Jump to content

Daƙiƙa:Suratul Zariyat

Daga wikishia
Domin ganin kammalallen nassin wannan shafi. ku duba: Nassin: Suratul Zariyat.
Suratul Zariyat
Lambar Sura51
Juzu'i26 da 27
Jerantuwa Ta Sauka67
Adadin Ayoyi60
Adadin Kalmomi360
Adadin Haruffa1546
Makkiya/MadaniyyaMakkiya


Suratul Zariyat (Larabci: سورة الذاريات) Sura ta 51 cikin Juzi'i na 26 da 27 cikin ƙur'ani mai girma, sura ce da aka saukar a Makka, kuma sunanta an ciro shi ne daga aya ta farko, wannan sura tana magana ne kan ranar Alƙiyama, da kaɗaita Allah da magana kan baƙon Ibrahim (A.S) daga cikin mala'iku, da ƙissar Musa (A.S) tana magana kan al'ummomin da suka ƙi yarda da annabawansu, kuma tana umartar Annabi (S.A.W) da ya yi haƙuri idan ya sami kanshi a cikin wahala.

Daga cikin shahararrun ayoyinta akwai wannan ayar: Kuma ban halicci mutum da aljanu ba sai don su bauta mini Akwai ruwayoyi da yawa da suka zo kan falalar karanta wannan sura, daga cikin abin da aka rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta suratul Zariyat, to Allah zai bashi lada guda goma gwargwadon yawan iskar da ts kaɗa da gudana a duniya.

Sunanta Da Ayoyinta

An sawa wannan sura wannan suna Zariyat, saboda farawa cikin ayar farko da wannan kalma faɗar Allah, (وَالذَّارِيَاتِ ذَرْوًا)[1] Azzariyat tana nufin iskar da take ɗibar ƙasa da wasu abubuwa yayin da ta kaɗa, hakan yana nufin iskar da take rarrabawa da watsar da ƙasa da abubuwa.[2] Ayoyinta 60 ne kalmominta 360 haruffanta 1546, ana la'akarinta a matsayin Mufassalat surar da take gajera amma da ayoyi da yawa.[3]

Jerantuwa Ta Sauka

Suratul Zariyat tana cikin surorin Makka[4] ne kuma a jerin sauka ita ce sura ta 67 da ga sauka gurin Annabi (S.A.W), amma yanzu lambarta a cikin ƙur'ani ita ce ta 51, cikin juzu'i na 26 da 27.[5]

Ma'anar Kalmominta

Mafi muhimmancin ma'anonin kalmomin surar

  • Kalmar (الذَّارِيَاتِ ذَرْوًا) ma'ana iskar da take ɗaukar turɓaya ta yi watsi da ita guri daban-daban.
  • Kalmar (الْحَامِلاتِ وِقْرًا) ma'ana gajimare ko gizagizai waɗanda suke ɗauke da ruwa.
  • Kalmar (الْجَارِيَاتِ يُسْرًا) tana nufin jiragen ruwa waɗanda suke tafiya cikin ruwa da sauƙi
  • Kalmar (الْمُقَسِّمَاتِ أَمْرًا) ma'ana Mala'iku waɗanda suke raba al'amarin ibada ko iskar da take rarraba ruwan sama.
  • Kalmar (ذَاتِ الْحُبُكِ) wannan kalma jam'i ce ta habika, ai abin nufi duk abin da ka iya da kyau.
  • Kalmar (الْخَرَّاصُونَ) Alkarras yana nufin kazzab, Maƙaryaci.
  • Kalmar (مُسَوَّمَةً) tana nufin ma'abociyar alama.
  • Kalmar (الْيَمِّ) tana nufin kogi

Kalmar (ذَنُوبِ) Idan aka yiwa harafin Zal wasalin fataha, tana da ma'anar wani yanki daga azaba.[6]

