Lailatul Ƙadri

Daga wikishia
(an turo daga Lailatul Qadri)

Daren lailatul ƙadri ko Lailatul ƙadri, dare ne na saukar Alkur’ani da ƙaddara al’amuran da za su faru a shekara mai zuwa ga mutum, Alkur’ani ya yi Magana kan wannan daren cikin suratul ƙadri da suratul Dukhan, kan asasin ayoyi masu yawan gaske da riwayoyi, haƙiƙa wannan dare ya fifita kan watanni dubu, ya kasance mafi falalar dare daga dararen shekara, dare ne na saukar rahamar Allah da kuma gafarta zunubai, a cikin wannan dare Mala’iku suke saukowa ƙasa, kan asasin rahotannin wasu hadisai daga Shi’a ana kawowa Imami ƙaddarorin Bayi na shekara mai zuwa. Babu ingantacciyar Magana kan wanne dare ne daren lailatul ƙadri, sai dai kuma kan asasin bayanan riwayoyi masu tarin yawa, an bayyana cewa daren lailatul ƙadari yana cikin ɗaya daga dararen cikin watan Ramadan daga daren 19, 21, 23, haƙiƙa ƴan Shi’a sun fi ƙarfafar cewa yana cikin daren 23 su kuma Ahlus-sunna sun tafi kan ƙarfafar kasancewarsa daren 27 na watan Ramadan. A cikin waɗannan darare haƙiƙa ƴan Shi’a cikin koyi da Imamai Ma’sumai (A.S) suna himmatuwa cikin raya waɗannan darare da karatun Alkur’ani, Addu’a, Ibada, Muzakarar Ilimi da neman ilimi da ma’arifa, sannan a daren da aka sari Imam Ali (A.S) a Masallacin Kufa suna himmatuwa cikinsa da ibada ƙari kan Makoki da ta’aziyya ga Imam.

Sanya Suna

ƙadar, kalma ce daga harshen Larabci, da take da ma’anar awo da miƙdari da kuma ƙaddarawa da kuma ƙaddara. [1] A mahangar wasu adadin Malamai misalin Allama ɗabaɗaba’i, kasancewa ana ƙaddarar dukkanin al’amuran da za su faru da mutum a shekara mai zuwa a cikin wannan dare shi ne ya sanya ake kiransa da sunan daren lailatul ƙadri, [2] Ayatullahi Makarim Shirazi yana ganin cewa kiran wannan dare da daren ƙadri ya fi dacewa da abin da ya zo a riwayoyi kuma shi ne ra’ayin da aka fi sani. [3] Dangane da dalili kiransa da daren ƙadri Imam Khomainin ya kawo tsammani kan fuskoki uku, ta farko ksancewarsa dare mai daraja da ƙima, sannan Alkur’ani ma’abocin girma ta hannun Mala’ika mai girma zuwa ga Annabi Mai girma ya sauka ga al’umma mai girma, da wannan dalili ne ake kiransa da daren ƙadri. Fuska ta biyu sakamakon cikin wannan dare ne ake ƙaddara al’amurra da arziƙin al’umma shi ne dalili kiransa da wannan suna, fuska ta uku, saboda hallarar adadi mai yawa daga Mala’iku sai ƙasa ta ƙuntace ta takure, da wannan dalili ne ake kiransa da daren ƙadri. [4] Imam Khomaini ya rinjayar da fuska ta biyu kan sauran fuskokin, ya ce mai yiwuwa (lailatul ƙadri) ta kasance ga wannan ma’abocin girma, wannan dare ne na sadarwar cikamakin Annabawa kuma dare ne na sadarwar Masoyi na haƙiƙa, Masoyin Allah. [5] Shima Nasir Makarim Shirazi ya kawo tsammanin fuskoki uku daga ma’abocin daren ƙadri da kuma muƙamin masu raya wannan dare da ibada, babbar darajar wannan dare da kuma saukar Alkur’ani cikin wannan dare yana daga cikin dalilin kiran wannan dare da daren ƙadri. [6] Haka zalika an kira shi da sunan (Lailatul Al-Azma) da kuma (Lailatul sharafi) [7]

