Daƙiƙa:Suratun Najmi
Ɗur Suratun Najmi Ƙamar | |
| Lambar Sura | 53 |
|---|---|
| Juzu'i | 27 |
| Jerantuwa Ta Sauka | 23 |
| Adadin Ayoyi | 62 |
| Adadin Kalmomi | 359 |
| Adadin Haruffa | 1432 |
| Makkiya/Madaniyya | Makkiya |
Suratun Najmi ita ce ta sura 53 cikin Juzi'i na 27 a Alƙur'ani mai girma, sura ce da ta sauka a Makka, sunanta ya samo asalin daga aya ta farkonta, wannan sura ɗaya ce daga cikin surorin da ake kira da Suwarul Aza'im waɗanda cikin akwai ayoyin da wajibi ne yin sujjada lokacin karatunsu, wannan sura tana magana kan haƙiƙar wahayin da aka saukarwa Annabi Muhammad (S.A.W) da kuma camfe-camfen mushrikai cikin bautar gumaka da bautar mala'iku kazalika wannan sura ta yi magana kan Tuba, da bayani kan tashin Alƙiyama, da sakamakon al'ummun da suka shuɗe, kamar al'umar Nuhu (A.S) da Samud da Adawa da kuma Luɗ.
Daga cikin ayoyi mashahurai na wannan sura, akwai faɗar Allah cikin aya 3-4 (Baya magana da son zuciya* Ba wani abu bane face wahayi da ake yi masa). da faɗinsa maɗaukaki: (San nan ya kusanto ya kuma matso* Sai ya kasance gwargwadon tazarar baka biyu ko kuma mafi kusa). da faɗinsa maɗaukaki: (Kuma mutum ba shi da komai face abin da ya yi ƙoƙari a kai.)
An rawaito kan falalar wannan sura cewa duk wanda ya dawwama yana karanta ta zai rayu a matsayin abin yabo da ƙauna a tsakanin mutane.
Sunanta Da Ayoyinta
Ana kiran wannan sura da Najmu, saboda surar ta fara da rantsuwa a ayarta (Na rantse da tauraro idan ya faɗi),[1] kuma ana kiranta da Wan Najmu[2] Ayoyinta 62 kalmomi 359 da haruffa 1432. ana la'akarinta cikin surorin Mufassalat ana nufin wannan sura tana ɗauke da ayoyi da yawa ƙadan kuma gajeriya ce.[3]
Tsarin Saukar Da Ita
Suratun Najmi an saukar da ita a Makka,[4] amma a jerin sauka ita ce ta ashirin da uku da ta sauka ga Annabi (S.A.W), amma a cikin Alƙur'ani ita ce ta 53 cikin juzi'i na 27 cikin surorin Alƙur'ani.[5]
Ma'anar Kalmominta
Ma'anar wasu kalmomi masu muhimmanci a wannan sura: (Annajmu Iza Hawa): Annajmu yana nufin tauraro, amma Kalmar Hawa tana nufin ya faɗi. (Zu Mirratin): mai ƙarfi (Fatadalla): zurowa da miƙewa daga sama zuwa ƙasa ko karkata zuwa ƙasa. Kamar yadda idan reshe ya zuro ƙasa, kamar yadda ake cewa (Tadallal Gusnu). (Sidratul Muntaha): Sidra tana nufin bishiyar magarya, amma abin da ake nufi anan shi ƙurewar matsayi da muƙami. (Allatu Wal Uzza Wa Manata): Allat sunan Gunki ne na ƙabilar Saƙif, amma Al'uzza shima Gunki ne na ƙabilar Gaɗafan, kazalika Manata sunan gunki ne na ƙabilar Huzail da Khuza'a. (Diza): Azzaluma marar adalci (Rabo na zalunci) (Allamam): Ƙananan zunubai waɗanda mutum baya dawwama a kansu. (Ashshi'ira): Tauraruwa mai haskawa ko wasu mutane da suke bautawa tauraruwa mai haske. (Al-Mu'utafikatu): Wannan kalma tana nufin ƙauyukan mutanen Luɗ wanɗanda Allah ya kifar da su. (Al-Aziffa): Ranar ƙiyama. (Samidun): daga Sumud ma'ana wasa (wanda suka shagalta da wasa).[6]
Abin Ciki
Ga abubuwan da wannan sura ta ƙunsa a taƙaice:
- Wannan sura bayan rantsuwa tana magana ne kan haƙiƙar wahayi da kore duk wani furucin son rai daga Annabi (S.A.W) baya faɗin komai face wahayin da ya sauka gare shi.