Abin da Yake Cikin Surar

Abubuwan da ke cikin surar sun taƙaita zuwa sassa da dama:

  1. . Tana magana kan ranar Alƙiyama
  2. . Wannan sura tana magana kan kaɗaita Allah, ayoyin kuma suna magana kan tsari wajan samar da halittu.
  3. . Tana magana kan baƙon Ibrahim daga cikin mala'iku da umarnin da aka ba su na ruguza garuruwan mutanen Annabi Luɗ (A.S)
  4. . Tana bayyana ƙissar Musa (A.S) da wasu alumma, kamar mutanen Adawa da mutanen Samud da mutanen Nuhu .
  5. . Tana magana kan fuskantar wasu al'umma da suka kangarewa annabawansu kuma tana umartar Annabi (S.A.W) da ya yi haƙuri kuma ya jajirce wajan fuskantar matsaloli da wahala.[7]

Shahararrun Ayoyinta

"Kuma ban halicci aljannu da mutane ba face domin su bauta mini."

Faɗar Allah: Kuma ban halicci mutum da aljani ba sai don su bauta mini.[8] A cikin ƙur'ani akwai magana iri-iri kan al'amarin halittar ɗan'adam da hadafin halittarshi[9] abin da ayar take nufi a nan shi ne cewa Allah bai halicci mutum da Aljan ba face dan su bauta mishi, saboda haka dalilin yin halittar mutum shi ne domin ya sami lada, wanda lada ba zai samu ba har sai mutum ya bautawa Allah, hakan ta sa kamar Allah ya halicci ɗan'adam ne domin ya bauta mishi[10] bautar Allah tana nufin ƴancin ɗan'adam daga bautar wani Allah, kamar bautar kuɗi ko matsayi da duk wani son zuciya da adalci[11] hadisi ya zo daga Imam Sadiƙ (A.S) kan wannan aya, cewar Allah ya halicce su ne domin ya ba su umarni ya kuma hane su da ɗora musu wani nauyi, amma fa ba ya haliccesu ba ne domin tilas su bauta mishi ba, a a zai jarrabe su da ba su umarni da hana su, domin ya ga wane ne zai bi shi kuma wane ne zai saɓa mishi.[12]

Falaloli Da Hususiyoyi

Akwai falaloli da yawa da suka zo kan karanta wannan sura daga cikinsu akwai:

  • An rawaito daga Annabi (S.A.W) duk wanda ya karanta suratul Zariyati, Allah zai ba shi lada goma gwargwadon iskar da ta kaɗa da gudana a duniya.[13]
  • An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk wanda ya karanta wannan sura da rana ko dare, to Allah zai gyara abin da yake buƙata na rayuwa, ya bashi arziƙi mai yawa kuma zai haskaka kabarinshi da wata fitila mai haskawa har zuwa ranar Alƙiyama.[14]

An rawaito abubuwan da suka keɓanta da wannan sura da yawa:

  • Ya zo daga Manzon Allah (S.A.W) cewa duk wanda ya rubuta wannan sura, ya wanke ya sha, to cuwan cikinshi zai gushe, idan kuma aka rubuta ta aka bawa mai ciki mai tsananin naƙuda, to za ta haihu da sauri.[15]

