Jump to content

Daƙiƙa:Waraka Ta Hanyar Kur'ani

Daga wikishia

Waraka ta hanyar Kur'ani na nufin tasirin ayoyin Kur'ani wajen magani da warkar da cututtukan aƙida, ɗabi'a da na jiki. Ana ɗaukar wannan a matsayin ɗaya daga cikin siffofin Kur'ani na musamman da suka wuce abin da ake iya gani na zahiri. Malaman tafsiri sun ɗauki gurɓacewar ruhi kamar kafirci, munafunci da hassada a matsayin misalan "Cututtukan zuciya", wadda za a iya gyara ta ta hanyar shiriyar Kur'ani. Wasu surori da ayoyi, kamar Fatiha, Nas, Falaƙ da Ayatul Kursiyyu, an ambace su a cikin ruwayoyi a matsayin abubuwan da ake amfani da su wajen neman maganin wasu cututtuka.

Ana danganta wannan tasiri da Ikon Allah da kuma nufinsa, kuma ana ganin ya wuce dalilan halitta na yau da kullum. Duk da haka, a cikin sunnar Annabi da Ahlul Baiti, ana amfani da Kur'ani tare da magani da likita. Haka kuma, akwai labaran abubuwan da muminai suka fuskanta, bayanan wasu malaman Shi'a, da kuma wasu binciken ilimin halayyar ɗan Adam da suka nuna tasirin Kur'ani wajen taimakawa wajen magance cututtuka; amma hakan yana tare da sharaɗin samun yaƙini da tasirinsa, yin karatu cikin tsarkin zuciya, da kuma aiki da koyarwar Kur'ani.

Ma'anar Waraka Ta Hanyar Kur'ani Da Matsayinta

Waraka ta hanyar Kur'ani tana nufin warkarwa ko samun sauƙi daga cututtuka ta hanyar ayoyin Kur'ani.[1] Ana ɗaukarta daga cikin siffofin Kur'ani na abubuwan da suka wuce abin da ake iya fahimta ta hanyoyin zahiri.[2] A ra'ayin malaman tafsiri, dukkan ayoyin Kur'ani suna da damar samar da waraka,[3] kuma suna ɗaukar aya ta 82 a cikin Suratul Isra'i a matsayin ɗaya daga cikin ayoyin da suka yi ishara da wannan siffa.[4] A cewar wasu masu bincike, an yi amfani da kalmar shifa (Shifa) da dangoginta a cikin ayoyi shida na Kur'ani,[5] waɗanda aka fi sani da Ayoyin Shifa' (ayoyin waraka).[6]

Bisa ga wasu ruwayoyi,[7] Kur'ani yana iya taimakawa wajen warkar da cututtukan aƙida, ɗabi'a har ma da cututtukan jiki;[8] sai dai ana ganin tasirin warakar Kur'ani yana da alaƙa da aiki da koyarwarsa.[9] Ayatullahi Khamna'i yana kallon Kur'ani a matsayin magani ga raɗaɗin al'ummomin duniya, kamar yaƙe-yaƙe, zalunci da rashin adalci.[10]

Tabbatar da Warakar Kur'ani da Nufin Allah

Warakar Kur'ani ana danganta ta da nufi da ikon Allah; wato Allah yana iya samar da waraka ga marasa lafiya fiye da dalilan halitta na yau da kullum. Kamar yadda Kur'ani ya ambaci warkar da marasa lafiya da kuma rayar da matattu ta hannun Annabi Isa (A.S) da izinin Allah,[11] hakan ya nuna ikon Allah wajen samar da waraka.[12]

Duk da haka, a cikin nazarin ruwayoyin da suka shafi falalar surori da warakar Kur'ani, an samu ra'ayoyi daban-daban.[13] Wasu suna kallon maganin Kur'ani kamar magani ne da yake da amfani ga kowa. Wasu kuma suna ganin waraka tana daga cikin falalar Allah da wani nau'i na karamarsa. Wasu kuwa suna ganin cewa karanta wasu surori kawai yana samar da yanayin da waraka za ta iya faruwa, ba wai shi ne ainihin dalilin kai tsaye na samun sauƙi ba.[14]

