Jump to content

Maƙam Ra'asil Husaini (Al-ƙahira)

Daga wikishia
Maƙam Ra'asil Husaini (Al-ƙahira)
Wanda ya kafaƊala'i'u Bin Razik waziri a salsalar Faɗimiyyan
KafawaShekara 548-549 bayan hijira
Mai amfaniMasallaci. Wurin Ziyara
WuriBirnin Al-ƙahira ƙasar Misra
Sauran sunayeMasallacin Husaini (A.S), Mashad Husaini
Sabunta giniShekarar 1401 kalandar Farsi


Maƙam Ra'asil Husaini Al-ƙahira (Larabci: مقام رأس الحسين القاهرة ) Gurin da aka binne kan Imam Husaini (A.S) guri ne da mutane suke ziyarta a Al-ƙahira ƙasar Masar wasu litattafan tarihi sun ambaci cewa an binne kan Imam Husainin(A.S) a wannan gurin bisa abin da ya zo cikin wasu littafai mahukunta a gwamnatin Faɗimiyya ta canzawa kan Imam Husaini (A.S) guri daga garin Asƙalan zuwa A-lƙahira a Masar a ƙarni na 16 sakamakon tsoron da suke ji kada a wulaƙanta kan Imam Husaini(A.Smai daraja, wannan duk ya fau ne sakamakon Kiristoci sun mamaye wannan yanki, aka binne kan a shekara ta 548 ko 549 hijira, sannan aka gina masallaci da ake kira da masallacin Husaini.

Akwai mabambantan ra'ayoyi dangane da kan da aka binne a masallacin Husaini na A-lƙahira, amma bisa ra'ayin da ya shahara a tsakanin malaman Shi'a shi ne cewa an binne kan Imam Husainin (A.S) a Karbala tare da gangan jikinshi mai tsarki, saboda haka wasu suke cewa kan da aka binne a wannan guri da yake A-lƙahira na wani ne daga cikin Sharifai Alawiyyawa ko na ɗaya daga cikin shahidan Karbala ko ɗaya daga cikin iyalan gidan Imam Husaini (A.S).

‘Mutanen ƙasar Masar suna girmama wannan guri, kuma suna ziyartarshi. Akwai yiwuwar an ajiye wasu abubuwa da suke da alaƙa da Annabi (S.A.W) da kuma rubutu na Kur'ani wanda ba'a buga shi ba. Har ila yau ana gudanar da zama na karatun Kur'ani a wannan guri, wasu fitattun makaranta Kur'ani suke halarta.

Matsayin Wannan Wuri A Gun Mutanen Masar

Gurin da aka binne kan Imam Husaini (A.S) guri ne da ake jingina shi ga Imam husaini (A.S) kuma wannan guri shi ne na biyu wajan haɗuwar mutane bayan Masallacin Jami'ul Al-Azhar.[1] A cewar Sayyid Muhsin Amini wanda ya kai ziyara wannan guri a shekara ta 1321 hijira Misirawa suna dandazon kai ziyara wannan guri mazansu da matansu kuma suna gudanar da addu'o'i.[2] Har ila yau Ibn Jubairi Andulusi wanda ya rasu a shekara ta 614 hijira ya faɗi cewa yawancin mutane masu kai ziyara wannan guri suna tabarruki da Imam Husaini (A.S)[3] wasu daga cikin Salafawa sun bayyana mamakinsu kan yadda Misirawa suke dandazon kai ziyara wannan guri da aka binne kan Imam Husain (A.S) amma Baban masallacin Jami'ul Al-Azhar mai makwabtaka da wannan guri yana shara-shara ba sa dandazon a can.[4]

Mutanen Misra duk shekara suna bikin zagayowar shekarar kawo kan Imam Husaini (A.S) wannan guri,[5] wannan biki ana yinshi duk shekara a ranar Talata ƙarshan watan Rabi'us Sani, inda ake kafa runfuna da tanti-tanti a guraran da suke kewaye da wannan guri.[6] Ana cewa tsawon zamani shuwagabanin Misrawa sun dage kan cewa sai anci gaba da sallar Idi a wannan guri, haka ne ya faru ne a lokacin mulkin Jamal Abdun-nasir a shekara ta (1956-1970 miladiya)[7]

