Jump to content

Daƙiƙa:Sayyid Muhammad Tijjani

Daga wikishia
Sayyid Muhammad Tijjani
Cikakken SunaSayyid Muhammad Tijjani Samawi
Tarihin haihuwa1936M
MahaifaBirnin Ƙafsa a kudancin Tunisiya
Wurin karatuTunisiya • Faransa (Jami'ar Sorbonne da Cibiyar Babbar Ilimi ta Paris).
Wallafe-wallafeFassarar Nahjul Balaga zuwa harshen Faransanci • Summah TadaituKullu al-Hulul Inda Alir-RasulAsh-Shi’a Hum Ahlus-SunnaLi Akuna Ma'as SadiƙinFas'alu Ahlaz ZikriƊariƙun NajatFasiru fil-Ardi Fanzuru
Sauran abubuwaNazarin kwatance tsakanin addinai• Karatu a fannin falsafa da ilimin ɗan Adam• Digirin digirgir na ƙasa da ƙasa a fannin ƙwarewa na tarihi da mazhabobin Musulunci• Koyarwa a Cibiyar Balzam ta Paris.


Sayyid Muhammad Tijjani Samawi, (an haife shi a shekara ta 1936M), malamin addini ne ɗan ƙasar Tunisiya, wanda ya sauya mazhabarsa daga Ahlus-Sunna zuwa Shi'anci. Da farko Tijjani yana bin mazhabar Malikiyya. Bayan ya yi tafiya zuwa Saudiyya, ya karkata zuwa Wahabiyanci, kuma ya fara yaɗa aƙidun Wahabiyawa. Sai dai bayan wata tafiya zuwa Najaf da kuma tattaunawa da malaman Shi'a, ya zaɓi bin mazhabar Shi'a.

Bayan ya karɓi mazhabar Shi'a, ya rubuta littattafai domin kare wannan mazhaba. Daga cikinsu akwai littafin Summah Tadaitu (A lokacin ne na samu shiriya), wanda a cikinsa ya ba da labarin yadda ya koma Shi'a da kuma ganawarsa da malaman Shi'a. Komawar Tijjani zuwa Shi'a ta jawo mummunar martani daga Wahabiyawa. Wasu daga cikinsu sun bayyana ayyukansa a matsayin ƙirƙira, kuma suka kira shi matsayin wanda ya yi ridda.

A cewar Tijjani, littattafan Al-Muraja'at da An-Nassu wal Ijtihad, waɗanda Sharafud-Din ya rubuta, da kuma ayyukan Sayyid Muhammad Baƙir Sadar, daga cikin malaman Shi'a masu matsayin maraji'an taƙlidi, su ne suka fi yin tasiri wajen sauyawar mazhabarsa zuwa Shi'a.

Haihuwa Da Karatu

Muhammad Tijjani Samawi ya haife shi a shekara ta 1936M a birnin Ƙafsa da ke kudancin Tunisiya.[1] A cewarsa, asalinsu daga garin Samawa ne da ke Iraƙi, kuma a zamanin Abbasiyawa ne kakanninsa suka yi hijira zuwa Arewacin Afirka.[2]

Ya yi karatun farko na tsawon shekaru biyu ko uku a Jami'ar Zaituna da ke Tunisiya. Bayan samun ƴancin kan Tunisiya, ya ci gaba da karatu a makarantun Faransa da Larabci (Franco-Arab). Daga baya ya fara koyarwa, inda ya yi aikin koyarwa na kimanin shekaru 17. A cewarsa, asalinsu daga garin Samawa ne da ke Iraƙi, kuma a zamanin Abbasiyawa ne kakanninsa suka yi hijira zuwa Arewacin Afirka.[3]

Daga baya Tijjani ya tafi Faransa domin ci gaba da karatu. Ya shafe fiye da shekaru takwas a Jami'ar Sorbonne da kuma Cibiyar Manyan Karatu ta Paris, inda ya yi nazarin kwatanta addinai, musamman addinan tauhidi. Bayan ya samu digirin farko a fannin bincike na musamman a wannan batu, ya kammala karatunsa a Jami'ar Sorbonne. Daga nan ya samu digirin digirgir na ƙasa da ƙasa a fannin Falsafa da Kimiyyar Bil'adama, sannan ya kware a fannin Tarihi da Mazhabobin Musulunci. Taken kundin digirgir ɗinsa shi ne Tunanin Musulunci a cikin Nahjul-Balagha. Ya kuma fassara Nahjul-Balagha zuwa harshen Faransanci. Bayan ya samu digirgir, ya koyar na shekara guda a Jami'ar Sorbonne, sannan ya koyar na tsawon shekaru uku a Cibiyar Balzam da ke Paris. A cewarsa, asalinsu daga garin Samawa ne da ke Iraƙi, kuma a zamanin Abbasiyawa ne kakanninsa suka yi hijira zuwa Arewacin Afirka.[4]

A lokacin ƙuruciyarsa, Tijjani ya haddace rabin Alƙur'ani. Saboda haka, a cikin watan Ramadan, yana shiga cikin jagorancin sallar Tarawihi a matsayin limamin jam'i.[5] A cewarsa, sunan Tijjani ya samo asali ne daga Ɗariƙar Tijjaniyya, wadda ta shahara a Tunisiya, Maroko, Aljeriya, Libya, Sudan, Masar da sauran ƙasashe. Masu wannan ɗariƙa sun yi imanin cewa dukkan shehunan ɗariƙa da waliyyan Allah sun samu iliminsu daga juna, ban da Shaik Ahmad Tijjani, wanda ya samu iliminsa kai tsaye daga Annabi Muhammad (S.A.W).[6]

