Shafa Kwalli

Daga wikishia
wannan wani rubutu ne na bayani kan ra'ayin fikihu ba zai zama madogaa ba kan ayyukan addini, a duba wasu madogaran domin ayyukan addini
Risala Ilmiyya

Shafa kwalli a Idanu, (Larabaci الاكتحال) yana daga cikin ayyuka na mustahabbi kuma sunna ce ta Annabin Muslunci (S.A.W) da Imaman Shi’a da suke umartar mutane da shafa shi, cikin riwaya an yi bayani kan fa’idoji na zahiri ba ma’anawiyya daga shafa kwalli daga cikinsu akwai rigakafi da kuma magance ba’arin cutukan idanu, haka kuma yana taimakawa cikin tashin dare domin raya shi da ibada. Fiƙihu ya ambaci wasu hukunce-hukunce da suka shafi shafa kwalli, wasu jama’a daga Malaman fiƙihu ba sa ganin shafa kwalli cikin kwalliyar da ta haramta ga mata idan sun kasance gaban wanda ba Muharraminsu ba, sannan makruhi ne shafa kwalli ga masu azumi idan ƙamshinsa ko ɗanɗanonsa zai kai ga maƙogaransu, haka kuma wasu adadin Malamai suna ganin kwalli yana hana isar ruwa zuwa ga jikin mai alwala yayin da yake alwala, Malaman fiƙihu suna ƙirga shafa cikin abbubuwan da aka haramta bayan ɗaura Ihrami.

Sanin Mafhumi

Kwallin Sarmadan yana daga jinsin duwatsu da yake ta’allaƙa da ƙarni na 4-6 h ƙamari da yake danganewa da Iran da ƙasashen Asiya ta tsakiya. Shafa kwalli a idanu wanda ake kiransa a fiƙihu da “Iktihal” [1] ɗaya ne daga kayayyakin ado [2] kuma ɗaya ne daga ayyukan mustahabbai da maza da mata suke shafa shi a idanu. [3] Cikin masadir ɗin muslunci ana kallon kwalli ɗaya daga sunnonin Annabi (S.A.W) a cikin tarihin rayuwarsa, [4] haka A’imma (A.S) suma sun yi wasicci da amfani da kwalli [5] suna ganinsa matsayin alamomin Imani [6] sun kasance suna kwaɗaitar da Sahabbansu da shafa kwalli, [7] wasu ba’arin litattafan riwayoyi sun keɓance fasali guda da ya tattaro riwayoyin da suke Magana kan shafa kwalli a idanu. [8] Iktihal (Shafa kwalli) a luggance yana nufi shafa wani abu a saman idanu, [9] ko kuma duk wani abu mai amfani da aka shafa shi cikin idanu domin magani. [10]

Hukunce-hukuncen Kwalli

Tandun kwalli na dutse na Iran a karni na hudu zuwa shida bayan hijira da yake

Cikin babukan fiƙihu an yi Magana game da shafa kwalli a idanu: Cikin hukunce-hukuncen Tufafi Wasu adadin Malaman fiƙihu basa ƙirga shafa kwalli cikin ado da aka haramtawa mata shafawa a gaban waɗanda ba muharramansu ba. [11] haka wasu ba’arin masu bincike suna ganin shafa kwalli cikin misdaƙan

«إِلّا ما ظَهَرَ مِنْها»

Sai abin da ya bayyana daga gareta. Ado wanda ba wajibi ne a ɓoye shi gaban waɗanda ba muharramai ba, cikin ayar:

«وَ لا یبْدِینَ زِینَتَهُنَّ إِلّا ما ظَهَرَ مِنْها»

Kada su bayyanar da adonsu sai abin da ya bayyana daga gareta. [12] kwalli yana daga ciki [13] cikin tafsirin ayar da aka ambata an naƙalto riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) [14] da Imam Baƙir (A.S) [15] cewa shafa kwalli yana da ado da ƙawata ta zahiri kuma abu ne da ya halasta ga mata

