Jump to content

Sunnar Allah

Daga wikishia

Sunnar Allah ko sunnonin Allah (Larabci: سنة الله) isɗilahi ne na kur'ani da yake ɗaukar ma'anar hanyoyi da dokokin Allah cikin gudanar da al'amura halittu, sunnonin Allah a mahangar musulmi masana suna ɗauke da wasu siffofi da hususiyoyi misalin cika, tabbata da kasancewa tare da dokoki, a faɗin kur'ani su sunnonin Allah abubuwa da ba basa karɓar canji da sauyi.

A imanin musulmi masana, sunnonin Allah bisa la'akari da yanayin da suke faruwa a cikinsa, an karkasa su zuwa sunnoni na lahira da duniya, sannan kuma bisa lura da tasirin tsarin aikin mutum an karkasa su zuwa muɗlaƙar sunna saki babu ƙaidi da da kuma sunnoni da suke da sharaɗi, sunnar istidraj, sunnar taimakon muminai, sunnar yanke uzuri suna cikin jumlar sunnoni da ambatonsu ya zo cikin kur'ani. Ba'arin malamai suna ɗaukar bayyanar Imam Mahahi (A.S) da imanin da dawowarsa matsayin ɗaya daga tajallin sunnoni sunnonin Allah, suna cewa sunnonin Allah misalin wilayar salihai, nasarar gaskiya kan ƙarya da halifancin raunana duka zasu kasance lokacin bayyanar Imam Zaman (A.S).

A cewar masu dandaƙe bincike, sanin sunnonin ubangiji yana da matuƙar tasiri cikin samar da ma'rifa da fahimtar Allah da kuma bayyanuwar tauhidi cikin al'umma, a imaninsu fahimtar tabbatattun dokokin halitta yana zama sababin kyawuntar yanayin gudanar da abubuwa da suke faru na ɗaiɗaiku da jama'a, haka kuma an ce jagororin jamhuriyar muslunci ta Iran, sun tsara jagorancin siyasarsu da zamantakewa kan tushen sunnonin Allah, kuma sun yi Imani da larurar ɗabbakuwa tare da sunnonin Allah domin cimma abin da suke cimma da kuma samun nasara kana bin da suka sanya a gaba.

Sanin Ma'anar Sunnar Allah

Sunnar Allah na nufin hanyoyi da dokoki a cikin ayyukan Allah da la'amuran duniyar halittu suke gudana kan asasin waɗannan dokoki da hanyoyi[1] Abdullahi Jawadi Amoli, masanin falsfa da faƙihi kuma malamin tafsiri a shi'a, sunnoni Allah suna nufin tsari cikin dokokin halitta da kuma ma'aunin ubangijintaka, waɗanda ƙarƙashin taimakon hankali da falsafa ana iya fahimtarsu da riskarsu.[2]

A ra'ayin masu dandaƙe bincike, ma'anar sunnar Allah tana da alaƙa da wata ma'ana cikin kur'ani tare da wasu kalmomi misalin “Amru", “Irada", “ƙaulu", “Hukmu", “Ja'al", “Faraz", “ƙaza" da “ƙadar".[3] a cewar masu dandaƙe nazari da bincike, sunnonin Allah suna tattaro komai da komai ta fuskoki biyu: na farko daga fuskar nau'antuwar hanyoyi daban-daban da kuma matakai na ubangiji, ɗayan kuma daga fuskanin tattarowa cikin dukkanin halittu, ma'ana babu wata halitta daga halittun Allah da ta kasance a wajen sunnoninsaa ko ina take da ko wane lokaci ne tabbas sai ɗaya daga cikin sunnonin Allah sun gudana kanta.[4]

Muhimmanci Da Matsayi

Abdullahi Jawadi Amoli, yana ɗaukar sunnar Allah matsayin abun da ya dace da bashi take na ilimi mai cin gashin kansa, da yake da tanadin tajalli da bayyanuwa cikin fuskoki daban-daban daga siyasa, zamantakewa, al'ada, tattalin arziƙi da…; sai dai cewa ilimin boko sakamakon rabuwa da mabda (Asali) da ma'ad, shi ne ya zaune mazaunin sunnonin Allah a wasu lokuta ya kan yi illa ga ɗan Adam.[5]