A cewar wasu masu bincike, a cikin tafarkin Annabi (S.A.W) da Ahlul-Baiti, an yi amfani da Kur'ani tare da magani da likita; amma bai kamata a rage shi zuwa matsayin magani na yau da kullum kawai ba, domin ana fassara tasirinsa ne tare da la'akari da dalilan halitta.[15]

Tasirin Kur'ani wajen magance cututtukan ruhi da na tunani

Kur'ani yana warkar da dukkan cututtukan akida da ɗabi'a na ɗan Adam; yana warkar da jahilci, wanda shi ne mafi munin cutar cikin zuciya, ta hanyar ilimi; yana kawar da shakku ta hanyar yakini; yana magance baƙin ciki da damuwa ta hanyar samun natsuwa; yana kawar da tsoro da firgici ta hanyar kwanciyar hankali da bege; sannan yana kawar da tashin hankali da damuwa game da gaba ta hanyar azama da tsayuwa kan manufa.

Jawadi Amoli, Tafsire Maudu'iye Qur'ane Karim, shafi na 236.

An ɗauki Kur'ani a matsayin mai warkar da cututtukan ruhi.[16] Ayatullahi Makarim Shirazi, wanda yake malamin tafsirin Shi'a, a cikin tafsirin aya ta 67 na Surar Yunus,[17] ya bayyana cewa manufar cutar zuciya ita ce gurɓacewar ruhi da ta ma'ana.[18] An bayyana irin waɗannan cututtuka a fannin imani (kamar kafirci da shirka), da kuma ɗabi'a da halaye (kamar hassada, rowa da ƙiyayya).[19]

A ra'ayin Fakhrur Razi, daga cikin malaman tafsirin Ahlus-Sunna, Kur'ani yana gyara aƙidun da ba su dace ba ta hanyar bayyana gaskiyar halittar duniya da kuma gabatar da ainihin mutum, tushen samuwarsa da makomarsa ta ƙarshe; sannan ta hanyar bayyana munanan ɗabi'u, yana samar da hanyar magance su da shiryar da mutum zuwa ga kyawawan halaye.[20]

Bisa wata ruwaya daga Imam Ali (A.S),[21] kafirci, munafunci da ɓata hanya suna daga cikin manyan cututtukan ruhin ɗan Adam, kuma an gabatar da Kur'ani a matsayin maganinsu.[22] Ali Nasiri, wanda ya kafa Cibiyar Sanin Wahayi da Hankali, bisa dogaro da aya ta 57 a Surar Yunus da aya ta 82 a Surar Isra'i, yana ganin cewa Kur'ani yana da damar warkar da cututtukan aƙida ga dukkan mutane, sannan kuma yana iya warkar da cututtukan ɗabi'a ga muminai.[23]

Tasirin Kur'ani Wajen Rage Damuwa Da Tashin Hankali

A cewar wasu masu bincike, nazarin ilimin halayyar ɗan Adam ya nuna cewa karatun Kur'ani da fahimtar ma'anarsa suna taimakawa wajen rage damuwa da baƙin ciki.[24] Nazarin da aka gudanar a kan ƙungiyoyi daban-daban, kamar mata masu juna biyu da marasa lafiya, ya nuna cewa sauraron karatun Kur'ani yana taimakawa wajen inganta yanayin ruhi da na jiki.[25] Haka kuma, ci gaba da karatun Kur'ani kullum na tsawon watanni shida yana da alaƙa da raguwar damuwa sosai a tsakanin matasa.[26]