Wasu malamai sun yi imani cewa kan Imam Husaini (A.S) yana taka rawa wajan motsa mutane kan bijerewa azzalumai da masu mulkin mallaka kamar yadda haramin Imam Husaini (A.S) a Karbala yake motsa mutane kan yin gwagwarmaya da bore ga azzalumai.[8]

Ibn Kasir malamin tarihi na Ahlus-Sunna wanda ya rasu a shekara ta 774 hijira ya ce Misrawa suna kiran wannan guri da Tajul Imam Husaini (A.S)[9] Ibn Nama Hilli yana cewa su Misrawa suna kiran wannan guri da Mashad mai girma.[10] Malikul Hazin a wata maƙala da ya rubuta mai ɗauke da sunan masallacin Imam Husaini (A.S) da matsayinshi a cikin zukatan Misirawa, yana cewa sun ɗauki wannan guri a matsayi mai girma da har ta kai ga wasu malaman tarihi sun yi amfani da sunan Masallacin Haramin Misra ga wannan guri.[11] Kamar yadad suke kiran shi da sunan masallacin Imam Husaini (A.S),[12] ko Maƙam Ra'asil Husaini (A.S),[13] ko Mashad Husaini.[14]

Shin An Binne Kan Imam Husaini (A.S) A Al-ƙahira?

Ya zo cikin wasu littafai cewa kan Imam Husaini (A.S) an binne shi a garin [[Asƙalan],[15] a lokacin da garin Asƙalan ya kasance ƙarƙashin Kirista, Musulmi sun ɗauke kan Imam Husaini (A.S) daga Asƙalan sun kai shi A-lƙahira,[16] ance wanda ya canzawa kan guri shi ne Ɗala'i'u Bin Razik wanda ya kasance Waziri ne na gwamnatin Faɗimiiyya a wancan lokacin ya rasu a shekara ta 556 hijira,[17] kuma ya bawa Kirista kuɗi da yawa kafin ya samu su yarda da canzawa kan guri, domin kai shi Misra da binne shi a can[18] Bisa abin da Maƙrizi malamin tarihi na Misra a ƙarni na 9 hijira ya ce an sauyawa kan Imam Husaini (A.S) guri ne a watan Jimada Akhir a shekara ta 548 ko 549 hijira.[19] ya zo cewa ƙamshin Almiski yana cika titina da layika da ƙanshi a duk lokacin da aka wuce da kan Imam Husaini (A.S), kuma saboda haka ne ake kiran wata unguwa a A-lƙahira da Unguwar Almiski a cikin garin A-lƙahira[20] Ibn Kasir malamin tarihi na Ahlus-Sunna ya yi imani cewa Faɗimiyyan sun canzawa kan guri ne domin ƙarfafar i irarinsu na cewa su nasabarsu tana komawa ne zuwa ga Imam Husaini (A.S).[21]

Faɗimiyyan da wasu sufaye,[22] kazalika da wasu malaman Ahlus-Sunna Misirawa kamar Ali Jumu'a Muftin Misira kuma ɗan Majalisar malaman Azhar,[23] sun yi imani cewa an binne kan Imam Husaini (A.S) a wannan guri. A daidai lokacin da fitaaccan ra'ayi a gun malaman Shi'a shi ne cewa an binne kan Imam Husaini (A.S) a Karbala ne tare da gangan jikinshi.[24] Amma Salafiyya,[25] da wasu malaman Ahlus-Sunna sun yi inkarin binne kan Imam Husaini a wannan guri da yake Al-ƙahira.[26]

Wasu daga cikin malamin Shi'a Imamiyya sun ambaci ra'ayi guda uku dangane da kan Imam Husaini (A.S) wanda aka binne a Asƙalana, wanda daga bayan aka canza mishi guri zuwa A-lƙahira; na farko cewa kan ɗaya ne daga cikin Alawiyyawa, ko ɗaya daga cikin shahidan Karbala ko ɗaya daga cikin iyalan gidan Imam Husaini (A.S).[27]

