Muɗahhirat
- Wannan wat Kisada ce mai bayani game da ra'ayi na fikihu kuma ba zata iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.
Mutahirrat, (Larabci: المطهرات) ma’ana Masu tsarkakewa, wani Isdilahi ne na FIkihu da ake amfani da shi kan wasu abubuwa da suke tsarkake abubuwan da suka tabu da Najasa, Mutahhirat suna da Rabe-Rabe daban-daban, kowanne daya cikinsu tare da cika sharuddan da aka ambata cikin litattafan fikhu yana tsarkake Najasa. Wasu ba’arin Mutahhirat sun kasance kamar haka: Ruwa, Kasa, Rana, Istihala, (canjawar Mahiyar abinda ya kasance Najasa) Inkilab (jirkicewa Barasa zuwa Tsimi) Intikal, Muslunta, tab’iyyat da kawar da ainahin Najasa.
Ta’arifi na Fikhu dangane da Mutahhirat
Mutahhirat, wasu abubuwa ne da suke zama sababin kawar da Najasa [1] Mutahhirat suna da kashe-kashe daban-daban, ance Malaman Fikhu sun kirga har adadin abubuwa guda Ashirin matsayin Mutahhirat [2]
Rabe-raben Mutahhirat
Cikin Littafan Risalolin Fikhu an bayyana abubuwan da bayaninsu zai zo a kasa a matsayin Mutahhirat: Ruwa, Kasa, Istihala, Inkilab, Intikal, Muslunta, Tab’iiyat, kawar da Gundarin Najasa, Fakuwar Musulmi, Raguwa kaso biyu cikin uku na Ruwan Tafasashshen Inibi, fitar da Jini da aka al’adantu daga gwargwadonsa daga Dabbar da aka yanka, yin Istibra kan Dabbar da take cin Najasa, [3] Hukunce-hukuncen Mutahhirat Kowanne daya daga cikin Mutahhirat tareda cika sharudda yana zama sababin tsarkakar Abubuwan da suka tabu da Najasa, a kasa ga wasu ba’arin Hukunce-hukuncen Mutahhirat:
Ruwa
Asalin Makala: Ruwa hakika Ruwa yana tsarkake duk wani abu da ya tabu da Najasa [4] tare da sharadin Kasancewar Ruwan a kankin kansa tsarkakakke ne, kuma bai kasance Muzafu ba (Ruwan ya cudanya da wani abu da ya fitar da shi daga sunan tsantsar ruwa), bayan an wanke gundarin Najasa ainahinta ya kau sannan kuma Ruwan da za tsarkaketa bai Kasance Muzafu ba, [5] hakika Ruwa yana da Rabe-rabe misalin Jari (Mai gudana) Kur (Ruwan da Nauyinsa ya kai 376-480 kg, bisa sabanin Fakihai) da kuma Kalil (Ruwa mara yawa) akwai bambanci cikin ba’arin hukuncin wasu, [6]
Kasa
Kasa, idan ta kasance Mai tsarki kuma a bushe, tana tsarkake wasu abubuwa misalin kasan Kafa da Takalmi da suka tabu da Najasa. Na’am tareda sharadin cewa idan aka tattaka kan Kasa gundarin Najasar zai fita [7]
Rana
Hakika Rana tana tsarkake Kasa da Gine-gine da wasu abubuwa misalin Taga aka dorata kan Gine-ginen Gidaje, amma fa tareda cikar sharudda guda shida [8]
Istihala da Inkilab
Istihala na nufin canjuwar Mahiyya (hakikar abu) da ya tabu da Najasa, misalin Katako idan ya canja ya zama Toka ko kuma ya zama tsutsa [9] Shi kuma Inkilab a Fikhu yana nufin Barasa (Giya) idan ta sauya ta koma Tsimi [10] na’am wasu daga Malaman Fikhu suna ganin Inkilab matsayin wani nau’i ne daga Istihala [11] Mukarim Shirazi daya daga cikin Maraji’an Taklidi yana ganin Inkilab matsayin canji ne na Sura kamar misalin sauyuwa da canjuwar Giya zuwa Tsimi, shi kuma Istihala canjuwar Mahiyya (hakikar Abu) ce misalin canjuwar Kare zuwa Gishiri. [12]
Raguwar Kaso Biyu daga uku na Tafasashshen Ruwan Inibi
Malaman FIkihu suna ganin Haramcin Shan tafasashshen Ruwan Inibi, wasu suna ganinsa matsayin Najasa. [13] Ruwan Inibi idan ya tafasa sannan kaso biyu cikin uku ya ragu sakamakon tafasarsa, to yana tsarkaka kuma ya halasta a sha shi amma tareda sharadin cewan baya bugarwa baya sanya yin Maye dajin jirwa. [14]
Intikal
Intikal yana nufin Jinin Mutum ko jinin wata Dabba da jinita nata yake tsartuwa misalin idan an yankata, to idan aka dauki wannan jini aka shigar da shi jikin wata dabbar ko wani Mutumin to jininsa ba Najasa bane amma cikin surar da zai zama ana lissafa jinin da aka shigar jikinsa matsayin Jininsa to ya tsarkaka, misalin jinin da Sauron da ya zuki jini daga jikin wani ana lissafa shi a Jinin Sauro [15]
