Kishi
Kishi, (Larabci: الغيرة) yana daga kyawawan Dabi’u masu tarin Falala wanda cikinsa ne Mutum yake Mikewa tsaye kan Kare Mutuncinsa dana Iyalinsa, Addininsa haka ma Kasarsa da Dukiyarsa, kan asasin Riwayoyi, Nuna Kishi yana daga cikin Siffofin Allah, Malam Mulla Ahmad Naraki a cikin Littafin Mi’rajul As-Sa’ada yace: samsam Bai kamata ba a samu Mumini da Gafala kan Iyalansa cikin lamarin da karshen zai jawo Fasadi bai kamata su yi sako-sako da sakaci ba cikinsa, sannan Malamin ya na ganin yin Umarni da kyakkyawa da hani da Mummuna da tashi tsaye kan Kalubalantar Bidi’a suna daga Misdakan Kishi. Cikin riwayoyin Shi’a Kame kai da Samun Katanguwar Iyali da tabbatuwarsu daga barin afkawa cikin Fasadi suna daga Kufaifayin Kishi, haka kuma cudanyar wadanda ba Muharraman Juna ba, sauraren Wakokin Haram, Kallon wanda ba Muharram aba, Shan Barasa (Giya) suna daga Illoli da suke haifar da rashin Kishi. Kan Asasin wata riwaya daga Imam Ali (A.S) ya bayyana ceewa hakika shima Wuce gona da iri cikin Nuna Kishi zai iya Haifar da Natija da sakamako mara kyau.
Sanin Mafhumi
Kishi a Sakafar Muslunci ana kidaya shi matsayin wani take ne na Falala da Daraja ta Kyawawan Dabi’u [1] cikin Mutum na tsayu Kyam kan Kare Mututncinsa da Addininsa, Mazhabarsa, Dukiyar da Kasarsa [2] Kalmar Giratu (Kishi) ba a yi amfani da ita ba Kai tsaye cikin Alkur’ani, sai dai kuma Ayatullahi Nasir Mukarim Shirazi daga Maraji’an Shi’a kuma Babban Malamin Tafsirin Alkur’ani, yana ganin aya ta 60-62 Suratul Ahzab [Tsokaci 1] ayoyi ne da suke bayani kan Mafhumin Kishi, Hakika Muslunci yayi barazanar yi Ukuba Mai tsanani Kan Munafukai, Masu tsatar Zukata, da Masu Yada jita-jita dangane da Kamammun Mata, ukubarsu ta Kasance misalign Kisa da Korarsu daga Gari. [3] Kan asasin Riwayoyin Shi’a Nuna Kishi Sifface ta Allah kuma hakika Ubangiji baya son Mutum Mara Kishi [4]kan asasin wasu riwayoyi An La’anci Mazan da Basu da Kishi. [5]
Nau’ukan Kishi da Misdakansa
Mulla Ahmad Naraki, Malamin Fikihu a karni na Goma sha uku h Kamari, a cikin littafin Mi’irajul As-Sa’ada, kari kan Kishi kan Mata, yayi bayani kan Kishi domin Addini, Kishi don kare Mutunci da Dukiya. A Akidar Mulla Ahmad Naraki bai kamata Muminai su gafala daga barin Iyalansu ba musammam ma cikin al’amarin da karshensa zai Haifar da Fasadi, kwata-kwata bai kamata a same da sakaci ba cikinsa, [6] Naraki ya cigaba Yin Umarni da Kyakkyawa da Hani da Mummuna komai kankantarsa yana daga cikin Alamomin Kishi [7] Husaini Mazahiri daga Maraji’an Taklidi na Shi’a kari kan nuna Kishin Mutum da aka yi wasicci da shi cikin riwayoyi, ya kawo wasu wuraren daban kan Kishi, daga jumlarsu akwai Nuna Kishin Al’umma kan naki dayan Mata [8] Kishin Kasa da Gari, ma’ana nuna soyayya ga Kasarka da kuma aiki domin cigabanta [9] Kishin Addini ma’ana bada kariya ga alfarmar Addini. [10] An ambaci Illolin da suka haifar da Rashin Kishi a cikin Riwaya, daga Jumlarsu akwai, cudanyar Maza da Mata wanda ba Muharramai ba. [11] [Tsokaci 2], Sararen Wakokin Haram, [12][Tsokaci 3] kallon wanda ba Muharrami ba, [13] Shan Barasa, [14] [Tsokaci 4] cin Naman Alade, [15] [Tsokaci 5]
Kufaifayin Kishi da Tasirinsa da Fa’idojinsa
Kufaifayin Kishi da Tasirinsa da Fa’idojinsa an ambace su cikin riwayoyin Ma’asumai:
- Kamai Kai: ance idan mutum yana ganin Mutuncin kansa to zai nuna kishin kan wannan Mutunci nasa, ba zai taba bawa kansa izinin keta alfarmar Mutuncin wasu ba [16] riwaya daga Imam (A.S) ta zo dangane da haka cewa: (Mutum Mai Kishi bait aba aikata Zina) [17]
- Katange kai daga Fasadi: kamar yanda rashin Kishi da nuna ko in kula yake haifar da dama ga fasadi, haka nuna Kishi da damuwa da kulawa suke hana yaduwar Fasadi, [18]
- Katanguwar Iyali: Nuna Kishi yana haifar da tabbatuw ada Katanguwar Iyali, saboda Al’umma da take da Mazaje masu Kishi Lalatattun Mutane ba sa samun damar Mike Kafa cikinsu, sannan Kamammun Mata zasu samu nutsuwa da kwanciyar hankali cikin wannan Al’umma. [19]
Wuce Gona da Iri cikin Nuna Kishi
Annabi (S.A.W):
اَلا وَ اِنَّ اللهَ حَرَّمَ الْحَرامَ وَ حَدَّ الحُدودَ وَ ما اَحَدٌ اَغْیرَ مِنَ اللهِ وَ مِنْ غَیرَتِهِ حَرَّمَ الْفواحِشَ. ku saurara lallai Allah ya haramta haram ya iyakance iyakoki, babu wani mutum da ya wuce Allah kishi kuma daga kishinsa ne ya haramta alfasha.
Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 73, shafi na 332.
Cikin riwayoyin da aka nakalto daga Ma’asumai, anyi hani kan Kishi Mara tsari, da mummunan zato, da neman faka da za a samu lefin mace, saboda yin hakan zai haifar da Natija mara kyawu wacce za ta iya haifar da Fasadi, [20] dangane da haka an jigina da wata Jumla a cikin wasikar da Imam Ali (A.S) ya rubutawa `dansa Imam Hassan (A.S): (kayi taka tsantsan ka da kayi kishi a mahallin da bana sa ba, saboda yin kishi a mahallin da bana sa yana kora Kamammiyar Mace zuwa Kazanta da rashin kame kai) [21] [Tsokaci 6] Haka zalika cikin wata Riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) na kore yin Kishi ciki Abinda yake Halal (La Girata Fil Al-Halal) [22]
Nazari
Anyi wallafe-wallafe daban-daban kan Maud’in Kishi, daga Jumlarsu akwai:
- Gohare Girat< talifin Fatima A’azami. Markaz Hifzi wa Nashar Arzeshahaye Difa Mukaddas, Isfahan shekara 1390 h shamsi.
- Mukamu Girat Dar Akhlak wa Irfani Islami, Talifin Ali Akbar Iftkhari Fur. Nashir Asaru Madran, Shekara ta 1394 h Shamsi.
- Giratu Husaini Wa Iffat Zainabi: Muhammad Hassan Wakili, Nashir, Muassaseh Mutala’at Rahburdi Ulum Wa Ma’arif Islam, shekara 1395
- Giratu Dar Maktab Itrat: Talifin Farid Najaf Niya, Nashir Usweh shekara 1394.
- Rabideh Girat Dini Ba Amru bi Marufi wa Nahaye Az Munkar, Talifin Rida Ali Karami, Nashar Kalamga, shekara 1393 h shamsi.
Bayanin kula
- ↑ Naraghi, Jame al-Saadat, 2001, juzu'i na 1, shafi na 266; Tabatabai, Al-Mizan, 1374, juzu'i na 4, shafi na 280.
- ↑ Makarem Shirazi, Akhlak Dar Kur’an, 2013, juzu’i na 3, shafi 431
- ↑ Makarem Shirazi, Akhlak dar Kur'an , 2006, shafi na 433 da 434.
- ↑ Kulainy, Usul Al-Kafi, 1401, juzu'i na 8, sTashihu Sobhi Saleh, Hikmat 305, shafi na 529.
- ↑ Sheikh Hurrul Amili, Wasa'il Al-Shia, 1414 AH, juzu'i na 20, shafi na 235.
- ↑ Naraghi, Meraj al-Saada, Javidan Publications, shafi na 152-153.
- ↑ Naraghi, Meraj al-Saada, Javidan Publications, shafi na 152-153
- ↑ Mazaheri, Marafet Nafs, 1394, juzu'i na 3, shafi 135.
- ↑ Mazaheri, Marafet Nafs, 1394, juzu'i na 3, shafi na 137.
- ↑ Mazaheri, Marafet Nafs, 1394, juzu'i na 3, shafi na 138.
- ↑ Hurrul Ameli, Wasal al-Shia, juzu'i na 14, shafi na 174
- ↑ Har Ameli, Wasa'il al-Shia, Kitabul Bay'u, Babi na 100, 1414 AH, Juzu'i na 12, P. 232, H1; Kulainy, Usul Kafi, 1401 AH, juzu'i na 6, shafi na 655, h14.
- ↑ Noori, Mostadrak al-Wasail, 1408 AH, juzu'i na 14, shafi na 268.
- ↑ Har Ameli, Wasa'il Al-Shia, 1414 AH, juzu'i na 17, shafi na 253.
