Jump to content

Daƙiƙa:Sayyid Ali Husaini Sistani

Daga wikishia
Sayyid Ali Sistani
Marja'in Taƙlidi
Cikakken SunaSayyid Ali Husaini Sistani
Tarihin haihuwa4 Agusta 1930M (9 Rabi'ul AwwalH)
Wurin rayuwaNajaf
Fitattun dangiMuhammad Rida da Muhammad Baƙir (Ƴaƴa) Sayyid Jawad Shahristani (Siriki)
MalamaiSayyid Muhammad Hujjat KuhekamariSayyid Husaini BurujerdiSayyid Abul Ƙasim KhuyiShaik Husaini Hilli
Izinin Ijtihadi dagaSayyid Abul Ƙasim KhuyiHusaini Hilli
ZamantakewaMarja'in Taƙlidi Na Shi'a
Shafin yanar gizo mai lasisihttp://sistani.org


Sayyid Ali Husaini Sistani, (Larabci: السيد علي السيستاني) haihuwa:1930 miladiyya, ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a a ƙarmi na sha biyar hijira ƙamari. Daga cikin muhimman ayyukansa akwai kare tabbatar da wanzuwar haurzar ilimi ta Najaf (Makarantun addini na Najaf) a lokacin gwamnatin jam'iyyar ba'as, kare haɗin kan ƙabilu daban-daban na Iraƙ bayan faɗuwar gwamnatin Saddam Husaini da kuma taka muhimmiyar rawa cikin tsara dokokin kundin mulki na ƙasar Iraƙ.

Sistani ya fara karatun addini a shekarar 1940-1941M a garin Mashad. Bayan nan ya shiga darasussukan kharijul fiƙihu a birnin na manya-manyan malamai kamar Sayyid Husaini Ɗabaɗaba'i Burujerdi da Sayyid Muhammad Hujjat Kuhekamari, bayan nan a shekarar 1951M sai ya tafi birnin Najaf. Ya samu izinin Ijtihadi daga Sayyid Abul Ƙasim Khuyi da Husaini Hilli tun yana ɗan shekara 31. Sistani ya fara bayar da darasin kharijul fiƙihu a shekarar 1961M, bayan rasuwar Ayatullahi Khuyi a shekarar 1992M, tare da shawara da nasihar malaman Najaf, bayan wani lokaci ya zama babban marja'in duniyar Shi'a, masu taƙlidi da shi sun faɗaɗa sosai tun daga Iraƙ, Iran har zuwa Indiya, Fakistan da Amurka.

An ce bayan faɗuwar gwamnatin Saddam Husaini, Sayyid Sistani tare da ƙarfafa aƙidar kishin ƙasar Iraƙ, kare haɗin kai tsakanin Shi'a da Ahlus-Sunna, tabbatar da shigar dukkanin ɓangarorin ƴanƙasa cikin gwamnati, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa sabuwar gwamnatin Iraƙ. Haƙiƙa goyan bayan tsarin dimokraɗiyya, adawa da mamayar turawan yamma, fitar da fatawar jihadi domin kare Iraƙ daga hatsarin ƴanta'addan ISIS da kuma ganawa ta tarihi da ya yi tare da Fafaroma Faransis, suna daga cikin fitattu sanannun ayyukansa.

Ofishinsa yana tsarawa da kula da cibiyar sadarwa ta hukumomi na ilimi, al'ada da bincike da ayyukan jin ƙai a ƙasashe daban-daban daga ciki har da Iran, Iraƙ, Turkiyya, Birtaniya. Haka nan Sistani yana da aikace-aikace da rubuce-rubuce a fagagen fiƙihu, usul, hadisi da rijal (Ilimin sanin mazajen riwaya)

