Tarikus Salat
Tarikus salat ko mai barin sallah, (Larabci: تارك الصلاة) take ne da yake nuni zuwa ga Musulmi wanda da gangan yake ƙin yin sallah, bisa koyarwar shari'a Muslunci ana la'akari da misalin wannan mutumi a matsayin wanda yake aikata manya-manyan zunubai, idan wani yaƙi yin sallah saboda yana inkarin kasancewarta wajibi, lallai hakan zai zama dalilin riddarsa da fita daga Muslunci. Kur'ani ya bayyana rashin yin sallah yana daga cikin abubuwan da suke hana samun ceto a ranar Alƙiyama.
An naƙalto daga Annabi idan wani ya bar sallah ba tare da wani uzuri ba, Allah zai ɓatar da ayyukansa na alheri. Bisa abin da ya zo a riwayoyi, Shaiɗan yana amfani da barin sallah cikin jefa mutane cikin manya-manyan zunubai, kuma Allah yana da haƙƙin sanya mai barin sallah a sahun munafukai ya kora su zuwa Jahannama. A wasu riwayoyin an kira masu barin sallah da Kafirai.
Musulmai sun yi ijma'i kan cewa da wani zai yi inkarin asalin sallah ya kuma yi shakkun kasancewarta wajibi, to ya yi ridda, sai dai idan ya yi da'awar cewa barin yin sallarsa ya kasance ne bisa shubuha kamar dai sabbin muslunta.
Wasu jama'a daga malaman fiƙihu sun yi imani idan wani bisa sakaci da kasala ya bar sallah ba tare da ya yi inkarin asalin wajabcin sallah ba, to za a ɗauke shi matsayin fasiƙi, amma wanda tare da imani da wajabcin sallah sai ya bar sallah ba tare da wani uzuri da yake da shi ba, to za a ladabtar da shi, a kuma umarce shi ya yi sallah; idan ya ci gaba da barin sallah, kuma wasu lokutan sallar ta zama ramuwa a wuyansa, to za a sake ladabtar da shi ta hanyar ta'azir
Zargi Kan Barin Sallah
Barin sallah yana cikin manya-manyan zunubai masu girman gaske,[1] a cikin wasu riwayoyi an kira mai barin sallah da kafiri.[2] Rashin yin sallah da gangan yana matsayin wulaƙanta sallah, kuma hukunci da shari'a ta tanada kan wannan aiki kamar yadda ya zo a wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya zarce hukuncin da aka tana da a kan wasu daga manya-manyan zunubai (Kamar shan giya), Shaik Hurrul Amili babban malamin fiƙihu na Shi'a a ƙarni na 11 hijira, ya dogara da wannan riwaya kan tabbatar da kafircin mai barin sallah.[3]
Nasir Makarim Shirazi, daga maraji'an taƙlidi na Shi'a, yana da ra'ayin cewa halin mai barin sallah ya fi munana daga mutanen da suke sakaci cikin sallah wanda Kur'ani ya bayyana su matsayin mutanen da suka cancanci bomi da azaba wanda aka yi amfani da jumlar (Wailun Lil musallin)[4] a kansu.[5]
An naƙalto daga Annabi (S.A.W), idan wani ya bar sallah ba tare da wani uzuri ba, Allah zai ɓatar da ayyukansa na alheri.[6] Kan asasin riwayoyi, Shaiɗan na amfani da barin sallah da mutane suke yi ya cuna su da hankaɗa su zuwa aikata manya-manyan lefuka[7] Allah yana da haƙƙin sanya masu barin sallah cikin sahun munafukai tare da aika su jahannama[8] Haka nan an naƙalto wata riwaya daga Imam Baƙir (A.S), ka da ku yi sanyin jiki cikin sallah, saboda manzon Allah a numfashinsa na ƙarshe-ƙarshe ya ce: ba ya tare da ni duk wanda yake wulaƙanta sallah.[9]
Hanyoyin Barin Sallah
