Aya Ta 139 Suratul Alu Imran
| bayanan aya | |
|---|---|
| akwai shi cikin sura | Suratul Alu Imran |
| lambar aya | 139 |
| juzu’i | 4 |
| bayanan abin da yake ciki | |
| game da | Alƙawarin nasara ga Muminai |
| ayoyi masu alaqa | Aya ta 35 suratul Muhammad |
Aya ta 139 Suratul Alu Imran (Larabci: آیه ۱۳۹ سوره آلعمران) aya ce da take yi wa Muminai alƙawarin samun nasara da galaba kan Kafirai, tare da ƙarfafa su kan dakewa gaban Kafirai.[1]
وَلَا تَهِنُوا وَلَا تَحْزَنُوا وَأَنْتُمُ الْأَعْلَوْنَ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ
Kuma idan kun kasance muminai, kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baƙin ciki. Alhalin ku ne mafifita..
(Quran: Ma'ida: Aya ta 3)
Cikin farko-farko, wannan aya ta fara da gargaɗin Musulmi ka da rashin nasara cikin yaƙi ya sanya su yi rauni da baƙin ciki[2]
Fadlu Bin Hassan ɗabarsi, malamin tafsiri ɗan shi'a a ƙarni na shida, cikin Tafsir Majma'ul Bayan, ya bayyana cewa wannan aya ta sauka domin yaye baƙin ciki da sanya fata ga Musulmi bayan yaƙin uhudu wanda a cikin wannan yaƙi an karkashe su tare da samun waɗanda suka ji rauni.[3] A wani naƙali da malamin ya zo da shi, kwana ɗaya bayan yaƙin uhudu Annabi tare da wasu jama'a daga waɗanda suka ji raunuka, domin gujewa sabon harin sojojin Makka kan Madina sai suka tafi Hamra'ul Asad, a wannan wuri Allah ya saukar da wannan aya.[4] Ana cewa wannan aya ta kira yi Muminai da su yi gwagwarmaya da yaƙi gaban Mushrikai.[5]
Sayyid Muhammad Husaini Ɗabaɗaba'i, malamin tafsiri masanin falsafa a Shi'a, yana ganin kalmar «تَهِنُوا» da Allah ya yi hani da ita- ta zo ne da ma'anar jin rauni cikin azamar yaƙi da nuna nuna rashin damuwa kan muhimmancin tabbatar da addini.[6] Sannan kuma dangane da kalmar «وَأَنْتُمُ الْأَعْلَوْنَ» an ce daga ƙarshen Muminai ne za su ci nasara.[7] Muhammad Jawad Mugniyya cikin tafsirin wannan aya yayi ishara da Hadis I'itila da aka naƙalto daga Annabin muslunci (S.A.W), kan asasin wannan hadisi muslunci shi ne mafi fifiko kan komai, kuma babu wani abu da zai iya galaba kansa.[8] Har ila yau kalmar imani da ta zo cikin «إِنْ کنْتُمْ مُؤْمِنینَ» tana da ma'anar dogara da Allah da alƙawurranSa.[9] Ayatullahi Khamna'i, jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran, bayan harin da Isra'ila ta kai kan Iran, tare da kisan gilla kan wasu adadin kwamandojin soja na ƙasar, cikin saƙo da ya fitar zuwa ga al'ummar Iran ya karanta wannan aya.[10] Tare da jingina da wannan aya, ya yi imani da cewa matuƙar dai mun kasance Muminai, babu abin da maƙiya za su iya mana a filin daga na gaskiya.[11]
Sayyid Muhammad Taƙiyyu Mudarrisi shi ma yana ganin cewa wannan aya tana ishara zuwa ga sunnar Allah wace kan asasinta, fifiko da cin nasara ba kasa faruwa kwatsam ba zato ba tsammani babu shiri kuma ba tare da sadaukarwa ba, a a bari dai suna lazimta tanadi da juriya kan wahalhalu, saboda shi ma ai maƙiyi abokin gaba yana yin shiri da tanadi kafin ya kai hari.[12]
Aya ta 35 suratul Muhammad ita ma tana da ɗauke da ma'ana makamanciyar wannan; cikinta ya zo kamar haka: saboda haka ka da ku yi rauni, kuna masu kiran Kafirai zuwa sulhu, alhalin ku ne mafifita, Allah ba zai taɓa tauye muku ladan ayyukanku ba.