Tasirin Kur'ani wajen Magance Cututtukan Jiki

Bisa ga ra'ayoyin wasu masu tafsiri, Kur'ani yana iya taimakawa wajen magance wasu cututtukan jiki.[27] Karanta Kur'ani, neman albarka ta hanyarsa, da aiki da koyarwarsa an lissafta su daga cikin abubuwan da suke da alaƙa da wannan tasiri.[28]

Haka kuma, wasu masu bincike, ta hanyar yin nuni da koyarwar Kur'ani game da kiwon lafiya a fannoni kamar abinci,[29] tsaftar jima'i,[30] azumi,[31] da amfani da zuma,[32] suna ganin cewa Kur'ani zai iya taka rawa wajen kiyaye lafiya da taimakawa wajen inganta cututtuka ta hanyar hukunce-hukuncen kariya.[33]

Ruwayoyin da suka shafi Warakar Kur'ani

An ruwaito ruwayoyi da yawa game da falalar ayoyi da surorin Kur'ani;[34] bisa ga waɗannan ruwayoyi, an ba da shawarar amfani da wasu surori wajen magance wasu cututtuka.[35] Daga ciki akwai:

Sai dai an ɗaura waɗannan tasirori da sharadin yin imani da warakar Kur'ani.[42] Wasu malamai, kamar Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, sun yi shakku kan ingancin isnadin irin waɗannan hadisai, kuma sun ɗauki wasu daga cikinsu a matsayin ruwayoyin da masu riwaya suka ƙirƙira.[43]

Abubuwan Da Aka Fuskanta Na Warakar Kur'ani

Abubuwan da mutane suka fuskanta da kuma rahotanni sun nuna cewa wasu ayoyi da surorin Kur'ani sun taimaka wajen magance cututtukan jiki.[44] Ayatullahi Jawadi Amoli yana ganin cewa tasirin warakar Kur'ani dangane da cututtukan jiki abu ne da aka gwada kuma aka samu gogewa a kai.[45]

Mulla Salih Mazandarani, daga cikin malaman ƙarni na 11H, yana ganin cewa kowace aya daga cikin Kur'ani musamman idan an karanta ta da ikhlasi da yaƙini tana iya zama mai warkarwa. Ya kuma bayyana cewa an gwada Suratul Fatiha wajen magance nau'o'in cututtuka daban-daban, musamman idan an karanta ta sau saba'in.[46]

Muhammad Taƙiyyu Majlisi shi ma ya ambaci warkewar fiye da marasa lafiya dubu, waɗanda ya gani da kansa, ta hanyar karanta Suratul Fatiha.[47]

