Du'a'u Allahumma Kun Liwaliyyika
- Kar ku ruɗe da Du'a'u Faraj.
Du'a'u Allahumma Kun liwaliyyika (Larabci:اللَّهُمَ کُنْ لِوَلِیکَ)ko Addu’ar lafiya ga Imam Zaman (A.F) addu’a ce da ake yinta domin lafiyar Imam Mahadi (A.F) Imami na goma sha biyu cikin jerin Imaman Shi’a, wannan addu’a tana farawa da (Allahumma Kun liwaliyyika) kamar yanda aka naƙaltota cikin littafin Tahzibul Al-Ahkam daga Imam Baƙir (A.S) da kuma Imam Sadiƙ (A.S) An yi amfani da kalmomi daban-daban cikin wannan addu’a domin lafiyar Imam Mahadi (A.F), haƙiƙa wannan addu’a tana cikin jerin ayyukan Lailatul ƙadri a daren 23 ga Ramadan, amma za a iya karantata a kowanne lokaci, sanadin wannan addu’a ya kasance Mursali; sai dai cewa kuma tare da hakan bisa la’akari da gangarowarta daga ingantattun litattafan addu’a za a iya hukunci da ingancinta. Cikin Aksarin Masadir da wannan addu’a ta zo, maimakon sunan Imam Mahadi (A.S) za ka samu anyi amfani da kalmar wane ɗan wane, da wannan dalili ne wasu cikin Malamai suka kawo tsammanin cewa addu’a ce zuwa ga bakiɗayan Imamai bawai ta keɓantu da Imam Mahadi (A.F) Littafin (Sharh Du’aye Salamati Imam Zaman (A.F) talifin Muhsin ƙara’ati an wallafa shi domin sharhin wannan addu’a
Matani
Du'a'u Allahumma Kun liwaliyyika an naƙalto da Mabambantan kalmomi cikin Masadir, matanin wannan addu’a a cikin littafin Misbahul Al-mutahajjid na Shaik ɗusi ya kasance kamar haka:
Ya Allah ka kasance ga waliyinka wane ɗan wane cikin wannan lokaci da kowanne lokaci majiɓancinsa kuma mai bashi kariya jagoransa mai taimakonsa kuma mai shiryar da shi tare da sanya idanu kansa, har ka saukar da ƙasarka gare shi tare da buƙatuwar mutane zuwa gare shi tana mai miƙa wuya, ka amfanar da shi cikinta dogon lokaci. [1] wannan addu’ar an naƙaltota cikin littafin Iƙbalul A’amal tare da ƙarin wasu kalmomi. [2] Cikin littafin Tahzibul Al-Ahkam an naƙalto wannan addu’a daga Imam Baƙir (A.S) da kuma Imam Sadiƙ (A.S) [3] sai dai cewa a sauran Masadir ta zo da kalmar (Salihin) ba a kai ga tantacewa daga wajen wanne Imami aka naƙaltota ba. [4] cikin Aksarin Masadir da suka naƙalto wannan addu’a ta zo da Kalmar wane ɗan wane, [5] Sayyid Ibn ɗawus Babban Malamin hadisin Shi’a a ƙarni na shida da bakwai h ƙamari, cikin littafin Iƙbalul Al’amal maimakon Kalmar wane ɗan wane sai ya naƙaltota da misalin haka:
Cikin littafin Misbah Kaf’ami shima ya anƙaltota da kalmar (Muhammad Bn Hassan Mahadi) Maimakon wane ɗan wane, [7] Muhammad Taƙiyyu Majlisi, Malamin hadisin Shi’a a ƙarni na goma sha ɗaya, ya ce zahirin jumlar addu’ar tana shaida kan halascin ambaton sunan Imam Mahadi (A.F) maimakon wane ɗan wane, na’am idan aka yi amfani da laƙubbansa maimakon sunansa zai fi kyau, [8] a cikin Mafatihul Al-janan ya zo da (Alhujjatu Bn Hassan) maimakon wane ɗan wane, [9] sakamakon zuwan kalmar wane ɗan wane cikin addu’ar wasu sun kawo tsammanin cewa wannan addu’a ta tattaro Imamin kowanne zamani bata keɓantu da Imam Zaman (A.F) ba. [10]
Lokacin Da Ake Karanta Wannan Addu’a
Kan asasin kalmomin farkon wannan addu’a [yadash 1] duk da cewa wannan addu’a ce ta daren 23 ga watan Ramadan tare da haka za a iya karantata a kowanne lokaci, saboda ance wannan addu’a ana iya karantata a kowanne irin hali a tsaye ne ko a zaune ko cikin sujjada, kai zama a iya karantata a bakiɗayan dararen watan Ramadan bawai kaɗai daren 23 ba, ana iya karantata a bakiɗayan lokutan cikin rayuwa. [11] kan wannan asasi ne aka ce maimaitata a kowanne dare da yini da kuma cikin sallah yafi dacewa. [12] haka kuma an yi wasicci da karanta wannan addu’a bayan yin godiya ga Allah da salatin Manzon Allah (S.A.W). [13]