Masallacin Husaini Da Tarihinsa

A lokacin gwamnatin Faɗimiyyawa shekara ta 549 hijira a ƙarƙashin wazir Ɗala'i'u na gwamanatin Faɗimiyyawa aka gina masallaci a gurin da aka binne kan Imam Husaini (A.S),[28] kuma aka sanya masa suna da masallacin Husaini, an gina wannan masallaci ne da farar Marmara ko farin dutse kuma yana da ƙofofi guda uku.[29] Sarakunan Misra suna nuna kulawa ta musammam ga wannan guri(A.S)[30] Misali an yi mishi kwaskwarima a ƙarni na 13 da umarnin Kuduyuwi Isma'il wanda ya sarkin Misra a wancan lokacin[31] A shekara ta 1443 an sake gina wannan masallaci ta hannun Bohra Isma'iliyya,[32] Hakan nan an sake buɗe shi a shekara ta 1444 hijira da halartar Abdul-Fatah Sise shugaban ƙasar Misra na wannan lokacin, yayin wannan sabunta gini ne aka kafa zariha a wurin da aka binne kan nasa.[33]

A shekara ta 2022 hukuma kula da wakafi ta Misra suka zaɓi wannan masallaci a matsayin masallacin na musammam bisa la'akari da girmansa da ayyukan da ake yi a cikinsa.[34] Masallacin Husaini yana unguwar da ake kira da unguwar Imam Husaini(A.S)[35] a A-lƙahira, unguwa ce da take da daɗaɗɗen tarihi[36] Wuri na da yake maƙwabtaka da Jami'ul Azahar, sannan ana kallon wannan unguwa matsayinn cibiyar ilimin addini a Misra,[37] Haka nan titin Khan Alkhalili wanda yake cikin wannan unguwa shima ya kasance cikin unguwanni na wayewa da al'adun muslunci a Al-ƙahira,[38] kusa da wannan unguwa akwai Cibiyar Darbi Atrak wanda ita ma wata cibiya ce da ake sayar da litattafan Muslinci.[39]

Masallacin Sayyida Zainab bayan an kammala gyaransa da sabunta shi, tare da halartar Shugaban Masar, Abdel Fattah El-Sisi, da Sultan Mufaddal Saifuddin, jagoran ƙungiyar Bohra

Ajiye Daɗaɗɗun Kayayyakin Muslunci A Wannan Masallaci

An ajiye wani Alƙur'ani wanda ake jingina shi da Imam Ali (A.S), ya yi shahada a shekara ta 40 hijira,[40] wasu suna ganin wannan ƙur'ani an rubuta shi ne a rabi na biyu daga ƙarni na 1.[41]Cikin wannan masallaci akwai abubuwa da ake jinginasu ga Annabi Muhammad (S.A.W) waɗanda suka haɗa da takobinshi da tandun kwallinshi da ƙashinshi da wani gutsiran tsumma daga rigarshi da wani gutsire na sandarshi.[42]

Masallacin Husaini Guri Ne Da Ake Karanta Kur'ani

Ana shirya zaman karatun ƙur'ani ga wasu mashahuran masu karatun ƙur'ani na Misra, irinsu Minshawi da Abdul-Basiɗ Abdus-Samad da wasunsu,[43] kuma wannan masallaci yana daga cikin guraran da makaranta ƙur'ani suke shirya gasar karatun ƙ ur'ani.[44]