Shafa Kwalli A Lokacin Ihrami

Akwai saɓanin ra’ayoyin Malamai cikin haramci ko makruhancin amfani da baƙin kwalli a lokacin da aka ɗaura Ihrami, [16] wasu adadin Malaman fiƙihu suna ganin hamarcin shafa kwalli ga maza da mata [17] bayan ɗaura ihrami, [18] ko da kuwa babu niyya ado da ƙawata, [19] amma tare da haka idan ya zamana wani ya tilastu da amfani da kwalli alhalin yana cikin ihrami to ba zai zama haramun ba. [20] Wasu daga Malamai sun yi da’awar ijma’i da shuhura dangane da haramcin amfani da kwalli halin ihrami, [21] duk da cewa Shaik ɗusi yana ganin haka a matsayin makruhi ba haramun ba, [22] cikin ba’arin littafan riwaya misalin Wasa’ilul Shi’a, [23] Mustadrak Al-Wasa’il [24] akwai fasali mai cin gashin kansa da ya tattaro riwayoyin haramcin shafa kwalli a lokacin Ihrami. Wasu ba’arin Malaman fiƙihu sun tafi kan cewa babu kaffara kan wanda ya shafa kwalli a halin ihrami, amma idan ya zama kwallin yana da daddaɗano da ƙamshi bisa fatawa dole ne ya bada kaffara. [25]

Cikin Sallah Da Azumi

Wasu adadin Malamai sun halasta shafa kwalli a halin azumi, wasu kuma suna ganinsa matsayin abin da yake karya azumi, [26] amma wasu adadi daga Malaman fiƙihu sun ce idan ya zamana ƙamshi ko ɗanɗanon kwalli zai tsallaka zuwa makogaro to makruhi ne shafa shi. [27] Wasu ba’ari suna ganin kwalli yana hana ruwa isa ga jikin mai alwala. [28]

Fa’idoji

Cikin riwayoyin muslunci an yi ishara kan fa’idojin shafa kwalli, [29] a wani gutsire daga riwayoyi an yi wasicci da amfani da kwalli domin rigakafi [30] da kuma maganin wasu ba’arin cututtukan idanu, [31] cikin wani gutsire daga wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) shafa kwalli da daddare yana da amfani ga jiki sannan kuma cikin yini yana kasancewa ado, [32] Girman gashin ido, kaifin ido, [33] kawar da kura daga idanu, [34] taimakawa rayuwa da daddare, [35] doguwar sujada, [36] da hasken fuskar mutum ta hanyar shafa kwalli yayin barci, [37] duka sunan daga fa’idojinsa. Cikin ba’arin riwayoyi an yi ishara zuwa ga jinsin kwalli [38] [yadahst 1] gwargwadon wanda za a shafa [39] lokacin shafa shi [40] da kuma keɓantacciyar addu’’a da ake yi a lokacin shafa shi. [41] [yadasht 2]