Matsayi da Muhimmanci

Daren ƙadri ya kasance ana ƙirga shi daga mafi fifitar dare kuma dare mafi muhimmanci a shekara cikin Al’adun muslunci, [8] kan asasin wata riwaya daga Annabi (S.A.W) ya zo cewa haƙiƙa daren lailatul ƙadri yana daga cikin kyaututtukan Allah ga Musulmai babu wata al’umma daga al’ummomin da suka gabata da ta samu wannan baiwa da kyauta. [9] cikin Alkur’an akwai cikakkiyar sura da ta keɓantu cikin siffanta wannan dare, wacce da wannan dalili ne ake kiranta da sunan (suratul ƙadri) [10] cikin wannan sura an bayyana cewa darajar daren ƙadri ta fifici watanni dubu. [11] aya ta shida cikin suratul Dukhan ita ma ta zo da bayanin muhimmancin wannan dare. [12] Cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya zo cewa mafi alherin wata shi ne watan Ramadan, kuma daren ƙadri shi ne zuciyar watan Ramadan, [13] [yadahst 1] haka kuma an naƙalto daga Annabi (S.A.W) cewa daren ƙadrin shi ne shugaban darare. [14] a wani hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S) daren ƙadri shi ne farkon shekara. [15] me yiwuwa abin da yake nufi daga farkon shekara shi ne farkon shekara ta ma’anawiyya da ibada, ko kuma ayyana ƙaddarar mutum ta shekara mai zuwa. [16] kan asasin masadir na riwaya dana fiƙihu, ranar ƙadri kamar dai daren ƙadri rana ce mai daraja da falala. [17] afkuwar wasu abubuwa misalin saran Imam (A.S) da Abdur-Rahman Bn Muljam (L.A) ya yi a daren 19 da kuma shahadarsa a daren 21 ƙari kan kasancewarsa daren lailatul ƙadri yana da wata daraja da ƙima ta musammam a wurin ƴan Shi’a bayan raya dararen da ayyaukan mustahabbi suna makokin shahadar Imam Ali (A.S). [18] Cikin ba’arin wasu riwayoyi ya zo cewa Fatima (S) ita ce sirrin daren ƙadri, [19] duk wanda ya samu dacewa da kamallalen sanin Fatima haƙiƙa ya riski daren ƙadri. [20]

Saukar Alkur’ani

Aya ta farko cikin suratul ƙadri da aya ta uku cikin suratul Dukhan ayoyi ne da suke bayanin kan saukar Akur’ani cikin daren ƙadri, [21] kuma Aksarin Malaman Tafsiri sun tafi kan cewa Alkur’ani ya sauka lokaci guda wurin Annabi (S.A.W) a wannan dare, [22] ana kiransa da sunan Nuzuli Daf’i (saukar lokaci guda) [23] amma wasu ba’ari sun tafi kan cewa farkon sauka mataki-mataki sannu-sanne a hankula ta kasance a cikin watan Ramadan. [24]

ƙaddara Al’amura

an naƙalto daga Imam Baƙir (A.S) cikin ƙarin bayani kan aya ta 4 suratul Dukhan ya ce a kowacce shekara wannan dare ne ake rubuta ƙaddarar mutum ta shekara mai zuwa, [25] kan wannan asasi cikin ba’arin wasu riwayoyi an bayyana daren ƙadri da taken farkon shekara, [26] Allama ɗabaɗaba’i yana cewa (abin nufi daga ƙadri, shi ne ƙaddara da kuma aunawa, kuma cikin wannan dare Ubangiji yake ayyana al’amurra daga misalin rayuwa, mutuwa, arziƙi da tsiyatar Mutum, [27] kan asasin wasu rwiayoyi ya zo cewa wilayar Imam Ali (A.S) da sauran Ahlil-Baiti (A.S) suma cikin wannan dare aka sa hannu a kansu. [28]

Gafarta Zunubai

Kan asasin wani ɓangare daga riwayoyi haƙiƙa cikin watan Ramadan ana ɗaɗɗaure Shaiɗanu da sarka da sasari, sannan kuma ana buɗe ƙofofin Aljanna ga Muminai, bayan Annabi (S.A.W) ya yi wannan Magana sai ya maimaita faɗin wannan jumla har sau uku: haƙiƙa cikin wannan wata daren lailatul ƙadri yake dare ne da ya fifici watanni dubu, haramtacce na haƙiƙa shi ne wanda ya haramtu daga daren lailatul ƙadri, [29] an rawaito daga Annabi (S.A.W) duk wanda ya raya daren ƙadri kuma yana Mumini yana Imani da da ranar Sakamako, haƙiƙa an yafe masa dukkanin zunubansa. [30]

Saukar Mala’aiku

Kan asasin aya ta huɗu da ta uku cikin suratul ƙadri, Mala’iku da Ruhu suna saukowa ƙasa, [31] sannan kan asasin wasu Hadisai suna zuwa wurin Imami domin sanar da shi ƙaddarar shekara Mai zuwa da kuma abin da aka riga aka ƙaddara. [32] an naƙalto daga Imam Baƙir (A.S) cewa: cikin wannan dare Mala’iku suna ɗawafi kewayen gidajenmu (mu Imamai) da haka ne muke gane cewa daren lailatul ƙadri ne, [33] cikin wasu riwayoyin daban an umarci ƴan Shi’a da su yi amfani da wannan mas’ala cikin kafa hujja kan tabbatar da larurar imamanci da gaskiyar shi’anci; da wannan jeri da tsari ne ya zama wajibi a kowanne zamani dole ne a samu Imami Ma’asumi domin Mala’iku su isar masa da sakon ƙaddarori. [34] [yadasht 3]

Zamani

Dangane da batun wanne dare ne daren ƙadri cikin dararen shekara, akwai ra’ayoyi mabambanta.