Sayyid Muhammad Baƙir Sadar, faƙihi mutafakkir na shi'a, ya yi Imani cewa sunnonin Allah tare da hadafin kur'ani da manufofinsa na shiryarwa da tseratar mutum zuwa ga haske, suna da alaƙa da juna ta kusa-kusa, saboda bisa lura da wannan dokoki kai tsaye suna tasiri cikin sauyi da canji cikin ɗaiɗaikun mutane da kuma cikin al'umma.[6]

Sakamakon kasancewar sunnonin Allah suna karkata ne ga yadda aikin Allah da alaƙarsa tare da bayi ke kasancewa, wasu sun yi Imani da cewa haƙiƙa sunnonin Allah su ne mafi bayyana cikin tabbatar da samuwar da tauhidi. saboda haka ne da ma'aunin da ɗaiɗaikun mutane da al'umma suke da shi cikin fahima da gane waɗannan sunnoni, da wannan ma'auni ne dai sanin Allah ya assasu a cikinsa;[7] haka nan a cewar masu nazarin kur'ani, haƙiƙa juya baya da watsi da sunnonin Allah yana haifar da babbar asara duniya da lahir.[8]

Mutanen da suke ganin larura kashafin sunnonin Allah cikin rayuwar ɗan Adam domin gano ma'ana cikin abubuwa da suke faruwa a rayuwa, kuma suna cewa fahimtar sunnonin Allah matsayin tabbatattun dokoki, yana bawa mutum ƙarfin hasashe da ɗaukar matakan da suka dace cikin abubuwa da suke faruwa cikin ɗaiɗaiku da zamantakewa, kuma yana da matuƙar tasiri cikin tarbiyya.[9]

Mulki Da Ya ɗabbaku Tare da Sunnonin Allah

Sunnonin Allah suna da mahalli na musamman cikin matakan siyasa da zamantakewa a wurin shuwagabannin jamhuriyar muslunci ta Iran; ta kai ga wasunsu sun yi Imani tunanin gwagwarmayar Imam Khomaini wanda ya assasa gwamnatin muslunci ta Iran tunani da ya ɗabbaku kan sunnonin Allah da aka ambace su daga kur'ani,[10] kuma kakkausan kalamansa da ya yi kan amurka hatta kafin fara ɗauki ba daɗi da gwamnati Shahinsa pahlawi mai toshashshen basira da tunani, sun ɓuɓɓugo ne daga dogara da sunnonin Allah.[11]

Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran bayan Imam Khomaini, a cikin kalamansa yana ɗaukar mas'aloli misalin ɗaukaka kyawawan halaye, tabbatar da izza, ƙarfi da kuma gwagwarmaya, ƙarfafar zuciya, aiki da hankali, adalci, basira, sanin abokan gaba da tabbatar da ci gaba cikin al'umma ya dogara ne da ɗabbaka aiki da sunnonin Allah.[12] yana ganin rashin ingantacciyar fahimtar maƙiyan muslunci daga sunnonin Allah shi ne sababin faɗuwa lokaci bayan lokaci a cikin lissafinsu da da rawar da suke takawa, ya yi amanna cewa duk inda ka samu musulmi sun yi nasara a fagagen siyasa da soja, sun samu wannan nasara ne sakamakon aiki da ɗaya daga cikin sunnonin Allah, kuma duk inda ka samu sun faɗi sun ƙasƙantu da wulaƙantuwa, hakan ta faru ne sakamakon rashin kiyaye dokokin sunnonin Allah.[13]

Abdullahi Jawadi Amoli shi ma ya yi amanna cewa sakamakon su sunnonin Allah basa karɓar canji cikin ƙasƙantar da masu ɗagawa misalin fir'aunoni da suka yi girman kai da ɗagawa suke wuce iyaka, ƙasar amurka a ko wace rana ko wane minti suna ƙara kusantar faɗuwa da rushewa.[14]

Magudanar Sunnonin Allah

Madu dandaƙe bincike sun yi Imani cewa kur'ani a wasu lokuta ya na danganta zartar da sunnonin Allah ga shi kansa Allah kamar yadda ya zo cikin 1ya ta 23 suratul fatahu, wani lokaci kuma yana jinginawa ga Annabawa kamar misalin cikin aya ta 77 suratul Isra'i lokacin daban kuma ga mutane kamar misalin aya ta 13 suratul hajar.[13]