Ku Duba Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. Abdur Rahman Nahla، «بتوزيع الحلوى.. توافد المواطنين على مسجد الامام الحسين للاحتفال بالمولد النبوی الشريف»Shafin Qahira Life24, an saka shi: 25 ga Satumba, 2023 An kalla: 1 ga Janairu, 2024 .
  2. Al-Ameen, Luwa'ij Al-Ashjan fi Maqtal Al-Husayn(A.S)," wanda Dar Al-Amir suka buga, kuma yana shafi 191
  3. Rihlat Ibn Jubayr, wanda Dar Al-Hilal suka buga, kuma yana shafi 19.
  4. "Al-Istanbuli, Tahqiq Hukm Al-Qira'ah Ala Al-Amwat," wanda Jami'ar Islamiyya suka wallafa, kuma yana shafi 29
  5. Hijazi Wa Atif، «الحسين حبيب المصريين. "الوطن" تحتفي بسيد الشهداء فی احتفالات ذكرى استقرار "الرأس الشريف" بالقاهرة» موقع جريدة الوطن؛ الدیك و سامي، «مولد الحسين ليلة فى حب آل بيت الحسين»، Shurooq.
  6. «عاشوراء في مصر»، Shafin na musamman na Makaranta da Nazari na Al'umma da Al'adu..
  7. «الدور السياسي لمقام رأس الإمام الحسين في القاهرة في ندوة لندنية»، Shafin yanar gizo na Al-ijtihad.
  8. «الدور السياسي لمقام رأس الإمام الحسين في القاهرة في ندوة لندنية»، Shafin yanar gizo na Al-ijtihad.
  9. Ibn Kathir, Al-Bidaya wa'l-Nihaya," wanda aka buga a shekara ta 1408H, a juzu'i na 8, kuma yana shafi 222.
  10. "Ibn Nama Al-Hilli, Muthir Al-Ahzan," wanda aka buga a shekara ta 1406H, kuma yana shafi 107
  11. Al-Hazeen, "Masallacin Husayn da Matsayinsa a Zuciyar Masarawa Sunnah," wanda aka buga a Shabakat Hajr a ranar 19 ga Disamba, 1999, daga Al-Kourani Al-Amili, Al-Intisar, bugu na 1421H, juzu'i na 9, shafi 26.
  12. Misali ku duba: «حي الحسين.. هنا مر التاريخ وترك ذكرى».
  13. Misali ku duba:«ما لا تعرفه عن مقام رأس الحسين في القاهرة»، Tashar Kausar.
  14. Misali ku duba: Ansari «المشهد الحسیني بالقاهرة»، Shafin jaridar Abul Hulul.
  15. - Ibn Al-Umrani, Al-Anba fi Tarikh Al-Khulafa – bugu na 1421H, shafi 5, - Al-Harawi, Al-Isharat ila Ma'rifat Al-Ziyarat – bugu na 1423H, shafi 36 - Yaqut Al-Hamawi, Mu'jam Al-Buldan – juzu'i na 5, shafi 142- Al-Manawi, Faydh Al-Qadir – bugu na 1356H, juzu'i na 1, shafi 205, - Yaqut Al-Hamawi, Mu'jam Al-Buldan – juzu'i na 5, shafi 142 - Al-Manawi, Faydh Al-Qadir – bugu na 1356H, juzu'i na 1, shafi 205,
  16. - Al-Harawi, Al-Isharat ila Ma'rifat Al-Ziyarat – bugu na 1423H, shafi 36 - Yaqut Al-Hamawi, Mu'jam Al-Buldan – juzu'i na 5, shafi 142 - Al-Ameen, Luwa'ij Al-Ashjan fi Maqtal Al-Husayn عليه السلام – wanda Dar Al-Amir suka wallafa, shafi 191. - Yaqut Al-Hamawi, Mu'jam Al-Buldan – juzu'i na 5, shafi 142 - Al-Ameen, Luwa'ij Al-Ashjan fi Maqtal Al-Husayn عليه السلام – wanda Dar Al-Amir suka wallafa, shafi 191. - Al-Ameen, Luwa'ij Al-Ashjan fi Maqtal Al-Husayn عليه السلام – wanda Dar Al-Amir suka wallafa, shafi 19
  17. Al-Manawi, Faydh Al-Qadir", wanda aka buga a shekara ta 1356H, juzu'i na 1, shafi 205.
  18. Al-Manawi, Faydh Al-Qadir", wanda aka buga a shekara ta 1356H, juzu'i na 1, shafi 205.
  19. Al-Maqrizi, Al-Mawa'idh wal-I'tibar bi Dhikr Al-Khitat wal-Athar
