Du'a'u Hazin
Du'a'u Hazin (Larabci:دعاء الحزين) addu'a c da aka jingina ta ga Imam Sajjad (A.S), wace ake so a karanta ta bayan sallar dare.[1] A cikin wannan addu'a akwai ma'anoni kamar nadamar abin da mutum ya aikata na zunubi da neman gafarar Allah da ɗaukaka Allah da bayyana girmansa, da kaɗaita shi da kuma ayyana ba wani Ubangiji bayansa. da neman sauƙin mutuwa da neman gafarar Allah.[2] Wasu masu bincike sun yi imanin cewa jigogin wannan addu'a na nuni da wasu ma'anoni na asali a mahangar shi'a, kamar baƙin ciki da wahalhalun ɗan Adam, kadaitaka da rashin bege daga sauran mutane sai Allah, da neman tsarin Allah.[3]
A cewar Hassan bin Fadlu ɗabarsi, ɗaya daga cikin malaman hadisi na ƙarni na 6, Imam Sajjad (A.S) ya kasance yana karanta wannan addu'a bayan sallar isha'i,[4] amma Shaikh Ɗusi (Wafati: 460H) a cikin littafin Misbahul Al-Muttahajid bai kawo wani abu game da dangana wannan addu'a ga Imam Sajjad (A.S) ba.[5] Wannan addu'a ba ta zo a cikin sahifa Sajjadiya ba, kuma a cewar wasu masu bincike, ba a ambace ta a cikin wani mustadrak na Sahifa Sajjadiyya da aka rubuta tun kafin ƙarni na 14 ba.[6]
A cikin Miftahul Al-Falah, Sheikh Baha'i ya yi bayanin wasu sassa na wannan addu'a tare da ladubban sallar witri.[7] Sayyid Abbas Shushtari, wani masanin shari'a ɗan ƙasar Indiya (Wafati: 1306H) shi ma ya haɗa da addu'o'in da aka samo a cikin munajati a waƙoƙinsa.[8]
Bayanin kula
- ↑ Qomi, Mafatih al-Jinan, Bakhsh Mas'alat, “Dhikr Namazhay Mustahab”, shafi na 873.
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411H, shafi na 160.
- ↑ Mahroush, "hazin, du'a, An kira," shafi na 442.
- ↑ Tabarsi, Makarim al-Akhlaq, 1379 AH, shafi na 295.
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411H, shafi na 160.
- ↑ Mahroush, "hazin, du'a, An kira," shafi na 442
- ↑ Sheikh Bahayi, Miftah al-Falah, 1415 AH, shafi 701.5.
- ↑ Noshahi, Kitabeshinasi Shubhe-Qara, 1391 AH, juzu'i na 3, shafi na 1965.
Nassoshi
- Sheikh Baha'i, Muhammad bin Hossein, Miftah al-Falah a cikin aikin dare da rana, Kum, Jamia Madrasin, 1415H.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Misbah al-Mutahajjid, Tusi, Beirut, Institute of Fiqh al-Shi'ah, 1411H.
- Tabarsi, Hassan bin Fazl, Makarem al-Akhlaq, Kum, Al-Sharif al-Razi, 1370.
- Qomi, Sheikh Abbas, Mufatih al-Janan, Buga Cibiyar Nazarin Hajji.
- Mehroosh, Farhang, "Hazin, Dua" a cikin Babban Encyclopedia na Musulunci, Juzu'i na 21, Tehran, Babban Cibiyar Encyclopedia Musulunci, 1391.
- Noshahi, Arif,(Indiya, Pakistan, Bangladesh), Tehran, 1391.