Ba'arin suna ganin cewa faɗaɗuwa da yaɗuwar magudanan sunnonin Allah ya haɗowa da bakiɗayan sabubban ɗabi'a da saman ɗabi'a wanda mashi'a da iradar Allah kai tsaye ko bai kai tsaye tana gudana daga gare su.[16]

Muhammad Taƙiyyu Misbahu Yazdi, masanin falsafa malamin tafsiri a shi'a, ya yi amanna cewa sunnonin Allah da suke gudana a wasu magudanai na daban cikin duniyar halittu, Allah yana jingina waɗannan sunnoni zuwa ga kansa domin ƙara fahimtar mutane da ƙara ganar da su tauhidi af'ali.[17]

Hususiyoyin Sunnonin Allah

Malaman musulmi bisa la'akari da ayoyin kur'ani, sun lissafa wasu siffofi da hususiyoyi ga sunnonin Alllah, daga jumlarsu za a iya ishara da wuraren da za su zo a ƙasa:

  • Tattaro komai da komai: bisa la'akari da aya ta 38 suratul ahzab, babu wani wuri ko lokaci ka sharuɗɗa da aka togace su daga sunnonin Allah, sunnonin Allah sun haɗa komai da kowa ta hanya ɗaya.
  • Tabbatuwa da rashin karɓar canji: kan asasin aya ta 43 suratul faɗir, sunnonin Allah basa canjawa kuma wani abu baya maye gurbinsu.
  • Azabtar da gungu-gungun jama'a (Wanda yake da alaƙa da azabar Allah): aya ta 25 suratul anfal, sunnar Allah bata taƙaitu kan iya masu aikata lefi ba; bari dai al'umma da suke nuna ko in kula, suka zaɓi kame baki suma abin yana haɗawa da su.
  • Rashin ɗaukar ɓangare da kuma kasancewa bisa doka: kan asasin aya ta 140 suratul alu Imran, duk mutanen da suka fahimci sunnonin Allah, za su iya amfana daga waɗannan sunnoni cikin haduffansu, kuma dukkanin wanda ya saɓa musu zai faɗi ƙasa warwas; kamar yadda musulmai suka yi rashin nasara a yaƙin uhud sakamakon rashin biyayya ga umarni da kuma rashin tsayuwa da dakewa.[18]

Rashin Sauyi Da Canji Cikin Sunnonin Allah

Cikin aya ta 43 suratul faɗir, an bayyana cewa sunnonin Allah basa karɓar canji “tabdil" da sauyi “tahwil", a ra'ayin Murtada Muɗahhari, malami a shi'a, rashin canji ya zo ne da ma'anar rashin goge sunnar Allah da canja ta da wata sunnar, shi kuma rashin sauyi yana da ma'anar cewa cikin sassanta ba za a samu sauyi ba.[19]

Allama ɗabaɗaba'i, malamin tafsiri masanin falsafa a shi'a, yana kan Imani da cewa canja “Tabdil" sunna shi ne cewa lafiya da ni'ima su zauna mazaunin azaba, shi kuma sauyi “Tahwil" shi ne azaba ta cirata daga kan wasu mutane zuwa kan wasu mutane daban.[20]

Wasu masana sun yi Imani da cewa yawan maimaita kalmar sunna tare da kalmomin “ƙablu" da “Awwalin" a cikin kur'ani,[tsokaci 1] yana da ma'anar ishara kan cewa abin da ya faru da mutanen da suka gabata ba zai karɓi canji ba, lallai sai ya faru da waɗanda za su daga bayansu.[21] saboda haka kur'ani bisa la'akari da aya ta 137 suratul alu Imran yana sa rai mutane za su yi yawo a ban ƙasa tare da ɗaukar darasi da wa'aztuwa daga yadda ƙarshen mutanen da suka gabace su ya kasance, su yi nutso cikin tunani su fahimci sunnonin Allah.[22]

Rabe-raben Sunnonin Allah

Ba'arin masanan cikin musulmai, bisa la'akari da inda suke faruwa, sun kasa su zuwa rukuni biyu, sunnonin duniya da sunnonin lahira.[23] bugu da ƙari ita ma sunnar duniyar ta kasu zuwa rukuni guda biyu, sunnoni muɗlaƙai saki ba ƙaidi ko dabaibayi da kuma sunnoni masu sharaɗi. Abin nufi daga sunnoni mudlaƙai, su ne waɗannan sunnoni da basu tasirantu da da illolin mu'amalar da mutum yake yi ba, misalin sunnar gama garin shiriya daidai da abin da ya zo a aya ta 155 suratul baƙara da aya ta 85 suratul ɗaha, su waɗannan sunnoni suna gudana kan kowa da kowa.