Gabatarwa, Tarihin Rayuwa Da Matsayi

An haifi Sayyid Ali Husaini Sistani a birnin Mashad Iran a ranar 9 Rabi'ul Awwal shekarar 1349H wanda ya yi daidai da 14 Agusta 1930M. Mahaifinsa Sayyid Muhammad Baƙir ya kasance daga sanannun malaman Shi'a, mahaifiyarsa ta kasance ƴa ga Sayyid Rida Mehrabani Sarabi.[1] Kakansa Sayyid Ali Sistani, ya kasance cikin almajiran Mirzaye Shirazi a birnin Najaf wanda a shekarar 1900 bayan kammala karatu sai ya dawo birnin Mashad ya karɓi ragamar marja'iyyar al'amuran addini.[2]

An ce Sayyid Ali Sistani ya samu shahara sakamakon irin matakan da ya dinga ɗauka cikin kare wanzuwar hauzar ilimi ta Najaf a zamanin Saddam Husaini.[3] Bayan Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, da kuma matakansa na siyasa bayan faɗuwar Saddam da wayar da kan mutane cikin fagen siyasa game da abubuwan da suka dinga faruwa a Iraƙ a wancan lokacin, ta yadda wannan matakai nasa suka ba da babbar gudummawa wajen kare haɗin kai tsakanin ƙabilu daban-daban na Iraƙ,[4] ana la'akari da hakan matsayin muhimmiyar rawa wajen gina asalin ƙasa[5] da kuma tasiri wajen rubuta sabon tsarin kundin tsarin mulki.[6]

Karatu

Sayyid Ali Sistani ya fara karatun hauza a shekarar 1941 a birnin Mashad. Ya yi karatun share fage da matakai na sama a wurin malamai kamar Muhammad Taƙiyyu Adib Naishabur, Sayyid Ahmad Mudarris Yazdi, Mirza Hashim Ƙazwini, sannan ya yi karatun Falsafa a wurin Mujtaba Ƙazwini. Haka nan, ya halarci darasussukan Mirza Mahadi Isfahani da Mirza Mahadi Ashtiyani. A shekarar 1949M, ya dawo garin Ƙum, ya halarci darasin kharij na Sayyid Husaini Ɗabaɗaba'i Burujerdi da Sayyid Muhammad Hujjat Kuhekamari.[7]

Shaidar ijtihadi da Shaik Husaini Hilli ya bai wa Ayatullahi Sistani
Shaidar ijtihadi da Ayatullahi Khuyi ya bai wa Ayatullahi Sistani

Hijira Zuwa Najaf

Sistani a shekarar 1951M ya yi hijira zuwa Najaf inda ya zauna a makarantar Bukharayi, a lokacin zamansa a Najaf ya halarci darasul kharij na Sayyid Abul Ƙasim Khuyi da Husaini Hilli, haka kuma ya amfana daga darusussukan Sayyid Muhsin Ɗabaɗaba'i Hakim da [[Sayyid Mahmud Husaini Shahrudi][8]

Koyarwa Da Kuma Almajiransa

Ya fara darasul kharij a shekarar 1962 ya kuma ci gaba har zuwa 1991M. Daga mutanen da suka yi karatu a wurinsa akwai:

  1. .Sayyid Muhammad Rida Sistani
  2. .Sayyid Muhammad Baƙir Sistani
  3. .Sayyid Murtada Mihri
  4. .Sayyid Muhammad Ali Rabbani
  5. .Sayyid Hashim Hashimi
  6. .Sayyid Munir Sayyid Adnan Al-Ƙaɗifi
  7. .Shaik Mahadi Marwarid
  8. .Sayyid Ahmad Madadi
  9. .Shaik Musɗafa Harandi[9]

Ijtihadi

Sayyid Ali Sistani a cikin shekarar 1961M ya samu shaidar ijtihadi daga Sayyid Abul Ƙasim Khuyi da Husaini Hilli. Shi ne kaɗai mutumin da ya taɓa samun shaida da izinin ijtihadi daga wurin Husaini Hilli.[10] Agha Buzurg Tehrani shima ya rubuta cewa a shekarar 1961M, Sistani ya tababtarwa da duniya irin nutson da ya yi cikin ilimin rijal da hadisi[11]