Ra’ayin Shi’a

A cewar Malaman Tafsiri misalin Allama ɗabaɗaba’i tare da dogara da zahirin ayoyin suratul ƙadri da suratul Dukhan ya tafi kan cewa daren ƙadri bai keɓantu kaɗai da daren da Alkur’ani ya sauka a zamanin Annabi (S.A.W) ba, bari dai a kowacce shekara yana maimaituwa, [35] akwai riwayoyi masu tarin yawa, [36] da ake ganin sun kai darajar Mutawatirai, [37] suna ƙarfafar wannan Magana, a cewar Allama ɗabaɗaba’i riwayoyi sun yi ittifaƙi kan cewa kowacce shekara wannan dare yana maimaituwa. [38] Ka asasin ayoyin Alkur’ani haƙiƙa daren ƙadri an ajiye shi cikin dararen watan Ramadan, [39] sai dai cewa ba a ambaci wanne dare bane cikin Alkur’ani, [40] riwayoyi masu tarin yawa suma suna ƙarfafa cewa a cikin watan Ramadan yake. [41] A cewar Allama Majlisi, daren ƙadri a mahnagar Imamiyya yana cikin ɗayan dararen 19, 21, 23 daga watan Ramadan kuma riwayoyi da suke Magana kan haka suna da tarin yawa, [42] a ra’ayin Allama ɗabaɗaba’i, riwayoyin Ahlil-Baiti sun yi ittifaƙi kan cewa daren ƙadri yana cikin ɗayan dararen 19, 21, 23 daga watan Ramadan, [43] Shaik Saduƙ ya ce Malamanmu ra’ayoyinsu sun yi ittifaƙi kan cewa daren ƙadri yana daga 23 ga watan Ramadan, [44] a cewar Mulla Fatahullahi Kashani a cikin littafin Minhajul As-Sadiƙin, ra’ayin Aksarin Malaman Imamiyya daren 23 daga Ramadan shi ne daren ƙadri, [45] an ce akwai adadin hadisai [46] da suke ƙarfafar ra’ayin wanda suka zaɓi daren 23 daga Ramadan matsayin daren ƙadri, [47] kan asasin ba’arin wasu riwayoyi a daren 19 ake rubuta ƙaddarori, a daren 21 kuma ake tabbatar da su, sannan kuma a daren 23 ake sanya hannu na ƙarshe a kansu. [48] dararen 27 ga Ramadan da daren tsakiyar Sha’aban suma ana tsammanin kasancewarsu daga dararen ƙadri. [49] Daren 23 ga Ramadan bisa la’akari da riwayar Imam Baƙir (A.S) da Imam Sadiƙ (A.S) ya shahara da sunan daren Juhaniyyu, Zurara ya naƙalto: na tambayi Imam dangane da dararen da wanka cikinsu ya kasance mustahabbi watan Ramadan, sai Imam ya ce: daren 19, daren 21 daren 23, sannan ya ce: daren 23 dare ne na Juhaniyyu wanda hikayarsa ta kasance kamar haka: akwai wani mutum da ake kira da suna Abdullahi Bn Anis Ansari wanda ya gayawa Manzon Allah (S.A.W) cewa gidana yana da nisa da Madina, ka umarce ni da wani dare in zo Madina. sai Annabi (S.A.W) ya gabatar masa da daren 23. [50] bayan wannan tattaunawa da kuma abin da aka gani daga aikin Abdullahi Bn Anis Ansari cikin daren 23 sai ake kiran wannan dare da daren Juhaniyyu, lailatul Juhaniyyu ya zama suna daga sunayen daren ƙadri, [51] har ya zama Sahabban Imamai suna tambayarasu lokacin daren Juhaniyyu. [52] a cewar Muhammad Taƙiyyu Majlisi bisa la’akari da riwayoyi misalin daren Juhaniyyu, haƙiƙa Shaik Saduƙ da galibin Malaman Shi’a sun tafi kan cewa daren 23 shi ne daren lailatul ƙadri. [53]

Mahangar Ahlus-Sunna

Aksarin Ahlus-sunna tare da dogara da hadisin Annabi (S.A.W) sun tafi kan cewa daren ƙadri yana cikin ɗaya daga dararen goman ƙarshen watan Ramadan. [54] a cewar Allama ɗabaɗaba’i, sanannen batu tsakankanin Ahlus-Sunna shi ne cewa daren 27 daga Ramadan shi ne daren ƙadri. [55] wasu ba’arin Ahlus-Sunna suma sun tafi kan cewa daren ƙadri bai takaitu kaɗai da iya zamanin Annabi (S.A.W) ba bari dia duk shekara yana maimaituwa, amma bayansa babu wani daren ƙadri a cikin shekara, [56] a cewar wasu ba’arinsu haƙiƙa ba a ayyana wanne dare ne daren ƙadri ba a cikin dararen shekara. [57] wasu adadi sun yi Imani da cewa daren aiko da Annabta zuwa ga Annabi (S.A.W) da ya kasance watan Ramadan shi ne daren ƙadri, amma kuma zai iya yiwuwa bayansa a samu maimaitiwarsa a wasu shekarun cikin wasu watannin daban, [58] tare da haka kamar yanda ɗabarasi ya faɗa cikin littafin Majma’ul Al-Bayan gamewar Malamai ra’ayinsu ya yi ittifaƙi kan cewa daren ƙadri yana cikin watan Ramadan, [59]

