Jump to content

Daƙiƙa:Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya

Daga wikishia
Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya
Tambarin Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya
Tambarin Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya
KafawaShekarar 1990-1991M
Waɗanda suka kafaSayyid Ali Khamna'i
SaloKusanto da mazhabobin Musulunci da yaɗa fahimtar makarantar Ahlul-Baiti
Nau'in ayyukaKoyarwa, bincike da tabligi
Faɗaduwar aikiƘasa da ƙasa
ManufofiBayanin Musulunci, yaɗa ilimin Kur'ani da Ahlul-Baiti (A.S), kusanto da mazhabobin Musulunci da kare mabiya Ahlul-Baiti a Duniya
Babban sakatareRida Ramadani Gilani
HaliTana Aiki
Cibiyoyin da suke ƙasantaKamfanin Dillancin Labarai Na Ahlul-Baiti (A.S)Kundin Bayanai Na Yanar Gizo Na Makarantan Ahlul-Baiti (Wikishi'a)
Adireshin yanar gizohttp://www.ahl-ul-bayt.org


Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya ko Majma Ahlul-Baiti Jahani, wata majalisa ce mai zaman kanta (ba ta gwamnati ba) wadda aka kafa domin bayanin Musulunci, yaɗa ilimin Kur'ani da koyarwar Ahlul-Baiti (A.S), ƙarfafa haɗin kan Musulmi, da kuma tallafa wa mabiyan Ahlul-baiti a duniya. Wannan ƙungiya tana gudanar da ayyuka daban-daban domin cimma waɗannan manufofi. An kafa wannan ƙungiya a shekara ta 1990 Miladiyya (1369 Shamsi) tare da goyon bayan Sayyid Ali Khamna'i, jagoran jamhuriyar Musulunci Ta Iran. Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ke naɗa babban sakataren wannan majami'a. A halin yanzu, Rida Ramadani Gilani shi ne babban sakataren wannan majalisa

Tarihi, Manufofi da Tsari

Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya (Majma Jahani Ahlul-baiti) an kafa ta a ranar 10 ga watan De hijira shamsi 1369sh, (1 ga Janairu 1991 miladiyya).[1] Kafin kafa ta, fiye da mutane 300 daga cikin malamai Musulmi musamman mabiyan Ahlulbait ne suka halarci wani taro a Tehran. Bayan wannan taro suka nemi izini da amincewa daga Sayyid Ali Khamna'i, Jagoran jamhuriyar Musulunci ta Iran, domin kafa wannan majalisar Ahlul-baiti ta Duniya.[2]

Wasu daga cikin manufofin da aka bayyana na kafa wannan majalisa su ne:

  1. .Kare mutunci da tsaron Islam, da martabar Annabi, Kur'ani, da Ahlulbait.
  2. .Ƙarfafa haɗin kai tsakanin al'ummar Musulmi, musamman tsakanin mabiyan Ahlul-baiti (A,S)
  3. .Tallafawa da kare haƙƙoƙin Musulmi a duniya da kuma matsayin mabiyan Ahlul-baiti (A.S).
  4. .Haɓaka ginshiƙan tallafi na zahiri da na ruhi ga mabiyan Ahlul-baiti a duk faɗin Duniya.
  5. .Fitar da mabiyan Ahlul-baiti (A.S) daga zaluncin kafofin watsa labarai da kuma rashin damar ilimi da tattalin arziki.
  6. .Ƙoƙari wajen samar da zaman lafiya, abota, haɗin gwiwa da taimakon juna tsakanin dukkan mutane da al'ummomin Duniya.[3]

Babban mukami na gudanarwa a wannan majami'a shi ne Babban Sakatare, wanda shi ne mafi girman jami'in gudanarwa. Ana naɗa shi ne domin gudanar da majalisar Ahlul-baiti ta Duniya da aiwatar da manufofinta da umarnin Waliyul Faƙihi.[4] Zuwa yanzu an zaɓi mutane biyar a matsayin manyan sakatarorin wannan majalisa:

Ayyuka

  • Tashar Assaƙlaini: wata tashar talabijin ta tauraron ɗan-adam da ke watsa shirye-shirye da harshen Larabci da Turanci. An yi rajistar wannan tashar a ƙasar Holan, yayin da ofishinta na tsakiya yake a Turkiyya. Daga cikin manufofin wannan tashar shi ne samar da shirye-shirye da abubuwa na ilimi na Musulunci ga sassa daban-daban na al'umma. An kafa tashar a shekara ta 1388 shamsi (2009 miladiyya).
An gudanar da Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Imam Sajjad (A.S) a ranar 15 Agusta 2015 Miladiyya, tare da halartar baƙi sama da 500 daga ƙasashen waje, a Babban Zauren Taron Shugabanni.
  • Taron ilimi da nune-nunen al'adu: Domin yaɗa da kuma bunƙasa al'adun Ahlul-baiti (A.S), da kuma samar da damar halartar masana na duniyar Musulunci a muhawarorin tunani da na aƙida, ana shirya taruka da zaman tattaunawa iri-iri na ƙasa da ƙasa, na yankuna da kuma na duniya. Daga cikinsu akwai:
  • Taron ƙasa da ƙasa na Imam Hassan Mujtaba (A.S): Wani babban taro ne da aka shirya domin ƙarfafa da kuma faɗaɗa kulawa da bin tsari da salon rayuwar Ahlul-baiti (A.S). Haka kuma yana nufin samar da yanayi mai dacewa domin fahimtar asalin addini bisa mahangar Ahlul-baiti (A.S), gabatar da cikakken bayani game da halayen da martabar Imam Hassan Mujtaba (A.S), da kuma bayyana ra'ayin sulhu da dabarun shawo kan rikici a tunanin Imam Hassan (A.S)
  • Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Nasir Kabir,
  • Babban lambar yabo ga Annabi mafi girma Muhammad (S.A.W): Wani babban biki ne na al'adu da fasaha na Ahlul-baiti (A.S) da aka assasa shi domin amfani da hanyoyin fasaha wajen kare addini da kuma yaɗa saƙonnin Musulunci. Zagaye na farko na wannan biki, mai taken Babbar Kyautar Annabi Mai Girma, wanda jigonsa shi ne Annabin rahama da adalci, wato Muhammad, an gudanar da shi a shekarun 2013–2014M.[7]
  • Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Zanen Barkwanci Na Ranar Ƙudus Ta Duniya: A cikin watan Ramadan na shekarar 1435 Hijira (2014M) an gudanar da zagaye na farko na wannan biki na ƙasa da ƙasa na zane-zanen barkwanci na Ranar Ƙudus Ta Duniya, da taken Ranar Ƙudus , ranar haɗin kai da gwagwarmayar al'ummar Musulmi.[8]
  • Babban taro na ƙasa da ƙasa na kimiyya game da tsarin rayuwar Ahlul-baiti: Wani taron ilimi da bincike ne da aka shirya domin nazari da gabatar da salon rayuwar Ahlulbaiti (A.S)Taron Ƙasa da Ƙasa kan Imam Sajjad (A.S.) a matsayin abin koyi ga al'umma, Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Imam Sajjad (A.S): wanda majalisar Ahlul-baiti ta Duniya ta shirya.[9] Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Likitocin Shi'a: Wani babban taron ƙasa da ƙasa na likitocin Shi'a ne da aka gudanar ko dai tare da haɗin gwiwar majalisar Ahlul-baiti ta Duniya ko kuma da tallafinta.[10] Haka kuma an gudanar da wani baje kolin cibiyoyin al'adu masu alaƙa da majalisar Duniya ta Ahlul-baiti, tare da halartar hukumomi da cibiyoyin al'adu masu aiki a fagen ƙasa da ƙasa. An gudanar da wannan baje koli na tsawon mako guda a farkon watan Janairu-Fabrairu 2015 Miladiyya.[11]
  • Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Abu Ɗalib: Wani taro ne na ƙasa da ƙasa da majalisar Ahlul-baiti ta Duniya ta shirya domin girmama matsayin Abu Ɗalibibn Abdul-Muɗɗalib, mahaifin Imam Ali (A,S). An gudanar da wannan taro a birnin Qum a watan Maris 2021 Miladiyya.
  • Gina da tallafa wa cibiyoyin jin ƙai: Daga cikin ayyukan al'adu da na zamantakewa na majalisar Ahlul-baiti ta Duniya, kamar taimakawa wajen gina masallatai, husainiyoyi, asusun rancen kuɗi ba tare da riba ba (Ƙardul Hasan), cibiyoyin addini, makarantu, ɗakunan karatu, cibiyoyin lafiya da gidajen marayu. Ana aiwatar da waɗannan ayyuka ne tare da tallafin masu hannu da shuni mawadata da masu aikin alheri..[12]
  • Mu'amala da ƙungiyoyin Shi'a daban-daban: Majalisar Ahlul-bait ta Duniya tana hulɗa da mabiya Shi'a Imamiyya da kuma sauran mazhabobi ko rassa na Shi'a a wurare daban-daban..[13]