Sallar jana'izar da Sayyid Ali Sistani ya yi kan jana'aizar Sayyid Abul Ƙasim Khuyi

Marja'iyya

Bisa abin da aka yaɗa a shafin yanar gizo na ofishin Sayyid Ali Sistani, haƙiƙa bayan rasuwar Sayyid Abul Ƙasim Khuyi a shekarar 1992M, wasu jama'a daga malaman Najaf ciki har da Sayyid Ali Baheshti da Murtada Burujerdi, sun bawa mutane shawara da su yi taƙlidi da Sayyid Sistani, haƙiƙa wannan nasiha da shawara ta samu karɓuwa a wurin mutanen Iraƙ, Iran, Indiya, Fakistan da ƙasashen jazirar Larabawa, taƙlidi da Sistani ya ƙara bazuwa da karɓuwa bayan rasuwar Sayyid Abdul-A'ala Sabzawari (1993H) Muhammad Ali Araki da Sayyid Muhammad Ruhani, haka nan taƙlidi da Sistani ya yaɗu har zuwa al'ummun Shi'a da suke rayuwa a ƙasashen Turai da Amurka.[12]

Sistani bayan rashin lafiyar Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, babban marja'in taƙlidi na Shi'a a shekarar 1988M, ya karɓi ramagar limancin masallacin Khadrayi Najaf har zuwa shekarar 1993, bayan rasuwar Ayatullahi Khuyi shi ne wanda ya yi masa sallar jana'iza, an ce haka wata alama ce da take nuna shi ne zai gaji Khuyi.[13]

Siffofi Na Ilimi

Sayyid Jawad Shahristani sirikin Sayyid Ali Sistani, ya bayyana Sistani matsayin ƙwararre masanin fiƙihu wanda ta fuskacin nazari da binciken ilimi babu kwatankwacinsa a cikin maraji'ai.[14]Sayyid Munir Khabbaz ɗaya daga cikin almajiran Sistani shima ya yi bayanin siffofi na koyarwarsa kamar haka:

  • Gauraya tsakanin tsarin koyarwar makarantu uku mabambanta da juna ma'ana hauzar Mashad, Ƙum da Najaf
  • Samun ƙwarewa kan litattafan fiƙihu da hadisi da sauran mazhabobin Musulunci da amfana da su cikin ƙoƙarin fahimtar riwayoyin Ahlul-Baiti (A.S),
  • Amfani da ra'aoyin da suka yaɗu cikin ilimomin da ba na hauza domin ƙara zurfafawa cikin ilimomin hauza.[15]

Sayyid Ali Sistani, a fagagen fiƙihu, usulul fiƙhi da hadisi da rijal ya yi wallafe-wallafe masu yawa. Haka nan, almajiransa sun rubuta takardu (Taƙrirori) na darasussukansa wanda aka sanya cikin shafin yanar gizo na taƙrirat

Tubalan Tunani Da Ra'ayoyin Siyasa

Tsarin siyasa da zamantakewa na Sistani ya kasance tsakatsaki tsakanin tsarin Sayyid Abul Ƙasim Khuyi a gefe guda da kuma Imam Khomaini da Sayyid Muhammad Baƙir Sadar a gefe guda, da wannan bayani na cewa duk da kasancewar bai yarda da ra'ayin cewa malamin fiƙihu yana da rawar kai tsaye wajen kafa gwamnati, kuma Sistani ya kasance yana rinjayar da gwamnatin farar hula maimakon gwamnatin addini, sai dai kuma tare da hakan bai yarda janye jikin malaman fiƙihu ba daga al'amuran siyasa ba, yana da ra'ayin cewa ya kamata malaman addini su zama masu ba da shawara da sa idanu kan al'amuran hukuma.[16] Abdul-Wahab Furati, masanin fiƙihun siyasa, yana ganin tafiyar siyasa ta Sistani ta samo asali ne daga komawa zuwa tunanin Mirzayi Na'ini wanda ya kasance kan goyan bayan yarjejeniya farar hula tsakanin mutane da shugaba ƙarƙashin tsarin dimoƙraɗiyya.[17]