Abin da Ta ƙunsa
Ciki addu’ar Allahumma Kun liwaliyyika an yi addu’a ga lafiyar Imam Mahadi (A.F) tare da amfani da kalmomi daban-daban, [14] an yi mafani da kalmomi guda shida cikin wannan addu’a, daga Waliyan, ƙa’idan, Nasiran, Dalilan wa Ainan, an roƙi Allah da ya kasance Majiɓancinsa kuma Mai kareshi tare da sanya shi ƙarƙashin kariyarsa, jagoransa tare da taimakonsa da sa ido kansa. [15] Cikin amfani da Kalmar (Fi hazihil Sa’ati) ishara ce zuwa ga daren 23 ga Ramadan, (wa fi kulli Sa’ati) bayani ne kan fuskanta tare da addu’a ga Imam Mahadi (A.F) a cikin kowanne lokaci. [16] A ra’ayin Hassan Sulaimani Hilli, ɗaya daga cikin Malaman Shi’a a ƙarnina takwas, abin da ake nufi da Kalmar
Zamanin bayyanar Imam Mahadi (A.F) da samun ƙudra da ƙarfi, saboda a daurar gaiba an kwace masa haƙƙinsa bashi da ƙudra da damar bayyanar da gaskiya a tsakankanin mutane, [17] sannan abin nufi daga
Ishara ce ga Raja’a da kuma bayan Shahadar Imam Zaman (A.F) [18] a cewar Mushin ƙara’ati abin nufi daga (har ka amfanar da shi cikinta dogon lokaci) fata ne kan samun tsawaitar hukumar Imam Mahadi (A.F) ta duk duniya. [19]
Sanadi Da Ingancinsa
Addu’ar Allahumma Kun liwaliyyika, cikin Masadir ɗin riwaya da addu’o’i kaɗai an naƙalto ta hanyar Muhammad Bn Isa Ubaidi [yadasht 2] [20] akwai saɓanin Malamai kan wasaƙarsa. [21] Najjashi [22] ya ƙirga shi jerin layin Siƙa sai dai kuma Shaik ɗusi ya sanya cikin Raunana, [23] a ra’ayin Allama hilli mutum ne mai ƙarfin nazari kuma ya wassaƙa shi. [24] A cewar Allama Majlisi Sanadin wannan addu’a Mursali ne, [25] amma kuma tare da haka Muhsin ƙara’ati yana cewa shaidu misalin samuwarta cikin littafin Alkafi [26] Tahzibul Al-Ahkam [27] da sauran ingantattun litattafai misalin Al-Mazar Al-Kabir littafin Ibn Mashhadi, [28] littafin Misbahul Kaf’ami, [29] da Iƙbalul Al-A’amal littafin Sayyid Bn ɗawus , [30] da kuma dacewa da abin da addu’ar ta ƙunsa da hankali da naƙali kuma kasancewar bakiɗayan kalmomin da suke cikin wannan addu’a sun zo cikin wasu addu’o’in daban, dalili ne kan ingancin wannan addu’a. [31]
Menene Ya Sanya Ake Addu’a Domin Lafiyar Imam Zaman (A.F)
Littafin Sharh Du’aye Salamati Imam Zaman (A.F) talifin Muhsin ƙara’ati, haƙiƙa Imami na goma sha biyu shima kamar sauran Imamai yake yana rayuwa a ɗabi’ance yana rashin lafiya yana kuma fuskantar matsalolin rayuwa, da wannan dalili ne ya dace ayi sadaƙa da addu’a domin lafiyarsa, [32] Malamin ya yi bayanin wata fuskar daban kan addu’a ga Imam (A.S) shi ne yi masa addu’a domin kariya yayin sauke saƙo da kuma kiyaye imamanci a lokacin gaibarsa da bayyanarsa, saboda ɗaukar nauyayyan saƙo misalin wannan abu ne da yake buƙatar kariya da kulawa ta musammam daga Allah, [33] haka kuma akwai wasu addu’o’in na daban da aka naƙalto daga Imamai (A.S) suma duka domin lafiya da kariya ga Imam Zaman (A.F) [34]
Nazari