- Wannan sura tana magana kan Mi'irajin Manzon Allah (S.A.W) da wani ɓangarenshi cikin jumloli taƙaitattu kuma masu cike da ma'ana.
- Wannan sura tana magana kan camfe-camfen mushirikai kan abin da ya shafi gumaka da bautar Mala'iku da sauran abubuwa.
- Wannan sura tana magana kan abin da ya shafi tuba, da fatan samun gafarar Allah mai faɗi.
- Wannan sura tana bayyana mas'alar tashin Alƙiyama, da kafa hujja bayyananniya da misalin rayuwar duniya da cewa wannan dalili ne da yake nuna faruwa ranar alƙiyama.
- Wannan sura tana nuna abu mai muni da ya faru da al'ummun da suka gaba sakamakon ƙin gaskiyarsu kamar abin da ya faru ga mutanen Nuhu da Samudawa da Adawa da Mutanen Luɗ.
- Wannan sura tana ƙarƙarewa da yin umarni da sujjada ga Allah maɗaukaki da yin bauta gare shi, wataƙila wannan ita ce sura ta farko da aka saukar da sujjada ta wajibi a cikinta a garin Makka.[7]
Shahararrun Ayoyi
- Faɗar Allah maɗaukaki: (Baya magana da son zuciya* Ba wani abu bane face wahayi da ake yi masa),[8]
Ya zo a litattafan tafsiri cewa abun da ake nufi da Hawa shi ne san zuciya da bin abin da take so, lokacin da Annabi (S.A.W) ya kasance yana kiran Mushirikai zuwa ga addini ya karanta musu Alƙura'ani sai suka dinga jifanshi da cewa shi maƙaryaci ne da yake yi wa Allah ƙarya, sai wannan ayoyi suka sauka suna faɗar cewa babu wani abu da yake faɗa ko yake karantawa face wahayi da ake saukar mishi daga Allah matsarkaki,[9] ya zo a cikin Tafsir Nurus Saƙalaini daga Annabi (S.A.W) ya faɗawa Imam Ali (A.S) ya Ali na rantse da wanda ya aiko ni a matsayin Annabi cewa lalle wasiyya da halifanci da imamanci sun wajabta a gare ka bayana, sai munafukai suka ce, lalle Muhammad (S.A.W) ya ɓata da son ɗan baffansa, babu abin da yake faɗa game da shi sai son rai, saboda haka sai Allah ya saukar da wannan sura.[10]
- Faɗar Allah maɗaukaki: (San nan ya kusanto ya kuma matso).[11] Ya zo a cikin litattafan tafsiri cewa tababbas a sa'ad da Mala'ika Jibra'il ya bayyana ga Annabi Muhammad (S.A.W) kamar yadda Allah ya halicce shi, Kamar yadda Allah Ya halicce shi, jikinsa ya ɗaga sama zuwa sararin sama, sannan daga baya ya koma ga siffar da yake zuwa wajen Annabi da ita a lokacin da yake isar masa da wahayi, kuma ya kusanto shi har ba abin da ya rage tsakaninsu sai gwargwadon baka biyu, ko ma ƙasa da haka.[12]

- Faɗar Allah maɗaukaki: (Kuma mutum ba shi da komai face abin da ya yi ƙoƙari a kai),[13] Ya zo a cikin litattafan tafsiri, wannan aya tana faɗakar da mutum cewa ya dage da ya yi aiki tuƙuru kan abin da yake nema, kuma haka shi abin da ak
e buƙata mutum ya yi riƙo da shi a rayuwa koda bai kai ga burinshi ba a rayuwa, idan mutum ya yi niyyar alheri to Allah zai ba shi lada, saboda shi Allah yana karɓar niya bawai aiki kaɗai ba kawai.[14]
Falaloli Da Fa'idojin Wannan Sura
Akwai falaloli masu yawa da suka zo domin karanta wannan sura,
- An rawaito daga Annbai (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta Sutaun Najmi, Allah zai ba shi lada goma kwatankwacin waɗanda suka gasgata Muhammad (S.A.W) da waɗanda ba suyi imani da shi ba a Makka.[15]
- An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) duk wanda ya dawwama da karanta Suratun Najmi a kowace rana ko duk dare to zai rayu abin so a gun mutane.[16]
Wasu daga cikin abin da suka keɓanta da wannan sura An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk wanda ya rubuta wannan sura a fatar Damusa ya rataya ta a wuya, to zuciyarshi za ta yi ƙarfi wajan tinkarar kowane abu, kuma duk wani mai Mulki idan ya zo gunshi zai girmama shi.[17]
Bayanin kula
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 15, shafi na 218.