Rashin Amincewa Da Baiwa Malamin Fiƙihu Cikakken Iko

Sistani bai amince da ra'ayin bai wa malamin fiƙihu cikakken iko da mafi yawan malamai suka bijiro da shi ba. A ra'ayin Sistani malamin fiƙihu ba hi da wani iko da wilaya kan al'amuran da suke da alaƙa da hukuma,[18] Tare da haka, rashin amincewarsa da wilayatu faƙihi (Ikon malamin fiƙihu) kan al'amura na gaba ɗaya, baya nufin kore ikon malaman fiƙihu kan al'amura kamar al'amuran hisba da alƙalanci, saboda yana ganin jan ragamar waɗannan al'amura ga malamin fiƙihu kamar yadda ya zo a riwaya abu ne da yake wajibi.[19]

Ƴancin Mutane Cikin Yanke Hukunci A Wurin Da Babu Nassi Na Shari'a

A ra'ayin Sistani, a wurin da hukuncin shari'a bai zo ba, wajen da ake kira da wuraren hukunce-hukunce da ba na shari'a ba ko manɗiƙatul farag, mutane su ne masu yanke shawara, waɗannan wurare ba sa ƙarƙashin ikon malamin fiƙihu.[20] ya ƙara da cewa wannan wurare wani babban ɓangare ne na filin rayuwar jama'a, inda aka amince da haƙƙoƙi jama'a, kuma suna da ƴanci yin dokoki da sharaɗin cewa ka da dokokin su saɓa da shari'a, a wannan yankin babu wani mutum da yake da haƙƙi da ikon wilaya kan wani mutum, kaɗai su mutane ne suke da damar miƙa wannan wilaya da iko nasu zuwa ga wani wasu mutane.[21]

Gwamnati Da Take Ƙarƙashin Yardar Jama'a

A cewar Abdul-Wahab Furati, Sayyid Sistani bisa tubalan tunaninsa, kaɗai yana amincewa da kuma goyan bayan gwamnati da take tafiya kan tsarin dimoƙraɗiyya da mafi yawan mutane suka yarda da ita.[22] Abin da yake nufi da mafi yawan mutane bashi mafi yawa da ma'anar ƙungiyoyi ko wasu ayyanannun mutane ba, na'am mafi yawa da ma'anar mafi yawan mutane ƴanƙasar Iraƙ da suka shiga zaɓe suka kaɗa ƙuri'arsu. An ce sakamakon wannan tunani shi ne bayyanar ƙarfi da bunƙasar al'umma farar hula a Iraƙ, kuma idan aka tabbatar da wannan tsari kuma ya zama na dindin to da yawa-yawan neman a bani kasona daga iko da moriyar siyasa da ƙungiyoyin siyasa suka saba yi zai yi matuƙar raguwa.[23] Kan wannan tushe ne ake cewa dokokin kundin mulki wajibi ne su kasance ƙarƙashin amincewar al'ummar Iraƙ, sakamakon kasancewar Musulmi sune mafi rinjaye to dole ne ya zamana waɗannan dokoki ba su saɓa da ma'aunan addinin Musulunci ba.[24]