Haƙiƙa Musulmi sun yi ijma'i idan wani ya yi inkarin asalin sallah ya ƙaryata wajabcinta, to lallai ana lissafa shi cikin wanda ya fice daga Muslunci[10] kuma murtaddi,[11] Sai dai idan ya yi da'awar cewa barin sallarsa ya faru ne bisa shubuha da ya samu kansa a ciki, kamar sabon muslunta,[12] Amma da wani zai kasance ya yarda da wajabcin sallah amma sai ya bar sallah ba tare da uzuri ba, to za a masa ta'azir (ladabtarwa ta shari'a), a umrace shi da yin sallah, idan bayan ɗaukar wannan matakai a kansa ya ci gaba da barin sallah, wata sallah ta zama ƙara'i da ramuwa a kansa, to za a sake masa ta'azir (ladabtawa ta shari'a)[13] Idan wani bisa kasala da sakaci sai ya bar sallah bai yi ba, amma ba ya inkarin asalin sallar, za a masa hukunci da kasancewa fasiƙi.[14]
Kafircin Mai Barin Sallah
A wasu riwayoyi, an yi ishara kan kafircin mai barin sallah: Annabin Muslunci ya ce: wanda bisa ganganci ya bar sallah shi kafiri ne,[15] Imam Kazim (A.S) bisa maganar Annabi (S.A.W) a cikin wata riwaya ya lissafa manya-manyan zunubai, ya bayyana barin sallah da gangan da duk abin da Allah ya wajabta cikin manya-manyan zunubai.[16][Tsokaci 1]tsakanin bauatr Allah da kafirce masa, barin sallah ne tsakankani.[17] Imam Sadiƙ (A.S) a wata magana ya kira mai barin sallah da kafiri.[18]
A cewar Muhammad Baƙir Majlisi, malamin hadisi na Shi'a a ƙarni na 11 hijira, yana cewa imani bai taƙaitu da imani a zuciya ba, wajibi ne ya kasance tare da sauke wajibai na shari'a da abubuwan da shari'a ta haramta, a ra'ayin malamin, da wannan dalili ne a cikin riwayoyi aka kira mai barin sallah da kafiri.[19] Allama Hilli, babban malamin fiƙihu na Shi'a a ƙarni na bakwai da takwas hijira, ya yi da'awar cewa ijma'i ya ƙullu kan tabbatar kiran mai barin sallah da wanda ya yi ridda ya fita daga Musulunci.[20]
Musulmi sun yi saɓani kan mutumin da duk da cewa ya yi imani da wajabci sallah amma tare da haka yana barin sallah.[21] Wasu malamai sun bayar da umarni ta'azir kan mutumin da tare da cewa yarda da wajabcin sallah amma kuma yana barin sallah da gangan, idan ya sake maimaita barin sallah har karo uku ko huɗu[22] za a kashe shi[23] Tare da haka, Sayyid Ali Sistani ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a, yana da ra'ayin cewa barin sallah kaɗai ba ya jawo kafirci, duk da cewa hakan yana daga manya-manyan zunubai.[24] Mirza Jawad Tabrizi daga maraji'an taƙlidi na Shi'a, ba ya ganin mai barin sallah a matsayin najasa.[25]
Barin Sallah Da Kuma Sauran Zunubai
Bisa abin da ya zo cikin riwayoyi biyu da aka kawo su a litattafan Al-Kafi da Irshadul Ƙulub, zunubin barin sallah yana iya fin zunubin ƙona Kur'ani da aikata zina, kuma ana ɗaukar mai barin sallah ya matsayin kafirta da Allah da manzonsa,[26] Amma Shaik Saduƙ a cikin littafin Ilalush Shara'i da marubucin La'alil Akhbar, suna ganin cewa babban dalili nauyayar zunubin mai barin sallah shi ne, mutum ba tare da wani dalili ba, kuma ba tare da hatta jin daɗin haramun ba sai a same shi yana wulaƙanta wannan ibada, alhali a sauran lefuka, galabar sha'awa ko wani jin daɗin zunubi ne suke jawo shi zuwa ga aika waɗannan lefuka.[27]
Bayanin kula
- ↑ Tayyib, Atyab al-Bayan, 1378SH, Juz'i na 14, Shafi na 168.