Bayanin kula

  1. ↑ Farahidi, Kitabul Ain, "kalmar Shafi".
  2. ↑ Nasiri, Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim, shafi na 55.
  3. ↑ Fakhrur Razi, At-Tafsirul Kabir, juzu'i na 21, shafi na 390; Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 13, shafi na 184.
  4. ↑ Don misali, a duba: Hashimi Rafsanjani da masu bincike, Farhange Qur'an, juzu'i na 17, shafi na 302; Riza'i Isfahani da wasu masu bincike, Tafsir Qur'an Mehr, juzu'i na 12, shafi na 143; Muhammadi, «Nigahi be Shifa Bakshe Qur'ane Karim,» shafi na 195.
  5. ↑ Suratul Isra'i, aya ta 82; Suratul Yunus, aya ta 57; Suratul Fussilat, aya ta 44; Suratut Tauba, aya ta 14; Suratun Nahli, aya ta 69; Suratush Shu'ara, aya ta 80.
  6. ↑ Muhsini, «Qur'an wa Shifabakhshiye Bimarihaye Ruhi wa Jismi,» shafi na 59.
  7. ↑ Misali, a duba: Imam Askari (A.S) Al-Tafsir Al-Mansub Ila Al-Imam Al-Askari, shafi na 14; Nahjul Balaga Tashihu Subhi Salih," huɗuba ta 176, shafi na 252.
  8. ↑ Sa'adi, Persemane Qira'ate Qur'an, juzu'i na 32, shafi na 33; Furƙani da Haidari, Ashnayi ba Tafsir wa Rawesh-haye Tafsiri, shafi na 20.
  9. ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, juzu'i na 12, shafi na 242.
  10. ↑ «Bayanat dar Didare Sherkat-konandegan dar Musabeƙate Bainal Melaliye Qur'an,» shafi Ofishin Hifze Wa Nashre Asar Ayatullahi Al-Uzma Sayyid Ali Khamna'i.
  11. ↑ Suratul Ma'ida, aya ta 110; Suratu Ali Imran, aya ta 49.
  12. ↑ Muhsini, «Qur'an wa Shifabakhshiye Bimarihaye Ruhi wa Jismi,» shafi na 59.
  13. ↑ Ala'i da Riza'i, «Darmane I'jaz'amize Qur'an,» shafi na 83–85.
  14. ↑ Ala'i da Riza'i, «Darmane I'jaz'amize Qur'an,» shafi na 84–85.
  15. ↑ Ala'i da Riza'i, «Darmane I'jaz'amize Qur'an,» shafi na 84–85.
  16. ↑ Jawadi Amoli, Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim, shafi na 236; Muhsini, «Qur'an wa Shifabakhshiye Bimarihaye Ruhi wa Jismi,» shafi na 57.
  17. ↑ Suratul Yunus, aya ta 57.
  18. ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, juzu'i na 8, shafi na 318.
  19. ↑ Muhsini, «Qur'an wa Shifabakhshiye Bimarihaye Ruhi wa Jismi,» shafi na 57; Nasiri, Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim, shafi na 56.
  20. ↑ Fakhrur Razi, At-Tafsirul Kabir, juzu'i na 21, shafi na 389–390.
  21. ↑ Nahjul Balaga, Tashihu Subhi Salih, huɗuba ta 176, shafi na 252; Dailami, A'alamud Din Fi Sifatil Muminin, shafi na 105.
  22. ↑ Nasiri, Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim, shafi na 57.
  23. ↑ Nasiri,Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim, shafi na 56.
