WikiShi'a

Daga wikishia
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Hassan Ruhani ya kaddamar da Wiki na Shi'a a hukumance a ranar 1 ga Yuli, 2014.

Wikishia (Larabci: ويكي شيعة) wani Kundun bayanai da ilimi (Wasika ce da take kunshe da ilimi) da take yanar gizo da take dauke da bayanai game da neman sanin Shi'a da sauran Mazhabobin Mabiya Ahlil-baiti (A.S) wannan ilimumuka sun tattaro Akidu, Daidaikun mutane, da misalin ilimun Kalam Tauhidi, Fikihu da Usulul Fikihi, litattafai, wurare, abubuwan da suka faru, bukukuwan addini da Ibada, kungiyoyin Shi'a tarihin shi'anci da dukkanin wani mafhumi da yake da dangantaka da Ahlil-baiti da Mabiyan su, duk kalmomi da sunaye da suka kasance na larura yana zuwa da bayanin su.

A cikin Wikishia ana kawo Tahlili da mahangar mutum a kankin kansa, sannan kuma ana taka tsantsan cikin Mahangar da bata tabbata ba, hukunci kan sabani na ilimi da tarihi yana kan wuyan Masu karatu, Wikishia a wannan mahallin bata da bangare, bisa lura da sabanin Mazhaba, Maginar Marubuta hakika Wikishia suna karbar daga shi'a da Ahlus-sunna, Wikishia suna jingine da Mu'assasar Majma'u Jahani Ahlil-baiti, wannan Wasikar bayanan ilimi zuwa yanzu tana aiki da yaruka daidai har guda goma sha biyar, a iya kadai yaran Farisanci an shigar da Makala 7193

Manufa da Hadafin samar da ita

Cikin wasikun bayanai akwai bayanai masu tarin yawa dangane da muslunci da shi'anci, sai dai cewa Marubutan cikin Wasikun tattara bayanai ko dai basu da ingantaccen sani da ilimi ko kuma dai basu yi imani da muslunci da Shi'anci ba, zaka samu cikin rubuce-rubucen su kan muslunci da shi'anci akwai tarin kura-kurai, sakamakon fadaka da lura da wannan matsala mai girma da take cikin dandamalin intanet yanar gizo, sai yan shi'a suka mike tsaye don taimakawa masu bincike dama yan shi'ar da samun kaiwa ga akidun shi'a na asali da muslunci, hakika cibiyar yada al'adu Majma'u Jahani Ahlil-baiti sun taka rawa wajen samar da Wikishia da niyyar zama garkuwa da zata bada kariya ga Maktaba din Ahlil-baiti (A.S).

Takaitaccen tarihi

A daya ga watan Kordad hijira Shamsiyya, zama na farko na samu hadin kai daga Marubutan Wikishia ya kasance, sannan bayan wasu adadin tarurruka na ilimi, har ila yau 28 ga watan Kordad, an yada Makala ta farko a cikin Wikishia , sannan a watan Tir shekara 1392 shamsiyya sayit din Wikishia ya sauka ga dukkanin mutane kowa na iya bude shi ya gani ya yi karatu. Wikishia a 1 ga watan Tir 1392 hijiri shamsi a lokacin taron Jikan Annabi (S.A.W) da ya kasance a birnin Tehran karkashin Jagorancin Shugaban Kasar Jamhuriyar muslunci ta Iran Hassan Ruhani an shelanta shi sayit a hukumance.

Abubuwan da ya Kebantu da su

Cikin ba'arin abubuwan da Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Hassan Ruhani ya kaddamar da Wikishia a hukumance a ranar 1 ga Yuli, 2014. Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Hassan Ruhani ya kaddamar da Wikishia a hukumance a ranar 1 ga Yuli, 2014. ya kebantu da su akwai:

Fadaduwar abin da ta kunsa da Nau'antuwar Batutuwa

Hakika sayit din Wikishia ya kunshi abubuwa kamar haka:

  • Akidu, daidaikun mutane, ilimummuka, misalin Fikhu, Usululul fikhi, litattafai, wuraren tarihi, abubuwan da suka faru a tarihi, bukukuwan Addini, kungiyoyin da suke imani da Ahlil-baiti, tarihin shi'anci, dama duk wani maudu'i da yake dangantaka da Ahlil-baiti da Mabiyansu.
  • Fahimtocin muslunci da suka kasance dukkanin musulmi sun yi imani da su ko kuma wanda suke da alaka da tarihin muslunci suma Wikishia bai manta da su ba an sajjala su ciki.
  • Gamammun Ma'anoni na muslunci da suke da dangantaka da sauran kungiyoyin musulmai a lokacin da Wikishia ya bayyana su zai zamana ko dai suna da alaka da Ahlil-baiti ko kuma sun kasance an yawaita amfani da su a ciki.

Sa idanu kan abin da Makala ta kunsa.

Sa idanu kan abin da ake shigarwa cikin wannan Sayit

Shafi na tushe: Wikishia: Matsayin Makaloli

ana bibiya da sa ido kan matanin kasidu, domin gudanar da wannan aiki, an kaddamar da wani tsari da yake nuna ingancin kasidu.

Ma'auni fifiko

Shafi na tushe: Wikishi'a fifikon makaloli

Makaloli da kasidun Wikishia a zuwa yanzu tana ayyukanta ne a iyakance kan asasin abin da aka fi bukatuwa da shi, Abubuwan da suka sa a gaba wajen gyarawa da rubuce-rubuce sun tabbatar da tasirin lakabin wajen sanin mazhabar Ahlul Baiti, duk sanda ma'aunin tasiri lakabi ya karu cikin sanin shi'anci to lallai rubuce-rubucensa zai samu daukaka.

Tsarin Tafiya na Kusanto da juna tsakanin Mazahabobin Muslunci

Makaloli da Kasidun Wikishi'a ana rubuta su kan asasin tsarin kusanto da juna tsakanin mazahabobin muslunci.

Siyasar rashin daukar bangare

  • Dole ya zamana an kiyaye Siyasar rashin bangaranci a cikin bahasosin tunani cikin Mazhabar Shi'a, sai dai cewa a bayyane yake cewa Wikishia wani sayit ne na yada Maktabar Ahlil-baiti da makaloli tare da hadafin bada kariya ne za a yi rubuce rubuce.
  • Makalolin Wikishia, ba makaloli ne na ilimi da bincike ba, da ma'anar cewa su ba irin rubutu ne a tahkiki na farko farko wanda ba a yada shi ba wanda ba zasu amfanar ba cikin warware matsalolin ilimi, shi asasin Wikishia shi ne nuna bayanai kan asasin tushen da ake da shi , saboda haka bai kamata Marubucin mu ya sanya mahangar tunanin sa cikin abin da zai yada a wannan Sayit ba.
  • Yanke hukunci kan sabani na ilimi ko na tarihi wannan duka suna hannun Masu karatu da bibiyar mu, Wikishia a wannan wuri bata da bangare, bisa lura da la'akari da sabani na Mazhaba, ginin Marubutanmu za su iya kawo abubuwa na fari da aka yarda da su daga manyan kungiyoyi biyu Shi'a da Ahlus-Sunna.
  • Bisa la'akari da sabanin mazahabobi, marubutanmu za su fi karkata ne cikin dogara da madogaran da bangarori biyu (Shi'a da Ahlus-sunna) suka yi tarayya cikinsu.
  • Cikin rubutun makaloli da kasidu a kauracewa amfandi da kalmomin da suke bakantawa juna da rusa hadin kai.

Dangantakar Wannan Kundi da Mazhabar Ahlul-Baiti

Mafi muhimmancin siyasar Wikishi'a shi ne wallafa batutuwa da maudu'ai daga sasannin dangantakarsu zuwa ga mazhabar Ahlul-Baiti. da wannan dalili ne cikin rubuta madu'ai da suke da mabambantan sasannai tare da karfafa da kuma mayar da hankali kan geffan shi'ancin wadannan maudu'ai. alal misali wallafa batutuwa misalin kasashe da suka tattaro zawiyoyi daban-daban daga tattalin arziki, Geography, siyasa, mai da hankali kan bahasosi da suke d adangantgaka da mazhabar Ahlul-Baiti kamar misalin takaitaccen tarihin zuwan shi'amci, wurare da fitattun mutane a shi'anci, ladubba da al'adun `yanshi'a. haka nan kuma cikin wallafe wallafen sababbin mas'loli na fikihu da kuma manyan mutane wadanda ba `yanshi'a ba tare da karfafa gaffan da suke da alaka da shi'a da Ahlul-baiti.