Bambance-bambancen Ufuƙi Da Kuma Ayyana Daren ƙadri =

Dare ɗaya ne yake kasancewa daren ƙadri a kowacce shekara, [60] amma sakamakon bambantar Ufuƙin ƙasashe misalin Iran da Saudiyya ya haifar da samun banbanci cikin farkon watan Ramadan, kan asasinsa ne dararen 19, 21, 23 daga watan Ramadan suna bambantuwa tsakanin ƙasashe, Malamai sun yi bayani kan wannan matsala da aka samu cin karo da juna sun ce bambantar ufuƙin ƙasashe ba zai zama dalili kan adadantuwar daren ƙadri ba, [61] Musulman kowanne yanki a duniya ya zama wajibi a kansu su ayyana daren ƙadri da sauran lokuta masu daraja daga misalin ranar Idin Fiɗir da Idin Adha kan asasin ufuƙinsu, [62] kan asasin mahangan Ayatullahi Makarim Shirazi, Dare inuwar rabin duniya yana kan sauran rabin, kuma wannan inuwar tana motsawa tare da jujjuyawar duniya, kuma cikakken lokaci yana ɗaukar sa'o'i 24. Saboda haka daren lailatul ƙadari yana iya zama cikakken kewayar duniya a kewaye da take; Yana nufin duhun sa'o'i 24 wanda ya mamaye dukkan sassan duniya. Don haka daren ƙadri yana farawa daga wani yanki guda kuma yana ɗaukar sa'o'i 24, kuma duk duniya za a fahimci daren ƙadri ya shiga. [63]

Sirar Ma’asumai =

Cikin wani hadisi daga Imam Ali (A.S) ya zo cewa Annabi (S.A.W) cikin goman ƙarshen Ramadan yana naɗe shimfiɗar baccinsa yana tafiya Masallaci domin Itikafi tare da cewa Masallacin Madina bai da rufi hatta lokacin damina Annabi (S.A.W) yana zaune ciki baya fita daga Masallacin, [64] haka kuma an naƙalto cewa Annabi (S.A.W) a dararen ƙadri kwakwata baya bacci haka yana tashin masu matsalar kamuwa da ciwon bacci ya fesa musu ruwa su tashi domin su samu amfana da wannan dare. [65] Tsarin Fatima (S) ya kasance tana raya daren har zuwa Asubahi haka kaf iyalanta ido biyu suke kasancewa basa bacci a waɗannan darare, tana tilasta su da yin ibada, sannan masu matsalar kamuwa da bacci tana maganceta ta hanyar sanya su cin abinci ɗan kaɗan da kuma yin bacci da rana. [66] Ma’sumai (A.S) a dararen ƙadri basa sakaci da hallara a Masallatai da raya waɗannan darare da ibada, [67] kan asasin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) da ya kamu da matsananciyar rashin lafiya cikin ɗaya daga dararen lailatul ƙadri, amma kuma tare da haka ya nemi mutane da suke tare da shi da su kai shi Masallaci domin ya yi ibada a can. [68]

Raya Daren Lailatul Cikin Yin Muzakarar Ilimi

Babban Malamin Hadisi Shaik Saduƙ cikin majlisi na 93 a littafin Amali bayan bayanin nafilfilin dararen watan Ramadan da kuma sallah raka’a 100 daga dararen 21 da 23 sai ya ce: (duk wanda ya raya waɗannan darare guda biyu da Muzakarar Ilimi shi ne Mafi Falala, [69] [yadasht 4] Ayatullahi Jawadi Amoli daga Maraji’an Taƙlidi ya naƙalto cewa mawallafin littafin Jawahir ya yi bayanin a ƙarshen shafin littafin jawahir yana cewa ina godiya ga Allah bisa cewa na kammala rubuta wannan littafi a daren 23 daga Ramadan, wannan yana nuna cewa Malamanmu suna shagaltuwa da ilmi a waɗannan darare, amma wasu mutanen suna hiyalin cewa neman ilimi da koyansa babban sabo ne a dararen ƙadri sai ka samu suna guje masa. [70]

Ayyukan Lailatul ƙadri

Ayyukan daren ƙadri sun kasu zuwa nau’i biyu: Ayyukan da ake yinsu cikin dukkanin dararen guda uku. Wanda aka fi sani A’amal Mushtarak [71] Kowanne ɗaya cikin dararen guda uku watan Ramadan. [72] Ayyukan daren ƙadri Ayyuka Mushtarak (ayyukan da dukkanin darare ukun suka yi tarayya cikinsu). Wanka. Sallah raka’a biyu, cikin kowacce raka’a bayan karatun Fatiha za a karanta suratul Tauhid kafa bakwai, bayan idar da sallah za karanta istigfari kafa 70

اَسْتَغْفِرُ اللّهَ وَاَتُوبُ اِلَیهِ

Raya dararen da ibada da rashin bacci. Sallah raka’a 100 tsakanin dukkanin raka’a biyu za a yi sallama. Karanta Du’a’u

«اَللهمَّ اِنّی اَمسیتُ لَکَ عَبداً...»

