Hadisan An Gina Muslunci Kan Rukunai Biyar

Daga wikishia

Hadisan gina ginshiƙan musulinci (larabci:أحاديث بُنِي الإسلام) hadisai ne da suka zo a cikin litattafan shi'a da ahlus-sunna kuma an rawaito su ne daga Annabi (s.a.w) da Imaman shi'a (a.s). kuma su hadisan suna magana ne kan ginshiƙan da aka gina musulinci a kai, wasu hadisai sun nuna cewa waɗannan sune rukunan musulinci ga su kamar haka: sallah, zakka, aikin hajji, azumi wilaya, a cikin wasu hadisan an ambaci kalmomin shahada guda biyu maimako wilaya, kuma kamar yadda dukkansu sun zo tare a wasu hadisan. Amma hadisan da suka zo a litattafan shi'a sun ƙarfafa muhimmancin wilaya. sun siffanta wilaya da cewa tafi duk sauran rukunan muhimmanci, wasu hadisai sun bayyana musulunci da wani gida da aka gina wanda ginshiƙan shi sune waɗannan abubuwa guda biyar da suka gabata, idan suka tabbata to shi ma gidan zai tabbata, ya kuma kafu da kyau, idan kuma suka rushe to ginin gidan bakiɗaya zai ruguje. Waɗannan hadisan masu naƙalto ruwaya misalin Abi hamza sumali, Fudailu Ɗan yasar, Zurara Ɗan A'ayan, Mufaddal Ɗan Umar da Abdullahi Ɗan Umar, malaman shi'a da malaman ahlus-sunna suna ganin inagncin galabin hadisan.

Nassin hadisi

Hadisan shiƙashiƙan musulunci guda biyar, waɗanda aka kawo a cikin litattafan hadisi tare da bambance-bambance daga Annabi (S.A.W),[1] da kuma imaman shi'a.[2]

  • An gina musulunci akan abubuwa biyar, shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah kuma Muhammad (s.a.w) bawan sa ne, kuma ɗan aiken shi ne. tsaida sallah da bada zakka da aikin hajji da azumin watan ramadana....

Wannan hadisin ya zo a litattafan Ahlus-sunna wanda aka naƙaltoshi daga Annabi (s.a.w),[5] a litattafan Shi'a daga daga Imam Baƙir (a.s).[6]

  • Imam Sadiƙ (a.s) ya ce, a lokacin da yake bawa Isah Ɗan Sirri amsa wanda ya tambaye shi akan rukunai da shikashikan muslunci sai ya ce, na farko shi ne, shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da shedawa da cewa Muhammad (s.a.w) manzon Allah ne, da kuma Iƙrari cewa duk abin da ya zo da shi to daga Allah ne, da kuma yarda da haƙƙin zakka a cikin dukiyar shi, da kuma yin imani da wilaya wacce Allah maɗaukaki ya yi umarni da abita wacce take wilaya ce ga iyalan gidan annabi Muhammad (s.a.w).[7]
  • Imam Sadiƙ (a.s) ya ce, ginshiƙan muslunci guda uku ne, Sallah, Zakka, da kuma Wilaya, kuma kowace ɗaya ba zata inganta ba ba tare da `yar uwarta ba.[8]

Ƙarfafawa Kan Muhimmancin Wilaya

Ku lura da abin da ya zo a hadisai waɗanda aka rawaito, wanda suke ƙarfafa wilaya a litattafan shi'a daga abin da ya kevanci hadisin gina muslunci, akwai ƙare-ƙare da suka zo domin ƙarfafa batun wilaya, daga cikinsu akwai misalin:

1. Ba a kira zuwa ga wani abu ba kamar yadda aka yi kira zuwa ga wilaya, sai mutane suka yi riƙo da hudu, suka yi watsi da wilaya.[9]

2. Zurara ya ce, sai na ce: wanne ne yafi fifiko a cikin ginshiƙan nan guda biyar? Sai Imam ya ce, wilaya ce tafi komai fifiko...[10]

3. Ba a yi shela kan wani abu ba kamar yadda aka yi shela kan wilaya a ranar ghadir khum.[11]

Wasu daga cikin hadisan gina muslunci kan abubuwa biyar sun yi bayani da ambatar wilayar Imam Ali (A.S) ƙarara da sauran Imamai (a.s), kamar yadda ya zo a cikin waɗannan hadisan kamar haka, wilayar Imam Ali da sauran imamai daga tsatson shi (a.s).[12]

