Daƙiƙa:Suratul Ahƙaf
Jasiya Suratul Ahƙaf Muhammad | |
| Lambar Sura | 46 |
|---|---|
| Juzu'i | 26 |
| Jerantuwa Ta Sauka | 66 |
| Adadin Ayoyi | 35 |
| Adadin Kalmomi | 648 |
| Adadin Haruffa | 2668 |
Suratul Ahƙaf sura ce ta 46 cikin juzi'i na 25 a Alƙur'ani, sura ce da ta sauka a Makka, an ciro sunanta daga aya ta 21 a cikin wannan sura, wannan sura tana gargaɗi ga mushirikai waɗanda suke inkarin da'awar imani da Allah da Manzonshi (S.A.W) da ranar tashin alƙiyama, kuma tana magana kan halakar mutanen Hudu da kuma magana kan halartar wasu aljanu inda ake karanta Alƙur'ani da sauraran Alƙur'ani mai girma da yin imani da shi, malaman tafsiri sun ce aya ta 15 ta sauka a game da Imam Husaini (A.S).
An rawaito ruwayoyi da yawa kan falalar karanta wannan sura, daga cikinsu an rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk wanda ya karanta wannan sura da dare ko a kowace Juma'a, Allah ba zai sanya ya fuskanci firgici a rayuwarshi ta duniya, kuma zai amintar da shi daga firgicin ranar alƙiyama.
Sunanta Da Ayoyinta
Ana kiran wannan sura da Ahƙaf, saboda faɗar Allah cikin aya ta 21 cewa: ( Kuma ka tuna da ɗan’uwan mutanen Ad, a lokacin da ya gargaɗi mutanensa a Ahƙaf)[1]Ahƙaf Jam'i ne na Hiƙfu, ance tana nufin tarin Yashi ne mai tsayi ko ƙasa wanda yake a karkace, wasu kuma sun ce kalmar tana nufin wani dutse ne a Sham, ko matsugunan da mutanen Yaman suke rayuwa tin daga Oman zuwa Hadramauti[2] ayoyinta 35 ne kalma 648 haruffa 2668[3] wannan sura tana cikin Hawamim, abin nufi surorin da suke farawa da Hamin.[4]
Tsarin Da Aka Saukar Da Ita
Suratul Ahƙaf tana cikin surorin Makka[5] amma a tsarin sauka ita sura 66 da ta sauka ga Annabi (S.A.W) amma a tsarin jerin surori a yanzu cikin surorin Alƙur'ani ita ce arba'in da shida.[6]
Ma'anonin Kalmominta
Ma'anuni masu muhimmanci na wasu kalmominta: (Iftarahu): Da'awa wani abu bisa ƙarya. ِ(Ifku): Ƙarya ko kawar da abu daga yadda yake. (Balaga ashuddahu): Isa zuwa ga ƙololuwar abu daga ƙarfinshi da hankali. (Ahƙaf): Gurare ne a Yaman inda ƙabilar Ad suka kasance suna rayuwa. (Ulul Azmi): Masu azama, ita kuma azama ita ce ƙoƙari da dagewa da haƙuri da tabbata.[7]
Abun Ciki
Wannan sura a taƙaice ta ƙunshi gargaɗi ga Mushirikai wanɗa suke inkarin kira ga yin imani da Allah da Manzon Allah, da alƙiyama da sakamakon wannan inkari daga azaba mai raɗaɗi. Kazalika a wannan sura akwai cika hujja kan kaɗaitar Allah da annabta, kuma wannan sura tana nuni kan halakar mutanen Hudu, da halakar mutuanen ƙauyukan Makka, da labarin wani gungun aljannu da suka je gun Annabi (S.A.W) domin saurarar Alƙur'ani da yin Imani da shi, da labarin komawar waɗannan aljannu gun mutanansu suna masu faɗakarwa.[8]
Asbabun Nuzul Aya Ta 15 Game da Imam Husain (A.S)
Ya zo cikin litattafan tafsiri daga Imam Sadiƙ (A.S) ya ce ya yin da Faɗima (S) ta ɗauki cikin Imam Husaini (A.S) Mala'ika Jibra'il ya je gurin Ma'aikin Allah, ya ce haƙiƙa Faɗima (S) za ta haifi wani yaro wanda al'ummarka za ta kashe shi bayanka, hakan ta sa Faɗima (S) ba ta ji daɗin ɗaukan cikinshi ba, kazalika sanda ta haife shi ba ta ji daɗi ba, sai Imam ya ce banga wata uwa a duniya ba da za ta haifi ɗanta kuma ta ji ba ta sonshi ba, Sai dai cewa ta ji rashin daɗi ne saboda ta ji cewa za a kashe shi. Kuma a kanshi ne wannan aya ta sauka, (Kuma mun yi wasiyya ga mutum da ya kyautata wa iyayensa, Mahaifiyarsa da ɗauki cikinsa cikin wahala, kuma ta haife shi cikin wahala.[10][11]
Falala Da Fa'idoji
Akwai falaloli da yawa wajan karanta wannan sura:
- An rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanata Suratul Ahƙaf za a rubuta mishi lada goma kwatankwacin yashin da yake duniya.[12]
- An rawaito ga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk wanda ya karanta wannan sura da dare ko a kowace Juma'a, Allah ba zai sanya ya fuskanci firgici a rayuwarshi ta duniya, kuma zai amintar da shi daga firgicin ranar alƙiyama.[13]
Akwai abubuwa da yawa da suka keɓanta da wannan sura:
- An rawito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa duk wanda ya rubuta wannan sura, ya ratay ata a wuyan yaro ko ya rubutata ya wanke ya ba shi ya sha, to zai zamo mai ƙarfin jiki da lafiya daga duk wani abin da yake samun yara, kuma zai zamo abin so tin yana cikin zanin goyo.[14]
Bayanin kula
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fi Tafsir, juzu'i na 14, shafi na 389.