  24. ↑ Kungiyar marubuta, Majmu'e Maƙalate Awwalin Hamayeshe Naƙshe Din dar Behdashte Rawan, shafi na 88.
  25. ↑ Muhsinzadeh da Husaini, «Ta'asire Qur'an dar Darmane Bimariha, Moruri bar Mutale'at,» shafi na 25.
  26. ↑ Kungiyar marubuta, Majmu'e Maƙalate Awwalin Hamayeshe Naƙshe Din dar Behdashte Rawan, shafi na 79.
  27. ↑ Domin misali, a duba: Shaik Ɗusi, At-Tibyan, juzu'i na 6, shafi na 513; Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, juzu'i na 6, shafi na 673; Abul Futuh Razi, Raudul Jinan, juzu'i na 12, shafi na 277; Faizul Kashani, Tafsir As-Safi, juzu'i na 3, shafi na 213.
  28. ↑ Muhammadi, «Nigahi be Shifa Bakshe Qur'ane Karim,» shafi na 196; Muhsini, «Qur'an wa Shifabakhshiye Bimarihaye Ruhi wa Jismi,» shafi na 61.
  29. ↑ Suratul A'araf, aya ta 31; Suratul An'am, aya ta 145.
  30. ↑ Suratul Baƙara, aya ta 222; Suratul Isra'i, aya ta 32.
  31. ↑ Suratul Ahzab, aya ta 35.
  32. ↑ Suratun Nahli, aya ta 68–69.
  33. ↑ Ala'i da Riza'i, «Mabaniye Behdasht wa Salamat dar Qur'an,» shafi na 138.
  34. ↑ Misali, a duba: Ibn Hayyun, Da'a'imul Islam, juzu'i na 2, shafi na 146; Ibn Shu'uba Harrani, Tuhaful Uƙul, shafi na 106; Shaik Saduƙ, Al-Khisal, juzu'i na 2, shafi na 616; Ƙuɗbud-Din Rawandi, Ad-Da'awat, shafi na 188.
  35. ↑ Nasiri, Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim, shafi na 57.
  36. ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 623, hadisi na 15; Shaik Ɗusi, Al-Amali, shafi na 284, hadisi na 553.
  37. ↑ Bahrani, Al-Burhan, juzu'i na 5, shafi na 8120; Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 18, shafi na 71.
  38. ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 621, hadisi na 8; Shaik Saduƙ, Sawabul A'amal, shafi na 105.
  39. ↑ Ibn Shu'uba Harrani, Tuhaful Uƙul, shafi na 106; Shaik Saduƙ, Al-Khisal, juzu'i na 2, shafi na 616.
  40. ↑ Shu'airi, Jami'ul Akhbar, shafi na 157; Majlisi, Bihar al‑Anwar, juzu'i na 92, shafi na 132.
  41. ↑ Nasiri, Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim, shafi na 57; Muhsini, «Qur'an wa Shifabakhshiye Bimarihaye Ruhi wa Jismi,» shafi na 62.
  42. ↑ Muhammadi, «Nigahi be Shifa Bakshe Qur'ane Karim,» shafi na 196.
  43. ↑ Khuyi, Al-Bayan, shafi na 28–29.
  44. ↑ Muhsini, «Qur'an wa Shifabakhshiye Bimarihaye Ruhi wa Jismi,» shafi na 63.
  45. ↑ Jawadi Amoli, Tafsir Tasnim, juzu'i na 1, shafi na 263.
  46. ↑ Mazandarani, Al-Kafi, Al-Usul War Rauda.
  47. ↑ Majlisi Awwal, Raudatul Muttaƙin, juzu'i na 13, shafi na 137.