- ↑ Tayyib, Atyab al-Bayan, 1378SH, Juz'i na 14, Shafi na 168.
- ↑ Hurr al-Amili, Wasa'il al-Shia, Beirut, Juz'i na 3, Shafi na 28.
- ↑ Taleqani, Partovi az Quran, 1362SH, Juz'i na 4, Shafi na 273.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir-e Nemuneh, 1374SH, Juz'i na 27, Shafi na 361.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403ƙ, Juz'i na 79, Shafi na 202.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403ƙ, Juz'i na 79, Shafi na 202.
- ↑ Sheikh Saduq, Uyun Akhbar al-Ridha, 1378SH, Juz'i na 2, Shafi na 31.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407ƙ, Juz'i na 3, Shafi na 269.
- ↑ «حکم تارک الصلاه» Gidan yanar gizo na Muflihun.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1407ƙA, Juz'i na 5, Shafi na 359.
- ↑ Shahid Awwal, Al-Durus,1417ƙ, Juz'i na 1, Shafi na 144.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1407ƙ, Juz'i na 1, Shafi na 689.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1407ƙ, Juz'i na 5, Shafi na 359.
- ↑ Ibn Abi Jumhur, Awali al-La'ali, 1405ƙ, Juz'i na 2, Shafi na 224.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1987 AH, Juz'i na 2, Shafi na 287.
- ↑ Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, Najaf, Shafi na 74.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407ƙ, Juz'i na 2, Shafi na 279.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403ƙ, Juz'i na 66, Shafi na 127.
- ↑ Hillí, Tadhkirat al-Fuqaha,1414ƙ, Juz'i na 2, Shafi na 391.
- ↑ «حکم تارک الصلاه» Shafin yanar gizo na Muflihun.
- ↑ Shahid Awwal, Al-Durus, 1417ƙ, Juz'i na 1, Shafi na 144.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1407ƙ, Juz'i na 1, Shafi na 689.
- ↑ «پرسش و پاسخ، تارک نماز»،Shafin yanar gizo na ba da bayanai daga ofishin Ayatullah Sistani
- ↑ Tabrizi, Istifta'at-e Jadid, ba a kwanan wata ba, Juz'i na 2, Shafi na 115.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407ƙ, Juz'i na 2, Shafi na 287; Daillami, Irshad Al-Qulub ila al-Sawab, Juz'i na 1, Shafi na 190.
- ↑ Shaik Saduƙ Ilalush Shara'i juzu'i 2, shafi 339، «لئالی الاخبار، ص۱۲۹۷»،Dakin Karatu na Zamani na Cibiyar Koyon Ilmi ta Intanet ta Jami'ar Al-Qur'ani da Hadisi
Tsokaci
- ↑ وَ تَرْكُ الصَّلَاةِ مُتَعَمِّداً أَوْ شَيْئاً مِمَّا فَرَضَ اللهُ لِأَنَّ رَسُولَ اللهِ ص قَالَ مَنْ تَرَكَ الصَّلَاةَ مُتَعَمِّداً فَقَدْ بَرِئَ مِنْ ذِمَّةِ اللهِ وَ ذِمَّةِ رَسُولِ اللهِ. Tarjama:Kuma barin sallah da gangan, ko wani abu daga cikin abin da Allah ya wajabta, domin Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: "Wanda ya bar sallah da gangan, to lalle ya fita daga amanar Allah da amanar ManzonSa."
Nassoshi
- Daylami, Ḥasan bin Muḥammad, Irshad al‑ƙulub ila al‑Ṣawab, Qom, al‑Sharif al‑Raḍi, bugu na farko, 1412 ƙ.