Littafin Sharh Du’a’u Salamati Imam Zaman (A.F)rubutun Muhsin ƙara’ati tare da taimakon Hassan Abadi, sun yi bincike tare da sharhi kan sanadi da matanin wannan Addu’a, Marubucin littafin bayan bahasosin Muƙaddima da bincike kan sanadi, ya kutsa cikin bincike kan ɗaiɗaikun kalmomin da addu’ar ta ƙunsa da kuma jumlolinta, [35] a ƙarshe ya kawo bayanin fa’idoijin da suke cikin karanta wannan addu’a, da sharuɗɗan amsa addu’a, [36] marubucin ya bayyana cewa wannan addu’a ta shahara da sunan Du’a’u Faraj bisa kuskure, [37] cibiyar Hazrat Mahadi Mau’ud (A.F) da take ƙum Iran ta ɗauki nauyin buga wannan littafi da yaɗa shi.
Bayanin kula
- ↑ Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 630 da 631; Mufatih Al-Jannan,Tarjameh Hossein Ansariy ya fassara.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Iƙbal Al-Amal, 1419H, juzu'i na 1, shafi na 85.
- ↑ Tusi, Tahzeeb Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 102 da na 103.
- ↑ Duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 162; Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 630 da 631; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 612.
- ↑ Duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 162; Tusi, Tahzibul Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi.103; Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 630 da 631; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 612; Kaf'ami, Balad Al-Amin, 1418H, shafi na 203.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Iƙbal Al-Amal, 1419H, juzu'i na 1, shafi na 85.
- ↑ Kaf'ami, Al-Masbah, 1405 AH, shafi na 586.
- ↑ Majlesi, Raudatul Al-Mutaƙin, 1406 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 449.
- ↑ ƙommi, Mafatih Al-Janan, majma sakafatul Islamiyya, shafi na 307, karkashin Sallar daren 23 ga Ramadan.
- ↑ Duba: ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 48.
- ↑ Duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 162; Tusi, Tahzibul Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 102 da 103; Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi: 630; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 612; Kaf'ami, Al-Balad al-Amin, 1418 AH, shafi na 203; Sayyid Ibn Tawus, Iƙbal Al-Amal, 1419H, juzu'i na 1, shafi na 85.
- ↑ Duba: ƙaraati, Sharha Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 35 da 36.
- ↑ Duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 162; Tusi, Tahzib Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 102 da 103; Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi: 630; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 612; Kaf'ami, Al-Balad al-Amin, 1418 AH, shafi na 203; Sayyid Ibn Tawus, Iƙbal al-Amal, 1419H, juzu'i na 1, shafi na 85.
- ↑ Duba: ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 61.
- ↑ Duba: ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (AS), 1393, shafi na 61.
- ↑ Duba: ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (AS), 1393, shafi na 57.
- ↑ Hali, Mukhtasar Al-Basair, 1421H, shafi na 460.
- ↑ Hali, Mukhtasar Al-Basair, 1421H, shafi na 460-461.
- ↑ Duba: ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (AS), 1393, shafi na 87-91
- ↑ Duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 162; Tusi, Tahzib Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 102 da 103; Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi: 630; Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 612; Sayyid Ibn Tawus, Iƙbal Al-Amal, 1419H, juzu'i na 1, shafi na 85.
- ↑ Duba: Allama Hilli, Rijal Allamah Al-Hili, 1411 AH, shafi na 142.
- ↑ Najashi, Rizal Najashi, 1365, shafi na 333..
- ↑ Tousi, Rizal Al-Tousi, 1373, shafi na 391.