- ↑ Boroujerdi, Tafsir Jame, 1366, juzu'i na 2, shafi na 156.
- ↑ Akbari, Giratmandi wa-Asibha, 1390, shafi na 38.
- ↑ Nahj al-Balagha, Tashihu Sobhi Saleh, Hikmat 305, shafi na 529.
- ↑ Akbari, Giratmandi wa-Asibha, 1390, shafi na 38
- ↑ Akbari, Giratmandi wa-Asibha, 1390, shafi na 40-41
- ↑ Amadi, Ghurar al-Hekam wa Durar Al-Kalam, 1410 AH, 2704 H, shafi na 169; Jazayeri, Durus Akhlak Islami, 2008, shafi na 163.
- ↑ Amadi, Ghurar Al-Hekam, 1410 AH, 2704 H, shafi na 169.
- ↑ Abdus, Binsto Panj Asle Az Usuli Akhlaki imaman, 1377, shafi na 313.
Tsokaci
- ↑ لَئن لَم ینَتهِ المُنافِقُونَ و الّذین فی قلوبهم مَرَضٌ و الُمُرْجِفُونَ فی المدینة لَنغرینَّکَ بِهِم ثُمَّ لایجارونَکَ فیها اِلاّ قلیلاً مَلعُونینَ اَینَما ثَقفوا اُخِذُوا و قُتّلِوُا تقتیلاً سُنَّةَ اللهِ فی الّذین خَلَوا مِن قَبلُ و لَن تَجِدَ لِسُنَّةِ الله تبدیلاً.
- ↑ Imam Ali(A.S) na samu labari cewa matanku suna cudedeniya da maza a kan hanaya? shin baku jin kunya ne,Allah ya tsinewa wanda baya kishi.(Hurrul Ameli, Wasa'il al-Shia, juzu'i na 14, shafi na 174).
- ↑ Idan wani Shiadani mai suna Al-Qafandar ya kada garaya gidan mutum safiya arba'in sai mazaje suka shiga cikin wannan gida hali ya kasance haka... to ba zai yi kishi ba bayan haka.
- ↑ Mufadl ya tambayi Imam Sadik (a.s.): Me ya sa Allah ya haramta giya? Imam ya ce: Domin giyar tana sa mai sha'awarta ya girgiza. tana kawar da haskensa da basirarsa, yana lalatar da mutuncinsa, kishi, da kishinsa, yana sa shi ƙarfin hali ya yi zunubi, ya kashe marasa laifi, ya yi zina.
- ↑ Wani mutum ya tambayi Imam Sadik (AS) me ya sa Allah ya haramta naman alade? Imam ya ce: Allah Ta’ala bai sanya wani abu halal ba, kuma bai sanya wani abu da ya haramta ba, face ya kare maslahar mutane. An haramta naman alade saboda yana haifar da rashin kishi da lalata (Boroujerdi, Tafsir Jame, 1366, Vol. 2, shafi 156).
- ↑ Na haneka da yin kishi ba mahallinsa ba, lallai hakan yana janyo lafiyayye zuw ciwo, mara laifi zuwa ga kwakwanto(Amadi gurarul Al-hikam,1410 Q. hadisi 1704. shafi na 169
Nassoshi
- Akbari, Mahmoud, Giratmandi wa-Asibha, Qom, Fethian, 1390.
- Boroujerdi, Seyyed Mohammad Ebrahim, Tafsir Jame, Tehran, Sadr Publications, 1366.
- Jazayeri (Al-Ghafoor), Mohammad Ali, Durus Akhlak Islami, Qum, Qum Seminary Management Center, 2008.
- Hurrul Amili, Muhammad bin Hasan, Wasa'il Al-Shi'a, Kum, Al-Bait, 1414H.
- Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Mohammad Baqer Mousavi ya fassara, Qom, Islamic Publishing House, bugu na biyar, 1374.
- Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bugun Ali Akbar Ghafari, Beirut 1401H.
- Makarem Shirazi, Nassar, Akhlak dar Kur'an, Qum, Makarantar Imam Ali Ibn Abi Talib (AS), 1387.
- Naraghi, Ahmed, Mi'raj Al-Saada, Qom, Hijira, 1377.
- Naraghi, Mahdi bin Abi Dhar, The Science of Islamic Ethics: Translation of Jame Al-Saadat, Fassarar Jalaluddin Mojtaboi, Tehran, 2001.
- Nouri, Mirza Hossein, Mostadrak Al-Wasa'il, Beirut, Al-Bait Lahiya al-Trath Foundation, 1408 AH.
- Nahj al-Balagheh, Tashihu Sobhi Saleh, Beirut, Dar al-Kitab al-Lebanani ya gyara, 1980.
- Nahj al-Fasaha, Sukhnoni Payambar, wanda Abu Abulqasem Payandeh ya rubuta, Abdolrasul Peymani da Mohammad Amin Shariati suka gyara kuma suka gyara, Isfahan, Khatam al-Anbia, 1383.