Abin nufi daga sunnoni masu sharazi su ne waɗannan sunnoni da suke gudana sakamakon tsarin ayyukan mutum; misalin sunnar taimakon muminai (daidai da abin da ya zo a aya ta 47 suratul rum) da sunnar halifantarwa (daidai da abin da ya zo a aya 54 suratul ma'ida da aya ta 38 suratul Muhammad).[24]

Ba'arin masu dandaƙe nazari daga musulmi, tare da la'akari da ayoyin kur'ani mai girma sun rarraba sunnonin Allah zuwa rukuni guda dunƙule, ƙarƙashin ko wane rukuni sun kawo adadin ayoyi: 1. Sunnar Allah cikin shiryar da mutane zuwa ga ingantattun sunnoni (Misalin aya ta 26 suratul nisa'i),

2. Sunnar Allah cikin ruguza sunnonin ƙarya (Misalin aya ta 37-38 suratul ahzab), 3.Sunnar Allah cikin azabar magabata (Misalin aya ta 137 suratul alu Imran, aya ta 55 suratul kahaf aya ta 60-62 suratul ahzab).[25]

Ba'arin masu dandaƙe bincike, cikin rabe-raben sunnoni na daban, a tashin farko sun rarrabawa sunnonin Allah zuwa ga sunnoni na halitta da sunnoni na shari'a. haka nan sunnonin shari'a suma bisa la'akari da tsarin mutum sun kasa su rukuni biyu: sun haɗa da sunnonin ɗaiɗaiku da sunnonin zamantakewa.[26]

Samfura Daga Sunnonin Allah Daga Kur'ani

Kan asasin rubuce-rubucen malaman tafsiri da masu zurfafa nazari, ba'arin sunnonin Allah da aka yi maganarsu a cikin kur'ani su ne kamar haka:

  • Sunnar Imla (ɗaga ƙafa da jinkirtawa): ma'ana bada lokaci ga azzalumai da saran ko za su tuba, amma dai a mafi yawan lokuta wannan tana ƙarewa tare da illa gare su; saboda naunyin zalunci ya na ƙara ƙaruwa (Daidai da aya ta 178 suratul alu Imran da aya ta 45 suratul ƙalam).[27]
  • Sunnar Istidaraj: ma'ana jinkirin ubangiji ga azzalumai tare da ni'imta su da dawwamammun ni'imomin duniya da suke zama sababin gafalarsu, sannu-sannu a hankula za su dinga kusantar azabar Allah basu sani ba, (Daidai da aya ta 182-183 suratul a'araf, aya ta 55 suratul tauba, aya ta 85 suratul tauba).[28]
  • Sunnar Allah kan taimakon muminai: ma'ana rayuwar miminai cikin Imani ta kasance sababin saukar albarkokin sama da a ƙasa ga muminai, kuma taimakon ubangiji zai sauka gare su a lokutan da suka fi buƙatuwa zuwa gare shi (Daidai abin da ya zo a aya ta 96 suratul a'araf, aya ta 4 suratul fatahu, aya ta 25 suratul tauba, aya ta 40 suratul tauba, aya ta 124 suratul alu Imran).[29]
  • Sunnar yanke uzuri: ma'ana Allah baya halakar da mutane sakamakon zalunci da suka aikata ba tare da ya yanke uzuri da kammala duk wata hujja kansu ba, (Daidai da aya ta 131 suratul am'am da aya ta 15 suratul isra'i).[30]
  • Sunnar jarrabawa (Sunnatu Ibtila): Allah ya jarraba bakiɗayan mutane a rayuwar duniya da wahalhalu da kuma jin daɗi, (Daidai da aya ta 2 suratul ankabut da aya ta 35 suratul anbiya).[31]
  • Sunnar shiryarwa: Allah baya yin ko in kula dangane da makomar bayinsa, domin shiriyarsu ya aiko da Annabawa masu shiryar da su da manzanni (Daidai da aya ta 133 da 134 suratul ɗaha, aya ta 47 suratul yunus, aya ta 16 suratul nahli da aya ta 24 suratul faɗir).[32]
  • Sunnar azaba: ɗaiɗaikun mutane da al'ummu a suka kasance azzalumai, sakamakon rashin nuna godiya da kuma butulci suna shiga halaka da azabar Allah (Daidai da aya ta 59 suratul kahaf, aya ta 11 suratul anbiya, aya ta 117 suratul hud, aya ta 112 suratul nahli).[33]
  • Sunnar gyara: Allah yana azurta kowa gwargwadon halinsa (Daida aya ta 27 suratul shura).[34] idan wasu wurare muka ga arziƙin ɗawagitai a cikin gidan duniya yana ƙaruwa hakan ta faru sakamakon wasu sunnonin Allah daban misalin sunnar istidraj ko sunnar jarrabawa.[35]
  • Sunnar imdad: ma'ana tallafin Allah ga bakiɗayan mutane (Muminai da wanda ba muminai ba) domin cimma hadafinsu (Daidai aya ta 20 suratul shura da aya ta 20 suratul isra'i).[36]
  • Sunnar canji: ma'ana canja makomar al'umma ko ci gaban ni'ima kansu bakiɗayansu sun kasance kan asasin mu'amalarsu, shi kuma Allah daga nasa ɓangaren ba zai taɓa ɗauke ni'imarsa daga kansu (Daidai da aya ta 53 suratul anfal, aya ta 11 suratul ra'ad).[37]
  • Sunnar ƙayatawa: ma'ana Allah ya sanya ayyukan ko wace al'umma su yi kyawunta a idonsu (Daidai da aya ta 108 suratul an'am).[38]
  • Sunnar mudawala: ma'ana kekkewayawar kwanakin tsakanin mutane, da yanayin da ɗaya bayan ɗayan kowa wata rana amfana daga alfanun rayuwar duniya da daularta zai zagayo kansa shi ma ya samu wanda suka gabace shi kuma daular ta sauka daga kansu su zama tarihi.[39]

