Karkacewa Alƙibla

Daga wikishia
ƙasidar karkacewa daga alƙibla da ƙasidar canja alƙibla ko kuma ƙasidar alƙiblar musulmai ƙasidu ne duka da suke da alaƙa da juna

wannan ƙasida wani rubutu ne na siffantawa game da wata ma’ana ta fiƙihu, wannan ƙasida ba zata iya zama ma’auni game da ayyukan addini ba, domin ayyukan sai a koma zuwa ga wasu madogara daban.

karkacewa daga alƙibla(Larabci:الانحراف عن القبلة،) isɗilahi ne na fiƙihu da yake ɗaukar ma’anar mutumin da ya karkace da fuskar alƙibla, mas’alar karkacewa alƙibla wata mas’ala ce da aka bijira kan bahasinta a modagaran fiƙihu game da ayyukan addini misalin sallah, hajji, layya da kuma hukunce-hukunce keɓewa (biyan buƙatu). Malaman fiƙihu suna ganin karkacewa alƙibla a ba’arin ayyuka ibada misalin sallah yana haifar gurɓatar wannan aiki, haka nan daidai da fatawarsu wajibi a karkacewa alƙibla yayin keɓewa(biyan buƙata).

Ma’ana da Matsayi

Musulmai suna kiran ka’aba da fuskar da take da sunan alƙibla[1] abin da ake nufi da karkacewa alƙibla shi ne cewa a al’adance.[2] (bawai bisa dandaƙewar hankala a haƙiƙance ba),[3] ya zama mutum bai fuskanci alƙibla ba.[4]

Malaman fiƙihu cikin da yawa-yawan taklifin shari’ar addinin muslunci, misalin sallah, hajji, azumi, layya, hukunce-hukuncen keɓewa (biyan buƙata) da hukunce-hukunce matattu sun tsunduma bahasi cikin maudu’in fuskantar alƙibla, kuma rashin kiyaye shi yana sanya ɓacin ba’arin wasu ayyukan ibada.[5] A wurin wasu malamai fuskantar alƙibla da rashin karkacewa daga ita, ƙari kan kasancewarsa ɗa’a da biyayya ga umarnin ubangiji, wani abu ne da yake haɗa kawukan musulmai.[6]

Domin samun ƙarin bayanai ku duba: Alƙibla da kuma Fuskantar Alƙibla

Hukunce-hukuncen Fiƙihu Game da Karkacewa Alƙibla

Malaman fiƙihu suna ganin karkacewa alƙibla yana lalata ba’arin ayyukan ibada, kuma suna lissafa karkacewa alƙibla cikin ba’arin wasu ayyuka matsayin abin da yake wajibi ko haramun.[7]

  • Idan ya zama mai sallah ya karkacewa alƙibla bisa ganganci, da yadda ba za a ce ya fuskanci alƙibla ba, ko kuma ya zamana kansa ya juya hagu ko dama, sallarsa ta lalace,[8]

Amma idan ya zamana ya karkace ne bisa mantuwa da rafkana kuma bai haura daraja 90 ba, sallarsa ta inganta.</ref> ولی اگر انحراف از قبله سهواً بوده و کمتر از ۹۰ درجه باشد، نماز صحیح است.[9] haka nan karkacewar kansa kaɗan babu matsala a ciki.[10]

  • Yayin yanka dabba, wajibi ne gaban jikin dabba ya fuskanci alƙibla.[11] saɓanin haka dabbar da aka yanka za ta kasance najasa kuma haramun ne cin namanta.[12] na’am idna ya zamana sakamakon mantuwa ne ko rashin sani ya zama an yanka dabbar ba tare da fuskantar alƙibla ba, yankan ya inganta.[13] madogarar wannan hukunce wasu riwayoyi ne,[14] da kuma Ijma’i.[15]
  • Wajibi ne a karkacewa alƙibla yayin keɓewa,[16] fuskantar aƙibla da bata baya a wannan hali ya

haramta.[17]

  • Yayin ɗawafi daura da ka’aba, wajibi ne kafaɗar hagun mai ɗawafi ta kasance gefen ka’aba,[18] kuma a al’adance ya zamana bai karkace mata ba.[19]