- ↑ Alusi, Ruhul Ma'ani, juzu'i na 26, shafi na 251.
- ↑ Khurramshahi, Mausu'at Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, juzu'i na 2 shafi na 1251.
- ↑ Ma'arifat, At-Tamhid, juzu'i na 1, shafi na 313.
- ↑ Ɗusi, Tafsir At-tibyan, juzu'i na 10, shafi na 496; Razi, At-Tafsirul Kabir, juzu'i na 28, shafi na 3.
- ↑ Ma'arifat, At-Tamhid, juzu'i na 1, shafi na 169.
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 14, shafi na 396-426.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 18, shafi na 189.
- ↑ Khamagar, Sakhtare Surahaye Qur'an Karim.
- ↑ Suratul Ahƙaf: aya ta 15.
- ↑ Ƙummi, Tafsirul Ƙummi, juzu'i na 3, shafi na 969: Huwaizi, Nurus Saƙlaini, juzu'i na 7, shafi na 10-11.
- ↑ Zamakhshari, Tafsirul Kashshaf, juzu'i na 4, shafi na 1496.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami, juzu'i na 3, shafi na 343.
- ↑ Bahrani, Tafsirul Burhan, juzu'i na 9, shafi na 27.
Nassoshi
- Alusi, Mahmud Bin Abdillah, Ruhul Ma'ani fi Tafsiril Qur'anil Azim was Sab'ul al-Masani, Beirut – Lebanon, Dar Ihya'il Turasil Arabi, bugu na 1, 1421H.
- Bahrani, Hashim Bin Sulaiman, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Beirut – Lebanon, Dar Ihya'il Turasil Arabi, bugu na 1, 1429H.
- Huwaizi, Abdul-Ali Bin Jum'ah, Tafsir Nuris Saƙalain, Beirut – Lebanon, Cibiyar al-Tarikh al-Arabi, bugu na 1, ba tare da kwanan wata ba.
- Khurramshahi, Baha' al-Din, Mausu'at Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, Iran – Tehran, Cibiyar Al-Asdiƙa, 1377Sh.
- Ma'arifat, Muhammad Hadi, At-Tamhid fi Ulumil Qur'an, Qum – Iran, Zawil Qurba, bugu na 1, 1428H.
- Musawi, Abbas bn Ali, Al-Wadihu Fi Tafsir, Beirut – Lebanon, Cibiyar al-Ghadir, bugu na 1, 2012.
- Razi, Muhammad Bin Umar, At-Tafsirul Kabir, Beirut – Lebanon, Dar al-Kutub al-'Ilmiyya, bugu na 4, 1434H.
- Zamakhshari, Mahmud Bin Umar, Al-Kashshaf, Beirut – Lebanon, Dar Sadir, bugu na 1, 1431H.
- Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husain, Almizan fi Tafsiril Qur'an, Qum – Iran, Dar Al-Mujtaba, bugu na 1, 1430H.
- Ɗabrisi, Fadlu Bin Hassan, Tafsir Jawami'il Jami', Qum – Iran, Cibiyar Annashrul Islami, na Jama'atul Mudarrisin, bugu na 2, 1430H.
- Ɗusi, Muhammad bn al-Hasan, At-Tibyan fi Tafsiril Qur'an, Qum – Iran, Cibiyar Annashrul Islami, bugu na 1, 1431H.
- Ƙummi, Ali bn Ibrahim, Tafsirul Ƙummi, Qum – Iran, Cibiyar al-Imam al-Mahadi, bugu na 1, 1438H.
- Qur'an Karim.
- Khamagar, Muhammad, Sakhtare Surahaye Qur'an Karim, Cibiyar Farhangiyye Qur'an wa Itrate Nurus Saƙalain, Qom, Mawallafar Nashra, bugu na 1, 1392Sh.