Bayanin kula

  1. Musawi, Al‑Wadih fi at‑Tafsir, Juzu'i na 15, Shafi na 146
  2. Alusi, Ruhul Ma'ani, Juzu'i na 27, Shafi na 5
  3. Khurmushahi, Mawsu'atul Qur'an wal‑Buhuth, Juzu'i na 2, Shafi na 1252
  4. Tusi, Tafsirut at‑Tibyan, Juzu'i na 10, Shafi na 614; Razi, At‑Tafsiru al‑Kabir, Juzu'i na 28, Shafi na 167
  5. Ma'arifat, At‑Tamhid fi Ulumil Qur'an, Juzu'i na 2, Shafi na 169
  6. Musawi, Al‑Wadih fi at‑Tafsir, Juzu'i na 15, Shafuka na 147–178
  7. Makarim Shirazi, Tafsiru al‑Amsal, Juzu'i na 17, Shafi na 44
  8. Suratul Zariyat: aya ta 56.
  9. Makarim Shirazi, Tafsiru al‑Amsal, Juzu'i na 17, Shafi na 86
  10. Tabrasi, Majma'ul Bayan, Juzu'i na 9, Shafi na 398
  11. Mughniya, Tafsiru al‑Kashif, Juzu'i na 7, Shafi na 158
  12. Huwaizi, Nurus Saqalain, Juzu'i na 7, Shafi na 147
  13. Zamakhshari, Tafsirul al‑Kashshaf, Juzu'i na 4, Shafi na 1555.
  14. Tabrasi, Jawami'ul Jami, Juzu'i na 3, Shafi na 425
  15. Bahrani, Tafsirul al‑Burhan, Juzu'i na 9, Shafi na 122

Nassoshi

  • Alusi, Mahmudu bn Abdullahi, Ruhul Ma'ani fi Tafsiril Qur'ani al‑Azim was‑Sab'il Mathani, Bayrut – Lebanon, Gidan Rayar da Gadon Al'adun Larabawa, Bugu na 1, 1421 H.
  • Al‑Kur'anil Kareem
  • Bahrani, Hashimu bn Sulaiman, Al‑Burhan fi Tafsiril Qur'an, Bayrut – Lebanon, Gidan Raya gadon Larabci, Bugu na 1, 1429 H.
  • Huwaizi, Abdu Ali bn Jum'a, Tafsirul Nuris Saqalain, Bayrut – Lebanon,Gidauniyar Tarihin Larabawa, Bugu na 1, ba a sa shekara ba.
  • Khurmu‑shahi, Baha'uddin, Mawsu'atul Qur'an wad‑Dirasat al‑Qur'aniyya, Iran – Tehran, Cibiyar al‑Asdiqa', 1377 Sh.
  • Makarim Shirazi, Nasiru, At‑Amthal fi Tafsiri Kitabillahil Munazzal, Bayrut – Lebanon, Gidauniyar al‑Amira, Bugu na 2, 1430 H.
  • Ma'arifa, Muhammadu Hadi, At‑Tamhid fi Ulumil Qur'an, Qum – Iran, Mawallafar Dhawi al‑Qurba, Bugu na 1, 1428 H.
  • Musawi, Abbasu bn Ali, Al‑Wadih fi at‑Tafsir, Bayrut – Lebanon, Cibiyar Ghadir, Bugu na 1, 1433 H.
  • Razi, Muhammadu bn Umar, At‑Tafsiru al‑Kabir, Bayrut – Lebanon, Gidan Littattafai na Kimiyya, Bugu na 4, 1434 H.
  • Tabrasi, Al‑Fadlu bn Hassan, Majma'ul Bayan, Tehran – Iran, Gidan Uswa, Bugu na 1, 1426 H.
  • Tabrasi, Fadlu bn Hassan, Tafsirul Jawami'ul Jami, Qum – Iran, Gidauniyar Yada Littattafan Musulunci ta Ƙungiyar Malaman Makarantun Addini, Bugu na 2, 1430 H.
  • Tusi, Muhammadu bn Hassan, At‑Tibyan fi Tafsiril Qur'an, Qum – Iran, Gidauniyar Yada Littattafan Musulunci, Bugu na 1, 1431 H.
  • Zamakhshari, Mahmudu ɗan Umar, Al‑Kashshaf, Bayrut – Lebanon, Gidan Bugawa na Gidan Sader, Bugu na 1, 1431 H.
  • Mughniya, Muhammadu Jawad, Tafsirul al‑Kashif, Bayrut – Lebanon, Gidan Anwar, Bugu na 4, ba a sa shekara ba.