Muslunci
Idan Kafiri ya Muslunta ya Tsarkaka. [16]
Tab’iyyat
Tab’iyyat yana nufin tsarkakar wani abu Najasa da tsanin Tsarkakuwar wani abu da ya tabu da Najasa, misali idan Kafiri ya Muslunta to `ya`yansa za su biyo shi cikin tsarkaka sakamakon tsarkakarsa, idan Giya ta canja ta zama Tsimi to Kwanon da take cikin shima zai bita cikin tsarkakuwa [17]
Kawar da Najasa
Asalin Makala: Kawar da Najasa Kawar da gundarin Najasa shi ne kawar da ainahin Najasar da take jikin wani abu, kawar da Najasa tana tsarkakewa a wasu wurare, daga jumlarsu shi ne idan Jikin Dabba ya tabu da Najasa, idan aka kawar da ainahin Najasar daga jikin Dabbar ya wadatar ba sai an wanketa da ruwa ba. [18]
Istibra’in Dabbobin da suke cin Najasa
Dabbobin da ya halasta aci Namansu da suka Al’adantu kan cin Najasa Fitsari da Kashinsu Najasa ne, domin tsarkake su dole ayi Musu Istibra’i, ma’ana a daure su tsawon wani lokaci a hana su cin Najasa, kowacce Dabba akwai kwanakin da ake tsare da hanata cin Najasa, [19]
Fakuwar Musulmi
Idan Jiki ko Tufafin Musulmi ko wani abu da ya kasance Mallakinsa ya tabu da Najasa, sannan tsawon lokaci bamu ganshi ba, idan ya zamana muna tsammanin ya tsarkake su, sai mu yi gini kan haka mu tafi kan cewa ya tsarkake su din [20]
Fitar da Jini da Muka Saba da Shi Daga Jikin Dabbar da Aka Yanka
Bayan Yankan Shari’a, Hakika Dabbobin da Namansu ya Halasta a ci bayan lokacin da suke Raye Jini Ya fita daga Jijiyoyinsu bayan Yanka su kuma Jini ne da aka saba ganin Fitar Irinsa to sauran Jinin da ya ragu cikin Dabbar Ba Najasa bane tsarkakakke ne. [21]
Bayanin kula
- ↑ Meshkini, Mustalahat Al-Fikhi, 1392, shafi na 528.
- ↑ Mu'assaseh Dayiratul Almaref Fkh Islami, Farhang Fiqh, 1387, juzu'i na 5, shafi na 239
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 99.
- ↑ Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1392, juzu'i na 1, shafi na 132.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 99.
- ↑ Imam Khumaini, Tahrir Al-Wasila, 1392, Vol.1, PP. 132-133.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 114.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 99
- ↑ Mashkini, Mustalaht Al-Fikhi, 1392, shafi na 70.
- ↑ ,Mu'assaseh Dayiratul Almaref Fkh Islam Farhang Fiqh, 1387, juzu'i na 1, shafi na 742.
- ↑ Mu'assaseh Dayiratul Almaref Fkh Islam Farhang Fiqh, 1387, juzu'i na 1, shafi na 742.
- ↑ <a class="external free" href="https://www.makarem.ir/main.aspx?typeinfo=21&lid=0&catid=0&mid=273090#:~:text=پاسخ%20%3A%20انقلاب">https://www.makarem.ir/main.aspx?typeinfo=21&lid=0&catid=0&mid=273090#:~:text=پاسخ%20%3A%20انقلاب</a>
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 122.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 122.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 125.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 126.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 127.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 129.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 131.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Almasa'il, 1381, juzu'i na 1, shafi na 132.
- ↑ Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1409 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 146.
Nassoshi
- * Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir Al Wasila, Tehran, Imam Khumaini Editing and Publishing Institute, 1392.
- Bani Hashemi Khomeini, Sayyid Mohammad Hassan, Tauzihul Al-Masa'il Maraji, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na Qum Seminary Society, 1381.
- Meshkini Ardabili, Ali, Mustalahat Al-Fiqh, Qum, Darul-Hadith, 1392.
- Muassaseh Dayiratul Alma'arif Fikihu Islami, Farhang fikihu Mutabik Ahlul Baiti, Qum, Cibiyar Muassaseh Dayiratul Alma'arif Fikihu bar mazhab Ahlul Baiti, 2007.