Zaɓar Mazhabar Shi'a

Ganawar Tijjani Samawi tare da Sayyid Muhammad Baƙir Sadar

Tijjani mabiyin mazhabar Malikiyya ne. [7] A shekara ta 1964M, ya halarci wani taro a Makka da ya shafi Larabawa Musulmi. A wannan tafiya ne ya karkata zuwa Wahabiyanci, sannan ya fara yaɗa aƙidun Wahabiyawa.[8]

A wata tafiyarsa zuwa Beirut, Tijjani ya haɗu da wani malamin Shi'a na Jami'ar Bagdad mai suna Mun'im. A tattaunawarsu, Tijjani ya zargi Shi'awa da kafirci da shirka; sai dai Mun'im ya gayyace shi zuwa Iraƙi domin ya san mazhabar Shi'a sosai.[9]

Tijjani ya amince da gayyatar Mun'im, kuma a tafiyarsa zuwa Iraƙi ya ziyarci Haramin Imam Ali (A.S), Haramin Kazimaini, da kabarin Shaik Abdul-Ƙadir Gilani, sannan ya gana da wasu malaman Shi'a.[10] Ganawarsa da Ayatullah Khuyi da Sayyid Muhammad Baƙir Sadar, daga cikin malaman Shi'a kuma maraji'an taƙlidi, ta sa aka gyara wasu daga cikin ra'ayoyinsa game da Shi'awa.[11]

Ya bayyana irin tasirin malaman Shi'a, musamman Sayyid Muhammad Baƙir Sadar, a kansa. A cikin littafinsa Summah Tadaitu, ya kawo waɗannan ganawa, tambayoyin da aka yi da kuma amsoshin Ayatullah Sadar.[12]

Bayan waɗannan ganawa, ya fara yin bincike domin ya kai ga gaskiya. Ya bayyana cewa ya yi wa kansa alƙawarin cewa zai dogara da ingantattun hadisai waɗanda Shi'a da Ahlus-Sunna suka yarda da su a matsayin hujja tabbatacciya, sannan ya bar hadisai waɗanda wata mazhaba ɗaya ce kawai ta dogara da su.[13] Daga nan Tijjani ya zurfafa nazari kan aƙidun Shi'a. Daga cikin muhimman littattafan da suka yi tasiri a kansa akwai Al-Muraja'at da An-Nassu Wal Ijtihad, waɗanda Sayyid Abdul-Husaini Sharafud-Din ya rubuta.[14]

Wallafe-wallafe

Bayan Tijjani ya zama Shi'a, ya rubuta littattafai domin tabbatar da gaskiyar mazhabar Shi'a da kuma mayar da martani ga ra'ayoyin Ahlus-Sunna, daga cikinsu akwai: Summah Tadaitu, Kullu al-Hulul Inda Alir-Rasul, Ash-Shi’a Hum Ahlus-Sunna, Li Akuna Ma'as Sadiƙin, Fas'alu Ahlaz Zikri, Ɗariƙun Najat da Fasiru fil-Ardi Fanzuru.[15]

A cikin littafinsa " Summah Tadaitu", ya rubuta labarin sauya mazhabarsa daga Ahlus-Sunna zuwa Shi'a. A cikin littafin, tare da ba da tarihin rayuwarsa, ya ba da labarin tafiyarsa zuwa Iraƙi da tattaunawar da ya yi da malaman Shi'a. A wannan littafin, ya dogara da hadisai na Ahlus-Sunna wajen kare aƙidun mazhabar Shi'a. An fassara littafin zuwa harsuna 14, kuma an buga shi sau da dama a Iran. Fassarar Farisancinsa ana kiranta "Angahi Hidayat Shodam".

Littafin Cekide Andisha kuwa wani taƙaitaccen bayani ne na littattafai shida na Tijjani, wanda Husaini Gaffari Sarawi ya tattara.[16] Martanin da aka yi

Tijjani ya bayyana a wata hira cewa, bayan ya koma mazhabar Shi'a, ya fuskanci martani mai tsanani daga Wahabiyawa da ƴan Saudiyya. A cewarsa, da farko sun musanta samuwar wani mutum mai suna Tijjani da ya zama Shi'a gaba ɗaya. Daga baya suka yi iƙirarin cewa littafin Summah Tadaitu aikin Isra'ilawa ne. Wasu daga cikinsu kuma suka ce shi ba Shi'a ba ne, ba kuma Ahlus-Sunna ba ne; a maimakon haka, ya zama cikin wanda suka yi ridda (murtaddi).[17]

Bayanin kula

  1. «زندگینامه سید محمد تیجانی», Shafin Cibiyar Duniya ta Mustabṣira
  2. «مشروح مصاحبه فارس با علامه تیجانی سماوی», Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Fars
  3. «مشروح مصاحبه فارس با علامه تیجانی سماوی», Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Fars
  4. «مشروح مصاحبه فارس با علامه تیجانی سماوی», Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Fars
  5. Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 11–12.
  6. Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 12-`13.
  7. Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 28–29.
  8. Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 16–17.
  9. Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 29–31.
  10. Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 45–46.
  11. Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 49.
  12. Ku duba: Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 53–60.
  13. Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 76.
  14. Ku duba: Tijjani, Summa Ihtadeytu, Manshurat Madinatul-Ilmi, shafi na 75.
  15. «مجموعه کتاب‌های دکتر محمد تیجانی», Shafin Tibyan
  16. «چکیده اندیشه‌ها», Shafin Gidauniyar Muhaƙƙiƙ Ɗabaɗaba'i,
  17. «مشروح مصاحبه فارس با علامه تیجانی سماوی»Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Fars

Nassoshi