Karanta Du’a’u Jaushan Kabir Karanta Ziyarar Imam Husaini (A.S) ɗora Alkur’ani a ka tare da rantsuwa da Allah da kuma Imamai goma sha huɗu.

Daren Goma Sha Tara

Zikirin (Astagfirullaha Rabbi wa Atubu Ilaini) ƙafa 100 Zikirin (Allahumma Il’an ƙatalata Amiril Muminin) ƙafa 100 Du’a’u (Allahumma Ij’al fima taƙdi wa tuƙaddir minal amril Almahtum) ƙafa 100

Daren Ashirin Da ɗaya

Karanta Addu’o’in da suke da alaƙa da goman ƙarshen Ramadan. Karanta Du’a’u (Ya mulijal Al-Laili fin An-Nahar…)

Daren Ashirin Da Uku

Karanta Addu’o’in da suke da alaƙa da goman ƙarshen watan Ramadan. Karanta Surorin Ankabut da Rum da Dukhan. Karanta suratul ƙadri ƙafa 1000. Karanta Addu’o’in Jaushan Kabir, Makarimul Akhlaƙ da Iftitahu. Wanka a farkon daren da ƙarshen dare. Du’a’u: (Allahumma umdud li fi umri wa ausi’i li fi rizƙi...) Du’a’u: (Allahumma inni As’aluka fima taƙdi wa tuƙaddir minal amril mahtum…) Du’a’u: (ya baɗinan fiz zuhurihi wa ya zahiran fi buɗunihi…) Karanta Addu’ar newama Imam zaman (A.F) lafiya.

Al’adu da Ibadu

ƴan Shi’a a cikin kowacce shekara suna raya dararen lailatul ƙadri da ibada da muhadarori cikin gidaje, Masallatai, Hubbarori masu daraja, tun farko dare har zuwa Asubahi, [73] tare da karanta Addu’o’i misalin Du’a’u Abi Hamza, Jaushan Kabir da kuma karatun Alkur’ani. [74] da kuma bada sadakar abincin buɗa baki, da sauke bakance da suka yi, da yin sadaka ga ruhin waɗanda suka mutu da ciyar da Mabuƙa da dai sauransu. [75] Sakamakon shahadar Imam Ali (A.S) cikin goman ƙarshen watan Ramadan, ƴan Shi’a suna zaman makoki, [76] an ce a wasu garuruwa a ƙasar Iran a daren 27 ga watan Ramadan wanda shi ne daren da aka tsayar da haddi kan Abdur-Rahman BN Muljam (L.A) mutane suna shirya walimar farinciki, yawanci suna cin farfesun naman kai tare da tsinewa Makashin Imam Ali (A.S). [77]

Daren Lailatul ƙadri cikin Adabin Farisanci

Wannan dare ya samu himmatuwa hatta daga ɓangaren Mawaƙa. Sa’adi cikin littafinsa Gulistan dangane da daren ƙadri yana cewa (da a ce dukkanin darare sun kasance misalin daren ƙadri da daren lailatul ƙadri ya zamana bai da wata ƙima. [78] cikin littafin Bustan Sa’adi nan ma ya rera baitukan waƙa dangane da wannan dare mai daraja. [79] Sannan kuma Hafiz [80] Nasir Khosro, [81] Auhadi, [82] da sauran Mawaƙa suma duk sun rera waƙa dangane da wannan dare.

Sanin Littafi

An wallafa litattafai masu zaman kansu kan falalar Lailatul ƙadri, da ayyukan cikinsa. [83] daga jumlarsu akwai: Shabe ƙadri, talifin Muhammad Baheshti, Tehran, Buƙ’atu, bugun a shekara 1383 h shamsi. Shabe ƙadri: ƙalbe Mahe Ramadan, talifin Nasir Baƙiri Bidihindi, ƙum Bustane Kitab, bugu na biyu a shekara 1375 h shamsi. [84]