- ↑ Alusi, Ruhul Ma'ani, Juzu'i na 27, shafi na 63.
- ↑ Khurramshahi, Daneshname Qur'an Wa Qur'an Pajuhi, juzu'i na 2 shafi na 1253.
- ↑ Ɗusi, Tafsir At-Tibyan, juzu'i na 11, shafi na 23, Fakhrur Razi, At-Tafsirul Kabir, juzu'i na 28, shafi na 239.
- ↑ Ma'arifat, At-Tamhid Fi Ulumin Qur'an, juzu'i na 1, shafi na 168.
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 15, shafi na 219-245.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Amsal, juzu'i na 17, shafi na 128-129.
- ↑ Suratun Najmi: aya ta 3-4.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Tafsir Almizan, juzu'i na 19, shafi na 28.
- ↑ Huwaizi, Nurus Saƙlaini, juzu'i na 7, shafi na 162.
- ↑ Suratun Najmi: aya ta 8-9.
- ↑ Mugniyya, Tafsirul Kashif, juzu'i na 7, shafi na 174.
- ↑ Suratun Najmi: aya ta 39.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Amsal, juzu'i na 7, shafi na 166-167.
- ↑ Zamakshari, Tafsirul Kashshaf, juzu'i na 4, shafi na 1568.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami, juzu'i na 3, shafi na 447.
- ↑ Bahrani, Tafsirul Burhan, juzu'i na 9, shafi na 145.
Nassoshi
- Alusi, Mahmud Bin Abdullah, Ruhul Ma'ani fi Tafsiril Qur'anil Azim Was Sab'ul Masani, Beirut – Lebanon, Dar Ihya'il Turasil Arabi, bugu na 1, 1421H.
- Bahrani, Hashim Bin Sulaiman, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Beirut – Lebanon, Dar Ihya' al-Turath al-Arabi, bugu na 1, 1429H.
- Huwaizi, Abdul-Ali Bin Jum'a, Tafsir Nurus Saƙlaini, Beirut – Lebanon, Cibiayar At-Tarikh Al-Arabi, bugu na 1, ba tare da kwanan wata ba.
- Khurramshahi, Baha'ud-Din, Daneshname Qur'an Wa Qur'an Pajuhi, Iran – Tehran, Cibiyar Al-Asdiƙa, 1377Sh.
- Fakhrur Razi, Muhammad Bin Umar, At-Tafsirul Kabir, Beirut – Lebanon, Darul Kutubil Ilmiyya, bugu na 4, 1434H.
- Zamakhshari, Mahmud Bin Umar, Al-Kashshaf An Haƙa'iƙ Gawid Tanzil Wa Uyunul Aƙawil Fi Wujuhil Tawil, Beirut – Lebanon, Dar Sadir, bugu na 1, 1431H.
- Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husaini, Almizan Fi Tafsiril Qur'an, Qom – Iran, Dar Al-Mujtaba, bugu na 1, 1430H.
- Ɗabrisi, Fadlu Bin Hassan, Tafsir Jawami'il Jami', Qom – Iran, Cbiyar AnnashrulIslami ƙarƙashin Jama'atul Mudarrisin, bugu na 2, 1430H.
- Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, At-Tibyan Fi Tafsiril Qur'an, Qum – Iran, Mu'assasat al-Nashr al-Islami, bugu na 1, 1431H.
- Musawi, Abbas Bin Ali, Al-Wadihu Fit Tafsir, Beirut – Lebanon, Cibiyar Al-Ghadir, bugu na 1, 1433H.
- Ma'arifat, Muhammad Hadi, At-Tamhid Fi Ulumil Qur'an, Qom – Iran, Zawil Qurba, bugu na 1, 1428H.
- Mughniyyah, Muhammad Jawad, Tafsir al-Kashif, Beirut – Lebanon, Dar al-Anwar, bugu na 4, ba tare da kwanan wata ba.
- Makarim Shirazi, Nasir, Al-Amsal fi Tafsir Kitabillahil Munzal, Beirut – Lebanon, Cibiyar Al-Amira, bugu na 2, 1430H.