Sauran sunnonin Allah da bamu ambata ba su ne: sunnar Allah cikin asbabu da musabbabat, sunnar makirci, sunnar Allah game da arziƙin bayinsa, sunnar Allah game da Imani, taƙawa da ayyuka nagari, da sunnar ni'ima da ma'abotanta.[40]

Mahadawiyya, Bayyanuwar Sunnonin Allah

Ba'arin masu dandaƙ bincike sun yi Imani cewa mas;alar mahadawiyya cikin aƙidun musulmai da mas'alar sunnonin Allah abubuwa ne guda biyu da suka da alaƙa ta kusa-kusa da juna kuma tunanin mahadawiyya cikin kankin kansa yana tattare da adadin sunnoni Allah da za su faru lokacin bayyanar Imam Mahadi kamar misalin:

  • Sunnar wilayar Salihan bayin Allah cikin wilayar Allah (Daidai da aya ta 55 suratul ma'ida da aya ta 59 suratul nisa'i)
  • Sunnar kasancewar halifan Allah da ɗaukar nauyi (daidai da aya ta 30 suratul baƙara da aya ta 72 suratul ahzab)
  • Sunnar kasancewar gaskiya ita ce mai nasara daga ƙarshe a kan ƙarya (Daidai da aya ta 16 suratul nisa'i, aya ta 8 suratul anfal, aya ta 34 suratul tauba),
  • Sunnar halifantar da raunana kan doran ƙasa (Daidai da aya ta 5 suratul ƙasas),
  • Sunnar tseratar da muminai (Daidai da aya ta 103 suratul yunus)
  • Sunnar shugabancin salihai (Daidai da aya ta 105 suratul anbiya da ya ta 55 suratul nur),
  • Sunnar ta'allaƙar gobe ga masu tsoran Allah (Daidai da aya ta 128 suratul a'araf),
  • Sunnar galabar muslunci kan sauran addinai (Daidai da aya ta 33 suratul tauba, aya ta 28 suratul fatahu).[41]

ba'arin malamai suna ganin sunnonin halifantarwa, jarrabawa, tantancewa, imla da istidraj bisa lura da ayoyin kur'ani da riwayoyi suna da ƙarfafaffar dangantaka da mas'alar mahadawiyya, gaibar Imam Mahadi (A.S) da jiran bayyanar Imam Mahadi (A.S).[42]