  20. الشناوي، «مصر كنانة أهل البيت...»، Shafin yanar gizo na Cibiyar Karbala don Nazari da Bincike،«في ذكرى احتفال المصريين بقدوم الرأس الشريف للإمام الحسين إلى مصر في آخر ثلاثاء من ربيع الآخر في كل عام – لماذا يشكك السلفيون في وجود الراس الشريف بمصر ؟!!»، shafin Tafsirin Al-Naba' Al-Azim.
  21. Ibn Kathir, Al-Bidaya wa'l-Nihaya", wanda aka buga a shekara ta 1408H, juzu'i na 8, shafi 222
  22. "Al-Khalidi, Rihla fi Al-Diyar Al-Masriyya fi Al-Qarn Al-Thamin 'Ashar", wanda ke bayanin tafiya a ƙasar Masar a ƙarni na 18, kuma yana shafi 24.
  23. «إظهارات مفتي مصر السابق في خصوص مقام رأس الحسین في القاهرة»، Shia News
  24. - Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar – bugu na 1403H, juzu'i na 45, shafi 145 - Mohammadi Al-Ray Shahri da wasu marubuta, Al-Sahih min Maqtal Sayyid Al-Shuhada wa Ashabihi – bugu na 1392Sh, juzu'i na 2, shafi 391
  25. Ibn Taymiyyah, Ra's Al-Husayn," wanda aka bincika kuma aka shirya ta hannun Jamili, kuma yana shafi 181
  26. Al-Qurtubi, Al-Tadhkira bi Ahwal Al-Mawta wa Umur Al-Akhira", wanda aka buga a shekara ta 1425H, kuma yana shafi 1122.
  27. Al-Mousawi, Madfan Ra’s Al-Husayn", wanda ke tattauna wurin da aka binne kan Imam Husayn عليه السلام, kuma yana da shafi 558
  28. Al-Maqrizi, I'ti'az Al-Hunafa bi Akhbar Al-A'imma Al-Fatimiyyin Al-Khulafa", wanda aka buga a shekara ta 1416H, juzu'i na 3, shafi 251.
  29. "Al-Maqrizi, Al-Mawa'idh wal-I'tibar bi Dhikr Al-Khitat wal-Athar", wanda aka buga a shekara ta 1418H, juzu'i na 2, shafi 323.
  30. "Masjidul Husayn wa Manzilatuhu Fi Nufus Almisriyun As-Sunna", wanda aka wallafa a Shabakat Hajr a ranar 19 ga Disamba, 1999, daga Al-Kourani Al-Amili, Al-Intisar, bugu na 1421H, juzu'i na 9, shafi 26.
  31. Abdullahi «تجديد مسجد الحسين يعيد جدل أزمات ترميم الآثار بمصر»
  32. «السيسي يفتتح اليوم مسجد الحسين بعد تجديده (صور)»، موقع RT Arabic؛ «السیسي، البهرة وتوسعة مسجد رأس الحسین»، Din Online.
  33. «الرئيس المصري يفتتح مسجد الحسين ويصلي فيه»، Sjafaqna.
  34. «مسجد «رأس الحسین» القاهرة، المسجد الأمثل لسنة 2022م»،Shafin Shabastan.
  35. «جامع الحسين»، Shafin Hukumar Bayani ta Jama'a a Masar,.
  36. «حي الحسين.. هنا مر التاريخ وترك ذكرى»، Aljazeera.
  37. - Malik Bin Nabi, Mudhakkirat Shahid Lil-Qarn – bugu na 1404H, shafi 13- Al-Hazeen, "Masjidul Husayn wa Manzilatuhu Fi Nufus Almisriyun As-Sunna", wanda aka wallafa a Shabakat Hajr a ranar 19 ga Disamba, 1999, daga Al-Kourani Al-Amili, Al-Intisar, bugu na 1421H, juzu'i na 9, shafi 26
  38. «كيف عادت الأجواء الروحانية إلى مسجد الحسين بالقاهرة بعد حظر دام عامين؟»، Aljazeera.
  39. «حي الحسين.. هنا مر التاريخ وترك ذكرى»، Al-jazira.
  40. Fahhama، «المصاحف المنسوبة لأمير المؤمنين (عليه السلام)»، Shafin Yanabi.
  41. Assiqara، «مخطوطات القرآن المكتوبة في القرن الهجري الأول تشهد بموثوقية نص القرآن العظيم»، Shafin I'ijaz Kur'an was sunna.
  42. جمال، «آثار النبى ص في القاهرة المحروسة»،Shafin Ahram.
  43. «کشف أسباب تنافس قراء مصر المشهورين للتلاوة في مسجد «الحسین»،Shafin Ikna.
  44. Ka duba Buhairi، «انطلاق مقرأة كبار القراء من مسجد الإمام الحسين.. صور»،Almisri Yaumi.

Nassoshi