Matsayi a Kungiyance

Wikishi'a tana karkashin cibiyar Majma Jahani Ahlul-Baiti (A.S) wacce take damfare da ma'aikatar kula da al'adu a kasar Iran, wata majalisa ce daga shugabanni harsuna, shugabannin ayyukan ilimi da masana na Wikishi'a, da suke kula da sa idanu tare da bibiya kan siyasa da tsare-tsare kan bangarori daban-daban na Wikishi'a.

Wasu abubuwa da WikiShia ta kebantu da su

Dama a kowanne lokaci a kan warware abubuwan da aka shigo da su.

  • Samar da shafin takaitaccen tarihin Makala. Cikin shafin takaitaccen tarihi duk wani canji da ya kasance a makala zai zama za a ganshi, masu bibiyar mu da Marubutan mu za su iya tsinkaya kan canji da aka samu.

Shafin canje canje na karshe, wannan shafi zai mika karshen canje canje da aka samar cikin dukkanin Wiki zuwa ga masu amfani da wannan Sayit.

  • Samun damar kaiwa ga maudu'ai da canje-canjen da suka gabata.

Alakar kofofin shiga tsakanin wannan da wancan,, ta haka Mai karanta makala domin fahimtar kowacce jumla da ta zo cikin matani ba tare da shan wahala bincike ba, kai tsaye zai bude shafin da yake da alaka da wannan abin da yake son fahimta sai ya karanta, wannan hususiya zata taimakawa Mai bibiyarmu ya samu damar karanta kowacce mashiga, cikin sauki dukkanin mafhuman da aka kawo a wannan mashiga zai same su yan kuma kai ga kammalallun bayanai game da maudu'in da yake karantawa. Dangantakar kowacce makala tare da wannan maudu'i cikin wani yaren daban na Wiki. Amfani da raddeha a karshen makala raddeha wani take ne game gari da ake kirga taken makala a kasan sa, Raddeha ba wani abu bane face Fihirisar Wiki.

  • Navigations template wani abin kwaikwayo ne da yake tattaro makala ya ajiyeta cikin wani akwatu da yake a Ufuki a kasan Makalar, Navigation wani lokaci yana kasance da surar akwatin Amudi a saman makaloli da yake amfani, dangantaka tsakanin unwanai an ajiye shi cikin wannan jadawali da surar bijira, ma'ana baki dayan unwanai suna kasancewa cikin jelar wani unwani guda da yake tattaro su.
  • Akwatun bayanai (Inforbox) wata akwatu ce da take saman makala da take tattare bayanai masu muhimmanci a takaice, tare da leka wanna akwatu ba tare da ka karanta makala ba zaka iya tsinkaya kan bayanai na asali a cikin matanin Makalar .

Shafin bahasi. Kowanne shafi da makala a Wiki suna da shafi bahasi guda daya, amasu amfani da shafin bahasi za su iya bayyanarwa da Marubuci ko mai duba Makala ra'ayin su dangane da makalar, shafin bahasi a hakika wani mahalli ne na tattaunawar Ma'abota ra'ayi a masu alaka da maudu'in makala, hakan zai taimaka kan makalar da aka wallafa. Zuwa yanzu Sayit din Wikishia yana da yaruka 22.

Tambari

A shekarar 2022 m, Wikishi'a ta kaddamar da tambarinta, wannan tambari ya tattaro haruffan "w" da "و" da yake nuni kan harafin farawa Wikishi'a a Farisanci da Latin, cikin wannan tambari akwai hasumiya da mihrabi a matsayin wata alama da muslunci da shi'anci. gabanin haka Wikishi'a ta kasance a baya tana amfani da tambarin Majma Jahani Ahlul-Baiti tare da `danbambanci kadan.

Bayanin kula

Nassoshi