Bayanin kula

  1. Vojdani Fakhr, Al-Jawahar al-Fakhriyya, 1426 AH, juzu'i na 4, shafi na 255.
  2. Ameli, Ma'alim Al-Din, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi na 906; Jam'i Az Mualllifan, Mujallar Ahlul Baiti Fiƙh, ƙum, juzu'i na 22, shafi na 69.
  3. Noori, Mustadrak al-Wasail, 1408H, juzu'i na 1, shafi na 396.
  4. Noori, Mustadrak al-Wasail, 1408H, juzu'i na 1, shafi na 396.
  5. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 6, shafi na 493.
  6. Hurru Amili , Hidaya Al-Ummah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 150; Tabarsi, Makarem al-Akhlaƙ, 1412 AH, shafi na 46.
  7. Hurru Aamili, Hidaya Al-Ummah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 149.
  8. Misali, koma zuwa: Kulaini, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi na 6, shafi na 493.
  9. Ibn Manzoor, Lasan al-Arab, 1414 AH, juzu'i na 11, shafi na 584; Mahmoud, Ma'jam Almustalahat, Mujalladi na 1, shafi na 270.
  10. Azdi, Kitab al-Ma'a, 2007, juzu'i na 3, shafi na 1102; Zubeidi, Taj al-Arus, 1414H, juzu'i na 15, shafi na 649.
  11. Misali, duba: Imam Khumaini, Tauzihul al-Masa'il (Mohshi), 1424H, juzu'i na 2, shafi na 928-929.
  12. Suratul Nur, aya ta 31.
  13. Jam'i Az Muallifan, Mujallar Ahlul Baiti Fiƙh, ƙum, juzu'i na 54, shafi na 155.
  14. Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 5, shafi na 521; Faiz Kashani, Tafsir Al-Safi, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi.430; ƙureshi, ƙamus Kur'ani, 1412 AH, juzu'i na 3, shafi na 197.
  15. ƙomi, Tafsir ƙommi, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi 101; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 101, shafi na 33.
  16. jam' Az fajuheshgaran, Mausu'ati Fiƙhu Islami, 1423, juzu'i na 6, shafi na 613.
  17. Jam'i az Fajuheshgaran, Mausu'atu Alfikhi Al-Islami, 1423 AH, juzu'i na 6, shafi na 613; Imam Khumaini,Manasik Hajji, Bita, shafi na 101; Khamenei, Manasik Hajji, Beta, shafi na 26.
  18. Wadjani-Fakhr, Al-Jawahar Al-Fakhriyyah, 1426 AH, Mujalladi na 4, shafi na 255; Sheikh Ansari, Manasik Haji Mohashi, 1425 AH, shafi na 36; Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, ƙum, juzu'i na 1, shafi na 422; Khamenei, manasik Hajji, Beta, shafi na 26; Vahid Khorasani, Manasik Hajji, 1428H, shafi na 124; Mahmoudi, Manasik Umrah Mufrsdeh Mohashi, 1429 AH, shafi na 65-66.
  19. jam'i az Fajuheshgaran, Mausu'atu Al-Fiƙh Al-Islami, 1423 AH, juzu'i na 6, shafi na 613; Imam Khumaini, manasik Hajji, Bita, shafi na 101; Khamenei,Manasik Hajji, Beta, shafi na 26.
  20. Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, ƙum, juzu'i na 1, shafi na 422; Mahmoudi, Manasik Umrah Mufradeh Mohashi, 1429 AH, shafi na 65-66.
  21. Jam'i az Fajuheshgaran, Mausu'atu Al-Fiƙh Al-Islami, 1423 AH, juzu'i na 6, shafi na 613.
  22. Tusi, Al-Jamal wa Al-Aƙod, 1387H, shafi na 136.
  23. Hurru Amili, Wasa'il Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 12, shafi.468
  24. Nouri, Mostadrak Al-Wasail, 1408H, juzu'i na 9, shafi na 217.
  25. Wadjani-Fakhr, Al-Jawahar Al-Fakhriyyah, 1426 AH, Mujalladi na 4, shafi na 255; Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, ƙum, juzu'i na 1, shafi na 422; Mahmoudi,Manasik Umrah Mufradeh Mohashi, 1429 AH, shafi na 65-66.
  26. Lari, Majmu'eh Maƙalat, 1418 AH, shafi na 591.
  27. Jam'i az Fajuheshgaran, Farhang Fiƙh, 1426 AH, juzu'i na 3, shafi 178; Imam Khumaini, Tauzihul Al-Masa'ili, 1426H, shafi na 345.
  28. Fayyaz, Risala tauzihul Al-Masa'il, 1426H, shafi na 40.
  29. Misali, duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi.492; Sheikh Sadouƙ, Thawab Al-Amal, 1406H, shafi na 22.
  30. Sheikh Sadouƙ, Thawab Al-Amal, 1406H, shafi na 22.
  31. Abna Bastam, ɗibbul Al'imma, 1411H, shafi na 83; Ɗabarasi, Makarem Al-Akhlaƙ, 1412 AH, shafi na 46.
  32. Ameli, Ma'alim Al-Din, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi na 906; Majlesi, Lowame Sahib Al-ƙarani, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 461.
  33. Ɗabarasi, Makarem Al-Akhlaƙ, 1412 AH, shafi na 45.
  34. Ibn Hayyun, Da'aim al-Islam, 1385 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 146.
  35. Tabarsi, Makarem al-Akhlaƙ, 1412 AH, shafi na 45.
  36. Majlesi, Lowa'me Sahib al-ƙarani, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 461.
  37. Sheikh Sadouƙ, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 1, shafi na 237
  38. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 6, shafi na 493.
  39. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 59, shafi na 287.
  40. Misali duba: Tabarsi, Makarem al-Akhlaƙ, 1412 AH, shafi na 46.
  41. Tabarsi, Makarem al-Akhlaƙ, 1412 AH, shafi na 47.