Kare Haɗin Kai Tare Da Jadda Riƙo Da Kishin Ƙasa

A cewa masu bincike, Sayyid Ali Sistani domin taƙaita rigingimun siyasa, ƙabila da addini, cikin sanarwarsa da bayanansa ya kasance yana jaddada faɗin: ita Iraƙ ta dukkanin Iraƙawa ce, ba ta keɓantu da wata ƙungiya ko wata mazhaba ba, duk da kasancewarsa malamin fiƙihu mabiyin tafarkin shi'anci, bai taɓa ɗaukar matsaya da take nuna fifiko ko rinjayar da Shi'a ba. Ba ya halatta cin zarafi ko kai hari ga sauran mutanen Iraƙ da ba Shi'a ba, ya kasance yana jaddada riƙo da hanyar ruwan sanyi cikin warware rigingimu da rikice-rikice.[25] Irin wannan matsaya ta Sistani, ana ɗaukar ta matsayi mafi kusa da dimoƙraɗiyyar ta ƙungiyoyi wace da turanci ake kira da (Consociational) wace kan tushenta wajibi ne gaba ɗayan ƙabilu da mazhabobin Iraƙ su kasance suna da hannu cikin kafa gwamnati, kuma suna da haƙƙi su kasance masu cin gashin kansu a cikin al'amuransu, sannan a ƙarshe ana sa ran su kasance masu biyayya da goyon baya wajen kare sabon tsarin hukumar Iraƙ.[26]

Salon Da Ake Bi Wajen Tafiyar Da Al'amuran Siyasa Da Zamantakewa

An ƙimanta salo da tsarin siyasa da zamantakewa na Sayyid Sistani musamman bayan faɗuwar Saddam, a matsayin aiki da ya yi daidai da tubalin tunaninsa, wanda ya taimaka sosai ciki haifar da kare haɗin kan Iraƙi, samar da tsarin siyasa na zamani, adawa da mamayar Turawa, da kuma hana rarrabuwar Iraƙ ta hannun ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.[27]

Ayatullahi Sistani:
Ƙoƙarin Kare Haɗin Kan Shi'a da Ahlus-Sunna A lokuta da daman gaske na faɗa kuma yanzu ma zan sake maimaitawa, ka da ku ce Ahlus-Sunna ƴan uwanmu ne, a a su suna matsayun rayukanmu.[28]

  • Ƙoƙarin Kare Haɗin Kan Shi'a da Ahlus-Sunna

Sayyid Sistani tare da jaddada magana kan haɗin kai na tsakanin yawancin addinan Iraƙ, ya haramta kai hari kan rayuka, dukiya, mutunci da aƙidun Musulmi (Daga Ahlus-Sunna da Shi'a) da wannan dalili ya yi fatawar haramta tsinuwa kan wasu Sahabbai.[29] Cikin batun abin da ya faru a shekarar 2007M, Sistani ya jaddada kiyaye haɗin kan Musulunci da kiyaye daidaito cikin haƙƙoƙi ga baki ɗayan al'ummar Iraƙi, ya kuma kira Shi'a su kasance a sahun gaba cikin kare haƙƙoƙin Ahlus-Sunna.[30]

Shiga Cikin Sauya Tsarin Mulki Da Dokoki

Bayan hare-haren da sojojin Amurka suka ƙaddamar kan Iraƙ wanda ya janyo faɗuwar gwamnatin Saddam Husaini, Sistani cikin adawa da kuma nuna ƙin amincewa da shawarar Amurka cikin tsara dokokin kundin mulkin sabuwar gwamnatin Iraƙi, ya bayyana cewa al'umma Iraƙi kaɗai suke da wannan haƙƙi, kuma yana da ra'ayin cewa dole ne membobin kwamitin tsara sabon kundin mulki su kasance ta hanyar zaɓe.[31]