- ↑ Allameh Hilli, Rijal Allama Al-Hilli, 1411 AH, shafi na 142.
- ↑ Majlesi, Mir'atul Al-Uƙool, 1404 AH, juzu'i na 16, shafi na 394; Majlisi, Mulad Al-Khiyar fi Fahm Tahzib Al-Akhbar, 1406 AH, juzu'i na 5, shafi na 106.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi 162, h4.
- ↑ Tusi, Tahzeeb Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi 102, h37.
- ↑ Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419H, shafi na 612.
- ↑ Kafami, Al-Misbah, 1405 AH, shafi na 586.
- ↑ Sayyid Ibn Tawus, Iƙbal Al-Amal, 1419H, juzu'i na 1, shafi na 85.
- ↑ ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 26-29.
- ↑ ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 62.
- ↑ ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 67.
- ↑ Misali, duba: Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, Juzu’i na 1, shafi na 409 da 413 da Mujalladi na 2, shafi na 405.
- ↑ >ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 5-6
- ↑ >ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 93-103
- ↑ >ƙaraati, Sharh Du'aye Salamati Imam Zaman (A.S), 1393, shafi na 7
Nassoshi
- Allama Hilli, Hassan bin Yusuf bin Motahar, Rizal al-Allamah al-Hali, bincike da gyara na Muhammad Sadiƙ Bahr al-Uloom, Najaf, Dar al-Zakhaer, bugu na biyu, 1411H.
- Hilli, Hasan Suleiman bin Muhammad, Khazrat al-Basair, Mushtaƙ Muzafar, ƙum, Cibiyar Buga Musulunci, bugun farko, 1421H.
- Ibn Mashhadi, Muhammad bin Jafar, Al-Mazar Al-Kabir, Jaɓad ƙayyumi Isfahani, ƙum, daftare nashare islami, bugun farko, 1419 Hijira, ya yi bincike kuma ya gyara shi.
- Kaf'ami, Ibrahim bin Ali Ameli, Al-Balad Al-Amin w al-Dara al-Hussein, Beirut, Al-Alami Institute, bugu na farko, 1418H.
- Kaf'ami, Ibrahim bin Ali Ameli, al-Masbah, Kum, Dar al-Razi, bugu na biyu, 1405H.
- Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, Al-Kafi, bincike da gyara na Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
- Majlesi, Mohammad Taƙi, Rawda Al-Mutaƙeen fi Sharh Man Lai yahzarahul Al-Faƙih, bincike da gyara na Hossein Mousaɓi Kermani da Alipanah Eshtherdi, ƙum, Cibiyar Al'adun Musulunci ta Kushanpur, bugu na biyu, 1406 AH.
- Majlisi, Mohammad Baƙir, Mir'atul Al-Uƙool fi Sharh Akhbar Al-Ar-Rasoul, bincike na Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiya, bugu na biyu, 1404H.
- Majlisi, Mohammad Baƙir, Mlazul Al-Akhyar fi Fahm Tahzeeb al-Akhbar, bincike na Mehdi Rajaei, ƙum, Ayatullah Murashi Najafi Library, bugu na farko, 1406H.
- Najashi, Ahmed Bin Ali, Rizal Najashi, ƙum, Islamic Publishing House, bugu na 6, 1365.
- Sayyed bin Tawus, Ali bin Musa, Iƙbal Al-Amal, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na biyu, 1419H.
- Tousi, Muhammad bin Hassan, Misbah al-Mutahajjid wa Salahul al-Muta'abbid, Beirut, Cibiyar Shari’a ta Shi’a, bugu na farko, 1411H.
- Tousi, Muhammad bin Hassan, Rizal Al-Tousi, Jaɓad ƙayyumi Isfahani, ƙum, Cibiyar Buga Musulunci, bugu na uku, 1373 ya yi bincike kuma ya gyara shi.
- Tousi, Muhammad bin Hassan, Tahzib Al-Ahkam, bincike da gyara na Hasan Mousaɓi Khorsan, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na hudu, 1407H.
- ƙaraati, Mohsen, sharhi Du'aye Salamti Imam Zaman (A.S), Hassan Salam Abadi, ƙum, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation (AS), 1393.
- ƙummi, Sheikh Abbas, Mafatih Al-janan, Majalisar Rayar da Al'adun Musulunci, Bita.