Nassoshi

  • Abul Futuh Razi, Husain Bin Ali, Raudul Jinan wa Ruhul Jinan fi Tafsiril Qur'an, masu bincike da masu gyara: Dakta Yahaya, Muhammad Jafar da Dakta Nasih, Muhammad Mahdi; Mashhad: Bunyade Pajushhaye Islami Astan Quds Rezawi, 1408H.
  • Ala'i Husain Ali da Riza'i, Hassan Riza, «Darmane I'jaz'amize Qur'an,» (Maganin Mu'ujiza na Kur'ani), a cikin mujallar wata uku-uku ta Qur'an Wa Ilm, shekara ta bakwai, lamba ta 9, Pajushhaye Tafsiri Wa Ulum Qur'an, Qom, damuna da hunturu, 2011–2012M. dubawa: 27 Yuli 2026M.
  • Ala'i Husain Ali da Riza'i, Hasan Riza, «Mabaniye Behdasht wa Salamat dar Qur'an,» (Tushen Kiwon Lafiya a cikin Kur'ani), a cikin mujallar wata uku-uku ta Qur'an Wa Ilm, shekara ta bakwai, lamba ta 12, Pajushhaye Tafsiri Wa Ulum Qur'an, Qom, bazara da rani, 2013–2014M. dubawa: 27 Yuli 2026M.
  • Bahrani, Sayyid Hashim, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Tehran: Gidauniyar Bi'sat, bugu na farko, 1416H.
  • Dailami, Hassan Bin Muhammad, A'alamud Din Fi Sifatil Muminin, Qom: Cibiyar Alul Baiti (A.S), bugu na farko, 1408H.
  • Faizul Kashani, Mulla Muhsin, Tafsir As-Safi, bincike: A'alami, Husain; Wallafar Sadr, Tehran, bugu na biyu, 1415H.
  • Farahidi, Khalil Bin Ahmad, Kitabul Ain, gyara: Mahadi Makhzumi da Ibrahim Samarra'i; Qom: Wallafar Hijrat, bugu na biyu, 1410H.
  • Furƙani, Qudratullahi da Haidari, Ahmad, Ashnayi ba Tafsir wa Rawesh-haye Tafsiri, Qom: Cibiyar Tahƙiƙate Islami Sepahj Pasidaran Islami, bugu na farko, ba tare da shekara ba.
  • Hashimi Rafsanjani, Akbar, da masu bincike na Markaze Farhang wa Ma'arife Qur'an, Farhange Qur'an, Qom: Mawallafar Bostane Kitab, bugu na biyu, 1383Sh.
  • Ibn Hayyun, Nu'uman Bin Muhammad Magribi, Da'a'imul Islam wa Zikril Halal wal Haram wal Ƙada'iya wal Ahkam, mai bincike da mai gyara: Faizi, Asif; Qom: Cibiyar Alul Baiti (A.S.), bugu na biyu, 1385H.
  • Ibn Shu'uba Harrani, Hassan Bin Ali, Tuhaful Uƙul an Alir Rasul (S.A.W)," mai bincike da mai gyara: Gaffari, Ali Akbar; Qom: Ofishin Intisharate Islami, bugu na biyu, 1404H.
  • Imam Askari (A.S.), Hassan Bin Ali,Al-Tafsir Al-Mansub Ila Al-Imam Al-Askari, Madarse Imam Mahadi; Qom: bugu na farko, 1409H.
  • Jawadi Amoli, Abdullahi, Tafsir Tasnim, tsarawa da gyara: Rizki, Ruhullahi da Jamali, Ahmad; Qom: Cibiyar Wallafa Isra, bugu na uku, 1381Sh.
  • Jawadi Amoli, Abdullahi, Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim Qur'an dar Qur'an, tsarawa da gyara: Ghulam Ali Amin Din; Qom: Cibiyar Wallafa Isra, bugu na uku, 1381Sh.
  • Kulaini, Muhammad Bin Yakub, Al-Kafi, mai bincike da mai gyara: Gaffari, Ali Akbar da Akhundi, Muhammad; Tehran: Darul Kutubil Islamiyya, bugu na huɗu, 1407H.
  • Majlisi Awwal, Muhammad Taƙi, Raudatul Muttaƙin fi Sharhi Man La Yahduruhul Faƙihu, masu bincike da masu gyara: Musawi Kermani, Sayyid Husain; Ishtihardi, Ali Panah; Ɗabaɗaba'i, Sayyid Fadhlullahi; Qom: Cibiyar Farhangi Islami Kushanpur, bugu na biyu, 1406H.
  • Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al‑Anwar, Beirut: Darul Ihya'il Turasil Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Makarim Shirazi, Nasir, Tafsir Namuna, Tehran: Darul Kutubil Islamiyya, bugu na farko, 1374Sh.