Bayanin kula

 1. Shaker, “Shabi bartar Az hezar Shab”, shafi na 48.
 2. Tabatabaei, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur'an, 1390, juzu'i na 20, shafi.331; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, juzu'i na 27, shafi na 187.
 3. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, juzu'i na 27, shafi na 187.
 4. Imam Khumaini, Adabus As-Salat, 1394, shafi na 324
 5. Imam Khumaini, Adabus As-Salat, 1394, shafi na 326
 6. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, juzu'i na 27, shafi na 188.
 7. Majidi Khamene, "Shabhaye ƙadri dar Iran", shafi na 1.
 8. Torbati, "Hamra Ba Ma'asuman dar Shab ƙadr", shafi na 33.
 9. Siyuti,Addurul Al-Manthur fi al-Tafsir Bel-mathur, 1420 AH, Mujalladi na 8, shafi na 570.
 10. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, shafi na 178
 11. Suratul Kadri, aya ta 2.
 12. Suratul Dukhan, aya ta 1-6.
 13. Hawizi, Tafsirul Noor Al-Saƙlain, 1415 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 918.
 14. Majlesi, Bihar-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 40, shafi na 54.
 15. . Hurrul Amili, Wasa'l Al-Shi'a, bugun cibaiyar Al-Al-Bait, Juzu'i na 10, shafi na 353.
 16. <a class="eɗternal teɗt" href="https://www.farsnews.ir/news/14020122000866/">شب قدر موهبتی الهی مخصوص مسلمانان/ ویژگی‌های قلب ماه رمضان را بشناسید</a>خبرگزاری فارس.
 17. Sheikh Tusi, Al-Tahzeeb, 1365, juzu'i na 4, h101, shafi.331.
 18. Majidi Khamene, "Shabhaye ƙadr dar Iran", shafi na 19.
 19. Duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 479; Kufi, Tafsir Furat Al-Kufi, 1410 AH, shafi na 581; Majlesi, Bihar-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 25, shafi na 97.
 20. Kufi, Tafsir Forat Al-Kufi, 1410H, shafi na 581.
 21. Tabatabaei, Al-Mizan fi Tafsirin ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 330; Shaker, "Shabi bartar az hezar Mah", shafi na 50.
 22. Misali, duba: Sheikh Tusi, Al-Tabyan fi Tafsir al-ƙur'an, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, juzu'i na 10, shafi na 384; Tabarasi, Majma'ul Al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, 1372, juzu'i na 10, shafi na 786; Tabatabaei, Al-Mizan fi Tafsirin ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 330; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, juzu'i na 27, shafi na 182.
 23. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, juzu'i na 27, shafi na 182.
 24. Duba: Sheikh Tusi, Al-Tabyan fi Tafsir al-ƙur'an, Dar Ihya Al-Turath al-Arabi, juzu'i na 10, shafi na 384; Tabarasi, Majma al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, 1372, juzu'i na 10, shafi na 786; Ansari, “Nuzul Ijmali ƙur’an”, shafi na 227.
 25. Kulaini, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi 160.
 26. Al-Sheikh Hurrul Amili, Wasa'il Al-Shia, Al-Bait, juzu'i na 10, shafi na 353
 27. Tabatabaei, Al-Mizan fi Tafsir ƙur'an, 1390, juzu'i na 20, shafi na 331.
 28. Sadouƙ, Ma'ani Al-Akhbar, 1403 AH, shafi na 315 da 316.
 29. Majlesi, Bihar-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 94, shafi na 17
 30. Kashani, Tafsirul Manhaj Al-Sadikin, 1340, juzu'i na 10, shafi.308.
 31. Suratul ƙadr, aya ta 4.
 32. Majlisi, Bihar-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 46, shafi na 272.
 33. Majlisi, Bihar-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 97, shafi na 14
 34. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 25, shafi na 71-72.
 35. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan fi Tafsirul Al-ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 331; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, juzu'i na 27, shafi na 190.
 36. Hurrul Amili, Wasa'lul Al-Shi'a, Al-Al-Bait, Juzu'i na 10, shafi na 356
 37. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, juzu'i na 27, shafi na 190.
 38. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan fi Tafsirul Al-ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 334.
 39. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan fi Tafsirul Al-ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 334; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1375, juzu'i na 27, shafi na 188.