  • WikiShi'a: Wani kundin ilimi ne na yanar gizo (Encyclopedia) da ke aiki wajen gabatar da makarantar Ahlul-baiti (A.S) da yaɗa ilimin Musulunci da Shi'anci. Wannan kundin ilimi ya fara aiki a 2013 miladiyya, kuma a halin yanzu yana aiki da harsuna 22, yayin da a harshen Farsi kaɗai yake da kimanin maƙaloli 9,493, harshen Hausa kuma 780
  • Wallafawa, fassara da halartar baje-kolin littattafai: Jimillar littattafan bincike da aka wallafa ta majalisar Ahlul-baiti ta Duniya da cibiyoyin Ahlul-baiti masu alaƙa da ita sun kai kusana take 1800 zuwa lokacin rani na 2015 Miladiyya.[14] Haka kuma an fassara littattafai zuwa harsuna 55 daban-daban.[15] Bugu da ƙari, ma'aikatar wallafe-wallafen majalisar Ahlul-baiti ta halarci baje-kolin littattafai a wurare da dama na Duniya.[16]
  • Ɗakin karatu da cibiyar takardu: A cikin majalisar Ahlul-baiti ta Duniya akwai ɗakin karatu da cibiyar adana takardu ta Ahlul-baiti (A.S) wadda ke da sama da littattafai, mujallu da takardun bincike fiye da 30,000.[17]
  • Wallafa mujallu: A cikin aiwatar da aikinta na al'adu da wa'azi, majalisar Ahlul-baiti ta Duniya tana wallafa mujallu masu fitowa lokaci-lokaci da dama kamar Ahlul-baiti (A.S), Intizar, Balagh, Payame Saƙalaini, Payame Zaynab, Tawhid, Zawil Ƙurbā, Salam, Tubā, Farishtegane Kuchak, Faryad, Alƙibla, Kawsar da Ganjineh ye Majma. Ana wallafa waɗannan mujallu a cikin harsuna daban-daban a ƙasashe da dama, kuma tana tallafa wa da buga wasu mujallu da wallafe-wallafen Musulunci.[18]
  • Samar da kayan aiki ga ɗakunan karatu: Domin tallafawa al'adun Shi'a, majalisar Ahlul-baiti ta Duniya ta tallafa tare da samar da kayan aiki ga dakunan karatu da dama a yankuna daban-daban na duniya.[19]
  • Tallafi a lokutan bala'o'i: majalisar Ahlul-baiti ta Duniya a lokacin faruwar bala'o'i ko abubuwan gaggawa tana tattara mambobinta da masu alaƙa da ita domin tara taimakon kuɗi da kayan agaji. Bayan tattarawa da aikawa da taimakon, tana kuma sa ido kan rabon su yadda zai kasance cikin adalci da kuma yadda ya dace.[20]
  • Kamfanin dillancin labarai na Abna: Wannan kamfanin labarai an kafa shi a shekara ta 2004 miladiyya domin yaɗa labaran mabiya Shi'a na duniya da kuma sanar da su halin da juna ke ciki. Da farko an fara shi da harsuna uku, amma a halin yanzu yana aiki da harsuna 24, kuma ana ɗaukarsa a matsayin mafi shahara kuma mafi yawan masu karantawa a cikin kamfanonin labaran Shi'a.[21]
  • Samar da manhajojin Musulunci: Ɗaya daga cikin ayyukan majalisar Ahlul-baiti ta Duniya shi ne samar da manhajojin ilimi da faifan multimedia (CD) a cikin harsuna daban-daban na duniya.[22]
  • Samar da ayyukan fasaha: Sashen fasaha namajalisar Ahlul-baiti ta Duniya ya samar da zane-zanen addini masu daraja da dama daga ayoyin Kur'ani da riwayoyi, sannan an tattara tarin waɗannan zane-zanen a cikin littafi guda.[23]
  • Tashar ƙasa da ƙasa ma'arif Ahlul-Baiti (A.S): Wannan wata manhaja ce da aka ƙirƙira a 2023 Miladiyya domin samar da cibiyar sadarwa ta daidaitaccen tsari don gabatar da ilimin Ahlul-baiti (A.S) a harsuna daban-daban, da kuma gina wata cibiyar ma'anoni ta ilimin Ahlul-Baiti (A.S) a yanar gizo.
  • Shi'aData: Wata cibiyar yanar gizo ce da rumbun bayanai game da makarantar Ahlulbaiti, musamman bayanan WikiShi'a da WikiTuras. Ana sa ran nan gaba wannan rumbun bayanai zai zama injiniyar bayanai ta Shi'a inda shafukan yanar gizo, manhajoji, shirye-shirye, da fasahar hankali na wucin-gadi (AI) za su iya haɗuwa da shi.
  • WikiTuras: Wata dakunan karatu ta wiki a yanar gizo ce a fannin makarantar Ahlul-baiti, wadda aka kafa domin tattarawa, wallafawa, da fassara mafi yawan dukkanin rubuce-rubucen gadon ilimin Shi'a a siffofi daban-daban kamar littattafai (na bugaggu da na rubutun hannu), maƙaloli, kundin bincike (thesis), adabin addini, da takardu.