abubuwan da hadisin yake nufi

Bisa abin da ya zo a wasu hadisai rukunan musulici,su ne abubuwa da bai halasta ba a ce mutum bai san su ba sannan bai halasta ba a ce mutum ba ya aiki da su, wato bai halasta ba ace mutum ba ya ɗabbaƙa su ba, duk wanda bai san su ba ko kuma bai san ɗaya daga cikinsu ba, to addininsa yana da matsala, ba za a karɓi aikin shi ba. kuma duk wanda ya san su kuma ya yi aiki da su, to addininsa ya inganta, kuma za a karɓi aikinsa, kuma ba zai shiga takura b sabo da ya jahilci wasu abubuwa da bai saniba.[13] saboda haka nema aka ce a cikin hadisan gina musulinci kan abubuwa biyar haƙiƙa musulinci an kamantashi da wani gini ko gida wanda yake da ginshiƙai guda biyar, idan har suka kafu suka yi ƙarfi, to lalle gida ko gini zai kafu kuma zai yi ƙarfi, amma idan wannan ginshiƙan nashi ba su kafu da kyau ba, to fa ginin zai ruguje, kazalika musulinci, yana kafuwa ne da tabbata yayin da ginshiƙan shi suka tabbata, kuma idan har ba su tabbata to zai ruguje, saboda haka duk wanda yake aiki da rukunan musulinci guda biyar lallai addininsa zai cika.[14]

Rukunan musulinci guda biyar waɗanda suka zo a cikin hadisai sune rukunai na asali na musulinci.[15] amma wajibai da mustahabbai su suna cika shi ne da kammala shi.[16]

Allama Ɗabaɗaba'i yana tinanin cewa, ita wilaya ta kunshi kalmar shahada, ko kuma rashin zuwan su a hadisan, ya faru ne sakamakon bayyanarsu ƙarara.[17]] kuma an anbaci dalilai uku da suka sa aka anbaci wilaya. na farko, ita wilaya tana daga cikin aƙida wanda ake imani da ita tare da sauran rukunai guda huɗu waɗanda suke su kuma abubuwa ne na rassa da ibada, domin tafiya da Ahlussunna kamar yadda aka bayyana cewa wilaya tana nufin soyayya da biyayya, kuma abin da ake nufi da sauran ginshiƙai guda hudu shi ne ayi imani da su, to idan akayi imani da su, za su zamo rukunai na addini da kuma larurin addini.[18]

Y azo a cikin wasu hadisai cewa an jeranta rukunan musulinci ne bisa muhimmancinsu wato na ɗaya ya fi na biyu muhimmanci har ƙarshan na biyar, ita wilaya ita ce mafificin rukuni, sabo da ita ce ki da ɗan mukullin sauran ginshikai bayan wilaya kuma sai sallah, ita kuma ita ce ƙashin bayan addini sai zakka saboda an gwamata da sallah cikin ayoyin Kur'ani kuma tana tafiyar da zunubi, kuma tafi sauran rukunai guda biyu da suka zo daga bayanta wato hajji da kuma azumi waɗanda suke zuwa a matsayi na ƙarshe.[19]

Waɗanda suka Rawaito Hadisin

hadisan gina musulinci bisa ginshiƙai guda biyar masu kawo ruwaya sanannu sun kawo su kamar Abi hamza sumali,[20] da Fudailu Ɗan Yasar,[21] da Zurara Ɗan A'ayun.[22] da Abdullahi Ɗan Ajlan daga Imam Baƙir (A.S).[23] da kuma Isa ɗan Sarriyi.[24] da Mufaddal Ɗan Umar daga Imam Sadiƙ (A.S).[25] da Abdullahi Ɗan Umar daga Annabi (s.a.w).[26]

Ingancin hadisin

Allama Majlisi ya ce, isnadin da aka samu daga wasu hadisan gina Musulunci, kamar hadisin da Isah Ɗan Sarri da Zurara, da Fudail Ɗan Yasar suka ruwaito ingantaccen isnadi ne, kuma ya ce wasu daga cikin hadisan da aka ruwaito masu rauni ne.[27] Amma malaman Ahlus-sunna, sun bayyana cewa, abin da Abdullahi ɗan Umar ya ruwaito ya zo a cikin Sahihul Bukhari,[28] Bayan haka kuma ya zo a cikin Sahihu Muslim.[29] Wasu kuma daga cikinsu sun bayyana ingancinsa ƙarara kamar: Tirmizi da Nasa'i, da Nawawi[30]