 40. Ɗabaɗaba'i, al-Mizan fi Tafsirul Al-ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 334
 41. Tabarasi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 786.
 42. Majlesi, Mir'atul Al-Uƙool, 1404 AH, juzu'i na 16, shafi na 381.
 43. Ɗabaɗaba'i, Al-Mizan fi Tafsirul Al-ƙur'an, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 334.
 44. Saduk, Al-Khesal, 1362, shafi na 519.
 45. Kashani, Manhaj Al-Sadeghin,Kitabe Furushi islami, juzu'i na 10, shafi na 306.
 46. Misali, duba: Saduk, Man La yahzara Al-Faƙihu, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 160.
 47. Majlesi, Mir'atul Al-Uƙool, 1404 AH, juzu'i na 16, shafi na 381.
 48. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi na 4, shafi na 159 da 160.
 49. Kashani, Manhaj al-Sadeghin, 1344, juzu'i na 4, shafi na 274, be Nakal az Eftekhari, "Du'a'u Shab Al-ƙadr Az Manzare Musa Sadr", shafi na 17.
 50. Sheikh Saduk, Man La Yahzara Al-Faƙihu, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 160.
 51. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 97, shafi na 3-5.
 52. Duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 156; Sheikh Saduk, Man La Yahzara Al-Faƙihu, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 160.
 53. Majlisi, Lowame Sahib-ƙarani, 1404 AH, juzu'i na 6, shafi na 599.
 54. Siyuti, Addurul Al-Manthur Fi al-Tafsir Bel-mathur, 1420 AH, Mujalladi na 8, shafi na 571.
 55. Ɗabaɗaba'i, Tafsirul Al-Mizan, 2013, juzu'i na 20, shafi.334.
 56. Ghasemi, Tafsir Al-ƙasimi, Beta, juzu'i na 17, shafi na 217.
 57. Ibn Al-Miftah, Sharh Al-Azhar, Bita, juzu'i na 1, shafi na 57.
 58. Ibn Al-Miftah, Sharh Al-Azhar, Bita, juzu'i na 1, shafi na 57.
 59. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 786.
 60. Sheikh Tusi, Al-Tahzeeb, 1365, juzu'i na 3, shafi na 85.
 61. Mokhtari, Ruyait Hilal, 1426 AH, juzu'i na 4, shafi 2972.
 62. Makarem Shirazi, Estaf'ta'at Jadid, 1427 AH, juzu'i na 3, shafi na 103.
 63. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1375, shafi na 192.
 64. Majlisi, Bihar-Anwar, juzu'i na 95, shafi na 145, be nakle az Torbati , "Hamra Ba Ma'asuman dar lailatul kadri", shafi na 33.
 65. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403H, juzu'i na 94, shafi na 9-10, Be nakale az Shakir, "Shabe bartar az hezar Mah", shafi na 52.
 66. Mostadrak Al-Wasa'il, juzu'i na 7, shafi na 470, be nakale az : Torbati, "Hamra ba Ma'suman dar lailatul kadri", shafi na 34.
 67. Torbati, "Hamra Ba Ma'asuman dar Shab ƙadr", shafi na 32.
 68. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 97, shafi na 4.
 69. Sheikh Saduk, AMali, Mu'assatul Al-Besath, 1417H, shafi na 747
 70. <a class="eɗternal free" href="https://jaɓadi.esra.ir/fa/w/مبلغان-و-مفسران-وظیفه-دارند-به-شبهات،-پاسخ-عالمان">https://jaɓadi.esra.ir/fa/w/مبلغان-و-مفسران-وظیفه-دارند-به-شبهات،-پاسخ-عالمان</a>
 71. Makarem Shirazi, Mafatih Noɓin, 2005, A'amal Maha, Zailu A'amal Mushtarak shabhaye Kadr, shafi na 759.
 72. Makarem Shirazi, Mafatih Noɓin, 2005, A'amal Maha, Zailu A'amal Maksus Shabhaye ƙadri, shafi na 762.
 73. Majidi Khamene, "Shabhaye ƙadr dar Iran", shafi na 21.
 74. Majidi Khamene, "Shabhaye ƙadr dar Iran", shafi na 22
 75. Majidi Khamene, "Shabhaye ƙadr dar Iran", shafi na 22
 76. Majidi Khamene, "Shabhaye ƙadr dar Iran", shafi na 19
 77. Majidi Khamene, "Shabhaye ƙadr dar Iran", shafi na 21
 78. Kulliyat Saadi, Golestan, 2007, babi na 8 na Adabu Suhubat, shafi na 100.
 79. Kulliyat Saadi, 1387, Mawa'iz, Ghazal 9, shafi na 604.
 80. Diwan Hafez, 2006, Ghazal No. 206, shafi 164.
 81. Diwan Nasser Khosrow, 1357,ƙasayid, shafi na 141.
 82. Diɓan Auhadi, 1340, h shamsi 231.
 83. <a class="eɗternal teɗt" href="https://bookroom.ir/news/29282">کتاب‌شناسی شب‌های قدر</a>بگاه پاتوق کتاب فرد<a class="eɗternal teɗt" href="https://www.ibna.ir/fa/report/276042">کتابشناسی آثار منتشر شده درباره شب های قدر در یک دهه اخیر در قم</a>خبرگزاری کتاب ایران.
 84. duba:<a class="eɗternal teɗt" href="https://bookroom.ir/news/29282">کتاب‌شناسی شب‌های قدر</a>

