Danne Fushi

Daga wikishia
(an turo daga Kame fushi)

Kame fushi (Larabci: كظم الغيظ), yana daga cikin kyawawan dabi'u, ma'ana nisantar fushi, Alkur'ani mai girma ya yi la'akari da shi a matsayin ɗaya daga cikin sifofi masu kyau, kuma ruwayoyi sun yi nuni kan alfanunsa, kamar samun yardar Allah da tsira daga azaba, malaman aklaƙ sun yi bincike kan wannan siffa ƙarƙashin aibobin da fushi yake haifarwa, kuma sun ambaci hanyoyin da za a bi domin magance fushi. Haƙiƙa Imam Musa Kazim (A.S), ya siffantu da wannan ɗabi'a ta kame fushi a tarihinshi, saboda haka ne ma wannan siffa ta zamo daga cikin sanannun laƙubbanshi.

Abin da Wannan Siffa Take Nufi

kalmar "Gaizu" tana nufin Fushi mafi tsananin fushi, kuma shi ne zafin da ke faruwa a cikin zuciyar mutum idan jininshi ya tafasa (abin nufi idan ranshi yaɓaci)[1] Alkazmu yana nufin danne zuciya a lokacin fushi, kuma danne fushi kalma ce ta ɗabi'a ko halayya, wace take nufin kame fushi da kamewa daga nuna shi ta hanyar magana ko aiki[2] ana amfani da kalmar Alkazim kan wanda ya saba danne fushinshi.[3]

Ma'anar danne fushi, yana kusa da ma'anar haƙuri, kuma daga nan masana ilimin akalaƙ suka ce, dangane da bambanci tsakanin danne fushi da haƙuri, danne zuciya (kan wasu abubuwa da suke ɓatawa mutum rai) ga mutumin da yake da haƙuri,to shi ake ƙira da "Hilmu", amma danne zuciya ga mutuman da bashi da haƙuri, kawai yana ƙoƙarin danne fushin shi, to shi ake da Kazmul Gaiz (danne zuciya ko kame fushi).[4]

Alƙur'ani ya faɗa mana cewa, kame fushi yana daga cikin siffofin masu kyautatawa, yayin da yake cewa,

وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ

ma'ana da masu danne fushinsu da masu yiwa mutane afuwa, Allah yana son masu kyautatawa,[5] kuma riwayoyi daga Imamai ma'asumai sun zo suna ƙarfafa siffantuwar mumini da wannan sifa,[6] kamar yadda Kulaini ya kawo wata ruwaya a cikin littafinshi Alkafi a babi na Kame fushi,[7] Imam Sajjad (A.S) ya yi nuni kan kame ko danne ko shanye fushi a cikin addu'arshi ta Makarimul aklaƙ a cikin Sahifa sajjadiyya,[8] ruwayoyi da yawa sun zo kan tasirin kame fushi, daga cikin akwai buwaya da ɗaukaka da kuma tsira daga azaba da samin yardar Allah, Annabi (S.A.W), ya ce duk wanda ya kame fushi shi, to Allah ba zai mashi azabarshi ba.[9]

Hanyoyin Magance Matsalar Fushi

Malamai masana halayyar ɗan adam, sun ambaci fushi a ƙarƙashin halayya marar kyau,[10] sun faɗi hanyoyin da za a shawo kan fushi da maganceshi:[11]

hanyoyi na ilimi:

  • Yin tinani kan ruwayoyin da suke umarni kan danne fushi da yin haƙuri da afuwa da kuma ladan da mutum zai samu idan ya aikata hakan.
  • Tinani kan ƙudirar Allah da fushinsa
  • Mutum ya yi tinani kan munin kamaninsa idan ya yi fushi kuma ya tina kamannin wani a lokacin da ya yi fushi.
  • Mutum ya yi magana da kanshi kan sakamakon yin ƙiyayya da ɗaukar fansa.[12]

hanyoyin a aikace domin shawo kan fushi

  • Faɗar neman tsari.
  • Canja yanayin da mutum yake ciki, misali ya zauna idan a tsaye yake ko kuma ya kishingiɗa idan a zaune yake.
  • Ya yi alwala domin kwantar da fushi. Ya zo a cikin wasu ruwayoyi cewa; shi fushi daga wuta yake, babu abin da yake kashi wuta sai ruwa.[13]
  • Mutum idan ya yi fushi, to ya ɗora kumatunshi kan ƙasa.

An rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa; ku sani shi fushi garwashi ne a cikin zuciyar ɗan adam, shin baku lura ba da garwashaan da yake cikin idansa da kunburar jijiyoyinshi? Duk wanda ya sami kanshi a cikin irin wannan hali (wato idan mutum ya yi fushi.) to ya ɗora kuncinshi kan ƙasa, sai Warama ɗan Abi Faris ya ce abin da ake nufi da ɗora kunci kan ƙasa, shi ne yin sujjada, domin mutum ya ji ƙasƙanci, da haka ne sai ya iya shawo kan fushinshi.[14]

Kame Fushin Imam Musa ɗan Ja'afar

Haƙiƙa Imam Musa ɗan Ja'afar (A.S) ya shahara da laƙabin Kazim (mai danne ko kame fushi), saboda ya kasance yana kyautatawa wanda ya musgunamashi, kuma hakan ita ce al'adarshi kodayaushe,[15] haƙiƙa akwai ƙissosi daban-daban a cikin litattafai na tarihi kan danne fushishi kan maƙiyanshi da kuma waɗanda suka musgunamasa,[16] ga abin da aka rawaito kan haka;

Wani mutum jikan Umar ɗan Khaɗɗab ya kasance yana musgunawa ImamuMusa ɗan Ja'afar (A.S), ta hanyar zagin kakanshi Imam Ali (A.S), sai sahabban Imam Musa ɗan Ja'afar suka so su ɗauki fansa a kanshi ta hanyar yi masa kisan gilla, sai Imam ya hana su aikata hakan, bayan wani lokacin sai Imam ya tafi gurinshi, sai ya sameshi a gonarshi, yana ganin Imam sai ya yi sauri yace, ka da ka taka min shukata! Sai Imam ya ci gaba da tafiya har ya je gurinshi, sai ya ce mishi cikin tattausar murya da tausayi, nawa ka kashe kan wannan shuka? Sai mutumin ya ce Dinare ɗari, sai Imam ya tambayeshi, kuma nawa kake fatan za ka samu? Sai mutumin ya ce, ni bansan Gaibu ba, sai Imam ya ce, ni kawai na ce maka ne, nawa kake tinanin za ka samu? Sai ya ce, ina fatan na sami dinare ɗari biyu, sai Imam ya ba shi dinare ɗari uku, ya ce mishi wannan naka ne, kuma shukarma taka ce, sai Imam ya juya ya tafi zuwa masallaci, lokacin da Imam ya shiga cikin masallaci, kawai sai ga wannan mutumin a ciki a zaune, sai wannan mutuman ya tashi daga gurinshi, sai ya karanta wannan ayar;  :﴿اللهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِ‌سَالَتَه٨] ma'ana: Allah shi ne mafi sani inda ya kamata ya ba da saƙonsa.[17][18]