Fatawar Jihadi Kan ISIS

Sistani bayan faɗuwar birnin Mosul na Iraƙi da kuma ci gaban mamayar ƴanta'addan ISIS zuwa biranen tsakiyar Iraƙ, ya yi kira da cewa kare ƙasa, al'ummar ƙasa da wurare masu tsarki a yanzu yana matsayin wajibi kifa'i, ya kuma buƙaci Iraƙawa da suke da ikon ɗaukar makami da tunkarar ƴanta'adda da su gaggauta shiga cikin dakarun tsaron ƙasa.[32] Wannan kira na Sistani ya fito ta hannun Abdul-Mahadi Karbala'i babban limamin juma'a na birnin Karbala, duk da cewa wannan kira bai kasance fatawa ba,[33] amma bisa nazari an bayyana cewa yana ɗauke da tasiri irin na fatawa, kuma ya zama dalili da ya sanya da yawa-yawan Iraƙawa shiga ayarin yaƙar ƴanta'addan ISIS.[34]

  • Ganawa Da Fafaroma Firansis

Fafaroma Firansis shugaba majami'un Katolika a ranar 6 ga watan Maris 2021M, cikin ziyara da ya kai Iraƙi ya gana tare da Sayyid Ali Sistani a gidansa da yake a birnin Najaf. Cikin wannan ganawa sun tattauna game da muhimman batutuwa da suke damun wannan yanki an gabas ta tsakiya, ciki har da yaƙe-yaƙe, talauci, tauyen ƴancin mutane, takunkumi na zalunci, da raba al'ummar Falasɗinu da matsugunansu.[35]

Cibiyoyin Da Suke Ƙarƙashin Ofishinsa

Ofishin Sayyid Ali Sistani ya kafa wata cibiyar sadarwa ta cibiyoyin ilimi, al'adu, bincike da ayyukan jin ƙai a ƙasashe daban-daban ciki har da Iran, Iraƙ, Turkiyya da Birtaniya, da cikin waɗannan cibiyoyi za a iya nuni da cibiyar Imam Ali (A.S) da take a birnin Ƙum, cibiyar al'adu ta Alul Baiti (A.S) a Istanbul, Markaz Almostafa ta binciken Muslunci, Markaz ta bincike na aƙida a Ƙum, Markaze Ihya'u Miras Islami, Markaz ta bincke Falaki da ɗakunan karatu na musamman.[36]