- Ḥilli, Ḥasan bin Yusuf, Tadhkirat al‑Fuƙuha, Qom, Cibiyar alul al‑Bait Alayhim al‑Salam,bugu na farko, 1414 ƙ.
- Ḥurrul Amili, Muḥammad bin Ḥasan, Wasaʾil al‑Shiʿa ila Taḥṣil Masaʾil al‑Shariʿa, bincike Abd al‑Raḥim Rabbani Shirazi, Bayrut, Mawallafar Gidan Raya Gadon Larabawa, babu kwanan wata.
- Ibn Abi Jumhur, Muḥammad bin Zayn al-Din, ʿAwali al-Laʾali al-ʿAziziyya fi al-Aḥadith al-Diniyya,bincike da gyara Mujtaba ʿIraqi, Qom, Mawallafar Sayyid al-Shuhadaʾ, 1405ƙ.
- Shaʿu'airi, Muḥammad bin Muḥammad, Jamiʿ al‑Akhbar, Najaf, mabugar Ḥaydariyya, bugu na farko babu kwanan wata.
- Shaykh Ṣaduƙ, Muḥammad bin ʿAli, ʿIlal al‑Sharaʾiʿ, Qom, shagon littafi Dawari, bugu na farko, 1385 Sh.
- Kuliyni, Muḥammad bin Yaƙub, al‑Kafi, bincike da gyara Ali‑Akbar Ghaffari da Muḥammad Akhundi, Tehran, Mawallafar Gidan Littattafan Musulunci, bugu na huɗu, 1407ƙ.
- Majlisi, Muḥammad‑Bāqir, Biḥār al‑Anwar, Bairut, Mawallafar Gidan Raya Gadon Larabawa, bugu na biyu, 1403 ƙ.
- Makarim Shirazi, Naṣir, Tafsire Nemuneh, Tehran, Mawallafar Gidan Littattafan Musulunci, bugu na farko, 1374 Sh.
- Shahid Awwal, Muḥammad bin Makki, al‑Durus al‑Sharʿiyya fi Fiƙh al‑Imamiyya, ofishin mawallafar Musulunci, Qom, bugu na biyu, 1417ƙ.
- Shaykh Ṣaduq, Muḥammad bin ʿAli, ʿUyun Akhbar al‑Riḍa (A.S),bincike da gyara Mahdi Lajvardi, Tehran, Wallafe-wallafen Jahan, bugu na farko, 1378ƙ.
- Shaykh Ṭusi, Muḥammad bin Ḥasan, al‑Khilaf, bincike da gyara ʿAli Khurasani, Sayyid Jawad Shahrastani, Mahdi Ṭaha Najaf, da Mujtaba Iraƙi, Qom, Ofishin Wallafa na Musulunci, bugu na farko, 1407 ƙ.
- Tabrizi, Jawad, Istiftaʾat‑e Jadid, Qom, Ofishin Ayatullah Tabrizi, bugu na farko, babu kwanan wata.
- Ṭaleqani, Sayyid Maḥmud, Partovi az Qurʾan, Tehran, kamfanin wallafa littattafai na “Enteshār” wanda yake kamfani mai hannun‑jarin jama’a. bugu na huɗu, 1362 Sh.
- Ṭayyib, Sayyid ʿAbd al‑Ḥusayn, Aṭyab al‑Bayan fi Tafsir al‑Qurʾan, Tehran, Intisharat‑e Islam,bugu na biyu, 1378 Sh.
- «حکم تارک الصلاه, (fikihu/Sallah/Hukunce-hukunce-Hukuncin Mai Barin Sallah Tarik al-Salah) Gidan Yanar Gizo na Muflihun, ranar dubawa: 24 ga Satumba, 2022M.
- «پرسش و پاسخ، تارک نماز, (Tambaya da Amsa: Mai Barin Sallah (Tarikus al-Salah) Gidan Yanar Gizo na Ayatullah Sistani, ranar dubawa: 24 ga Satumba, 2022.M