Bayanin kula
- ↑ Tayyib, Atyib al-Bayan, 1378, juzu'i. 3, shafi. 366.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir-e-Namaneh, 1374, juzu'i. 3, shafi. 108.
- ↑ Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1372, juzu'i. 2, shafi. 843.
- ↑ Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1372, juzu'i. 2, shafi. 843.
- ↑ Tha'labi Neyshaburi, Al-Kashf da Al-Bayan, 1422 AH, juzu'i. 3, shafi. 172.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i. 4, shafi na 26-27.
- ↑ Fakhr Razi, Mafatih al-Ghayb, 1420 AH, Juz. 9, shafi. 371.
- ↑ Mughniyah, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, Juz. 2, shafi. 163.
- ↑ Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1372, juzu'i. 2, shafi. 843.
- ↑ «دومین پیام تلویزیونی آیتالله خامنهای خطاب به ملت ایران در پی تهاجم رژیم صهیونی»،Yanar Gizo na Ayatullah Khamenei.
- ↑ «بیانات در دیدار مسئولان نظام»، Yanar Gizo na Ayatullah Khamenei.
- ↑ Madrasi, Man Huda al-Quran, 1419 AH, Juz. 1, shafi. 666.
Nassoshi
- «بیانات آیتالله خامنهای در دیدار مسئولان نظام», Shafin yanar gizo na Ayatollah Khamenei, ranar shiga: Yuli 6, 2014, ranar ziyarar: Yuli 1, 2025.
- Tha'labi Neyshaburi, Ahmad ibn Ibrahim, Al-Kashf da Al-Bayan kan Tafsirin Alqur'ani, Beirut, Dar Ihya' Al-Turat Al-Arabi, bugu na farko, 1422 Hijira.
- «دومین پیام تلویزیونی آیتالله خامنهای خطاب به ملت ایران در پی تهاجم رژیم صهیونی»،Yanar Gizo na hukuma na Ayatollah Khamenei, ranar shiga: 18 ga Yuni, 1404, kwanan wata ziyara: 1 ga Yuli, 1404.
- Taleghani, Seyyed Mahmoud, Partovi az Quran, Tehran, Haɗin gwiwar Publication Company, bugun 4, 1362 AH.
- Tabatabaei, Sayyid Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir Al-Qur'an, Qum, Ofishin Daba'ar Musulunci, Bugu na 5, 1417H.
- Tabarsi, Fadl bn Hassan, Tafsir al-Jawam al-Jama’i, Tehran, Tehran University Press, Qum Seminary Administration, bugun 1st, 1377H.
- Tabarsi, Fadl ibn Hassan, Majma’ al-Bayan fi tafsir al-Quran, gabatarwar Muhammad Javad Balaghi, Tehran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
- Tayyib, Sayyid Abdul Hussein, Atib al-Bayan fi tafsir al-Quran, Tehran, Islam Publications, bugu na biyu, 1378.
- Fakhr al-Razi, Muhammad bn Omar, Mafatih al-Ghayb, Beirut, Dar Ihya al-Turat al-Arab, bugu na uku, 1420H.
- Modarresi, Seyyed Mohammad Taqi, Man Huda al-Quran, Tehran, Daram Habi al-Hussein, bugu na farko, 1419H.
- Mughniyeh, Mohammad Javad, Tafsir al-Kashif, Tehran, Daral al-Kutub al-Islamiyyah, bugun farko, 1424H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir al-Numno, Tehran, Daral al-Kutub al-Islamiyyah, bugun farko, 1374H.