Bayanin kula

  1. "Zindigi-nama..." , sayt-i rasmi-yi daftar-i Ayatullah SistAni.
  2. AqA Buzurg-i TehrAni, TabaqAt-u A'lAm-ish-Shi'a, 1430q, j16, s1435.
  3. Fathi, "Faqihi barA-yi hama-yi a'sAr", sayt-i Din-AnlAyn
  4. KAzimi, "RaftAr-i siyAsi-yi Ayatullah Sistani (bA ta'kid bar vahdat va nafy-ish-ightirAlgi)", s76-79.
  5. NigahbAn va hamkarAn, "Rahburd-hA-yi siyAsi-yi Ayatullah Sistani jihat-i takvin-i huviyat va dawlat-i milli dar Iraq", s124-134.
  6. AhmadiyAn, "DidgAh-hA va mavAzi'-i Ayatullah Sistani dar ravand-i tadvin-i qAnun-i asAsi-yi Iraq-i navin", s123-125.
  7. "Zindigi-nama..." , sayt-i rasmi-yi daftar-i Ayatullah SistAni.
  8. "Zindigi-nama..." , sayt-i rasmi-yi daftar-i Ayatullah SistAni.
  9. "Zindigi-nama..." , sayt-i rasmi-yi daftar-i Ayatullah SistAni.
  10. "Zindigi-nama..." , sayt-i rasmi-yi daftar-i Ayatullah SistAni.
  11. "Zindigi-nama..." , sayt-i rasmi-yi daftar-i Ayatullah SistAni.
  12. "Zindigi-nama..." , sayt-i rasmi-yi daftar-i Ayatullah SistAni.
  13. "Zindigi-nama..." , sayt-i rasmi-yi daftar-i Ayatullah SistAni.
  14. ShahristAni, "Sabk-i zindigi-yi hazrat-i Ayatullah SistAni", sayt-i Hawza.
  15. KhabbAz, "Vizhigi-hA-yi shakhsiyAti va sira-yi siyAsi-yi Ayatullah SistAni", sayt-i Shi'a-Nyuz.
  16. Hakim, an-Najaf wa HawzatuhA (al-kitAb al-khAmis), 2018m, s157-179; Haji-Yusufi va Arif-Nizhad, "Nishana-shinAsi-yi guftimAn dar IslAm-i siyAsi va mardum-sAlAr-i Ayatullah SistAni", s58-63.
  17. Farati, "Ayatullah Sistani va nazariyya-yi irAdat-il-umma", s86-87
  18. Husayni SistAni, al-IjtihAd wat-Taqlid wal-IhtiyAt, 1437q, s105-128.
  19. Husayni SistAni, al-IjtihAd wat-Taqlid wal-IhtiyAt, 1437q, s86.
  20. Husayni SistAni, al-IjtihAd wat-Taqlid wal-IhtiyAt, 1437q, s 86.
  21. Hakim, an-Najaf wa HawzAtuhA (al-kitab al-khamis), 2018m, s159.
  22. Farati, "Ayatullah Sistani va nazariyya-yi irAdat-il-umma", s88-89.
  23. Khaffaf, an-Nusus-us-sAdira 'an samAhat-is-Sayyid is-Sistani fil-mas'alat-il-'Iraqiyya, 2007m, s13, 28, 31, 142.
  24. Ahmadiyan, "Didgah-ha va mavazi'-i Ayatullah Sistani dar ravand-i tadvin-i qanun-i asasi-yi Iraq-i navin", s123-125.
  25. RabbAni va hamkaran, "Naaqsh-i Ayatullah Sistani dar mahar-i munazi'a miyAn-i Shi'iyan va Sunni-ha-yi Iraq-i pas az 2003m", s273-274.
  26. Farati, "Ayatullah Sistani va nazariyya-yi irAdat-il-umma", s89-90.
  27. Nigahban va hamkarAn, "Rahburd-hA-yi siyAsi-yi Ayatullah Sistani jihat-i takvin-i huviyat va dawlat-i milli dar Iraq", s134-135.
  28. «Sunnis not only our brethren, but our souls: Ayatollah Sistani»، Kamfanin dillancin labarai na Mehr.
  29. RabbAni va hamkarAn, "Naaqsh-i Ayatullah Sistani dar mahAr-i munAzi'a miyAn-i Shi'iyan va Sunni-hA-yi Iraq-i pas az 2003m", s275-276.
  30. RabbAni va hamkarAn, "Naaqsh-i Ayatullah Sistani dar mahAr-i munAzi'a miyan-i Shi'iyan va Sunni-hA-yi Iraq-i pas az 2003m", s275-276.
  31. Khaffaf, an-Nusus-us-sAdira 'an samAhat-is-Sayyid is-Sistani fil-mas'alat-il-'Iraqiyya, 2007m, s18-19.
  32. HattAb, "Tavzif-ul-Hashd-ish-Sha'bi fil-mudrak-is-siyAsil-'Iraqi", s108; "Naqsh-i fatvA-yi jihAdi-yi Ayatullah Sistani dar jilugiri az tajziya-yi Iraq", KhabarguzAri-yi Mihr.
  33. Ma'muri, "Naqsh-i Ayatullah Sistani dar afzayish-i mas'uliyyat-i akhlAqi dar jang bA DA'ish", sayt-i Bi-Bi-Si.
  34. "Ayatullah Sistani fatvA-yi jihad sAdir kard", KhabarguzAri-yi Hawza.
  35. "BayAniyya-yi daftar-i AyatullAh-il-'UzmA Sistani az didAr-i PAp", KhabarguzAri-yi irnA.
  36. "Markaz va mu'assasAt", sayt-i daftar-i Ayatullah SistAni."

Nassoshi