Kwanakin Goman Ƙarshen Watan Safar

Daga wikishia
Majalisin Makokin Na Shi'a A Arba'in (Rana Ta Farko A Gomar Karshen Watan Safar) A Karbala

Kwanakin goman ƙarshen Safar, (Larabci: عشرة صفر) ko kuma goman karshen watan Safar, suna farawa ne daga ranar ashirin zuwa karshen watan Safar, kuma sun haɗa da arba'in ta Imam Husaini (A.S), da shahidan Karbala, wafatin Manzon (S.A.W) da shahadar Imam Hassan (A.S) da Imam Rida (A.S) a wannan ranaku `yan Shi'a suna cikin zaman makoki. Kamar yadda ranar ashirin ga watan Safar ta zo daidai da ranar arba'in na shahadar Imam Husaini (A.S), da shahidan Karbala,[1] da kuma ranar 28 ga watan Safar ta yi daidai da zagayowar ranar wafatin manzon Allah (S.A.W)[2] da shahadar Imam Hashan (A.S),[3] kuma a ranar karshe ta Safar ta yi daidai da shahadar Imam Rida (A.S).[4] Ranar farko ta goman karshe na watan Safar (ranar 20 ga watan Safar) ana kiranta da ranar Arba'in,[5] kamar yadda ruwayoyin Shi'a suka ɗarfafa ziyarar Arba'in a wannan rana.[6] Sabo da wannan tattakin Arba'in, ana kafa tantina a kan hanyar sabo da zuwa masu ziyara waɗanda suke zuwa dayawa daga yanki daban daban daga ƙasashen duniya domin ziyarar Imam Husaini (A.S) a ranar arba'in.[7]

A Iran ma ana gudanar da tarukan zaman makoki na kwanaki goma na karshen watan Safar da kuma goman farkon watan Muharram.

Bayanin kula

  1. Muhadidsi na, Farhang Ashoura, shafi na 45.
  2. Al-Qummi, Muntaha Al-Amal, juzu'i na 1, shafi na 249.
  3. Al-Tabarsi, I’lam Al-Wara, juzu’i na 1, shafi na 403.
  4. Al-Tabarsi, I’lam Al-Wara, juzu’i na 1, shafi na 403.
  5. Mazaheri, Farhang Sugh Shia, shafi na 99.
  6. Al-Tusi, Tahdheeb Al-Ahkam, juzu'i na 6, shafi na 52.
  7. Mazaheri, Farhang Sugh Shia, shafi na 99.

Nassoshi

  • Al-Tabarsi, Al-Fadl bn Al-Hasan, 'Ilam Al-Wara bi'lam Al-Huda, Qom, Mu'assasa Al-Bait don Rayar da Al'adunmu, bugu na 1, 1417 Hijira.
  • Al-Tusi, Muhammad bin Al-Hasan, 'Tahdheeb Al-Ahkam, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, bugu na 4, 1365H.
  • Al-Qumi, Abbas, Muntaha al-Amal fi Tarikh al-Nabi wa al-Ahl, Kum, Hujja, 1379H.
  • Muhaddiththi, Jawad, Farhang Ashura (Al'adun Ashura), Kum, sanannen bugu, 1376H.
  • Mazaheri, Mohsen Hossam, Farhang Sugh Shi'i (Al'adun Ta'aziyyar Shi'a), Tehran, Khaymeh Publishing, 1395 AH.