Maƙaloli Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. Ha'iri, Ruzeshomare Shamsi, sh 698
  2. ««معرفی مجمع جهانی اهل بیت(ع)»،Cibiyar Takardun Tarihi ta Juyin Juya Halin Musulunci.
  3. Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S). Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baoto (Alaihis Salam), sh 8
  4. Majma Jahani Ahlul-Baiati (A.S). Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (Alaihis Salam), sh 9
  5. Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S). Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (Alaihis Salam) 8
  6. «انتصاب حجت‌الاسلام رمضانی به‌عنوان دبیرکل مجمع جهانی اهل‌بیت(ع)»، Shafin yanar gizon Cibiyar Kula da Adanawa da Yaɗa Ayyukan Ayatullahi Khamenei.
  7. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 64
  8. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 64
  9. Shafin Yanar Gizo na Taron Ƙasa da Ƙasa kan Imam Sajjad Zainul Abidin (A.S.). العابدین(ع).
  10. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 24
  11. «اولین همایش و نمایشگاه خانواده بین‌الملل اسلامی برگزار شد»، Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA..
  12. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 22
  13. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 29
  14. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 35
  15. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 36
  16. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 38
  17. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 39
  18. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 40
  19. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 50
  20. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 56
  21. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 58-59
  22. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 63
  23. Ashnayi Ba Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S), sh 65

Nassoshi