Nassoshi

 • Al-ƙur'an Al-Kareem
 • Ibn Al-Muftah, Abdullah, Sharh Al-Azhar, Al-Hijaz, Alkahira, Bita.
 • Eftekhari, Sayyid Ataullah, “Du'a wa Shabe ƙadri az Manzare Musa Sadr”, dar Mujalle Ulum Kur'an wa Hadis mai lamba 3, winter 2009.
 • Al-ƙasimi, Mohammad Jamaluddin, Tafsir Al-ƙasimi, Beirut, Beta.
 • Auhadi Maraghei, Diwan She'er, edited by Saeed Nafisi, Tehran, Amir Kabir Publishing House, 1340.
 • ‌ «جستجوی کتاب: شب قدر»، شبکه جامع کتاب گیسوم، تاریخ بازدید: ۲۱ فروردین ۱۴۰۲ش.
 • Hafez Shirazi, Shamsuddin, Diwan Hafez, Mohammad ƙazɓini da Dr. ƙasim Ghani , Nashare ƙom, bugun Kome, 2006.
 • Hawizi, Ali bin Juma, Tafsirul Noor Al-Saghalin, ƙum, Ismaili, 1415H.
 • Saadi, Moslehuddin, Kulliyat Saadi, Mohammad Ali Foroughi, Tehran, Parse Publishing House, ya sake dubawa, 1387.
 • Seidenjad, Razi, "Bazkoni wa Negahe dubare be fada'il wijegihaye shabe ƙadr, dar mujallae Payam halayen Shab ƙadr", No. 118, Spring 2015.
 • http://www.imam-khomeini.ir/fa/
 • Siyuti, Jalal al-Din Abd al-Rahman bin Abi Bakr, Al-Durrul Al-Manthur Fi al-Tafsir Bel mathur, Beirut, Darul-Fikr, 1420H.
 • Shaker, Abu al-ƙasim, "shabi bartar az hezar Mah", dar mujalle "Morabian", lamba 36, ​​bazara 2018.
 • Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, al-Khesal, bugun Ali Akbar Ghafari, Kum, Jamia Modaresin, 1362.
 • Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Ma'ani al-Akhbar, ƙum, Islamic publiiled with the Madrasin community, 1379.
 • Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Man La yahzara al-Faƙihu, Ali Akbar Ghafari, ƙum, Islamic Publications, bugu na biyu, 1413 AH ya yi bincike kuma ya gyara shi.
 • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Tahzib, Tehran, Darul Katb al-Islamiyya, 1365.
 • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, al-Tabyan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Dar Ahya al-Tarat al-Arabi, Bita.
 • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Al-A'lami Institute, bugu na biyu, 1390H.
 • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosro, 1372.
 • Abedinzadeh, Ahmed, "Imam wa Lailatul ƙadr", a cikin mujallar Alƙur'ani da ilmin Hadisi, lamba 82, rani 2009.
 • Abedinzadeh, Ahmed, "Gata da al'adun Shab ƙadr", a cikin Mujallar Fiƙh da Usul, No. 131, Agusta da Satumba 2009.
 • ƙabadiani, Nasser Khosrow, Diwan She'er, Mojtabi Minaɓi, Tehran, Institute of Islamic Studies, 1357 ya gyara.
 • Kadamyari, Karam Ali, "Shab ƙadr Ghazliat Hafez", a cikin Mujallar Binciken Rubutun Adabi, Na 17, bazara da bazara 2013.
 • Kashani, Molafathullah, Tafsir Manhaj al-Sadeghin, Tehran, Ilmi, 1340.
 • «کتاب‌شناسی شب‌های قدر»، وبگاه پاتوق کتاب فردا، تاریخ درج مطلب: ۱۴ تیر ۱۳۹۴ش، تاریخ بازدید: ۲۱ فروردین ۱۴۰۲ش.
 • «کتابشناسی آثار منتشر شده درباره شب های قدر در یک دهه اخیر در قم»، خبرگزاری کتاب ایران، تاریخ درج مطلب: ۴ خرداد ۱۳۹۸ش، تاریخ بازدید: ۲۱ فروردین ۱۴۰۲ش.
 • Kulaini, Mohammad bin Yaƙub, Usulul Al-Kafi, Tarjameh Mohammad Baƙer Kameraei, ƙum, Osweh, 1375.
 • Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, al-Kafi,tahƙiƙ wa tashih Ali Akbar Ghafari wa Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na hudu, 1407H.
 • Kufi, Firat bin Ibrahim, Tafsir Furat Al-Kufi, tahkik Mohammad Kazem, Tehran,weazarat farhang wa isrhad Islami, bugu na farko, 1410H.
 • Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar al-Ahiya al-Trath al-Arabi, 1403H.
 • Majlesi, Mohammad Baƙir, Mir'atul Al-Uƙool fi Sharh Akhbar Al-Ar-Rasoul, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na biyu, 1404H.
 • Majlesi, Mohammad Taƙi, Lowami Sahib- Alƙur'an Mashhur be Sharh Fakih, bugu na 2, 1404H.
 • مجیدی خامنه، فریده، «شبهای قدر در ایران»، در مجله گلستان قرآن، شماره ۳۷، آذر ۱۳۷۹ش.
 • Mokhtari, Reza da Mohsen Sadeghi, Ruyat Hilal, ƙum, Intisharat DaftareTabligat Addini Islami, 1426 Hijira.
 • Masoudi, Mohammad Mahdi, "Shab ƙadr", Dar MUjallaeh Ulum Hadis, lamba 35 da 36, ​​bazara da bazara 2004.
 • Melabi, Masoud wa Majid Sadeghi, "Lailatul ƙadri dar neagahe Mufassiran", dar mujallaeh Alƙur'an wa ulum Hadis, lamba ta 39, rani 2013.
 • Makarem Shirazi, Nasser, Estafta'at Jadid, ƙum, Instisharat Madraseh Ali Bin Abi Talib, 1427H.
 • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1375.
 • Makarem Shirazi, Nasser, Mofatih al-Janan Noɓin, ƙum, Wallafar Madraseh Ali Bin Abi Talib, 1385.
 • Wafa, Jafar, "shabe ƙadri az manzare Alƙur'an", dar mujalle Habal al-Mattin (Bakin Sama) lamba 1, rani 2013.
 • شب قدر موهبتی الهی مخصوص مسلمانان/ ویژگی‌های قلب ماه رمضان را بشناسید، خبرگزاری فارس، تاریخ درج مطلب: ۲۲ فروردین ۱۴۰۲، ۱۳ خرداد ۱۴۰۲.