Bayanin kula

  1. Rajeb Esfahani, Mufradat alfaz Alqur'an, 1404 AH, shafi 392; Najafi, Jawahirlu al-Kalam, 1362, juzu'i na 7, shafi na 320.
  2. Mohaghegh Hilli, Al-Mutabar, 1363, juzu'i na 2, shafi 65; Ardabili, Majma Al-Faideh, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 57; Najafi, Jawahirul al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 7, shafi.329; Ruhani, Fiqhu Sadik, 1413 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 90.
  3. Mohaghegh Hilli, Al-Mutabar, 1363, juzu'i na 2, shafi 65; Ardabili, Majma Al-Faideh, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 57; Jawahirul al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 7, shafi na 329; Ruhani, Fiqhu Sadik, 1413 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 90.
  4. Tusi, Al-Khilaf, 1418 AH, Juzu'i na 1, shafi na 295; Najafi, Jawahirul al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 7, shafi.328; Hakim, Mustamsk al-urwa, 1404 AH, juzu'i na 5, shafi na 176 zuwa 179.
  5. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Wuhtghati, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 310-313; Meshkini, Mustalahat Fiqhi, 1392, shafi na 415.
  6. Tabataba'i, Tafsir al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi.337; Makarem Shirazi, TafsirNamuneh, 1374, juzu'i na 1, shafi na 415.
  7. Tabatabaei Yazdi, al-urwa al-Wuthghati, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 310-313; Meshkini, Mustalahat Fiqhi, 1392, shafi na 415.
  8. Misali, duba Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Wuthghati, 1419 AH, juzu'i na 3, shafi na 7-9; Bani Hashemi Khomeini, tauzihul masa'ili (Mohashi), 1424 AH, Juzu'i na 1, shafi na 617.
  9. برای نمونه رجوع کنید به طباطبایی یزدی، العروة الوثقی، ۱۴۱۹ق، ج۳، ص۹؛ بنی‌هاشمی خمینی، توضیح المسائل (محشّی)، ۱۴۲۴ق، ج۱، ص۶۱۷؛ «برگشتن و انحراف بدون عذر از قبله»، سایت رسمی آیت الله سیستانی.
  10. Bani Hashemi Khomeini, tauzihul masa'il (Mohashi), 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 618.
  11. Mufid, Al-Maqna, 1410 AH, shafi 419; Najafi, Javaher al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 36, ​​shafi 110; tauzihul masa'il (Mohashi), 1424 AH, juzu'i na 2, shafi na 573, mas'ala 2594.
  12. Tabrizi, Esfatatayat jadid, 2004, juzu'i na 1, shafi na 398.
  13. Tusi, Al-Khilaf, 1418, Juzu’i na 8, shafi na 319; Shahid Thani, Masalak al-Afham, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi 160; Najafi, Jawahirul al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 36, ​​shafi na 111 da 112; tauzihul masa'il (Mohashi), 1424 AH, juzu'i na 2, shafi na 573, mas'ala 2594.
  14. Harru amili, wasa'il al-Shia, 1412 AH, juzu'i na 14, shafi na 152-153.
  15. Tusi, al-Khilaf, 1418 AH, juzu'i na 6, shafi na 50; Najafi, Jawahirul al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 36, ​​shafi na 110.
  16. Mirdamad, shari'ul Al-Najat, 1426 AH, shafi na 301.
  17. Tusi, Al-Nahaye, 1400 AH, Juzu'i na 1, shafi na 9 da 10; Allameh Hilli, Qawa'edAl-Ahkam, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi 180; Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1416 AH, juzu'i na 1, shafi na 28.
  18. Khumaini, Muntakab manasik Hajji, 1426H, shafi na 142.
  19. Mahmoudi, ahkam Hajji (Mohashi), 1429 AH, shafi 298.

Nassoshi

  • Allameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Qawa'id al-Ahkam fi Marifah al-Halal wa Haram, Qum, Islamic Publication Institute, 1413H.
  • Ardebili, Majma al-Faedat wa al-Burhan, Qum, Islamic Publications, 1416H.
  • Bani Hashemi Khomeini, Seyyed Mohammad Hossein, tauzihul Al Masael (Mohashi), Qum, Ofishin Daba'ar Musulunci, bugu na 8, 1424H.
  • Mishkini, Ali, Mustalahat Fiqhi, Kum, Darul-Hadith, 1392.
  • Mofid, Al-Maqna, Qum, Islamic Publication Institute, 1410 AH.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher Al-Kalam, ta kokarin Quchani da sauransu, Beirut, Darahia al-Trath al-Arabi, 1362
  • Rouhani, Mohammad Sadiq, Fiqhu al-Sadiq (a.s.), Kum, Darul Katab, 1413H.
  • Tabrizi, Javad, Esftataat jadid, Qom, Dar al-Sadiqah al-Shahida, bugun farko, 1384.
  • Hakim, Seyyed Mohsen, Mustamsk al-Arwa al-Waghti, Qom, Al-Najafi School, 1404 AH.
  • Har Amili, Muhammad bin Hasan, Wasal al-Shia, Kum, Al-Bait, 1412H.
  • Khomeini, Sayyid Ruhollah, muntakab manasik hajji, Qum, bugu na Mashaar, bugu na biyu, 1426H.
  • Mahmoud, Abdurrahman, Mujam al-mustalaht wa al-Faz al-Fiqhiyyah, Alkahira, Darul Fadilah, 1419H.
  • Mahmoudi, Mohammadreza, Manasikul Hajj (Mahsh)i, Tehran, Mashaar Publishing House, 1429 AH.
  • Mai bincike Hali, Jafar bin Hassan, al-Muttabrab, Qum, Cibiyar Sayyid al-Shahada, 1363.
  • Mirdamad, Mohammad Baqer, Shariah al-Najat fi Ahkam al-Ibadat, Qum, Cibiyar Shari'a ta Musulunci, bugu na farko, 1426H.
  • Raghib Esfahani, Hossein bin Muhammad, Mufardat al-Faz al-Qur'an, Nash al-Kitab, 1404H.
  • Shaheed Thani, Zainuddin, Masalak al-Afham zuwa Tankih Shaaree al-Islam, Qom, Islamic Maarif, 1416H.
  • Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Wuthghati (Al-Mahash)i, wanda: Mohseni Sabzevari, Ahmad, Islamic Publishing House, Qum, bugun farko, 1419 Hijira.
  • Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Khalaf, da kokarin Khorasani da sauransu, Qum, bugun Musulunci, 1418H.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Nahaye, bisa kokarin Agha Bozur Tehrani, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1400H.
  • «برگشتن و انحراف بدون عذر از قبله»، سایت رسمی آیت الله سیستانی، تاریخ بازدید: ۱۲ اردیبهشت ۱۴۰۳ش..