abu Na'im Asbhani, Ahmad bin Abdullah Fadael Khulafa'ur Al-Rashidin, binciken Saleh bin Muhammad al-Aqeel, Madina, Darul Bukhari, bugun farko, 1417 Hijira.
  • Eiji, Azdad al-Din da Mirsyyed Sharif Jarjani, Sharh Almawakif, Badar al-Din Nasani ya gyara, Offset Qom, Sharif al-Razi, bugu na farko, 1325H.
  • Baghalani, Abu Bakr Muhammad bin Tayyib, Tahmhid Al-Awael fi Talkhis al-Dalael, wanda Imad al-Din Ahmad Haider, Lebanon ya yi bincike, Al-Katb al-Thaqafiyya Foundation, bugu na farko, 1987-1407 AD.
  • Bahrani, Sheikh Ali, Manar Al-Huda Fi Nass Ala Imamati A'immati Isna Ashar (AS), Abdul Zahra Khatib, Beirut, Darul Mantazhar, 1405H.
  • Taftazani, Saad al-Din, Sharh al-Maqasid, gabatarwa da bincike da dakatarwa: Abd al-Rahman Amsara, Offset Qom, Sharif al-Razi, bugu na farko, 1409 AH.
  • Homsi Razi, Sadid al-Din, Al-Munkiz Min Al-Taqlid, Qom, Al-Nashar al-Islami Foundation, bugu na farko, 1412H.
  • Rabbani Golpaygani, Ali, Imamat dar Bineshi Islami, Qum, Bostan Kitab, bugun 6, 1396.
  • Rabbani Golpaygani, Ali,Barahin wa Nususi Imamat, Qum, Raed, bugu na biyu, 1396.
  • Shabar, Sayyid Abdullah, Haq al-Iqin fi Marafah Usul al-Din, Qom, Anwar al-Hadi, bugu na biyu, 1424H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Al-Iqtaqadat, Kum, Al-Khangir al-Alami na Sheikh Al-Mufid, bugu na biyu, 1414H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Thawab al-Amal wa Aaqab al-Amal, Qom, Dar al-Sharif al-Razi, bugu na biyu, 1406H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza (a.s), bugun farko, Tehran, Nasharejahan, 1378H.
  • Tousi, Muhammad bin Hassan, Tahzeeb Al-Ahkam, Hasan Mousavi Khorsan, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya ya yi bincike, bugu na 4, 1407H.
  • Alameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Kashf al-Murad fi Sharh Tajrid al-Itqad, Tauhidi, bincike da sharhin Jafar Sobhani, Qum, Cibiyar Imam Sadiq (AS), 1382.
  • Fazil Moqdad, Moqdad bin Abdullah, Irshad al-Talbeen zuwa Nahj al-Mustarashdin, bincike na Seyyed Mehdi Rajaee, Qum, Laburaren Ayatollah Marashi, 1405H.
  • Fazil Moqdad, Moqdad bin Abdullah, Al-Wa'am al-Ilahiyyah a cikin batutuwan Al-kalamia, binciken Shahid Qazi Tabatabai, Qum, ofishin yada farfagandar Musulunci, bugu na biyu, 1422H.
  • Qazi Abd Al-Jabbar, Abd al-Jabbar bin Ahmad, al-Mughni fi Awab al-Tawheed wa al-Adl, bincike na George Qanawati, Alkahira, Masar, 1962-1965 AD.
  • Majlesi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar Al-Jama'a Ledar Akhbar al-Imam al-Athar (a.s.), Beirut, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Majlesi, Mohammad Taqi, Rawda Al-Mu'taqin fi Sharh Man Lai Hazra al-Faqih, Qom, Kushanbur Islamic Cultural Institute, bugu na biyu, 1406H.
  • Mohagheq Hilli, Jafar bin Hasan, Al-Maslak fi Usul-Din wa Rishala Al-Mata'iyyah, bincike na Reza Ostadi, Mashhad, Dandalin Binciken Musulunci, bugu na farko, 1414H.
  • Muzaffar, Mohammad Hossein, Dala'il Al-Sidki, Qum, Al-Bayt Institute, bugun farko, 1422H.
  • Mufid, Muhammad bin Muhammad,Awa'ilul Al-Makalat, fi al-mazahib wa Al-Mukhtarat, Qum, Al-Congres al-Alami na Sheikh al-Mufid, bugu na farko, 1413 AH.