  • Mazandarani, Muhammad Salih, Al-Kafi, Al-Usul War Rauda," Tehran: Darul Kutubil Islamiyya, bugu na farko, 1382H.
  • Muhammadi, Muhammad Ali, «Nigahi be Shifa Bakshe Qur'ane Karim,» (Dubawa kan Warakar Kur'ani Mai Girma), Mujallar wata uku-uku ta ilimi ta Musamman ta Rahe Tusha, lamba ta 9, bazara, 2022–2023M. dubawa: 27 Yuli 2026M.
  • Muhsini, Muhammad Salim, «Qur'an wa Shifabakhshiye Bimarihaye Ruhi wa Jismi,» (Kur'ani da Warakar Cututtukan Ruhi da Jiki), Mujallar wata uku-uku ta Ilm Wa Pajuheshi Wa Tibb, mujalladi na goma, lamba ta 1, bazara, 2025–2026M. dubawa: 27 Yuli 2026M.
  • Muhsinzadeh, Farida, da Husaini Munirussadat, «Ta'asire Qur'an dar Darmane Bimariha, Moruri bar Mutale'at,» (Tasirin Kur'ani wajen Magance Cututtuka: Bita kan Nazarce-nazarce), Mujallar Islam Wa Salamat, shekara ta uku, lamba ta 1, bazara, 2016–2017M. dubawa: 27 Yuli 2026M.
  • Nasiri, Ali, Tafsir Maudu'iye Qur'ane Karim, Tehran: Wallafar Ma'arif, 139Sh, shafi na 55–57.
  • Ƙuɗbud-Din Rawandi, Sa'id Bin Hibbatullah, Ad-Da'awat (Salwatul Hazin), Qom: Wallafar Madrase Imam Mahadi (A.F), bugu na farko, 1407H.
  • Riza'i Isfahani, Muhammad Ali, da wasu masu bincike, Tafsir Qur'an Mehr, Qom: Pajushhaye Tafsiri Wa Ulum Qur'an, bugu na farko, 1387Sh.
  • Sa'adi, Muhammad Jawad, Porsemane Qira'at Qur'ane, Qom: Cibiyar Bostan Kitab, bugu na huɗu, 1386Sh.
  • Sayyid Razi, Muhammad bn Husain, Nahjul Balaga, Tashihu Subhi Salih, Qom: Hijrat, bugu na farko, 1414H.
  • Shaik Saduƙ (Ibn Babawaihi), Muhammad bn Ali, Al-Khisal, mai bincike da mai gyara: Gaffari, Ali Akbar; Qom: Ofishin Intisharate Islami, bugu na farko, 1362Sh.
  • Shaik Saduƙ (Ibn Babawaih), Muhammad Bin Ali, Sawabul A'amal wa Iƙabul A'amal, Gidan Bugawa na Sharif Razi., Qom: bugu na biyu, 1406H.
  • Shaik Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, Al-Amali, Qom: Darus Saƙafa, bugu na farko, 1414H.
  • Shaik Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, At-Tibyan fi Tafsiril Qur'an, tare da gabatarwa ta: Shaik Agha Buzurg Tehrani; bincike: Ƙasir Amili, Ahmad; Dar Ihya'il Turasil Arabi, Beirut: ba tare da shekara ba.
  • Shu'airi, Muhammad bn Muhammad, Jami'ul Akhbar, Najaf: Mabugar Haidariyya, bugu na farko, ba tare da shekara ba.
  • Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husain, Almizan fi Tafsiril Qur'an, Beirut: Cibiyar A'lami ta Bugawa, 1390H.
  • Ɗabrisi, Fadhl bn Hasan, Majma'ul Bayan fi Tafsiril Qur'an, gyara: Yazdi Ɗabaɗaba'i, Fadhlullahi da Rasuli Mahallati, Hashim; Tehran: Mawallafar Nasir Khusruw, bugu na uku, 1372 Shamsi.
  • Kungiyar marubuta, Majmu'e Maƙalate Awwalin Hamayeshe Naƙshe Din dar Behdashte Rawan, Tehran: Hukumar Nahade Namayendagi Maƙam Mu'azzam Rahbari Dar Daneshgaha, bugu na farko, 2003–2004M.
  • Fakhrur Razi, Muhammad bn Umar, At-Tafsirul Kabir," Beirut: Dar Ihya'il Turasil Arabi, 1420H.
  • Khuyi, Sayyid Abul Ƙasim, Al-Bayan fi Tafsiril Qur'an, Qom: Cibiyar Ihya'i Asaril Al-Imam Khuyi, 1418H.
  • «بیانات در دیدار شرکت‌کنندگان در مسابقات بین‌المللی قرآن»، (Jawabi a ganawar da mahalarta Gasar Ƙasa da Ƙasa ta Kur'ani), shafi Ofishin Hifze Wa Nashre Asar Ayatullahi Al-Uzma Sayyid Ali Khamna'i. ranar wallafawa: 22 Fabrairu 2024M; ranar dubawa: 16 Nuwamba 2025M.