Bayanin kula

  1. Muslim, Sahihu Muslim, Dar Revival of Arab Heritage, juzu'i na 1, shafi na 45.
  2. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 2, shafi na 18-24, babul Da'imil Islam; , shafi na 13-29, babi na 1.
  3. Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 18, h. Al-Saduq, Al-Khisal, 1983 Miladiyya. Sashe na 1, shafi na 278, h. Al-Tusi, Al-Amali, 1414H, shafi na 124.
  4. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 7.
  5. Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422, juzu'i na 11, shafi na 26; Muslim, Sahih Muslim, Dar Revival of Arab Heritage, juzu'i na 1, shafi na 45; Al-Tirmizi, Sunan Al-Tirmidhi, 1395 AH, juzu'i na 5, shafi na 5.
  6. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 1.
  7. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 19-21, h. Al-Tusi, Al-Amali, 1414H, shafi 518, h.
  8. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 4.
  9. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 1 da na 3.
  10. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 5.
  11. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 2, shafi na 8.
  12. Al-Saduq, Al-Amali, 1997 AD. shafi 268, h.
  13. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 2, shafi na 19 da 20, na 6.
  14. Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422, juzu'i na 1, shafi na 11; Al-Nawawi, sharh matane Arba’in An-Nawawi fi ahadis Sahiha Annabawiyya, 1404H, shafi na 25.
  15. Al-Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 8, shafi na 57; Al-Nawawi, sharh matane Arba'in An-Nawawi fi ahadis Sahiha Annabawiyya, 1404H, shafi na 26.
  16. Al-Nawawi, sharh matane Arba'in An-Nawawi fi ahadis Sahiha Annabawiyya, 1404H, shafi na 26.
  17. Al-Majlisi, Mir'atul uƙool, 1404 AH, juzu'i na 7, shafi na 100.
  18. Al-Majlisi, Mir'atul uƙool, 1404 AH, juzu'i na 7, shafi na 100.
  19. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 18 da 19, h. Al-Mazandarani, Sharh Al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 8, shafi na 59-61.
  20. Al-Saduƙ, Al-Khisal, 1983 AD, juzu'i na 1, shafi na 21; Al-Tusi, Al-Amali, 1414H, shafi na 124.
  21. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 3.
  22. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 5.
  23. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 7.
  24. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 19, shafi na 19 da 21, juzu'i na 6 da 9.
  25. Al-Saduƙ, Al-Amali, 1997 AD. shafi na 268.
  26. Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422, juzu'i na 11, shafi na 26; Muslim, Sahih Muslim, Dar Revival of Arab Heritage, juzu'i na 1, shafi na 45.
  27. Al-Majlisi, Mir'atul uƙool, 1404 AH, juzu'i na 7, shafi na 100-113.
  28. Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422, juzu'i na 1, shafi na 8, shafi na 26.
  29. Muslim, Sahih Muslim, Darihya turath Arab, juzu'i na 1, shafi na 45.
  30. Al-Tirmidhi, Sunan Al-Tirmidhi, 1395, juzu'i na 5, shafi na 5;sharh matane Arba'in An-Nawawi fi ahadis Sahiha Annabawiyya, 1404 AH, shafi na 3.

Nassoshi

  • Al-Bukhari, Muhammad bin Ismail, Sahih al-Bukhari, bugun: Muhammad Zuhair bin Nasser al-Nasser, Dar Touƙ al-Najat, bugu na daya, 1422H.
  • Al-Hurr Al-Amili, Muhammad bin Al-Hasan, Wasa'il Al-Shi'a' ƙum, Mu'assasa Al-Baiti, bugu na 1, 1409H.
  • Al-Kulayni, Muhammad bin Yaƙoub, Al-Kafi, bugun: Ali Akbar Al-Ghafari da Muhammad Al-Akhundi, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, bugu na 3, 1407H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baƙir, Mir'atul uƙool, editan: Sayyed Hashim Rasouli Al-Mahallati, Tehran, Dar Al -Kutub Al-Islamiyyah, bugu na biyu, 1404H.
  • Al-Mazandarani, Muhammad Salih bin Ahmad, ' Sharhin Al-Kafi (Ka'idoji da Rassu), edita: Abu Al-Hasan Al-Shaarani, Tehran, Laburaren Musulunci, bugu na daya, 138H.
  • Al-Nasa’i, Ahmad bin Shuaib, Sunan Al-Nasa'i, edita: Abdel Fattah Abu Ghada, Aleppo, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na biyu, 1406H.
  • Al-Nawawi, Yahya bin Sharaf al-Din, Sharhe matane arba'in an-nawawi fi ahadis sahiha annabawiyya' Damascus, bugun Darul Fath Library, bugu na 4, 1404 Hijira / 1984 AD.
  • Al-Saduƙ, Muhammad bin Ali bin Babawayh, Al-Khisal, bugun: Ali Akbar Al-Ghafari, ƙum, Jam'at al-Mudarreen, bugu na daya, 1983 miladiyya.
  • Al-Saduƙ, Muhammad bin Ali bin Babawayh, Amali, Tehran, Kitabchi, bugu na daya, 1997 miladiyya.
  • Al-Tirmidhi, Muhammad bin Issa, Sunan al-Tirmidhi, edited by: Ahmed Muhammad Shaker, Muhammad Fouad Abdel-Baƙi, and Ibrahim Atwa, Egypt, Mustafa al-Babi al-Halabi, bugu na 1, 1395H. /1975 AD.
  • Al-Tusi, Muhammad bin Al-Hasan, Al-Amali, ƙum, House of Culture, bugu na daya, 1414H.
  • Muslim, Muslim bn Al-Hajjaj Al-Naysaburi, Sahih Muslim, editan: Muhammad Fouad Abdel-Baƙi, Beirut, Darul Ihya turath Arab, D.T.