Bayanin kula

  1. Al-Isfahani, Mufradat Al-AlFazil Al-Qur’an, shafi na 619.
  2. Al-Isfahani, Mufradat Al-AlFazil Al-Qur’an, shafi na 712
  3. Al-Naraqi, Jami’ al-Saadat, juzu’i na 1, shafi na 333; Al-Ghazali, Ihya’ Ulum al-Din, juzu’i na 3, shafi na 176.
  4. Al-Naraqi, Jami’ al-Saadat, juzu’i na 1, shafi na 333; Al-Ghazali, Ihya’ Ulum al-Din, juzu’i na 3, shafi na 176.
  5. Al Imrana: 134.
  6. Al-Kulayni, juzu'i na 2, shafi na 109-111; Al-Fayd al-Kashani, Al-Mahjat Al-Bayda, juzu'i na 5, shafi na 306-307.
  7. Al-Kulayni, juzu'i na 2, shafi na 109-111; Al-Fayd al-Kashani, Al-Mahjat Al-Bayda, juzu'i na 5, shafi na 306-307.
  8. Assahifa Al-Sajjadiyya, Duaa 20..
  9. Al-Fayd al-Kashani, Al-Mahjat Al-Bayda, juzu'i na 5, shafi na 306-307.
  10. Warram, Majmu'atu Warram, juzu'i na 1, shafi na 123 da 124.
  11. Al-Fayd al-Kashani, Al-Mahjat Al-Bayda, juzu'i na 5, shafi na 306 da na 307.
  12. Al-Fayd al-Kashani, Al-Mahjat Al-Bayda, juzu'i na 5, shafi na 306 da na 307.
  13. Al-Fayd al-Kashani, Al-Mahjat Al-Bayda, juzu'i na 5, shafi na 306 da na 307.
  14. Warram, Majmu'atu Warram, juzu'i na 1, shafi na 124.
  15. Ibn al-Atheer, Al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 6, shafi na 164; Ibn al-Jawzi, Tadhkirat al-Khawas, shafi na 312.
  16. Al-Mufid, Al-Irshad, juzu'i na 2, shafi na 233; Al-Qurashi,Hayatu Imam Musa bin Jaafar, juzu'i na 2, shafi na 160-162.
  17. Suratul An'am: 124.
  18. Al-Baghdadi, Tarikhu Baghdad, juzu'i na 13, shafi na 30.

Nassoshi

  • Sahifa Al-Sajjadiya.
  • Ibn al-Atheer, Ali bin Muhammad, 'Al-Kamil fi al-Tarikh, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Sader, 1385H.
  • Sibt Ibn al-Jawzi, Yusuf, 'Tadhkirat al-Khawas, Qom - Iran, mawallafi: Al-Sharif Al-Radi, 1418H.
  • Al-Khatib al-Baghdadi, Ahmed bin Ali, ' Tarikh Baghdad , edita: Mustafa Abdulqadir Atta, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Kutub Al-Ilmiyya, 1417 Hijira.
  • Al-Raghib Al-Isfahani, Al-Hussein bin Muhammad, Mufradat Al-Alfazil Alqur'an', mai gyara: Safwan Adnan, Damascus - Syria, mawallafi: Dar Al-Qalam - Dar Al-Shamiya , 1412 AH.
  • Al-Ghazali, Muhammad bin Muhammad, Ihya Ulum al-Din, Beirut - Lebanon, Publisher: Dar Al-Ma'rifa, D.T.
  • Al-Qurashi, Baqir Sharif, 'Hayat Imam Musa bin Jaafar, (A.S), mai bincike: Mahdi Baqir Al-Qurashi, D.M., Mawallafi: Mehr Dildar, 1429 Hijira.
  • Al-Fayd Al-Kashani, Muhammad bin Murtada, Mahajjatul Albayda, mai gyarawa: Ali Akbar Al-Ghafari, Qom - Iran, mawallafi: Mu'assasar Daba'ar Musulunci, D.T.
  • Al-Kulayni, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, proofreaders: Ali Akbar Al-Ghafari and Muhammad Al-Akhundi, Tehran - Iran, publisher: Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1407 AH.
  • Al-Mufid, Muhammad bin Numan, 'Al-Irshad, Qom - Iran, Mawallafi: Taron Sheikh Al-Mufid, 1413H.
  • Dumi, Ibn Abi Firas, Majmu'atu Waram, Kum - Iran, Mawallafi: Laburaren Shari'a, 1410H.
  • Al-Naraqi, Muhammad Mahdi, Jami'us Saadat, Beirut - Lebanon, Publisher: Al-Alami Publications Foundation, D.T.