Nassoshi

  • Ibn Hayoun, Nu'man bin Muhammad al-Maghrebi, Da'im Al-Islam wa Zikr Halal wa Haram wa Al-ƙadaya wa Al-Ahkam, ƙum, Al-Bait Institute (A.S.), bugu na biyu, 1385H.
  • Ibn Manzoor, Muhammad Bin Makram, Lasan al-Arab, Beirut, Darul Fikr Lalprinta da Al-Nashar da Al-Tawzi’ah, 1414H.
  • Abna Bastam, Abdullah da Hossein, ɗibbu Al-Imam (a.s.), ƙum, Dar al-Sharif al-Razi, bugu na biyu, 1411H.
  • Azdi, Abdullah bin Mohammad, Kitab al-Ma'a, Tehran, Cibiyar Tarihin Likitanci, Magungunan Musulunci da Ƙarin Magunguna - Jami'ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Iran, 2007.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah Musawi, Manasik Hajji, bija, bita.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah Mousavi, Tahrir Al-Wasila, ƙum, Dar al-Alam Press Institute, Beta.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah Musawi, Tauzihul Al-Masa'il (Mohashi - Imam Khumaini), ƙum, Ofishin Daba'ar Musulunci, bugu 8, 1424H.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah Musawi, Tauzihul Almasa'il, Bija, 1426H.
  • Jam,'i az Fajuheshgaran,e karkashin kulawar Shahroudi, Sayyid Mahmoud Hashemi, al'adun fikihu bisa addinin Ahlul-Baiti (AS), ƙum, Cibiyar Nazarin Shari'ar Musulunci ta Addinin Ahlul Baiti (AS), 1426H. .
  • Jam,'i az Fajuheshgaran, Shahroudi, Sayyid Mahmoud Hashemi, Encyclopedia of Islamic Jurisprudence bisa ga addinin Ahlul-Baiti (AS), ƙum, Cibiyar Nazarin Fikihu Kan Addinin Ahlul Baiti (AS), 1423 AH.
  • Rukunin marubuta, Mujallar fiƙihu Ahlul Baiti (a.s.), Farsi, Cibiyar Nazarin Fikihu ta Addinin Ahlul Baiti (a.s.), Bita.
  • Hurru Amili, Muhammad bin Hassan, JWasa'ilul Al-Shi'a, Mashhad, kungiyar bincike ta Musulunci, 1412H.
  • Hurru Amili, Muhammad bin Hasan, Wasa'il Al-Shi'a, ƙum, Al-Bait Institute (A.S.), 1409H.
  • Khamenei, Sayyid Ali,manasik Hajji, Bija, Bita.
  • Zubeidi, Mohammad Murtaza, Taj al-Aros Man Jawaher Al-ƙamoos, Beirut, Dar al-Fikr, 1414 AH.
  • Sheikh Ansari, Morteza, Manasik Hajji (Mohashi), ƙum, Majmael al-Fikr al-Islami, 1425 AH.
  • Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Al-Khisal, ƙum, Jamia Modaresin, 1362.
  • Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Thawabul Al-Amal, ƙum, Darul Sharif al-Radhi, bugu na biyu, 1406H.
  • Tabarsi, Hasan bin Fazl, Makarem al-Akhlaƙ, 1412 AH, ƙom, Al-Sharif Al-Razi, bugu na 4, 1412H.
  • Tousi, Mohammad Bin Hassan, Al-Jamal wa Al-Aƙud fi Al-Ibadat, Mashhad, Jami'ar Bubbuga Jami'ar Ferdowsi, 2007.
  • Ameli, Hasan bin Zain al-Din, Ma'alim al-Din da Muladh al-Mujtahidin (Ma'aikatar Shari'a), ƙum, Mu'assasar Buga da Bugawa ta Al-Fiƙh, 1418H.
  • Faiz Kashani, Mohammad Bin Shah Mortaza, Tafsir Al-Safi, Bincike na Hossein Alami, Tehran, Al-Sadr School, 1415 AH.
  • ƙurashi, Sayyid Ali Akbar, Kamus ƙur'an, Tehran, Littattafan Musulunci, bugu na 6, 1412H.
  • ƙommi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsir ƙommi, bincike na Tayyab Musavi Al Jazeari, ƙum, Dar al-Kitab, 1404H.
  • Fayyaz, Mohammad Ishaƙ, Tauzihul Al-masa'il, ƙum, Majlisi Publications, 1426H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, Al-kafi, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, 1407H.
  • Lari, Seyyed Abdul Hossein, Majmu Maƙalat, ƙum, Al-Maarif Islamic Foundation, 1418H.
  • Majlesi I, Mohammad Taƙi, Sahib Al-ƙarani, ƙum, Cibiyar Ismailiya, bugu na biyu, 1414 AH.
  • Majlesi, Mohammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Mahmoud, Abdur Rahman, Al-Tarmidhom wa Al-Alfaz al-Fiƙhiyyah, Bija, Bita.
  • Mahmoudi, Mohammad Reza, Manasik Umrah Mufrada (Mohashi), ƙum, Mashaar Publishing House, 1429 AH.
  • Nouri, Mirza Hossein, Mustadrak al-Wasail da Mustanbat al-Masal, Beirut, Al-Al-Bayt Institute (AS), 1408H.
  • Wajdani Fakhr, Ikon Allah, Al-Jawahar al-Fakhriyyah fi Sharh Al-Rauda al-Bahiya, ƙom, Sama ƙalam Publications, bugu na biyu, 1426H.
  • Vahid Khorasani, Hossein, Hajji, ƙum, Madaraseh Al-Imam Baƙir Al-Uloom (A.S.), bugun 4, 1428H.